AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   22 / 103

63K to 66K   out of 306.8K words

mata da suka goge. Kinga kuwa dole duk wacce zata je matsayin matarsa ta wanku da kyau ta kuma k ara samun gogewa gudun kar a samu matsala dukda ko a haka aka kai masa Ummul na tabbata baza a samu matsala ba amma kinsan ance idan kanada kyau ka k ara da wanka. Kinsan sha anin d an yau. Ta d an gyara tsayuwarta  Sann zamanta a can gidan naku wani tsautsayin na kuma giftawa Wanda bazamuyi fata ba. Kinga Har kawo wann lokacin kishiyar ki batasan abinda ake shiryawa ba.

Umma tai karaf tace  Ai Kinga wann  yaruwar tata da ta fice ko bala inta kad ai Ya isa ya iya jawo wani matsalan tinda kinga a nan take ce mata su gudu. Toh kafin ta koma can na shafa cikin dare naji sun gudu gwara ta zauna a nan asiri na a rufe a kula da ita idon masu ido bai ganta bakin masu baki bai tofa ba.

Asshe ta jinjina kai  Cikin kwanaki k alilan komai zai kammala da yardar Ubangiji Ummul d inki ta shige d akin aurenta mafarkin ki ya zama gaskiya.

Umma sai ta fara hawayen farin ciki tana fad in shikenan burinta yana gab da cika. Allah zai cika mata wann buri nata daga k arshe.

Asshe ta girgiza kai kafin ta fice ta bawa Umma waje tai mai isarta.

A haka Ummul ta k araso ta tadda Umma wacce itama hawaye ne kwance saman fuskarta.

Ta k urawa mahaifiyarta ido. Sai kuma tasa bayan hannunta ta share hawayen dan taji kaf tattaunawar da su Umma sukai.

 Alfarma d aya zan rok eki Umma. Ta fad i cikin rawar murya.

Umma ta dubeta wann karon hawaye ne saman k uncinta.

Ummul taci gaba  Ki kaini wajen Abba na gansa nai masa Sallama kafin ku killaceni a wann gidan.

Umma ta jinina mata kai tana sakin murmushi ta kamo hannayen Ummulkhairi  Zamuje Ummul. Zamuje kiga mahaifinki. Sann zan baki labarin duk abubuwan da suka faru dalla dalla tin daga lokacin da Tani ta fatattake ni naje na nemo kud ad den jinyar mahaifinku.

Bayan Umma ta labarta komai dangane da had uwarsu da Asshe da irin duk wani taimako da Asshe Tai mata. Da buk atan Asshen na nema ma d ansu aurenta. Jinina kai Ummul tai ba tareda tace komai ba dan kalamai sun k are saman harshenta. Abinda yai mata saura hawaye ne Wanda suma d in batada tabbaci idan basu kusan k arewa ba.

Driver ne ya d aukesu Ya kaisu Har asibiti wajen Abba.

Mama dake zaune a haraba tana hangosu ta mik e cikin sauri ta nemi wajen b oyo ta b uya yayinda Ummul da Umma suka shige d akin.

Umma ta dubi Ummulkhairy tace  Zan barki ki gana da mahaifinki Ummul. Ku biyu.

Ummul ta jinjina mata mai tana goge hawayen da suka kwararo mata.

"Ummul zaune gaban gadon mahaifinsu Wanda idanunsa ke lumshe, ta saka bayan hannunta ta share hawayen da suka gangaro mata, abubuwan da suke faruwa da ahalinsu sai gifta mata suke a k wayar idanu. Ta d aura hannunta guda saman na Abba. Cikin rawar murya take furta  Abba tinda ka kwanta komai bai k ara daidaita ba.. Umma ta canza Abba.. Sai kuma tai shiru tana share hawayenta  Abba koda bana nan& Ban sani ba ko zamu sake had uwa ba ko bazamu sake had uwa ba. Abba ka yafe wa mahaifiyata a bayana. Dan Allah ka yafe ma Umma.! Kuka ya hanta ci gaba da magana."

Da k yar kukan nata Ya tsagaita kafin taci gaba  Abba bazanso wani wanda ba kai ba ya aurar dani. Watak ila Umma ta hana maka wann damar ne domin ceto naka rayuwar.

Muryarta yaci gaba da rawa  Abba banida wani zab i.. Rayuwarka na kan gab a a nan.. Watak ila wann shine maslahan ahalinmu. Watak ila komai zaizo k arshe. Watak ila ni ce matsalar. Watak ila idan nayi nesa daku zaman lafiya da kwanciyar hankali zai wanzu tsakanin ahalin. Abba zanyi duk wata sadaukarwa sabida ahalina. Ka yafe mun Abba. Kuma ka yafe wa mahaifiyata . Ta k arashe tana mai kifa kanta gefen Abba hawaye na kuma kwararo mata.

Mama dake lab e bayan window ta waje taji duk abinda Ummul tace. Wato Suwaiba ta shirya aurar da Ummulkhairi ne a sirrance..? Shin wann shine dalilin canzawan Suwaiba..? Aiko idan haka ne sai taga ta yanda za ayi wann aure.. Idan Suwaiba tasan wata bata San wata ba. Toh amma ta ya zata b ata auren tinda Suwaiba bata nuna masu mijin Ummul d in ba.? Kar dai Suwaiba ta samo attajiri ne ma Ummul d inta.. Idan har al amra sukaci gaba da tafiya a haka kenan fah Suwaiba zata zamto sarauniya a gidan. Sai abinda tace. Harta  ya yan cikinta su Azeema sai Sun gagareta. Tin yanzu ma komai ya canza balle abubuwa suci gaba da tafiya a haka.. Uwa uba Har kawo wann lokacin basu saka Tasi u a idonsu ba... Dawowan Suwaiba dik shi ya karkata masu hankali ta kasa aiwatar da komai gameda b cewan Tasi u. Toh inaga Abubuwa sunci gaba da tafiya a haka.? Yanzu ita fah zata tashi a tutan babu kenan ga Suwaiba ta dawo da sabon sauyi..

Mama ta koma gefe saman benci ta zauna had ida buga uban tagumi. Kallo d aya zaka mata ka fahimci duniyar tai mata atishawan tsaki. Sai faman sauk e tagwayen ajiyan zuciya take tana canza salon tagumin ta. Babu babban abinda ya bata takaici kaman da ya kasance yanzu dik abinda suke ci daga wajen Suwaiba ya fito.. Shikenan Suwaiba fah ta amshe girman nata. Abinda yai saura kawai shine Suwaiba ta umarceta ta soma kiranta da Yaya.

Saiga Mama na hawaye tana fad in har abada bazata bari Suwaiba tai nasara akanta ba. Idan abinda zata aiwatar k arshe shine hana yuwan auren Ummulkhairi ta shirya yi. Da dai ta bari Suwaiba tai galaba akanta gwara tai komai dan nasara nata ne da yaranta ba na Suwaiba da nata  ya yan ba. Da wann tunani ta mik e tagajan magajan domin kaw zama bai ganta ba.

*

Kan Ummul na kife gefen mahaifinta tana ci gaba da cazgan kuka mai ban taisayi.

Umma ta k araso ta dafata.

Ummul batace komai ba Har Umma ta ta k araso wajen.

" Tashi kije Ummul direba yana jiranki. Ki sani bazan bari ki koma gidan mahaifinki ba har sai ranan Aure gudun kar wani abu ya gifta. Kindai san matsalarki da abubuwan da mukaita fuskanta a baya na fashe fashen Aurenki. Wann karon ban shirya ba ma wani k ofa ya lalata Aurenki ba. Naga Tani bata nan a nan, zan zauna wajen Abbanku Har Tani ta dawo. kuma zan karanto masa komai koda bazai bud e idonsa ba na tabbata kunnuwansa da zuciyarsa zasu saurareni. "

Ta murmusa tana duban Ummul  Na tabbata a yau mahaifinki ya farka ya ganki a d akin Aurenki zaifi kowa farin ciki sann wann kad ai Ya isa ya zama silan yaye damuwar dake k unshe cikin zuciyarsa.

Dubanta kurum Ummul Tai ba tareda ta iya cewa komai ba. Har yanzu dai a idon Umma itace matsalar ahalinsu da k addararta.

Ta kuma juyowa ta dubi Abba hawaye suka kuma gangaro mata. A hankali ta isa ta tofa masa addu o i kafin tasa kai ta fice jiki a mace.

**

Abuja..

Zaune suke gaba d aya a nan lambun dake farfajiyan gidan. Mommy Daddy harma da Anisa.

Mommy dai bata sama bata k asa gaba d aya kana ganinta zaka hango tsantsan farin cikin da take ciki.

Ta dubi Anisa tace maza ta sami one of the mades su shirya wajen cin abincin mutum guda.

Daddy ya dubeta  Are you expecting someone.?

Mik ewar da Anisa zatai ta hango shi ya nufo garden d in. Looking handsome as always. Zuciyarta yai wani irin yankewa.

"Mommy ta fad ad a murmushinta tana nuni da Haidar dake k arasowa  Oh! He s here already. Ta maido da dubanta ga mijinta  Ya kamata mu rinka samun lokaci irin haka na musamman domin ahali. After all, amarya za a kawo mana very soon. "

Baice komai ba yaci gaba da abinda yake. Dan yanzu ya kula Kwaise batada zance sai na auren D anta.

Haidar ya k araso Mommy na masa sannu da zuwa. Sai nan nan dashi take. Wani sabon kula da soyayya take nuna masa abinda bata masa a baya ba. Kaman tayi ma wofi haka ya d auki abun tinda yasan ba dan Allah take ba.

Koda Anisa ta kawo plate karb a Mommy tai tana k ok arin serving d insa sai haba haba dashi take tana tambayarsa me za a zuba masa.

"Cikeda k osawa Haidar Ya rik e hannunta Ya amshi plate d in  Mommy please that s enough, I can do it myself. I ve been doing it since childhood. "

"Jikinta ya d anyi sanyi ta soma Tina ita dai tin tasowarsa tin yarinta bata tab a tambayarsa yunwan cikinsa ko lafiyarsa ba. Masu aiki da Nannies Sune suka San lafiyarsa, cinsa ko shan sa. Har yayi ciwo ya gama bata san yayi ba kuma ba matsalar ta bane. The only abu da take tambaya ta kuma tada hankali akai shine karatunsa na boko da sakamakon da zai birge mahaifinsa. Idan kuwa bai kawo sakamakon da zai birge mahaifinsa ba ranan zai wuni ne a d aki mai duhu kuma a kulle cikin tsananin horo."

Mommy ta gyara zama ganin table d in Ya b ata shiru sai sautin cutlery dake tashi cikin plates.

Ta d an murmusa tana duban Haidar  Ya labarin aiki.. Ina nufin sabon project d in naku.. Kun fara ne.?

"Yasan so take tai creating hiran da zai had asa magana da mahaifinsa. Ya d an girgiza kai kad an  Still ironing out the details.. Ya d ago yana dubanta sosai tinda yasan tasan komai  In a couple of months, Mommy. Let s say two to three months. "

K arasowar wata mai aiki rik eda k aton frame a rufe Ya katse Mommy. Mai aikin ta k araso cikeda ladabi ta tsaya nan bayan Mommy rik eda frame d in tana sanar da ita security ne Ya shigo dashi.

Mommy ta jinjina Kai tana mai nuna mata yanda zata ajiye.

Ta maidoda dubanta ga Ahalinta tana kuma fad ad a murmushinta  Na had a mana wann cin abincin ne a tare domin na gabatar mana da wani mihimmin abu. Musamman gareka Haidar. Ta k arashe tana mai isa jikin frame d in.

Ta shiga bud ewa sannu a hankali tana mai furta  Kyakkyawar Amaryar mu. Matar D anmu Haidar. Sirkarmu wacce zata zamto silan dunk ulewar ahalinmu.

Cak ya tsaya da abinda yake. Lokaci guda yana mai matse fork and knife dake rik e cikin hannunsa. Bai iya janye idanunsa daga saman plate d in ba haka nan bai dubi hoton da mommy ke nuna masa ba wacce ta ambaceta da matarsa.

Girgiza kai Daddy yai yana tunanin matarsa ta zauce da wann auren da take yunk urin yima d ansu. Ya d auki tissue had ida goge bakinsa. Ya dubi Mommy kafin yace  Are you in your right state of mind. What s the meaning of this Kwaise.?

"Mommy tace  Gani ya kori ji Engr. Matar Haidar ce. Idan ba a hoto ba nasan bazaije ya ganta ba har sai Randa aka kawo mana ita gidan. So kafin a kawota yak i amincewa yace gaibu na auro masa. Gwara na samu dalilin kafa hujja. Look kalla kaga, zasu dace da Haidar.. Asshe ta iya zab e. Ta k arashe sai duban hoton take tana murmushi."

Daddy dai kallon wacce ta samu matsala yake mata. Lokaci guda ya girgiza Kansa  I m done here. Yai maganar yana mai barin wajen.

Zuciyar Anisa yaci gaba da bugawa tana mai duban hoton. Cewa da Mommy tai Asshe ta iya zab e shine keta yawo cikin kumnuwanta. Mai kenan hakan ke nufi.? Amminta ce ta zab o wa Haidar mata.? Mahaifiyarta ta turota gidan ne dan taci amanarta ta nema ma Haidar auren wata daban a garin Kano.? Ko kuwa mai Ammi take nufi da ita.?

SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!*

*18*

*©þSameena Aleeyou& *

"Haidar ya k arisa gaban mahaifiyarsa yana mata duban mamaki. Ya jinjina Kansa kad an har lokacin dubanta yake  Had I known, akan wann abun kika kirawoni nan. I wouldn t have wasted my time coming here. Yai maganar yana nuni da hoton Wanda ko kalla baiba. Daga haka sa Kai yai zai shige amma sai yaji kaman Wanda aka ce ya juya ya dubi hoton."

Bazai iya ce ga kamanninta ba ko wani abu mai Kama da wann. The only thing he noticed cikin hoton shine k wayar idanunta masu cikeda rauni ga kwantattun hawaye ciki. Yanda kasan magen dake cikeda tsoro. Ya janye idanunsa ba tareda ya kuma ceda Mommy komai ba yasa kai ya fice.

Mommy tai saurin bin bayansa cikin k ok arin dakatar dashi.

"Anisa kaw kasa janye idanu tai daga barin duban hoton. Ita wann d in wacece.? A ina Amminta ta samota.? Maiyasa Mommy ke yunk rin had a aurensu da Haidar Dikda cewa Haidar d in baya so. Cikin azama ta mik e tana Jin kuka na zuwa mata. Ta gaji ta gama zaman gidan, bazata zauna a kawo wata cikin gidan da sunan matar Haidar ba. Gwara ta tafi ta koma gida dik abinda Ammi zata k ulla ta k ulla Akan idonta dan tayi imani bazata bari wann auren ya tabbata ba. Idan ma anyi it won t last long. She promised. Table knife d in dake hannunta ta jefa jikin hoton Ummul Ya kuwa samu daidai tsakiyar fuskar hoton. Sai sakin huci take ta mik e ta shige cikin gida kaman zata fashe."

Tana shiga ta soma kiran layin mahaifiyarta. A zuciya take had a kayanta cikin suitcases. Ammi tana d agawa Anisa taci gaba  Wow congratulations Ammi. Aikinki yana kyau. So wann shine dalilinki na turo ni gidan nan..? Ki nemar wa Haidar auren wata can garin Kano.. Wato baki so na zame Miki matsala cikin abinda kike shiryawa shisa kika tarkaso ni kika turo ni nan..? Ta jinjina Kai tana mai ci gaba da huci  Ammi I thought plan d in shine nazo nan dan na Sami kusance da Haidar da kuma ahalinsa.? But what did you do Ammi.. You sent me here for you to carry out

whatsoever your plan might be. Zan dawo gobe goben nan.. Zan dawo garin Kano. Kuma ina mai tabbatar Miki na shirya b ata dik wani shirinki Ammi. Ta k arashe cikin huci.

Daga d aya b angaren Asshe ta katseta  Idan ke shashasha ce ki dawo Anisa. Abinda baki sani ba shine wann auren da kikaga na dage ina nemar ma Haidar ba ji ba gani ma ke nake Anisa.

Baki sake Anisa ta girgiza Kai  Wane irin ma ni kike Ammi bayan gashi na gani da idona kin turo picture d in yarinyar da kike nemar ma Haidar Aurenta. C mon Ammi mai kike nufi.?

Asshe ta murmusa kad an  Bazaki fahimci komai ba sai nan gaba kad an Anisa. Amma wann auren kaman fansar Haidar nake nemar Miki dashi. Idan har ba ayi wann auren ba bazaki tab a iya samun Haidar ba Anisa. Har abada.

Anisa ta girgiza kai cikin rashin fahimta  Ammi auren da kike nemar ma Haidar fansa kaman ya.? Ammi mai hakan yake nufi.? Ni fah ban fahimci komai ba.

Asshe ta kuma jinjina Kai  Bazaki fahimci komai a halin yanzu ba Anisa. Amma nan gaba kad an zaki gane duk abubuwan da nake fad a miki. Idan har kina so Haidar ya zama naki sai kin bada goyon baya d ari bisa d ari ma wann auren. Ki bawa Aunt d inki k warin gwiwa akan auren d ari bisa d ari. Idan har kina son D anta sai kinso wann auren Anisa. Ke idan an kawo matar ma ki shiga jikinta sosai ki tabbata ta samu kusanci da Haidar.

 Ammi kin kuwa ji abinda kike fad i. Ammi how can I possibly do that.? Maganar mutumin da nake so the most fah ake a nan. Ta ya zan so ya samu kusanci da wata bani ba.?

"Asshe ta murmusa kad an  Ni mahaifiyarki ce, kuma nafi kowa so ki kasance cikin farin ciki Anisa dan haka kiyi abinda nace idan har da gaske kina sonsa. Nan bada jimawa ba zai zama naki. Amma fah sai kin tabbata wann auren nasa ya yuwu. "

Anisa ta girgiza Kai kad an  Ammi wai meyasa dole sai anyi auren. Can t he just marry me instead.?

 Ke bana son shashanci kika auresa yanzu kashe kanki zakiyi.. Na fad a Miki Fansar Miki shi zanyi da wann auren wai meyasa mik ewa shashanci ne.?!

Da mamaki Anisa tace  Kashe kaina kuma Ammi dan na auresa.?

"Asshe Jin ta kusan

22 / 103