AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   73 / 103

216K to 219K   out of 306.8K words

magana.

Rintse idonta Tai ta toshe kunnuwarta sai ta fashe da kuka sosai  Bana so.. Bana so na saurari komai daga gareka..! Kawai ka bud e mun k ofa ni na fice.. Na tsaneka..! Na tsani ganin wann fuskar taka balle sauraron muryarka.!

Sosai kalamanta ke masa zafi.. Sosai zuciyarsa ke masa zafi.. Bai bari takai aya ba ya k araso da sauri ya rufe bakinta da nasa.. Ta shiga turasa da duka k arfinta amma kaman zugasa take. Duk iya k ok arinta na ganin ta hana Haidar abinda yake k ok arin aikatawa ta kasa. Haka Ya rik e bridal gown dinta ya k eta da k arfin gaske.

"Ba a haka yaso zuwa mata ba. Ba haka yaso su shimfid a tarihin soyayyarsu ba. Sam ba nufinsa bane ya saka mata force amma bazai iya jurewa ba, bazai iya jure kalamanta a garesa ba.. Idan hakan shine masa saura dan ta sauraresa zai aikata."

Taci kuka har ta gode Allah. Sabon tsanar Haidar da illahirin ahalinsa Ya kuma ruruwa cikin zuciyarta.

Hannayenta ya rik o cikin nasa yana shafa sumarta a hankali.. Idanunta a lumshe suke gashin idon duk Sun jik e da hawaye still hawayen basu daina fitowa daga lumsassun idonta ba.

Yaci gaba da Shafa gaban goshinta zuwa farkon sumarta da gumi yasa suka dada kwanciya luf. A hankali ya lumshe idanunsa ya sumbaci goshin nata  I.. I m sorry Khairy& I didn t mean to.. force myself on you.. But you forced me to.. Shiru yai ganin har lokacin idanunta a lumshe hawaye basu daina ziraro mata ba.

" Please don t hate me.. Don t hate me Khairy.. I grew up thinking.. My life was a complete mess.. Ba wani abu da yake gaskiya cikinta.. Duka k arya ce kawai.. But then you came.. And changed everything.. Yaci gaba da jinjina Kai yana dubanta  Idan akwai abu d aya da yake gaskiya cikin rayuwana.. It is you Khairy.. Kece..! Sai Ya d an murmusa yana k ok arin maida kwallan da suka ciko idonsa  You know, For the first time in my life.. I experience true happiness.. You filled the emptiness inside me Khairy.. With you, I feel complete.. Sai ya d ago yana dubanta sosai siririn hawaye ya gangaro masa  Punish me all you want.. But don t say na rabu dake Khairy..I.. I just.. can t bear the thought of it.. "

Sai sann ta d ago masa hannu alamun dakatarwa. Dan yanda kasan garwashin wuta haka takejin kalamansa.

Ta bud e lumsassun idanunta a galabaice. Ba tareda ta dubesa ba ta yunk ura zata tashi sai taji zafi sosai daga k asanta. Ta rintse idanunta tana jin wani kukan na zuwa mata.. Ba kukan physical wounds din dake jikinta take sai na rad ad in da zuciyarta ke mata.

Haidar yai k ok arin taimaka mata ganin tana so ta mik e amma sai yaji muryarta cikin kuka  Kar ka tab a ni.. Na rok eka kar ka sake d aura koda d an yatsa a jikina. Ta k arashe cikin k ok arin mik ewa.

Ya zuba mata ido yana dubanta zuciyarsa zallan k aunarta da tausayinta ne. Yanaji yana gani yana son taimaka mata Babu hali. A haka ta lallab a ta bud e k ofan da take tsammanin bathroom ne. Nan kuwa taga shid in ne ta shige Haidar na binta da kallo har ta b ace ma ganinsa. Ya lumshe idanunsa yana mai furzar da huci had ida shafe fuskarsa

da tafukan hannayensa. Ya maidoda dubansa kan bridal gown d inta da Ya b aci da stain. Ya kuma lumshe idanunsa yana jin wani abu kaman tsanar Kansa can k asar zuciyarsa& A hankali ya furta  Oh no.! What have you done Haidar.! Ya furzar da huci zuciyarsa na tuhumar sa  What if she hates you. ?.. Saurin girgiza Kansa yai bai so ma ya tuna. He needs to save their marriage at all cost.

A b angaren Ummul ma tana shigewa bathroom din wani sabon kuka ta fashe dashi. Zata iya cewa ita dai batasan wani abu soyayya ba sai akanshi.. Koda ace an gina Aurensu ba akan soyayya ba ta tsinci kanta da aukawa ma soyayyarsa..

A fili ta furta  labarin ya k are ne Tun kafin ya fara dan na tsaneka Haidar.! Ta kuma lumshe idanunta hawaye suka gangaro mata.

**

"A can gidan Hisham kaw cikin huci Ya mik e kaman zai shak o Dareen dake tsaye gabansa yake fad in  You damn fool.. Na fada miki so nake ki sheganta wann tsinannen cikin jikin naki, kan wani dalili zaki jingina kanki da kalmar Aure tareda Haidar.. Auren da Boka ya Miki alwali& Auren da akai Haidar bashi a hayyacinsa. Tsakaninki da Haidar babu wani kalma mai sunan Aure a tsarina.! Wann shegen dake cikinki shege ne shid in shege ne dole ki sheganta shi kaman yanda Kwaise Maitama ta shegantani ina jariri d an wata uku a ciki.. Ina so tarihi ya maimaita mata Kansa cikin ahalin Maitama Akan jikan Kwaise Maitama. Taji zafin samun jika shege kaman dai yanda ta shegantani. Kin fahimtaaa..! Ya k arashe kaman zai shak e wuyanta sai wani irin tururi yake."

"Girgiza kai Dareen take tana huci tana Shafa cikinta  No.. No way Hisham.. Bazan tab a abinda kake fad I ba, bazan tab a sheganta D a na da Haidar ba.. Koda ace Aurenmu bai kasance kaman ko wani Aure ba wann cikin da Aure aka same shi.. Kuma shine abu kad ai da zai maida Aurenmu da Haidar.. Ka cire wann a ranka.. Duk abinda zai faru Babu abinda zai hanani komawa ga masoyi na Haidar tareda D anmu dake cikina. Zamu Gina ahalinmu as it should be.! "

Kaman daga suka sinkayo muryar Anisa  Wann kuma k arya kenan.. Zancen banza kenan. Ban aikata komai ba ban sadaukar da komai dan wata kucaka irinki ta mallaki Haidar ba.!

Dareen ta juyo cikin tsananin mamaki tana duban wacce Tai maganar  And you.. Ke kuma wacece..?!

Anisa taci gaba da takowa  Ki kirani masoyiyar Haidar da ta sadaukar da komai tayi duk wani fad i tashi dan ta mallakesa..!

Dareen ta juyo tana duban Hisham da mamaki  Hisham.. Wacece wann.. And what is she saying.?

Anisa ta katseta  Kar ki tambayesa. I am his accomplice.. Mu biyun tare muka shirya dawowarki cikin rayuwar Haidar dan kawai mu raba Haidar da matar da Mahaifiyarsa ta aura masa. Ki kirani masoyiyar Haidar sann ki kira Hisham da masoyin Matar Haidar. Mu biyun are team. Ta murmusa  Ki yarda dani amfaninki Ya k are kinyi abinda muka kawo kiyi Dikda naji wani babban kwafsi.. Ki sani koda ace cikin jikinki na Haidar ne bakida wajen zama cikin rayuwarsa. Haidar nawa ne ni kad ai.!

Dareen ta juyo tana wani irin duba na cin amana ma Hisham dan batasan da zancen wata Anisa ba sai kawo wann lokacin. Ta soma girgiza kai tana jada baya  Lallai ka cika shed ani Hisham.! Ka cika babban mayaudari.. You are a Demon.! Na kasa yarda na Barka kayi amfani dani dan cimma bak in burinka akan Haidar a karo na biyu..! Amma ka sani wann shine zai zama na k arshe.. Zan tafi yanzu.. Zan sanar da Haidar komai duk wani mugun k ullinka akansa ko dan D ansa dake cikina.. Bazan tab a bari ka sake cutar da Haidar ba.. Zan sanar dashi komai koda zan rasa shi..! Tana ida fad in haka ta fice a guje.

Hisham Ya soma k ok arin binta a guje yana kiran sunanta yana fad in ta dakata.. Anisa tuni ta take masa baya.

Koda suka fito Sun tadda Dareen Har ta bud e gate ta fice.. Anisa ta shige mota tace da Hisham maza Ya shige su bi bayanta. Hisham Ya shige suka soma bin bayan Dareen dake gudu a k afa tana saka hannu tana neman abun hawa. Saidai akai rashin sa a babu alamun mutane a layin balle abun hawa. Dareen taci gaba da gudu a galabaice tana k ok arin tsere musu..

SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!*

*50*

*©þSameena Aleeyou& *

"Wasa wasa an shafe sati uku da mutuwar Auren Ummul da kuma Haidar. A wann lokacin Daddy ya shafe a k alla sati guda da dawo daga SouthAfrica, kuma labarin scandal din da yai erupting wajen bikin tariyar Haidar d in Ya cimmasa. Hankalin Mommy duk ba a kwance yake ba sanin mijinta mutum ne da ko kad an baiso wani abu ya shafi Kasuwancinsa. Yanda rayuwar ahalinta Ya soma daidaita bata fatan abinda zai kawo musu wani mishkila ko sab ani. Ga mamakinta sai Daddy ya tari abun bisa lumana ba kaman yanda Ya saba a baya ba. Dan ko zancen bai bata k ofan ta masa ba dikda taso yi masa. Bai canza ko kad an daga irin kulan da yake bata ba tin bayan da suka daidaita tsakaninsu. Hasalima k ara janta jiki yai yana fad in irin kewarta da yai. Ta d an dubesa a sanyaye tana so suyi zancen sai Ya kuma janyo hannayenta yace  Kwaise na gaji da tafiye tafiyen nan. Inaga lokaci yayi da zan mik a ma yaron nan ragamar kasuwancin.. Koda wani portion ne. We are not getting any younger.. Shekaru k aruwa suke.. "

Mommy ta jinjina kai duk jikinta a sanyaye. Alamun shigowar mota sukaji. Daddy ya lek a window sai Ya murmusa yace  Ina tunanin Yaronnan ne & Na kira shi yana company.. Na sanar dashi Ya bar aikin da yake yazo gida magana zamuyi.

K irjinta ya bada dam.! Dan tuni jikinta Ya bata ba magana mai k aramin mahimmanci bane zaisa ya kirawo Haidar ya bar aikinsa yazo gida dan kawai suyi magana.

 Let s go downstairs.. Ta sinkayo muryar Daddy yana k ok arin nufan k ofa.

Jikinta babu wani k wari tabi bayansa.

A parlor suka iske Haidar Har ya k araso yana jiran sauk owa mahaifin nasa.

Haidar ya risina ya gaida iyayensa. Duk suka amsa masa da sakin fuska saidai kallo guda zakai ma Mommy ka fahimci tana cikin damuwa.

Daddy ya dubi Haidar cikeda kulawa  Aliyu. Ya kirasa da asalin sunansa.

Haidar ya amsa cikeda girmamawa.

Daddy yaci gaba  Na dawo na taradda abubuwa marassa dad in gani da kuma sauraro. Garin yaya al amra suka lalace har haka.?

Haidar ya jinjina Kansa a hankali sai yace  Daddy Kai hak uri.. Ban.. san abubuwa zasu zama haka ba.. Amma tuni nasa jam ian bincike su binciko yanda Dareen take.. Kai hak uri Daddy.. Idan duka wann ya saka Kasuwancinka cikin had ari..

Daddy ya sauk e ajiyan zuciya kad an sai ya girgiza kai yace  Ba wann nake son ji ba.

Mommy ta dubesa da mamaki. Sai Daddy yaci gaba  Ba batun Kasuwancina da abinda zai shafesa nake son ji ba.. A a naka batun nake son ji.. Al amarinka da iyalinka. Because you matters to me more than any business.

Haidar yaji wani abu can k asar zuciyarsa. Yau Daddy ya zab i ya fifita al amarinsa sama da Kasuwancinsa da a baya yake d aukakawa.

Jikin Mommy yai sanyi musamman da taga Haidar yayi shiru. Duka laifin nata ne. Gwara ta sanar da Daddy yanda al amarin ya kasance.

Jiki a sanyaye Mommy tace  Dama.. Haidar bai bari takai aya ba yai karaf yace  Daddy scandal din da ya faru ya.. janyo sab ani tsakanina da Ummulkhair.. Kuma har ta kaiga na mata saki.. d aya.

"Sai Mommy ta dubi Haidar cikeda tausayawa.. Ta fahimci yasan duk abinda tai amma ya zab i ya rufa asirinta. Bazai bari mahaifinsa yaji ga abinda ta aikata ba gameda AUREN WATA UKU. Allah sarki D a da uwa. Sai taji girma , k ima da soyayyan d an nata ya k aru a kwayan idonta. Fatan ta Allah ya albarkaci rayuwarsa Ya daidaita al amarinsa da iyalinsa."

"Daddy ya dan numfasa sai ya dubi Mommy yace  Rankidad e, can I have a moment with my son.? Ya k arashe yana dan mata alama da ido."

Mommy tace  Badai cireni akai daga cikin ahalin ba.

Ya dan murmusa kad an  Waye ya isa ya cire ran gida cikin ahalinta. Magana ce tamu. Men talk.

Ta d an murmusa  Kace dai kawai wariya. Toh bara na baku waje dama inada abinyi. Ta k arashe tana mik ewa.

Daddy yai gyaran murya kad an yace  Haidar banji dad in abinda kai ba dukda sanin saki a musulunci ba haramun bane amma sai idan Ya zama dole akeyi. Idan akace daga samu sab ani za a dinga saki da ko mu nan iyayenka bamu kawo har wann lokacin muna tare ba. Kai shaida ne.. Kaga k alubale da iftila i na rayuwa da mukaita fuskanta. Amma dukda haka muka jajirce. Har hakuri ta kawo mu yanda muke yau. All marriages have ups and downs but this decision should not arrive easily. Sai Daddy ya mik e tsaye kaman Wanda ya tuna wani abu  Kaga tashi muje.. Akwai yanda nake so ka rakani.

Haidar ya jinjina Kai yana amsawa. Suka jera suna tafe shida mahaifinsa. Ta window Mommy ta hangesu sun jera Sun fice. A ranta tace ko ina D a da mahaifin suka nufa sai Allah. Ta murmusa tana jin dad in yanda sabo ya fara shiga tsakaninsu.

Koda suka fito Haidar ya tambayi Daddy ko Yai masa kiran driver d insa amma sai Daddy yace a a shi Haidar d in zai tuk a motar. Nan ma cikeda girmamawa Haidar ya amsa masa. Daddy ya shige mazaunin mai zaman banza yayinda Haidar ya shige wajen driver. Suna tafe Daddy yace dashi gidan Alhaji Gimba suka nufa. Kai tsaye Haidar ya d auki hanyar gidan aminin mahaifin nasa.

Koda suka isa Daddy yace da Haidar yai parking daga waje. Nan ma yabi umarnin mahaifinsa. Suka fito Daddy na d an gaba kad an yayinda Haidar ke take masa baya. Sai Haidar yaga Daddy ya nufi masallacin k ofan gidan Alhaji Gimba. Suka gaggaisa da mutane ya tambayesu Ya Sheikh bai fito ba. D aya daga cikin mutanen yace  Ai zai wahala Ya Sheikh ya fito yau sabida tun jiya yake cewa bai gane jikin ba. Daddy yai masa fatan samun lafiya. Ya kuma yi ma mutanen Sallama Wanda kusan dukansu Dattijai ne kaman sa da ma Wanda suka fisa. Da alama duk sun saba dashi dan tare suke d aukan karatu a nan masallacin tsakanin sallar magrib da isha wajen Imam ya Sheikh.

Sun fito tareda Haidar kenan saiga Alhaji Gimba. Nan suka tsaya suna gaisawa. Haidar ya dan matsa gefe ya basu waje.

Alhaji Gimba ya dubi Daddy ya dan girgiza kai  Lafiya dai naga ka taho tareda Haidar..?

Daddy ya dan sauk e ajiyan zuciya yace  Lafiyan zance ba lafiya ba tinda kanada masaniyar abinda ya faru lokacin bikin tariyarsa da iyalinsa.. Tinda Har business competitors dinmu sun so suyi amfani da wann su sokemu.

Alhaji Gimba ya jinina Kai  Haka ne.

Daddy yaci gaba  Toh Wato abinda ke faruwa shine.. Wann abu da ya faru har ya haifar da matsala tsakanin shi Haidar d in da iyalinsa.. Kuma kaga abu da yara tashi d aya yayi saki.. Kasan da yawan samarin nan ba a zama a fahimtar dasu menene ma Auren kansa kafin su shigesa which is wrong.. As a parent musamman ma Uba inaga yanada kyau idan D anka yakai munzanin Aure ya kuma zo maka da batu na Aure idan Har zaka nemar masa Auren  yar wani. Ko dai kai ka zaunar dashi ka fahimtar dashi menene Auren kokuma ka kaisa yanda za a zaunar dashi a sanar dashi Auren tareda hakkokinta da hukunce hukuncenta.. Dan nima har yau ina nadaman wasu kurakuren da nayi a baya kuma bana fata irin haka ya faru da D a na. Idan ka duba da yawa yanzu Shiyasa zakaga mace macen Aure yayi yawa dan shiga cikin Auren kawai ake ba karatun sanin hukunce hukuncenta.. Shine kaga na kawo shi nan dan

73 / 103