AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   46 / 103

135K to 138K   out of 306.8K words

Babu Wanda yasan wacece Amaryar ko  yar waye. Shin Aliyu Maitama ya aura ma D ansa  yar d aya daga cikin abokan adawarsa na kasuwanci ne dan ya ceci Kampaninsa?*

 Damn it.! Daddy ya furta a hankali. Ya juyo yana duban Alhaji Gimba  Ka gani ko.! kaga abinda nake fad a maka ko. Wann yaron brings nothing to me but trouble.

Alhaji Gimba Ya girgiza kai yana kallon labarin  Yanzu zaka yarda da batu na da nace da kai mu tafi asibitin. Rashin nuna damuwarka zai janyo hankalin press garemu. Idan son samu ne yarinyar tana warkewa ka kira koda kwaryakwaryar walima ce tsakanin business partners dinmu ka sanar da Auren D anka.

Daddy yaci gaba da girgiza kai yana fad in bazai bari Haidar Ya tarwasta shi ba. A fusce ya fice Alhaji Gimba na take masa baya.

**

A can asibiti kuwa Haidar ne ya k araso da yan sanda har guda biyu. Hisham na ganinsa da yansanda ya mik e yana girgiza kai  No.. This is not happening.! Haidar mai kake shirin aikatawa.?

Duk k ok arin Hisham na ganin Ya dakatar da Haidar bai nasara ba har saida Haidar d in Ya kutsa kai cikin recovery room da aka aje Ummul.

Hisham yai wani irin burki zuciyarsa na bugawa sakamakon hango mutum da yai kwance saman gado. Dukda na urar oxygen dake saman hancinta bai hana zuciyarsa bugawa sau uku a jere ba. Ji yai Ya kasa jurewa Har saida k afafunsa suka kaisa gaban gadon. A daidai lokacin da Anisa harma da Mommy suke duban Haidar cikin tsananin mamaki Wanda shigowarsa dakin kenan ga yansanda biye dashi.

SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!*

*33*

*©þSameena Aleeyou& *

Da tsananin mamaki Mommy ke duban Haidar. Ta kuma girgiza kai cikin rashin fahimta  Haidar meke faruwa. Why are the police here..? Who are they here for.?

Haidar da Har lokacin dubanta yake. Wane irin duba da za a iya fassara sa kai tsaye da duban k iyayya Ya k araso daidai gabanta. Ya d auki dak ik ai a haka kafin Ya rank wafo da kansa saitin kunnen Mommy  Isn t it obvious? They are here for you Mommy. Sunzo ne su tafi dake.

Mommy ta dago cikin tsananin mamaki tana dubansa. Ta girgiza kai cikin rashin yarda tana kuma duban  yansandan. Sai ta kuma duban Haidar cikin k ok arin tantance shin mafarki take ko kuwa da gaske ne hakan ke faruwa. Haidar ne ya kawo yansanda su tafi da ita. D anta da ta haifa. Tilon D anta da take duk wani fad i tashi sabida shi a rayuwarta yau ya kawo yansanda suyi arresting dinta. Innalillahi wa inna ilaihi raji un. Bata tab a tsammanin za a kawo wann gab ar ba. Duk k iyayya da Haidar ke masu daga ita Har mahaifinsa bata tab a tsammanin k iyayyar zai tasiri irin haka ba.

 Aliyu.! Ta ambaci sunansa cikin sanyin jiki  Ni ce ka kawo ma  yansanda su tafi dani.? Ta k arashe maganar nata tana nuni zuwa gareta da  yar yatsarta cikin tsananin shock.

Haidar da Ya kafe ta da ido lokaci guda yake jinjina kai  Remember this is a hospital Mommy. You can t make a scene here. Ki fita ki tafi tareda  yansanda a tsanake.

Mommy ta kuma girgiza kai tana jin hawaye na k ok arin ciko idonta. Ta tuna shekarun baya lokacin da ta haifi Haidar. Bata raine shi ba haka bata tab a shayar dashi drop na nononta ba. Ko zai kwana yana kuka a matsayin jariri bata tab a attempting lallashin shi ba irin yanda uwa keyi ma jaririn ta. Bata tab a rungume Haidar yaji d umin mahaifiyarsa ba. Ta tuna Asshe tasha nusar da ita cewa hakan zai iya yin tasiri tsakanin dangantakarta da D anta domin kuwa a wann lokacin ake samun bond na uwa da D ah. Wann shak uwa soyayya da tausayi dake tsakanin D ah da uwa a wann lokacin ake building d insa. Ba birgewa bane sabida gayu da zamani kice bazaki shayar da D anki da kika haifa ba wai gudun kar jikinki ya lalace. Kar ki losing figure dinki koh. Toh ki sani wann ba wayewa bane ba kuma birgewa bane. Ba birgewa bane kice ke bazakiyi d awainiyar komai ma D anki da kanki ba sai Nannies. At least ki samu lokaci na musamman tsakaninki da D anki koda bazaki masa wasu hidindimu na d abi a ba. Ke uwa ce mai k ok arin k ulla alak a mai kyau tsakaninki da D anki. Mommy ta dago tana duban cikin idon

Haidar Wanda sanda yake jinjiri bata bar shi ya kalli cikin nata idon ba. Bata hango tausayinta ba bata hango soyayyarta ba balle jin k anta sai akasin haka. Saiga hawaye suna gangarowa daga idon Mommy.

 Haidar ni mahaifiyarka ce. Ni ce na d auki cikinka tsawon watanni tara. Bai bari takai aya ba ya dakatar da ita  Ki aje duk wani bayananki Mommy. Wann labarin da kike bayarwa akwai ayan tambaya akansa a halin yanzu. Kuma kinsan me? Whatsoever you re hiding sai na binciko sa this is just the start. Ya dubi  yansandan  You can take her with you officers.

 Yarsandar macen ta soma k ok arin matsowa da sauri Anisa ta shiga tsakiya tana hawaye take girgiza kai  Don t touch her.! Don t you dare come near her. Do you really know who you are arresting.?! This woman here is Hajiya Kwaise Maitama. You just can t arrest her. Kudin zaku iya rasa aikinku gaba d aya.!

Haidar ne Ya matso kusan Anisa yana sakin huci Anisa ma na hawaye take dubansa cikeda firgicin yanayin da taga Haidar din ciki.

" Who the hell do you think you are to interfere.? Get out of the way now. Or else..! Bai kai aya ba Mommy ta katsesa  She s my niece, and she has every right to interfere.! Unlike you she s not ungrateful.. Wane irin D ah ne zai kawo wa mahaifyarsa yansanda..?! "

Jinina Kai yake yana duban Mommy  Since you went ahead and brought it up.. Are you really my real mother.? Da gaske kece mahaifiyata kodai sato ni kikai.? Tell me now Kwaise Maitama. Who are my real parents.? Where are they.? Did you kill them and kidnapped me.? Answer me now.! Ya k arashe idonsa na kuma kadawa.

Mommy ta kasa furta komai sai hawaye dake neman ciko idonta jin danta data dauki cikinsa tsawon watanni tara ta haifosa duniya na kokonto idan ita ta haifesa.

"Haidar yaci gaba da jinjina Kai jin bata basa amsa ba  Of course you don t have the answer. But I promise you, koda baki amsa yanzu ba zaki amsa a ofishin  yansanda. Idonsa na kanta yaci gaba  Officers take this woman with you right now.! "

Yarsandan ta kuma matsowa Mommy taci gaba da girgiza Kai  No Haidar. Baka cikin hayyacinka.. Ta dubi yarsandar dake kokarin kamo hannunta ta aika mata wani kallo  You are doing this to lose your job. Do you have any idea who I am.?!

Yarsandar ta d anyi gyaran murya  I m sorry Ma am but we have the warrant for your arrest. Ta k arashe tana k ok arin warware mata takardan hannunta.

Mommy zata kuma magana Haidar ya katseta  Ki adana duka bayananki har a isa ofishin  yansanda. Zaki sanar dasu yanda akai kika Saka guba a turaren da kikai niyyan Kasheni dashi ta hanyar gayyato wata mace cikin rayuwana da sunan aure.!

Mommy ta saki baki wann Karon cikin rashin fahimta  Turare kuma.? Mai.. Ni.. wane irin turare.?! Ta k arashe tambayar cikin rashin fahimta yarsandar na k ok arin janyota ta daka mata tsawa da fad in  I am Kwaise Maitama. You just can t arrest me.! Idan gayyata ta ofishin ku kuke zan iya tafiya a nawa motar amma baku Kai kuyi arresting dina a k asar nan ba. Even your superiors sunyi kad an.! Ta k arashe tana sakin huci ta fito asalin a Kwaisenta.

 And do you think you are above the law.? Just because you are rich and powerful.?! Haidar ya katseta.

D aya Dansanda namijin ya tare gaban Haidar yana dannarsa  Calm down Engr. If that s what she wants let s do it her way then.

Ya dubi Mommy cikin risinawa yace  We are sorry Hajiya. We understand that you are an important figure in the society. Zaki iya zuwa ofishin mu a motar ki tareda rakiyar abokiyar aikinmu guda d aya. I hope that s ok with you. Ya k arashe cikeda risinawa.

Takaici ya cika Haidar ganin yanda ikin tsaro ya lalace wai idan kanada matsayi da mukami cikin Al umma treatment dinka daban ne. Idan kuwa haka ne zai tabbata kudi da influence da Hajiya Kwaise keda shi baiyi tasiri a shari an da zasuyi da ita ba because he waged a war on her. Sai yanda k arfinsa ya k are.

Haka suka fice salim alim dan Mommy dai bata so taja idon mutane da hankali kanta. Anisa na biye dasu tana hawaye tana ci gaba da rok on Haidar.

Duk dramar nan da suka gama Hisham na tsaye gaban gadon ta har dai suka fice gaba d aya d akin ya rage saura su biyu Hisham da Ummul dake kwance saman gado ido a lumshe.

"Hannu yasa ya share hawayen da suka zubo masa. A hankali ya soma furta  You know, when I first met you.. I told myself& Hisham, this is the time.. You ve finally found her& Your soulmate.. The love of your life.. After all the rejections.. All the heartbreaks.. Muryarsa ya tike sanda ya kuma share hawayen da suka Zubo masa  Daga k arshe ka hadu da ita. But it turned out to be the worse of all..! Ya kuma murmusawa yana girgiza Kai  Do you know what s the funniest thing.. And yet the saddest.. I never got the chance to tell you how I feel about you.. It was all a dream.. Kuma zai tabbata a matsayin mafarki Wanda bazan tab a farkawa ba. "

Ya hade hannayensa biyu alamun rok o wasu hawayen na gangaro masa  You are now married to Haidar.. My best friend. He s like a brother to me you know. Kuma zan iya sadaukar da komai nawa for him if I had to.. Koda kuwa rayuwana ne.. so Please ki daina zuwa mun a mafarki na.. Please..! Ya k arashe wasu hawaye masu ciwo na kuma gangaro masa.

A hankali ya soma janyo k afafunsa da k yar cikin k ok arinsa na ficewa daga d akin. Aiko yana ficewa yai bursting cikin wane irin kuka yana mai k unshe bakinsa. Kai da gani kasan direct daga zuciya kukan ke fita.

**

Motan Mommy da su Daddy suka gani ya fice daga hospital ga na  yansanda biye dasu ya sanyasu cikin tsananin shock da mamaki. Uwa uba da sukaga motar Haidar biye dana su Mommyn.

Daddy ya dubi Alhaji dake gefensa  What.. What s the meaning of this..? Motar Kwaise nake gani tareda  yansanda.! Ya share gumin da yaji na tsartsafowa daga goshinsa  Kwaise da D anta bazasu tab a barina ba sai sunga bayana Gimba.!

Alhaji Gimba ya girgiza kai  Kar kayi magana haka Engr. Bamu san abinda ke faruwa ba. Let s follow them and find out. Ya k arashe maganar yana mai sanar da driver da yabi bayan motocin su Mommy.

Girgiza Kai Daddy yake sanda yaga sun nufi hanyar headquarter na yansanda  What.! No way Gimba.. I can t be seen there.. Bazai yuwu a haskoni a ofishin  Yansanda ba it will be a disaster for our business. Kai kasan hakan.! Yaci gaba da girgiza Kai yana fad in karshen zamansa da Kwaise harma da D anta yazo.

Wani Kayan tashin hankalin shine suna isowa kusan kofan ofishin suka hangi masu nad an rahotanni kowa na jefo masu tambayoyi cikin son sanin mai ahalin ke ciki.

Daddy ya shafe fuskarsa da duka hannaye biyu yana girgiza Kai. Sai wani irin huci da yake furzarwa. Ya dubi Alhaji Gimba  Saida nace maka zuwa police station ba shawari mai kyau bane. Kaga abinda nake sanar dakai. Our company is handling one of the top government infrastructure project at the moment. We can t afford to lose credibility a idon gwabnati.!

"Alhaji Gimba ya furzar da huci kad an dan shima abun na neman fin k arfinsa. Ya dubi Daddy yace  I ll take care of the media. Zan tabbata basu publishing wani labari ba. Wancan labarin Auren Haidar da suka daura, I ll make sure they take it off.. Ka shiga ka samu ahalinka.. Bamu San meke faruwa ba. Su d in suna buk atar ka. "

Da kyar da sud in goshi Alhaji Gimba ya shawo kan Daddy ya amince ya nufi ofishin yayinda aka barshi nata kokarin ji da Media.

Daddy yana shiga akai directing dinsa zuwa ofishin daukan bayanai yanda akai detaining Mommy ana koro mata laifukan da ake tuhumarta dashi ga Haidar tsaye a gefe ya kafeta da ido Kai kace shike interrogating din nata.

 D ansandan yaci gaba  Maiyasa kikai yunk urin kashe yarinyar.? Shin kinsan turaren da kika bata turare ne mai d aukeda guba.

"Zuciyar Mommy yaci gaba da tsinkewa. Shikenan boka ya sakata a uku. Ashe guba ya bata matsayin turaren da zai janyo Haidar zuwaga Ummul. Meyasa ta kasa yarda cewa boka mak aryaci ne.? Dama da ake cewa boka makaryaci ne bata yarda ba amma yau ta yarda. Wato ya bata turare mai guba ciki idan Ummul ta shak a ta Mutu shikenan sai ita kuma tai zaton asirin dake jikin D anta ne ya karye kaman yanda Bokan yace. Zatai zaton tsafin Boka ne yai aiki. Ashe ba haka bane annamimin guba ya saka cikin turaren Wanda zai ajalin Ummul shikenan ita kuma ta hau kan aikinsa ne yai tasiri. Kai Kaicon rayuwa cikin b ata. Gashi nan Boka mushuriki mak aryaci ya sakata a uku, ya kulleta cikin bala in da bata san yanda zata wanke kanta a idon mijinta da D anta ba."

Muryar Daddy suka sinkayo  Kisa Kwaise.?!

Mommy tai saurin juyowa tana duban Daddy hawaye na kokarin ciko idonta take girgiza masa Kai alamun a a.

"Daddy ya dubi  Yansandan  Would you please, excuse us.? "

" yansandan suka mik e cikeda risinawa suna fad in  Sure Sir, of course.! "

Haidar dake tsaye gefe jinjina Kai yake yana duban Daddy bayan  Yansandan Sun fice  Matarka tayi attempting kashe ni ta hanyar wann yarinyar da ta auro ta kawo cikin gidan da sunan matata.. Shiyasa ta dage sai nazo gidan na zauna tareda yarinyar. Tayi poisoning d inta cikin turare sabida motive dinta kawai shine taga bayana. Wann matar ba ita ta haifeni ba.. Kuma yau zata fad i a yanda ta sato ni.!

Daddy ya Kai k ololuwa cikin b acin rai a hasale ya maida dubansa ga Haidar  Ka daina maganar shiririta a nan.! Kwaise is your real biological mother. She gave birth to you. She s your mother.!

"Ya maida dubansa ga Mommy  Tell me Kwaise, meke faruwa a nan.. Meye wann yaron yake fad a..?! "

Mommy taci gaba sa girgiza Kai tana hawaye  Engr bansan komai ba. Wllhi bansan turaren da na baiwa yarinyar matsayin kyauta akwai guba ciki ba. Why would I poisoned her.. What could be my motive.? You need to believe me. Ina son yarinyar nan like my own. Kowa a gidan shaida ne. Ita kanta Ummul shaida ce.!

Daddy yaci gaba da girgiza Kai yana dubanta  You brought that girl into our family Kwaise. Bansan dalilin ki na dagewa sai kin aura ma D anki wann yarinyar ba.

 Her motive s quite clear. To use her and get rid of me without being detected. Maybe

46 / 103