AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   29 / 103

84K to 87K   out of 306.8K words

tayi k ok arin danne kukanta  Ummulkhairy kar ki neme ni& Kar ki tako

yanda nake Har na tsawon watanni uku.. Ko a waya kar ki kirani.. Ki min alk awarin.!

Da tsananin mamaki Ummul ke duban mahaifiyarta. Ta shiga girgiza kai cikin rashin yarda  Umma.. Mai hakan yake nufi..? Umma zaki yanke duk wata alak a dani ne..?

Umma ta jinjina mata kai alamun eh  K warai Ummul.. Kuma kema kimin alk awarin yanke alak arki damu.. Ina nufin da d aukacin ahalinki na tsawon watanni uku.. Kimin wann alk awarin..! Ta k arashe tana duban Ummul d in.

Girgiza kai Ummul keyi tana duban mahaifiyarta  Umma.. Kin kaw ji abinda kike fad i mun..? Umma yanke alak a da iyayena harda mahaifina dake kwance yana jinya..? Umma Anya..

Katseta Umma tai  Na tsawon watanni uku kacal.. Dan Allah ki mun wann Ummul..! Ta k arashe tana kamo hannayen Ummul d in alamun rok o hawayen da taketa k ok arin dannewa na kwaranyo mata.

A hankali Ummul ta zame hannayenta tana girgiza kai  A a Umma.. Baki tunanin Kin tafi da nisa Umma.. Bazan iya ba.. Bazan iya abinda kike nema daga wajena ba.. Bazan iya yanke alak a da ahalina ba.. Menene dalilinki Umma..?

"Umma taci gaba da matsan k walla. Sai kuma ta mik e tana huci  Wann Shine kad ai abinda na nema daga wajenki Ummul.. Kar ki nemeni, kar ki tako yanda nake Har na tsawon watanni uku.. Idan kuma kika nemi ni ko kika tako yanda nake kafin wata uku ban yafe miki ba.! Tana ida fad in haka tasa kai ta fice kuka na kuma b alle mata."

Ummul Tai zaune tamkar wacce aka dasa. Ta nemi kuka ta rasa. Sai ta shiga tambayan kanta Wacece ita..? Meyasa rayuwa yazo mata a haka..? Shin ita kad ai ce take fuskantar k alubale irin nata..? Shin Anya Umma itace ta haifeta..? Anya uwa takan haifi  ya tayi watsi da ita irin haka.. Tin daga tasowarta Umma bata tab a damuwa da al amarin rayuwarta ba. Ta mata aure a wulak ance. Daga k arshe ta datse alak a da ita ba tareda dalili ko hujja ba.. Anya ana samun irin wann uwar.. Anya ko a labarai ta tab a cin karo da uwa irin Umma..? Ta shiga girgiza kai tana duban d akin da aka ajeta. Lokaci guda ta mik e tana takawa a hankali. Daidai gaban madubi taja ta tsaya tana duban kanta cikin madubin.

Take zuciyarta Ya shiga karanto mata wacece ita. Tin daga lokacin k uruciyarta har kawo girmanta. Duban kanta take cikin mirror hawaye na zurarowa daga cikin idanunta d aya na bin d aya.

A hankali ta silale a wajen cikin kuka maras sauti tana jin tamkar bata a duniyar.

**

Umma ta kusan ficewa kenan taji an damk o hannunta an janyota wani d akin.

Asshe ta gani tsaye tana sakar mata murmushi  Kinyi abinda ya kamata.

Jinjina kai Umma tai tana duban Asshe  Ki sani da ace nasan irin auren da zakuyi ma D anku da Ummul kenan tun farko da ban amince ba. Amma saidai idona Sun rufe Allah Ya barni da iyawata a lokacin da na Shafa a da neman zab i daga gareshi. Watak ila wann shine hukunci na. Ta share hawayen da suka zubo mata kafin taci gaba  Nayi abinda kuke so.. Na yanke alak a na wucin gadi da Ummul kaman yanda kukai auren wucin gadi da ita.. Alak ata da  yata zai dawo ne bayan sharud anku Sun cika.. Wann lokacin kuma.. Nayi alk awarin sabanta alak ata da  Yata.. Nayi alk awarin bata kulan da ban bata ba tsawon rayuwarta.. Nayi alk awarin nuna mata soyayya irin Wanda na hana mata a matsayin uwa tsawon rayuwarta& Na.. Kuka ya hanata ci gaba da magana.

Da k yar ta iya saita kanta kafin taci gaba  Iyakacin abinda zan rok a daga wajenki shine ki kula mun da Ummul .. Dan Allah kar kici amanata Asshe.. Ke kad ai na sani cikin ahalin da Ummul zata shiga na watanni uku& Dan Allah Ki kular mun da ita.. Kuma ki rike amanata kar ki tab a tona sirri na ma Ummul& Kar ki sanar da ita AUREN WATA UKU tayi kuma inada masaniya. Dan Allah kimin wann..! Ta k arashe cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka hannayenta had e waje guda alamun rok o.

Asshe tab e da baki take duban Umma babu ko alamun tausayi. Cikin zuciyarta take ayyana dan ma baki san dalilin auren  yar taki shine ta karya sihiri ba. Sann auren yana nufin ajalinta. Ki gode ma Allah itama ta zama barazana ga

rayuwar Haidar Wanda hakan zaisa ki sake had uwa da  yarki bayan wata uku. Dan bazan tab a bari Haidar ya kusanci wann  yar taki ba. Ta murmusa kad an  Kin kware wajen iya wasan kwaiwayo Suwaiba.. Ban Miki alk awarin komai ba& Dan bayan amanata da kikaci bansan mai zai faru a tsakanin wata uku ba..!

Cikin zuban hawaye Umma ta shiga jinjina kai tana k ok arin mik ewa. Jiki a matuk ar sanyaye tasa k afa zata fice Asshe ta kuma dakatar da ita.

Umma taja ta tsaya Har lokacin hawaye take.

Asshe ta k araso tana duban Umma daga sama zuwa k asa. Lokaci guda tasa hannu ta shiga janyota da k arfin gaske

. A haka suka isa gate.

Suna isowa gate tai jifa da Umma gaban securities. Asshe ta shiga nuna masu Umma  Ko me kamannin matar nan kar ku bari ta kuma shigowa gidan nan..

Umma dake watse k asa kaman kayan wanki ta d ago idanunta da kyar tana duban Asshe dan yanzu ta daina mamakin abubuwa.

 Asshe& 

 Shiiii..! Asshe ta dakatar da ita tana mai d ora yatsa ta guda saman labb anta  Duk draman da akayi mijina baida masaniya Suwaiba.. Ni Ina son mijina kuma ina daraja aurena.. Ni ba irinki bace wacce ta watsar da mijinta dake kwance yana jinya sabida cikan burinta. Bazan bari mace irinki ta lalata mun aure ba.. Dan haka bake ba ni. Dama kema kinsan hanyar jirgi ba daidai bane da na mota. Ni da Ke ba d aya bane. Ciniki Ya had amu kuma ta k are. Babban goro sai magogin k arfe bayan wata uku zaki sake haduwa da  yarki idan d anmu Ya gama kwangilarsa dan ita ba ajinsa bane. Zaren ba kalar yadin bane. Tashi ki fice kafin nasa su fitar dake..! Ta k arashe tana nuna mata k ofa.

Jiki Babu k wari Umma ta mik e tana ganin duhu na gauraye mata k wayan idanu. Ta shiga had e hanya tana takawa da kyar tana jin wani abu mai zafi na yawo cikin k irjinta.. A haka Umma ta fice daga gidan ga duhun dare ba tareda tasan ina take zuwa ba.

SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU.!*

*22*

*©þSameena Aleeyou& *

A b angaren Inna Dije kaw koda ta fice sai ta tadda Khulsum a yanda tace ta zauna ta jirata. Dan dama lokacin da Umma ta kori Khulsum daga wajen Ummul Inna Dije ta had u da ita a k ofan gidan tana kuka. Nan take sanar da Inna Dije ga yanda sukai ita da Ummanta hakan yasa Inna Dije Tai mata umarni da ta jirata Har ta shiga ta fito zasu tafi tare.

Basu zarce ko ina ba sai asibiti wajen Abba.

Inna Dije ta k ura ma D anuwanta dake kwance idanu. Ta shiga jinjina kai tana mai furtawa a fili  Lallai Yaya ka gamu da jarabawan shed anun Mata.. Amma da izinin Allah ba macen da zata saka samun damar cutar dakai cikinsu.. Bazan bari hakan ta kasance ba.. Na maka alk awari D anuwana. Ta k arashe tana dafe hannunsa guda.

Khulsum dake zaune gefe ta goge hawayen da suka gangaro mata tana jin ciwon abinda mahaifiyarta da abokiyar zaman mahaifiyar nata sukai ma mahaifinta Wanda Babu mijin da Ya cancanci mata Irinsu.

"Mama Dije ta matso ta rungume Khulsum tace  Kar ki damu Khulsumu. In sha Allahu mahaifinki zai samu lafiya, zan d auke shi daga nan.. Zamu tafi gaba dayanmu.. Zamu fara sabuwar rayuwa gaba d ayanmu tare.. Su kuma Suwaiba da Tani ko waccensu zata girbi abinda ta shuka ne.. "

Khulsum bata iya cewa komai ba sai kauda fuskanta gefe da Tai tana mai kuma goge hawayen dake zubo mata. Dan Allah ya gani dukda Umma ta kasance mahaifiyarta sai taji sam bata ko k aunar a ambato mata sunan mahaifiyar tata musamman bayan rabuwar da sukai a daren yau d in.

"Mama Dije sai duban Khulsum take tana sak a abubuwa cikin zuciyarta  Tabbas sai ta cika Zuciyar Khulsum da tsanar mahaifiyarta.. Suwaiba zata rasa yaranta gaba d aya.. Bayan ta rasa Ummul zata rasa Khulsum ma. Zata rasa ahalinta gaba d aya dan mijin ma ta rasa shi kenan rashi na Har abada.. Sai ta tabbata rayuwa yayi k unci ma Suwaiba, k uncin da sai ta gwammaci mutuwa da wann rayuwar& Kaman yanda ta rasa Fa iz d inta D anuwanta tilo Ya kuma k ullaceta sabida soyayyan Suwaiba da ya rufe masa ido. Ta rasa soyayyan D anuwanta na tsawon shekaru zata tabbata tayi amfani da wann damar ta dawo da shak uwa da soyayya dake tsakaninta da D anuwanta.. Snn zata rattaba Auren Ummul ya Mutu kafin wa adinsa ya cika. Bayan auren ya Mutu ta bi ta sanar da Ummul irin auren tozarci da Suwaiba tai mata. Sai ta kwance ma Suwaiba zani kasuwa gaban  ya yanta. Dik irin biyayya da Ummul ke ma Suwaiba sai ta tabbata ta masu farrak u bayan ta kashe wulak antaccen auren da tai ma Ummul. Suwaiba zata zama batada tsuntsu batada tarko. Zata rasa kowa tin daga kan Yayanta Isubu da zata masa jinya a yanzu wanda makahon soyayyan da yake ma Suwaiba ya hanasa ganin aibun Suwaiban har dai suka sami sab ani mai muni duk sabida Suwaiba har izuwa kan yaranta guda biyu Ummulkhairy da kuma Ummulkhulsum.. Wann alwashi ne da ta d auka ma kanta. Ta saki murmushi a hankali tana jin zuciyarta na mata sanyi al amara suna tafiya mata yanda take so."

**

Ikon Allah ne ya kawo Umma gida. Tana isowa ta hangi fitilan d akin Tani a kashe. A nata tunanin Tani ta kwanta bacci tinda tasan kaman yanda Dije tace bazata kuma barin d aya daga cikinsu ta kusanci Abba ba tasan bazata bar Tani ta zauna can asibiti wajen Abba ba. Hakan yasa ta shiga sand a a hankali alamun bata so Tani taji dawowarta.

"Kaman Wata b arauniya haka ta shige d akinta cikin sand a tana addu an Allah yasa ta tadda Khulsum na bacci. Saidai koda ta shige d akin babu Khulsum Babu alamunta. Umma ta silale ta zauna da kyar tana duban gadon yaran nata da angle din da ko wacce ta Saba kwanciya.. Sai ta tuna irin rabuwar da sukai da Khulsum duk Akan Auren Ummul. Datse alak a tai tsakaninta da  yarta Khulsum. Innalillahi wa inna ilaihi raji un tana cikin hayyacinta ta aikata makamancin wann abu. Sai ta soma tunanin toh ina Khulsum ta shige.? Take zuciyarta ta bata amsa da fad in tana wajen mahaifinta a asibiti kaman yanda kika koreta daga gareki. Khulsum bata da wajen zuwa da ya shige wajen mahaifinta. Umma ta silale a hankali hawaye na kuma b alle mata. Sai tana jin wani abu da yafi yanayi da tashin hankali na ziyartarta& Yau dai Babu Ummul a cikin gidan, wacce a kullum idan ta bud e idanu ta ganta cikin gidan Babu aure zuciyarta ke mata ciwo, hankalinta ke tashi. Haka zalika taita kausasa harshenta Akan k addarar  yar tata. Meyasa bataji ciwon ya tafi ba..? Meyasa duk tulin damuwar da Tai a baya Wanda a nata zaton ganin Ummul ne a gida ba tareda aure ba ya haddasa mata. Meyasa taji babu abinda ya ragu a k uncin da takeji cikin ranta sai ma abinda ya k aru..? Meyasa..? Meyasa abubuwa suka kwabe meyasa auren Ummul da tai zaton zai zamto mabudin farin cikin ta da na ahalinta meyasa bai zama haka ba.. Meyasa auren Ummul ke barazanan zama mabudi da Mafarin tarwatsewar Ahalinta.. Ta rintse idanunta wasu hawayen masu tsananin ciwo suna zubo mata. Saida Umma tai kuka mai isanta ita kad ai cikin d aki with no shoulder to lean on. Babu wanda zaiji sautin kukan nata balle Ya lallasheta.. Ita kadanta cikin d aki tasha kukanta. Dakin ya mata girma, daren ya mata tsayi& Haka Umma taci kukanta a d aki cikin dare tamkar marainiyar kenwa."

**

Washe gari sassafe ake shirin tafiya da Amarya Ummulkhairi gidan mijinta dake Abuja.

Asshe ta fito taci uwar gayu yayinda Ummul ta kasa fitowa sai shesshek ar kuka take Wanda ya riga ya zame mata jiki. Tin Daren jiya take aikin abu d aya Akan dole Asshe ta tilasta ma cin abinci ma saida tai da gaske kafin ta saka ruwan shayi a cikinta. Kallo guda zaka mata ta baka tausayi. Asshe sai sababi take tana fad in haka za a Kai amarya a k anjale jiki duk yunwa kaman wata kazar mayu. Cikin ranta kuwa addu a take Allah yasa Ummul tafi haka lalacewa ko dan kar idon Haidar da hankalinsa ya sauk a kanta.

A haka suka fito da k yar bayan Asshe ta sanar da Ummul kar ta mance kud in Aurenta shine kud in jinyar mahaifinta dan haka tafiya gidan Miji ya zame mata dole idan har ba so take su janye komai ba.

Ummul na hawaye take janyo k afafunta. Tabbas wann auren sadaukarwa ne ga illahirin ahalinta. Bayan datse alak a da ita da Umma tai a daren jiya na tsawon watanni uku na farkon aurenta bata jin Umma zata tab a yafe mata idan tace ta fasa wann aure. Ta rintse idanunta zuciyarta na tausarta da cewa irin nata k addaran kenan. Watak ila hakan shine alkhairi ga d aukacin ahalinta. Idan tai nesa dasu Watak ila farin ciki da kwanciyar hankali zai wanzu cikin ahalin irin Wanda basu samu a baya ba.

Fitowar da zasuyi da zummar shiga mota kenan suka sinkayo wata murya.

 Ku dakata ku dakata. Direba a dakata ga pasinja d aya.! Ta k arashe tana kuma mak ale k aramar jakar Ghana must go d inta a hammata sai faman buga sauri take.

Asshe ta zaro ido tana duban matar nan shaye da tsananin mamaki  Dije.! Ta furta da k arfi.

Inna Dije taci gaba da sakin murmushi tana duban Asshe  Haba k awa ban gane wasa tare ci banban ba. Haka kika shirya tafiya da  yarmu babu wani nata. Ce Miki akai batada dangi ko tsawa akai ta fad o da zaki rufeta ki kaita kamar wata maras gata.

"Ummul tai saurin yaye rufin kanta hawaye na kuma b alle mata  Inna Dije. Ta furta a hankali tana duban Dije. Dije tai saurin k arasawa ta rungumi  yar D anuwanta  Ni ce nan Goggonki Ummul.. Innarki Dije, bazan bari a kaiki gidan miji kamar maras gata ba. Shige muje.! Ta k arashe tana mai shigar da Ummul cikin mota."

Har lokacin mamaki Ya kasa sakin Asshe. Watau matar nan ta ranste sai ta tona mata asiri. Inaa bazata bari hakan ta kasance ba.. Kafin Tai aune taji Inna Dije ta janyo hannunta ta jefata cikin mota. Fad i take  Direba tada mota muje birnin tarayya ba nan kusa ba.

Asshe ta matse hannun Inna Dije da k arfi tana k ok arin fiddota waje amma sai taji Inna Dije ko gizau bata motsa ba. Saitin kunnen Asshe take rad a mata  Kar kiyi wann ganganci dan tsaf zan kwance Miki zani a Kasuwa. Kama daga kan mijinki da kishiyoyinki Har izuwa kan  yaruwarki. Dan haka cikin salama ki shige mu tafi.! Ta k arashe tana firfito da idanu waje.

Asshe ta had iyi abinda Ya tsaya mata a mak oshi da k yar. Cikin sigan rad a take tambayarta  Fad a mun nawa kike so.?

"Inna Dije ta murmusa, cikin sigan rad a ta bata amsa da fad in Ki bari mu isa

29 / 103