AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   16 / 103

45K to 48K   out of 306.8K words

ta d ago tana murmushi ga hawaye na bin k uncinta  Kukan farin ciki nake Hajja Asshe. Burina zai cika Ummul d ita zatayi Aure. Zata bar gidan mahaifinta. Zan daina kwana kullum ina tashi na ganta gabana.. Wayyo ni Suwaiba Ashe wann rana zaizo..? Taci gaba da rera kuka.

Asshe ta zuba ma sarautar Allah ido ganin yanda Umma ke sunbatu tana fad in Yaya Tani zakici goron Auren Ummul.

**

A b angaren su Mama kuwa Tasi u yazo da wasu takardu yanda ya gabatar masu matsayin sabbin takardun shagon Abba. Harda sabbin makullai. Kai da ganinsa kaga maras gaskiya.

Ya dubi Mama da Badi a a yanda suka keb e daga can k asar wani bishiya wajen asibtin.

 Yauwa nace mu had u a nan sabida  yan sa ido. Mai saye zai iso yanzu da kud ad ensa naira dubu d ari uku kaman yanda muka tsaida magana.

Badi a tace  Haba Tasi dubu d ari uku saikace na sata.?

Tasi u yace banda abinki abu ne ake a sirrance kuma ko ina kikaje kayan magada karyawa ake. Ku gode ma Allah ma da muka samu mai saye dan na tabbata shima rahusa yaji shiyasa bai tsnanta bincike ba amma da zaran yasan Mai shagon na numfashi bai cika ba kinsan bazai sayi gaibu ba. Ni fah taimako nake a nan.

Mama tace  Kyaleta me ta sani wann. Ni fah da kike gani so nake ayi komai a gaggauce kafin Suwaiba ta bayyana. Dan na ranste kwandala bazasu samu ba daga ita har yaran nata.

Tasi u yace  Ah toh magana kenan.. Yauwa gashi can ya k araso. Yai masu nuni da mai sayen shagon Wanda Tasi un bai jima da masa kwatance yanda zai samesu cikin waya ba.

"Yana k arasowa Tasi u ya warware takarda  Wann takardan yarjejeniyar mallakar fili ne.. Ya saka yatsa a baki ya dangwali halshensa kafin ya d aga d aya takardan  Wann kuma takardun fili ne Wanda local government ta saka hannu akai, ga saka hannun sarkin Kasuwa. Kunsan ko wace kasuwa tana k ark ashin local government d in da take ne. "

Ya dubi Mama  Yauwa Mama nan wajen shine wajen saka hannun magada watau masu sayarwa kenan. Nan kuma wajen saka hannun mai saye ne. Nan kuma wajen saka hannun shaidu.

Badi a ta katsesa  Amma shi mai sayen baizo da shaidu ba.

Tasi u ya Washe baki  Wani aiki sai Badidi ta. Banda abinki meye amfani na. Ai duk dai a rubuce ne kawai ake abin ni duk zan iya saka hannu na zame maku shaidu.. Eh ai duk abun a rubutu ne kawai.

Ya dubi mai saye yace  Mutumi na ai sai ka saka hannu ko.. Mutumi Ya amshi takarda Ya saka hannu.

Tasi u Ya kuma Washe baki yace  Ai shikenan ka mallaki shago a garin Kano.. Burinka Ya cika.. Allah yasa ma kasuwa Albarka. Sai Washe baki yake dan dama mutumin k auye ne irin Wanda ko cirani basa fita cikin kauye suke kasuwancinsu burinsa Ya mallaki nasa shagon cikin garin Kano nan yai gamo da Tasi u.

Tasi u ya dubi su Mama  Yauwa Mama ga wajen da zaki saka hannu.

Mama ta dubesa a dak ile  Banida hankali ne zan saka hannu banga kud ad e ba.

Tasi u yace  Banda abinki Mama Tani waye yake yawo da kudade masu yawa irin haka. Ai sai b arayi su bi mu. Haba shi fah kud i d an sirri ne.

Mutumin Kauyen yace  Wann gaskiya ne. Daga nan zamuje tareda shi surkin naki Ya amsa kud in.

Tasi u yace  Ahtoh tare zamu tafi takardu suna hannuna bani damk a masa takardun Har sai ya dank a min kud ad en. Ko nima baki yarda dani bane. Na tabbata da baki yarda dani ba da baki bani  yarki Badi a ba.

Mama ta jinina kai  Shikenan.. Ta dubi Badi atu tace ta nuna mata yanda zata saka hannun. Tasi u kaman zai kamo hannayenta yake nuna mata. Yace Badi a ma ta saka duk suka saka.

Tasi u yace su koma asibiti wajen Abba shi zai k arisa ji da komai. Zuciyar Mama ba wai ya kwanta ba suka nufi cikin asibiti. Sam rawar k afan da Tasi u yake ba wai ta yarda dashi bane. Sai ta soma tunanin anya batayi gangancin barin Tasi u su tafi su biyu da mutumin amsar kud ad en ba. Koda yake ya Santa ya san halinta ita ba Badi a bace tsaf kwabo yai ciwon kai sai ta tatse. Da wann tunanin suka shige cikin asibiti.

(Rayuwar Duniya kenan. A wann babi munji yanda Matan Abba Wanda ke kwance gadon asibiti sukai cinikin dukiyarsa da kuma  yarsa. Mama dai tayi cinikin dukiyarsa yayinda Umma tayi cinikin  yarsa. Fad in Manzon Allah S.A.W cikin hadisin Abdullahi ibn Amr .  Duniya jin dad i ne kuma mafi alkhairin jin dad inta shine samun mace ta gari. Sahih Muslim 1467. Tabbas babban rahama ne Allah ya baka Matar kirki wacce zata tsare maka mutuncin kanta iyalanka da kuma dukiyarka Wanda suke amana a hannunta. Allah kasa mufi k arfin zukatanmu. Ameen).

SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU.!*

*15*

*©þSameena Aleeyou& *

Mama dai ta gaza zaune ta gaza tsaye tin bayan tafiyar Tasi u da mai sayen shagon Abba. Ta dubi Badi a dake shafen shafen waya tace  Ke kira min Tasu u shirun nan nashi yayi yawa.. Karb an kud i saikace karb an bashi.. Maza kirasa naji ina ya makara ne wai.

Badi a ta d an girgiza kai  Haba Mama ko fah awa d aya baiyi da tafiya amma kin d aga hankali a kirasa. Nasan halin Tasi barsa da shaye shayensa amma banda sata.

Zuciyar Mama yai wani irin bugawa. Ta dubi Badi a a zabure tace  Badi atu ina hankali na da tunani suka tafi Har na mance Tasu u Ya tab a shaye shaye.. Yo ina ake dank a amanan kud i hannun d an wiwi Bad ia..!

 Mama mijin nawa ne d an wiwi..? Ya tuba fah.

 Idan ba d an wiwi ba d an uwarki ne..! Mama tace tana danna mata dak uwa.. Zufa ya shiga keto mata ta ko ina  Na shiga uku.. Na kashe kaina ni Tani. Wani b atan basira ne ya d ebeni na dank a amanan dukiyar nan hannun Tasu u.

Badi a tai tsaki  Yo tsaban kina sauri mana a kauda shago kar ya shiga jinyar Abba ko Umman su Ummul ta dawo amsan hakkinta da na yaranta..

Mama taci gaba da safa da Marwa  A a Tasu u bazai tab a min wann gangancin ba. Wllhi akan kud in nan sai na cajesa daga hula har takalmi ba abinda ya shalleni ehe. Bayani d aya na sani na kud ad ena.. Ta kuma duban Badi a  Ki sake kiransa nace.. Ungo kirasa da nawa wayan..!

Badi a taja dogon tsaki tana mitan Mama ta isheta.

Wasu nurses suka fito suka tambayan iyalan Malam Isubu. Mama ko takansu batabi ba ita dai damuwarta kud inta. D aya nurse d in da ya ganesu Ya k araso yana fad in  Hajiya ashe kuna nan. Muna can munata nemanku a ward.

Mama wacce gaba d aya take a daburce ta dubesa a harzik e tace  Toh gashi ka ganmu ai me akayi..?

Nurse d in ya d an tab e baki ganin yanda ta hayayyak osa  Dama wasu magani da drip za a saya shine akace a sanar daku..

Bai kai aya ba Mama ta katsesa  Da uwar me za a sayi maganin inyi.. Kai kaga mun maka kalan masu bada kud i.? kuje ku masa abinda zaku iya mu nan bamu maganin k wandala ehe..!

Ta dawo kan Badi a tana fad in ko batir d in wayar mutuwa zai kar ta fasa kiran Tasu u.

Nurse d in Ya kuma bud e murya yace  Ku fah muke jira Dr zai iya shigowa round..

 Kai bana son fi ili wai bakaga tashin hankalin da muke ciki bane?

Nurse yace  Wann matsalar ku bari idan Kun bar nan sai ku warwareta dan Allah. Yanzu dai ku sayi abinda aka ce ku saya dan a samu a ceci rayuwar majinyacin.

Muryar Badi a yaja hankalin Mama alamun ta samu Tasi a waya. Badi a ta juyo tana duban Mama da murmushi saman fuskarta  Ki kwantar da hankalinki Mama barin saka miki shi a speaker kiji.

Daga d aya b angaren Tasi u Wanda daga jin yanda yake kana iya sauraran k aran ababen hawa alamun yana bisa kwalta kenan. Fad i yake cikin d aga murya irin na Wanda ke bisa abin hawa musamman babur  Mama ina bisa hanya ne shiyasa bani iya d aga kiran. Gasu na karb o su.. Go slow ne ya tare mu kinsan ana fashe fashe sabida k ara manyan titi.. Eh gani na ma kusa k arasowa kenan.

Mama saida ta silale ta zauna dirshan a k asa tana dafe k irji  Yauwa yanzu naji batu Ta marairaice murya tunanin yanzu kud inta na hannun Tasi u dole ta bisa a sannu kafin ta dafesu  Ayya ayya Tasu u na.. Sannu da k ok ari kaji d an albarka.. Muna nan muna jiranka.. Allah iso da kai lafiya.

Nurse da ya zuba ma sarautar Allah ido ganin Ya zo masu da muhimmin batu amma hankulansu na kan wani abu daban yace  Amma Hajiya kun saurari abinda na fad a kuwa.?

 Mun saurara mana. Meye.? Ko so kake mu maimaita maka ka tabbatar mu ba kurame bane.

Ya d an girgiza kai  Hajiya gaskiya ina ganin girmanki kuma ni aikina nake k ok arin yi a nan. Ya kamata ki dinga tantance kalamanki.

Mama ta tab e baki dan a halin yanzu hankalinta ya kwanta taji labarin kud ad enta  Kaga k aramin likita wllhi fah saidai ku k yalesa mai aukuwa Ya auku dan nan da kake gani bamuda abinda zamu bada.

Nurse d in yace  Ban gane mai aukuwa Ya auku ba. Ya kukeso ayi yanzu.? Kunsan cewa kud in kwanakin da aka biya masa ma sun kusa cika. Kwanan nan za a buk aci k arin kud i musamman duba da irin jinyar da majinyacin ke fama dashi. Jinya ne babba kuma mai cin kud i..

Mama ta dubesa galala  Au dama ba gwamnati bane Ke biyan kud in jinyar nasa.? Dan ita a nata zaton alfarmar gwamnati Abba ke ci tinda dai tasan tin zuwansu kwabo ba a amsa wajensu ba.

"Nurse ya girgiza kai cikin rashin yarda gajeriyar dariya na neman kufce masa  Mama kenan, a K asar mu ta gado kike fah ko kin mance ne na tuna miki. Nothing is free in this country. "

Mama ta tab e baki  Kai kasan me kace. Ni dai na fad a maka gaskiya bamu maganin fici ehe.

Nurse yace  Amma ina wann mutumin da yai settling bills d inku yake.. Ina nufin ina mutumin da ya biya kud ad en..?

Mama ta dubesa da mamaki  Wane mutumi kenan..?

 Wanda na ganshi nan ya rako wasu  yanmata biyu.. Ina tsammanin  ya yan majinyacin ne..

Mama tace  Toooh.. K irjinta na bugawa  Kar dai ace wai su Ummul kake nufi. Uban wa ya biya kud in toh..?

Badi a ta katseta  Wann mutumin mana da suke tare wanda har Azeema tace Miki saurayin Ummul ne kuma shine yaje yayi belin Khulsumu a police station. Ta tabbata dai saurayin Ummul ne.

Mama ta dafe k irji cikeda mamaki. idan har Wanda aka ambata da saurayin Ummul ya biya tulin kud ad en nan watau mai kud i kenan wann karon Ummul ta samo. Toh wllhi bazata saku ba wai bindiga a ruwa. Yanda sauran batun auren suka lalace shima wann haka zai lalace yabi iska. Bari ta gama da batun kud ad enta ta tabbata sun shiga lalitarta. Ya zama dole ta bincika tasan waye shi daga ina yazo dan tasan yanda zata b ullo ma al amarin amma bazata zuba ido Ummul ta k are a gidan maik o ba dukda wann canfi da aka mata.

Nurse yace  Ku nake sauraro.

Mama tace  Yo ina kaw zaku gansa. Dama yaran karuwai ne yaje yayi abinda zaiyi dasu ne shine ya biya ladan jinyar ubansu. Sai ku jira su zo su baku dan nasan yanda Uwarsu ta tafi nata yawon suma ba zama zasuyi ba qila sun had e a bayan gari. Ku jira Zasu zo so su kuma biyanku wasu kud ad en. Idan Har kuma basu samu ba sai Malam ya jira har ta Allah ta cimmasa. Idan kuma lokacinsa baiyi ba har wa adin kwanciyar sa saman gadon asibitin ya cika sai a maidasa can gida saman katifarsa ya cika a can.

Badi a tace  Ahtoh magana kenan..

Mamaki ya cika nurse d in. Wai dama a duniya akwai mutane irin haka. Shikam yasha cin karo da mutane daban daban a aikinsa na asibiti amma bai tab a cin karo da mutane irin wad ann ba. Girgiza kai kurum yai yasa kai ya shige zuciyarsa fal tausayin Malam Isubu.

**

Abuja.

A fusace Daddy Ke dubanta  Wai meyasa kike son b ata mun rai ne Kwaise. How many times do I have to tell you this.. Duk abinda ya danganci wann D an naki bai shafeni ba..

Mommy ta soma girgiza kai  Why.? Meyasa..? Aliyu D anka ne Engr.. He s your flesh and blood.. Meyasa kake masa irin wann k iyayyar haka..? Su waye suka shiga tsakaninka dashi har haka..?!

Cikin tsawatarwa Daddy ya katseta  Har sai kin tambaya waye ya shiga tsakani na dashi Kwaise.. Meyasa a kullum kike son tuna mun baya.! Kinfi kowa sanin wann D an naki only reminds me of my sin. He reminds me nothing but my past Kwaise. Kuskure mafi muni da na tafka a baya& All because of you and your selfishness..!

Mommy na hawaye take girgiza kai ganin hannun mijin nata Har na rawa yake nunata. Cikin kuka take furta  Ni ce na maka laifi ba Haidar ba. Amma ka daina hukunta Haidar kan laifin da baida masaniya akai.. Muryarta yaci gaba da rawa  Haidar Ya taso cikin k unci da tsangwama. A baya Nayi zaton izuwa wann lokacin zaka k aunace sa kuma ka mance komai sann ka zama mahaifi a gareshi kaman yanda ko wani uba yake. He s your only son our only son& 

Katse ta yai ta hanyar d aga mata hannu  This family can never be like a normal family Kwaise.. Kinfi kowa sanin haka. Farin ciki bazai tab a wanzuwa cikin wann ahalin ba..

Cikin rawar murya tace  Nayi zaton ka yafe mun.?

Ya jinjina mata kai  Na yafe miki amma idan Har zanga d anki sai na tuna Kwaise!

Mommy ta girgiza kai hawaye na kuma zubo mata. Tabbas an shiga tsakanin D anta da mahaifinsa. Dan idan ba aikin asiri ba ba yanda za ayi Ya d auki laifinta Ya d aura kan d anta Wanda baida masaniyar laifin har yai masa irin wann k iyayyar.

Ta kuma share hawayenta  Meyasa kake zaune damu ni da Haidar.. To build your image a duniyar kasuwancinka.? Taci gaba da huci  Fine.. Mun cika maka wann burin.. Kanada iyali da duniya zata d aga ido ta kalla ta kirasu da ahalinka. Amma babu komai cikin ahalin face k arya da k unci.. Nothing is real here..!

 Kwaise.!!! Ya ambaci sunanta cikin d aga murya.

Mommy na hawaye taci gaba  Eh kasuwancinka shine kawai gaskiyarka.. But your family..

 You are right& I only care about my business because it s the only thing that keeps me moving bayan tarwatsani da kikayi years back..!

Ta lumshe idanunta hawaye na kuma gangaro mata. Sai kuma ta sassauta murya  I endured everything.. I even lost my own son without even realizing it. Thinking maybe wataran zaka k aunacesa.. But than& I failed..! I failed as a mother and I failed as a wife..! Kuka yaci k arfinta sanda ta duk a k asa tana mai isarta.

Ta d an d auki lokaci a haka kafin taji hannun Daddy saman kafad

16 / 103