AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   5 / 103

12K to 15K   out of 306.8K words

kubi duniya a sannu rayuwar duka ba yawa ne da ita ba.. Bazan bari ku saka mun ciwon da bani da shi ba..

Murya a sanyaye Umma tace  Kai hak uri Abban Ummul in sha Allah zamu gyara.. Ko Yaya..? Tai maganar tana duban Mama.

Mama ta saci idanun mijin nasu kafin ta aikama Umma harara sama da k asa sai kuma ta juyo da duban nata ga Abba. Tai murmushi Wanda yafi Kama da yak e  Eh in sha Allah zamu gyara mun tuba Kaji Malam..Allah ya baka lafiya.

Jinjina Kai yai yace  Alhamdulillah.. Allah ya ganar damu baki d aya ya kuma had e mana kan ahalinmu ya shirya mana zuri armu.

Gaba d aya suka amsa da Ameen. Abba yai masu izinin tafiya sai kuma ya dakatar da Umma yace ita ta tsaya.

Wani birki Mama taja kaman zata dungura ta juyo tana duban Abba da yace Umma ta tsaya bayan yau girkinta ne.

 Malam ban gane Suwaiba ta tsaya ba.. Ni ce da alhakin abincika yau fah ko ka mance ne..? Tai maganar tana tururi kai kace ba itace yanzu ta gama ce ta tuba ba.

Abba ya murmusa yana ayyanawa cikin zuciyarsa Mata sai a barsu wajen kishi. So tari yakan yi ma Mama uzuri dan kishi Tabbas akwai ciwo. Wani abun yasan zafin kishi ne kawai yake sanyata yi amma Tani d insa tanada halin k warai.

 Magan zamuyi Tani ba wani abu ba.. Abba yace cikin sigan lallama.

Mama ta kad a Kai  Aiho.. Kardai garin dad in zance a zarce a shiga hakki ehe..!

Murmusawa kurum Abba yai ba tareda yace komai ba.

Saida Mama ta fice ya dawo da dubansa ga Umma.

 Suwaiba.. Ya kirawo sunanta

 Na am Abban Ummul.

 D azu a kasuwa mak ocin shago na ke jajanta mun al amarin auren Ummulkhairy.

Umma ta jinjina Kai alamun tana sauraro.

Abba yaci gaba  Bansan ko kin gane shi ba mai babban kanti na kayan masarufi da yake jikin nawa kantin.. Wasu lokutan har rancen kaya yake bani idan na saida na mayar masa uwar kud i hardai jarin nawa ya d an ja baya. Mutumin kirki ne Alhaji Kamilu..

Umma ta jinjina Kai tace  Allah sarki..

Abba yaci gaba  Toh nan dai nake labarta masa al amarin ita wann yarinya nawa Ummulkhairy.. Toh kwatsam sai ya sanar Dani yana so na bashi auren ita Ummulkhairin idan babu wani matsala.. Toooh wato gaskiya banyi garajen amsa masa ba duba da irin abubuwan dake faruwa. Ak alla aure nawa ake sakawa na Ummulkhairy abu baya yuwa.. Sann ko sati ba ayi ba da abinda ya kuma faruwa na amshe lefen shi yaron nan Zubairu. Amma dukda haka bazaka yanke tsammani daga rahamar Ubangiji ba. Ba wann dalilin ne yasa nace ya dakata ba.. Babban dalilina shine sai naji daga bakin  yata idan tana sonsa.. Idan har bata sonsa JINKIRIN aurenta bazai sa na aura mata mutumin da bata so ba.. Sabida shi Alhaji Kamilun lallai lallai ya nuna mun yana son na basa dama kuma Kinga akwai  yar kunya a tsakaninmu& Tooooh dai gaba d aya kaman ya d aure ni ne.. Dan a gaskiya.. Sai ya d anyi Shiru kuma kaman mai nazari  Bana so Ummul taga kaman na tak ura mata da batun aure ne tinda dudu ba a jima da fasa..

Bai kai aya ba Umma ta katsesa  Haba Abban Ummul.. Ta ya ma zakace haka.. Yo har wani lokaci zaa d ibar mata.. Shifa lokaci baya jira. Ka duba sa anninta duk suna d aki daga masu yara uku hudu kai har masu shida akwai sa anninta& Yo ai ko ta gansa ko bata gansa ba tinda har zai rufa mana asiri ya aureta ai shikenan..

"Katseta yai da fad in  A a Suwaiba, JINKIRIN Ummulkhairy ba zaisa na tilasta mata kasancewa da Wanda bata so ba.. Kece mahaifiyarta, ki kirata a d aki a natse ki sanar da ita. Idan tayi na am falillahil hamdu yau da dare sai na d aga waya na kirasa gobe idan Allah ya kaimu sai yazo su fahimci juna.. Alhaji Kamilu mutumin kirki ne kuma yanada matan aure biyu da yara da d an dama.. Ki kira ita Ummulkhairy ki sanar da ita a natse. Idan Sun daidaita kansu shikenan sai ai maganan aure tinda babban mutum ne ba wani Jan lokaci za ayi ba. Hasalima Jan lokacin baida wani alfanu.. "

Umma tai karaf tace  Ai ko gobe ma sai a d aura kawai nidai ta tafi d akinta.. Ta d aga hannu sama tana fad in  Oh Allah na gode maka ni Suwaiba.. Allah maji kukan bawansa mai maida asara da alkhairi..

Girgiza kai kurum Abba yai yana dubanta. Zaman Ummu a gabansa bai d aga masa hankali ba kaman fitinar mahaifiyarta matarsa Suwaiba . Fatansa Allah ya had a Ummul d insa da miji na gari wanda zai kular masa da ita ya kaunaceta tsakani da Allah dama sauran yaransa gaba d aya.

Cikeda farin ciki tamkar wacce aka yaye mata kaf damuwarta na gidan duniya haka Umma ta fito tana k wlla kiran Ummulkhairy.

A daidai bakin farandar d akin Abba ta riski Mama rik eda farantin abincin Abban. Umma tana ganinta ta tsuke Baki tana zancen zuci Wanda sam bata san ya fito fili ba tsaban farin cikin da ta tsunduma ciki  A sirrace nema a bayyana samu.

Rangaji Mama take tana dubanta daga sama zuwa k asa. Kafin tai murmushi mai sauti tace  Ayi dai mai mu gani wai gurguwa da auren nesa. Ta k arashe kaman zata bangaje Umman ta nufi parlorn Abba.

Umma ta tab e Baki ta nufi d akinta cikeda farin cikin abin alkhairin da ya sameta dan yau d in Ji take burinta na gidan duniya ya gama cika.

**

Abuja.

Cikin bacci yake Jin vibrating d in wayarsa na kuma k aruwa alamun wayar ta gaza yin Shiru. Yai k ok arin mik ewa had ida janye Dareen dake kwance saman k irjinsa. Hannu yasa ya d auki wayar dake aje gefen bedside yana ganin

lokaci quart after six na safiya. Lokaci guda ya d anyi relaxing jikin pillow yana k ara wayar a kunnensa yana rage girman idanunsa masu cikeda bacci wanda hasken hantsi da ya soma bayyana ya tilasta masa yin hakan.

 What Hisham. Ya Fad i yana gyara zaman wayar a kunnensa.

"Daga d aya b angaren Hisham Yace  Haidar, Kana Ina ne.. me kakeyi..? "

Da mamaki Haidar yace  What kind of question is that..? What could I been possibly doing at this time..? Bacci nake obviously kafin ka tadani.

Hisham ya katsesa  Have you seen the news..?

 What news..? Haidar yace cikin muryarsa mai cikeda bacci.

Hisham ya furzar da huci  Lallai na yarda kana bacci.. Check your phone ka karanta labarun kasuwanci kaga abinda muka tashi dashi. Daga haka katse kiran yai yayinda Haidar ya shiga shafa wayarsa. Tin daga saman fuskar wayan yake karo da notifications.

"Notification guda d aya ne ya d auki hankalinsa. THE BUSINESS PRESS. Yanda aka rubuta *Top Business Scandal.* Saurin clicking yai ya shiga kan labarin. Abinda ya soma karo dashi a labarin shine hotonsa da mahaifinsa lokacin da ya cakumosa a cikin Kampaninsu yana jijjigasa yana fad in yayi disappointing d insa, daidai wajen akai cutting a video d in Wanda aka fitar da hoton sosai yanda ya rik e kwalan Haidar d in ga jini gefen bakin Haidar. K asan hoton kad an an rubuta kamar haka *Owner of Maitama Builders Engr Aliyu Maitama gets into a physical fight with Son over augment.*"

 Damn it..! This is not happening. Ya furta a hankali. Sauri sauri ya mik e ya shige bathroom dan shiryawa.

Dareen dake baccinta peacefully ta soma bud e idanunta masu cikeda bacci wanda ko shakka babu shirin da Haidar d in keyi ne ya katse mata baccin.

Ta zuba masa idanu tana duban yanda yake komai a gaggauce. Ta saki murmushi zallan k aunarsa cikin zuciyarta. A hankali ta sakalo k afafunta ta sauk o daga saman gadon.

Yana tsaye gaban full length mirror yana k arisa shiri yaji ta rungumosa ta baya had ida matsesa sosai cikin jikinta.

 Good morning.. Ta furta tana mai d aura hannayenta saman nasa ta amshe agogon da yake k ok arin d aurawa taci gaba da d aura masa

 Are you leaving this early..? Tace sanda take kaikaitowa ta dawo ta gabansa.

 I have to.. I need to take care of something.. I ll see you later.. Yace a tak aice yana d aukan wayarsa da mabud in mota

Ta take masa baya ganin zai fice cikin sauri. Ta kamo hannunsa guda  What about breakfast..? Your cool tea is in the fridge.. Tun asuba na had a maka.. The way you like it.. Should I serve you..?

"D an dubanta yai kafin ta girgiza kai  Kar ki damu, I ll be fine.. "

Ta kuma rik e hannunsa  Does that mean ka amince da k orafina ka fasa aje aikinka a Kampanin Daddynka.? Tai maganar idanunta tar akansa.

Ya d anyi still yana dubanta  I don t know& I m not sure.. I.. must go now.. Take care.. Ya k arashe yana shafan b angaren fuskarta guda da tafin hannunsa.

Ta janyo hannunsa ta sumbaci tafin hannun kafin ta sakar masa murmushi tana masa fatan nasara har saida taga tashin motarsa. A hankali ta lumshe idanunta had Ida sauk e ajiyan zuciya kafin ta koma cikin gidan..

ya d auki car keys d insa da wayarsa ya fice a gaggauce.

Yana tafe saman kwalta wayar Hisham amininsa kuma abokinsa a wajen aiki ya kuma shigowa.

 Haidar this is bad.. Very bad.! Abinda Hisham yace kenan koda Haidar ya d aga kiran.

Jinjina Kai Haidar yai

" Yanzu zaka yarda da magana na.. Someone is sabotaging the company.. And trust me, I know exactly how to catch that rat. Shiru yai alamun yana sauraro daga b angaren Hisham."

Hisham yace  Kuma ba yanda za ai ka kamo wann b eran har sai kana aiki da Kampanin. Now more than ever you can t quit your job.. You need to fix this Haidar.. You need to clear your Dad s name.. Bazaka bari sunan Kampanin ya b aci ba..!

 Oh Shut up Hisham..! Ya fad i yana mai katse kiran lokaci guda yana mai k ara gudun motar.

A can gidan mahaifinsa kaw ya tsare mahaifiyarsa ta yanda yake shiga ba ta nan yake fita ba. Ga  yan jarida sunyi chaa a bakin gate suna jiran fitowarsa.

"Yaci gaba da nuna Mommy da yatsa  Call that pathetic son of yours and tell him to fix this mess immediately.. Bayan asaran da zamu tapka sabida shashashancinsa, I won t allow him to ruin my company s image.! Ya k arashe cikin tsananin huci yana mai ci gaba da zagaye katafaren parlorn nasa."

"Furzar da huci Hajiya Kwaise tai, tana mai kuma dialing layin Haidar amma shiru bai d agawa."

Dad ya kuma dubanta  He s not answering right..?

D an lumshe idanu tai had ida mik ewa tsaye  Engr please calm down.

"Ya kuma katseta  Seriously Kwaise..? Are you asking me to calm down.? Ko bakiga babban abun kunyan da wann shashashan d an naki yai bane.. Kwaise, I m a highly respected person. A well known businessman. I have a reputation to protect.. Bazan bari wann d an naki ya ruining d ina ba. "

Izuwa lokacin cikin ta tunzura itama  Aw laifin Haidar kake gani..? Kai bakaga laifinka ba.. Kan wani dalili zaka cakume kwalan d anka a bainar mutane.. Cameras all over ba dole masu Neman ganin bayanmu suyi amfani da wann damar ba.. Yanzu sai ka yarda da maganan Haidar da yace maka akwai mai maka zagon k asa cikin mutanen da ka aminta dasu..

"Katseta yai cikin b acin rai  This is natural in a business world. We ve business rivals and competitors. So ba abin mamaki bane idan sunada spy cikin Kampaninmu.. Amma babban abun takaicin shine yanda muka gaza handling such situations.. And this is all your Son s fault.. He s weak, idiot.. A pathetic loser.. Yana can ya saka mata a ransa.. What do you expect..? "

Ya kuma jinjina Kai yana sakin huci sai yarfe gumi yake kai kace ba sanyin AC ne ke circulating cikin parlorn ba.

Isowar Haidar k ofan gidan mahaifin nasa yai tozali da dandatson  yan jarida. Ai kuwa kaman jira suke suka nufosa suna jefo masa tambayoyi ta ko ina.  Yallab ai Aliyu. Da gaske ne mahaifinka ya tareka da fad a bayan cecekuce da ya kaure tsakaninku cikin Kampanin mahaifin naka..? Engr Maitama ka amsa mana..

Da kyar ya samu ya kutsa cikin gidan sabida tambayoyi da kalaman da manema labaren keta jefo masa.

Yana dosowa parlorn Daddy ya nufesa a zafafe kaman zai shak o sa Mommy tai saurin shiga tsakani cikin k ok arin dannar mijinta.

Sosai yake huci kaman zai kifa k asa yana nuni da Haidar hannunsa har rawa yake.

 You.. You and your entire existence is a disappointment..! Kai kayi kad an ka lalata mun suna da sunan Company.. You better find a way to fix this mess kafin business rivals d inmu su samu abun yawo damu kaji na fad a maka.. Bazan tab a bari bak in cikinka yayi ajalina ba.. I will make sure to cut you off kafin hakan ta kasance.. Yatsanshi na rawa yaci gaba da nuna Haidar  So Kar ka sake kayi abinda zaisa na haramta maka amfani da sunana..! Daga haka sa Kai yai ya haura sama dan a halin yau fita ma bai ganshi ba  Yan jaridu ta ko ina. Dan yasan K iris abokan adawansu na kasuwanci Ke jira. Har yayi step biyu ya kuma juyo ya dubi Haidar da idanunsa suka kad a sukai jazir  Kaje ka sallami mutanen can da ka tara mun kof ar gida.! Yasa kai yaci gaba da haurawa.

Furzar da huci Haidar yai yasa kai zai shige. Dan yasan mahaifinsa bazai tab a sauraransa ba. Momy ta dakatar dashi

 Mom please not now.! Ya katseta da fad in haka.

Cikin rawar murya take furta  What s wrong with you Haidar.. Why are you doing this to us to yourself.. Meyasa ka maida iyayenka Abokan gabanka.. Why can t you open your eyes and see my son.. Your Dad is only trying and struggling to make a proper man out of you..

 Oh really Mom.! Is he really trying to make me become a better person by pressuring me to meet all his expectations..? Muryarsa ya soma rawa sanda yake furta  Na gaji.. Na gaji.. I m fed up with everything around here..! Bai kuma tsayawa sauraronta ba yasa kai ya fice yana haki da huci ga wayarsa da ta gaza yin Shiru. Kira ne keta shigo masa.

Saiga Mommy ta koma gefe tana hawaye. Meke faruwa da rayuwar ahalinta.. Meke damun Haidar.. Dik yanda akai something is wrong a wani wajen.. Zama bai ganta ya zama dole ta tashi tsaye. Da wann tunanin ta nufi nata b angaren duk jikinta a mace kaman dai ba Mommy ba. Mace mai zafi da jajircewa.

Jiki a sanyaye Anisa ta k araso rik eda waya ta mik a ma Mommyn tana fad in  Ammi Ke son magana dake tana ta kiran wayarki bata samu.

Mommy tana amsar wayar ya fashe da kuka tana fad in  Asshe ba lafiya.. Asshe gidana a hargitse yake..

Jin haka yasa Anisa komawa dan ta baiwa  yan uwan waje su tattauna. Sosai hankalinta ya tashi da ganin yanayin Mommy dan tinda take bata tab a ganin  Yaruwar mahaifiyar nata cikin irin wann yanayi ba.

**

KANO

K aton parlor ne mai d aukeda kekunan d inki kusan guda biyar. Yafi kama da wajen koyon d inki.

Wata mata ce da ta d an data a shekare tsaye cikin babban zauren tana duba kekunan.

Ummulkhairy ce ta soma halarta cikin d aliban nata. Dama ita d in da wuri take zuwa kafin lokaci yayi dan ta taimaka da share share da gyare gyare.

Sallama saman bakinta ta shigo.

Matar ta fad ad a murmushinta  Wa slaikissalam uwar alkhairi. Dan haka take kiran Ummul d in a akasarin lokuta.

Ummulkhairy ta risina ta gaidata. Ta amsa kaman ko yaushe da sakin fuska  Uwar alkhairi kece dai kullum akan gaba kina masu wayo kina

5 / 103