AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   35 / 103

102K to 105K   out of 306.8K words

da  Shadow shadow. Looks like kana biye damu dik yanda muka je. Just like your name.. Before you ask. We are here on our third honeymoon. Oh! I forgot to put my cellphone on DND mode.

Muryar Haidar ta sinkayo daga bayanta  Who is Shadow.?!

Zuciyar Dareen yai wani irin tsinkewa tamkar statue haka ta kafe ko motsawa ta kasa.

SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!*

*26*

*©þSameena Aleeyou& *

Ko motsawa ta kasa.  Yan hanjin cikinta tuni Sun kad a. A hankali ta zame wayar daga kunnenta bayan ta katse kiran. Muryarsa ta kuma sinkayowa Ya daki dodon kunnwanta a karo na biyu.

 I think I ask you a question. Who were you talking to on the phone. Who the hell is Shadow.?!

Juyowa tai tana dubansa yanda ya tsareta da rikitattun idanunsa. Alamun yana jiran amsarta.

Abinka da gogaggiya sai tai murmushi  Shadow.. Inuwa.. Asalin sunansa Inuwa.. He s.. He s my cousin.. My cousin that I told you about lokacin auren mu.. Ka tuna..? Ta k arashe tana tsaresa da ido.

Kansa ya soma juyawa. Sai yaji ya soma wani tunani wanda bazai iya cewa ga specific abinda yake son tunowa ba. Sai ya zama lost and confused. Dan shi bazai iya cewa ga abinda ya faru lokacin auren nasu ba. Iyakacin abinda yakeda tabbaci akai shine sunyi aure. But baya iya tuna komai in detail.

"Dareen taci gaba  Cousin dina da na baka labari. Wanda yake so na ni bana sonsa. Because my heart belongs to you tun kafin mu had u. Ta kuma murmusawa  Yaron Uncle dina. Shine ya kira wai mu gaisa har kaji ina kiransa Shadow ina kuma ce masa ya daina damuna because ina tareda lovely husband d ina, enjoying our third honeymoon. Ta k arashe tana d aura duka hannayenta saman kafad unsa makirin murmushi saman fuskarta."

Kansa ne Ya kuma Ji ya cunk ushe sai ya rasa wane tunani yake guda d aya. Wani abu yake son tunawa amma bai sani ba. Ya kuma kasa tuna komai. Tinda Dareen ta d aura hannayenta saman kafadunsa sai ya kuma Ji ya zama confused. Sai ya zama baya tunanin komai cikin kwakwalwarsa baya kallon kowa cikin k wayar idonsa sai ita.

Dareen ta karkatar da kai tana dubansa har lokacin murmushin ne saman fuskarta  Shall we go now.?

Girgiza mata kai yai cikin rashin fahimta  To Where.?

Ta kuma murmusawa tana mai tallafo fuskarsa da tafukan hannayenta  You seem to forget things easily nowadays My love.. Har ka mance. Jiranka nake ka fito mu tafi Spa and fitness.. I thought kace zaka gym.

Shiru yai kaman mai nazari sai Ya karisa saman drawer ya d auki wayarsa had ida jefata cikin aljihun wandon three quarter dake jikinsa.

Har ya soma takawa ya juyo ta dubeta  Don t answer his calls again. Ya fad i cikeda gargad i.

Saurin jinjina masa kai tai  I m blocking his number right this instant.

Baice da ita komai ba yasa kai ya shige ba wai dan ya aminta da labaran da ta basa ba sai don Ya k asa tuna komai.

Bayansa tabi da kallo murmushin saman fuskarta  Bazaka tab a sanin waye Shadow ba Haidar.. Shadow has been shadowing you for a long time now.. Maybe tun kafin na shigo rayuwarka. But one thing I m sure of shine Shadow made a huge mistake da har ya bari na shiga rayuwarka. Because I ll protect you from him. Kuma bazan tab a bari ya cutar dakai ba for as long as we are together.. Ta k arashe zancen zucin nata tana take masa baya dan tuni Haidar ya fice.

Motsa jiki yake da iyaka kuzarinsa da k arfin sa ko zai iya tuna wani abu amma ya kasa. Why couldn t he remember a thing.? Meyasa yake ji kaman brain d insa na barazanar tarwatsewa.? Meyasa yakeji kaman chest d insa ya masa nauyi. Meyasa yakeji like he s lost in his own world. Rintse idanunsa yai yana kuma tuk a keken motsa jikin da iyaka k arfin sa.

**

Abuja..

Suna fitowa Leenah ta mik e a birkice tana duban fuskar k awarta da ya koma jazir abinka da farar fata. Fuskar tayi rod i rod i duk tayi jazir kaman k osan da ya sha wuta cikin mai.

 OMG.! Girl.. What happened to your face& ? Leenah tace tana zaro ido waje.

 Just shut up Leenah..! This is all your fault.. Anisa tace tana sakin huci. Lokaci guda tasa kai ta nufi mota.

Daidai lokacin Ummul ta fito fuskarta ta k ara kyau sai wani shek i na musamman da fuskar nata keyi. Sosai gyaran ya amsa fuskarta.

Leenah ta saki baki tana duban Ummulkhairi.

 But..But.. Wait.. How s this possible..? Leenah tace cikin rashin fahimta.

Murmushi Ummul ta sakar mata kafin tasa kai ta shige ta nufi mota.

Leenah tabi bayan k awarta Anisa cikin sauri tana tambayarta me Ya faru.

"Juyowa Anisa tai tana dubanta da toyayyan fuskarta  You know what Leenah, I don t want to listen to you. Just get in the car and let s get out of this place..! Ta k arashe tana furzar da huci had ida rausayar da ido."

Saurin rik ota tai ta dawo da ita baya  Hey hey easy.. Wai mai ya faru ne.. For as far as I know ba ma Ke na zuba cream din ba. How did it end up on your face..?

Anisa ta rausayar da ido  Because She outsmarted you Leenah.. Isn t it obvious..? You are so useless.! Ta k arashe cikin huci tana juya ido.

 Hey easy don t take it out on me. She s the culprit. She switched the bowls. Cewar Leenah tana nuni da Ummul dake zaune cikin mota.

"Anisa ta rausayar da ido  That s because you are stupid. You know what Leenah, I feel like punching your ugly face. "

Leenah ta shafa fuskarta  Hey don t be mean. I spent so much on this beauty.. Ta k arashe tana Shafa fuskarta da murmushi.

"Rausayar da ido Anisa tai tana sakin huci. Zata shige Leenah tai saurin kamo hannunta.  Girl, if she can do something terrible like this, with that innocent looking face. Then believe me she s dangerous.. She s a wolf in sheep s clothing. You need to eliminate her out of the picture.. As soon.. As possible..! Ta k arashe tana firfito da ido waje."

Tururi kurum Anisa take  Believe me Leenah. I won t play fairly this time around..She wants battle? then I ll give her war..Just watch and be amazed.! Ta k arashe tana sakin huci.

Leenah ta girgiza kai  You need to change your ways Neesa. Ki fito mata a musulma. Make sure you win her trust first before you make your move.

Anisa ta rausayar da ido  I don t think I have that kind of patience. I can t stand her one bit.

 You have to Neesa. You must put up with her. That is idan har kina so ki kawar da ita cikin sauk i.

Anisa tai Shiru without saying a word.

Murmushi Leenah ma ta saki amma sai murmushin ya rikid a Ya koma dariya dan sosai fuskar Aminiyar nata ya bata dariya yanda ya sauya halitta lokaci guda.

 What s got you laughing..? Anisa ta tambaya a hasale.

Leenah ta soma k unshe baki tana nuni da fuskar Anisa  Seriously Girlfriend you look like a monster. Ta dubi Ummul da ko kallon yanda suke batayi tace  Ita kuma makirar tayi kyau jibi yanda take glowing.. Awwn I m jealous of her skin.. Ta k arashe tana dafe fuska.

Tsawa Anisa ta darara mata tana fad in ta shige mota su tafi ko ta tafi ta barta nan wajen.

" Oh hey. Easy girl, I m just joking.. You are still more beautiful than her. Leenah ta fad i tana take ma k awarta baya."

Haka suke tafe Mota Leenah na kuma tunzurata da surutanta har dai aka sauk e Leenah a destination dinta shak e da kayyayakinta da sukai shopping.

Mota ya rage saura Ummul da Anisa. Ba mai ce da kowa komai har suka iso gida.

Ummul ta dubi Anisa Tai mata godiya wann murmushin Wanda sam Anisa bata k aunar gani saman fuskarta.

Suna shigowa cikin gidan suka tadda Mommy zaune da wasu mata masu sanye da rigar kampani na tailoring a first parlor.

Ma aikatan gidan da kusan ko yaushe suke cikin shiga ta uniform suka soma amsan kayyakin hannunsu suna masu sannu da zuwa cikeda girmamawa had ida ladabi.

"Ita dai Ummul duk ba wai ta Saba da irin wad ann abubuwan bane. Musamman idan taga manyan mutane suna girmamata suna gaisheta koda kuwa masu aiki ne. Sam batajin dadin irin abun. Sosai abun ya bata mamaki da safe kafin su fita yanda Anisa ta dinga masifa ma babban mata dake kitchen wai dan kawai bata kawo mata abinda ta buk ata kan lokaci ba. Tana jin wacce ta amsa Kayan hannunta tana tambayarta  Ma am, should I take these to your section..? Kasancewar akasarin ma aikatan gidan hiring d insu akai daga registered company na masu aikace aikacen gida da Office ba hausawa bane ba sosai suke hausa ba."

"Sai Ummul tai sakare tana dubanta. Ba wai dan bataji mai tace bane, kawai sabo ne da irin rayuwar da Sam batai ba. Rayuwar da gaba d aya ya banbanta daga irin rayuwar da ta girma ciki tai wayo ciki."

Mommy ce ta bata amsa da fad in ta kai mata su side dinta. Wato b angaren Haidar.

Maid din ta amsa da  Yes Ma. Cikeda risinawa.

Mommy ta k araso ga Ummul wacce tuni ta risina tana gaisheta.

Bata amsa gaisuwar ba sai kamo hannunta da Tai tana fad in suje ga masu d inki zasu gwadata su d auki measurement dinta. zasu d inka mata atamfofi da laces daidai size d inta.

Anisa ta saki baki tana kallon ikon Allah musamman da ta ga babban tailoring company da Mommy ta kira Wanda a garin ma ba ma kowa suke d inki ba sai ka cika elite. Ko ita kanta Anisa basu tab a mata d inki ba sai gashi wai zasuyi ma wann kucakar. Zuciyar Anisa ta kuma tunzura. Tsanar Ummul ya kuma cika mata zuciya. Ko ta kanta fah Mommy bata bi ba balle taga abinda ya samu fuskarta. Cikin k unan rai ta nufi d aki tana tuanin sabon hanyar da zata bi ta b ullo ma Ummul dan bata tunanin zata iya hak uri da Ummul d in kaman yanda Leenah ta bata shawari.

**

Kano&

Da kyar Mama ta amince ta fito wajen ganawa da mutane yanda Umma ke jiranta a nan police station da akai detaining dinta.

Umma ta zuba tagumi tana duban Mama yanda ta jeme ta rame duk tsawo da jiki irin na Tani duk ta lalace cikin k ank anin lokaci ta zama abun tausayi.

Banda Uwar harara Mama bata aika mata komai.

 Kinzo ne kimin dariya Suwaiba.? Kinzo ne dan kiji dadin ganina a k ask ance..? Muryar Mama ya soma rawa  Ki amsa min Suwaiba. Kinzo ne dan ki min dariyar abubuwan dake faruwa dani..? Ina nufin  Ya yana Sun jirge gida.

Badia miji ya gudu Ya barta ita kuma Azeema miji ya koreta.. Ni kuma gani a nan cikin k ask anci da tozarci.. A yayinda ke Allah ya cika miki burinki. Ummul d inki tayi aure.. Aure na gani a fad a irin Wanda nawa  ya yan basu samu ba.. Mutanen unguwa sun bar nunaki da baki sun koma nuna ni nida nawa  ya yan.. Mijinmu kuma yanzu na k ark ashin kulawarki.. Ya zama naki ke kad ai.. Haka ne Suwaiba..? Ta k arashe kuka na b alle mata yayinda Umma ma kukan take. Cikin zuciyarta cewa take Allah sarki Yaya baki san tashin hankalin da kike ciki mai sauk i ne gaban Wanda nake ciki. Baki san wani irin aure Ummul Tai ba. Baki san cewa Aure ne mai k ayyadadden wa adi ba. Baki san Aure ne da aka k ullasa bisa yarjejeniya na tsawon watanni uku.. Aure mai gib i auren da zan jima ina d an dana sanin yi ma Ummul irin wann auren Har tsawon rayuwata. Sann Mijinmu banida ikon taka yanda yake.

Muryar Tani ya kuma katseta cikin karaji sanda ta soma janyo Umma tana fad in  Tashi ki tafi Suwaiba. Ki tashi nace ki tafi kuma kar ki sake takowa yanda nake.!

Kuka Umma take tana girgiza kai  A a Yaya.. Dan Allah ki saurareni.. Wllhi ko d aya banzo nan dan abubuwan da kika zayyano ba.. Yaya ki saurareni.. Sai Umma ta rungume Tani tana kuka.. Su duka biyun kuka suke Wanda yafi kama da kukan nadaman rayuwa.

Mama ta fincike jikinta daga rik on da Umma tai mata. Zata sa kai ta shige Umma ta kuma rik o hannunta  Yaya dan Allah ki saurareni.. A halin yanzu bamuda kowa sai mu biyun..

Mama Tani ta goge hawaye da bakin zaninta Wanda yai duk un duk un  Yayane Suwaiba..? Ki sanar Dani yayane..?

Umma ta goge hawayenta da bakin mayafi  Yaya yanzu ba lokaci bane da zamu rik e juna abokan gaba. Lokaci ne da zamu fahimci dukkanmu masu kuskure ne.. Kuma Allah yana sonmu da ya nuna mana kura kurenmu tun a nan gidan duniya.. Saura ya rage namu mu d auki darasi ko mu bijire.

"Jikin Tani ya kuma yin sanyi wasu hawayen na zubo mata yayinda Umma taci gaba  Yaya babban abinda ya jefa mu cikin halinda muka tsinci kanmu shine son kanmu, rashin tawakkali da yin abu dan mu burge mutane Wanda Har yasa mun mance su waye mu. Mun mance auren mu, mun mance  ya yanmu da Allah ya dank a mana amanarsu. Mun mance mijinmu da yakeda girman hakki akanmu.. Sabida son zuciya irin namu.. Mun mance mu masu kiwo ne kuma za a tambayemu bisa abinda aka bamu kiwo.. Yaya duk mun mance wad ann mun saka son zuciya a farko.. Wanda shi ya kai mu ga halinda muka tsinci kawunanmu. Ta kuma jinjina kai tana hawaye  Watak ila Ummul tayi aure.. Amma ba irin auren da naci mata buri ba.. Dije ta rabani da Khulsum kaman yanda ta rabani da mijinmu.. Nida ke bamuda wani maraba Yaya. Yanda kike rufe a nan babu walwala nima a b angare na haka take.. Kullum ina kulle ne cikin d aki Babu walwala. Ta kuma share hawayenta yayinda Tani ta katseta  Wani irin aure ne Ummul Tai Wanda baki ci mata buri ba Suwiaba.? "

Tambayar da ya haifar ma Umma fad uwan gaba. Koda Ummul AUREN WATA UKU Tai bazata so ta sanar da Tani ga irin auren ba. Hasalima bazata iya ba. Batada wann k warin gwiwar.

Girgiza mata kai tai  Ki yarda dani Yaya na tapka babban kuskure.. Tai maganar cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka.

Mama ta jinjina kai  Na yarda da duka abubuwan da kika fad a Suwaiba.. Mun tapka kuskure.. Kuma idan bamu had e kawunanmu yanzu ba bazamu tab a k wato mijinmu daga hannun Dije ba. Tazo Har nan ta min d iban albarka ta kuma jaddada min tinda naci amanar d anuwanta dake kwance nida fita a gidan yari sai Randa jakin Baba yayi k aho. Zata tabbata ban samu wani k ofa da zan tsira ba. Sann yarana sun guje ni. Salima ce kawai ke zuwa nan ta dubani. Amma Azeema da Badia Wanda nake gark ame nan sabida su sun wofantar dani Suwaiba.. Ta kamo hannayen Umma  Suwaiba dan girman Allah ki taimaka min kafin a tafi Kotu. Sunce cikin satin nan za a shiga Kotu da mutumin k auye mai kudi. Dan girman Allah Suwaiba ki taimaka ki nemo kud d en nan a fitar dani.. Naga Sirakan Ummul masu hannu da shuni ne. Ki taimaka min Suwiaba ko wajensu kije ki nemo kud ad en nan ki fitar Dani a nan.. Ta k arshe tana tsare Umma da ido. Zuciyarta na tabbatar mata hanyar da zata bi kenan ta samu ta fita daga wann tuggun. Ta nuna ma Suwaiba

35 / 103