AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   84 / 103

249K to 252K   out of 306.8K words

*AUREN WATA UKU..!*

*55*

*©þSameena Aleeyou& *

Officer yana hango su Haidar yace  Yauwa Hajiya.. Ki adana duk wann magiya da kike. Gasu nan sun iso su yafi cancanta ki roka ba mu ba. Ya k arada barkanku da isowa.

Zuciyar Hajja yaci gaba da harbawa daga nan yanda take tsaye gaban kanta.

A hankali Daddy ke takowa kusan matar yana jin bugun zuciyarsa na k aruwa. A b angaren Hajja ma hakan ce ta kasance. Ta kasa koda motsawa balle ta waigo. Addu a kawai take cikin zuciyarta Allah Ya kawo mata da sauk i. Ji take tamkar numfashinta zai bar gangan cikinta haka nan k afafunta tamkar bazasu iya d aukanta ba. Tana jin officer

yana fad in  Ga mahaifyarsa nan tun safe take mana magiya a nan.. Tak i barinmu mu huta.. Cewa take lallai lallai sai mun bata belin D anta.

Haidar ne ya katse D ansandan da fad in  Idan D anki nada lauya kuna iya gabatar dashi k arshen gata da zaki masa kenan. Dan sai nayi sharia da D anki with every means and resources da nake dashi.! Ya k arashe yana aika ma Hisham dake tsare cikin cell mugun kallo kaman zai shak o sa.

Har lokacin jikin Daddy a matuk ar sanyaye yake dan matar tak i juyowa ta dubesu Har wann lokacin. Sai Ya d anyi gyaran murya yace  Sannu Baiwar Allah.!

Zuciyarta taci gaba da harbawa tana sanar da ita  Bakida sauran zab i da Ya wuce ki fuskanci baya Fannah. Komai yazo k arshe.. Yau dai gaki ga Aliyu Maitama.. Ki juya ki fuskance shi.. Dole ki juya koda zaki tuna masa bayansa da ya k yamata. Just turn and face the reality.! Lumshe idanunta Tai hawaye suka gangaro mata kafin ta soma k ok arin waigowa cikin wane irin yanayi.

Daddy ya daskare nan wajen. Ya kasa gaskgata abinda yake gani. It s her.. It s really her& Ta ya zai mance kamanninta bayan ya shafe tsawon shekaru yana nemanta.? Ta Ya zai mance wann fuskar nata koda ace sanin k uruciya yai mata. Fannah..! Fannah ce.. Fannah matarsa da ya d aukar ma Marigayin mahaifinta alk awarin rik eta bisa amana. Fannah da Ya datse igiyan Aurensu da jaririn cikinsa cikin jikinta. Cikin da Ya fidda shi daga cikin ahalinsa tun kafin ya shak i iskan duniya. Fannah da Ya tura fursuna da jaririn cikinsa. Cikin tsananin rawar murya Daddy ya furta  Fann.. Fannah..!

Sai tai bursting cikin kuka ba tareda ta iya furta komai ba.

Haidar ya dubi Daddy cikin tsananin shock sai ya kuma dubi matar. Ya sake duban Daddy da mamaki  Fannah kuma..?! Daddy& Fannah naji kace..?! Ya kuma girgiza kai kad an cikin rashin fahimta ko rashin aminta  Fannah.. Your exwife.. Matar da.. Matar da Mommy ta jima tana nema..? Daddy ita ce wann..?! Ya k arashe yana nuna Hajja cikin tsananin shock.

Daddy yaci gaba da jinjina Kai yana dubanta. Har lokacin cikin tsananin shock shima yake  Eh Haidar..! Ita ce.. Ita ce Fannah.. Matata..! Matata da muka rabu tsawon shekaru na kuma nemeta ban sameta ba.!

Daga nan cikin cell Hisham ke girgiza kai fuskarsa na nuni da tsananin mamaki yake furta  Hajja.. Hajja meye nake ji haka..? Meye suke cewa haka..?! Ya dubi Haidar Har lokacin da mamaki samar fuskarsa tamkar gaske  Meye nake ji haka..? Ta Ya mahaifiyata ta zama matar mahaifinka..?!

Sai sann Daddy yakai dubansa ga Hisham zuciyarsa na tsananta bugu. Bai san sanda ta soma takawa ya isa har gaban k arafunan cell da Hisham ke rufe ciki. Daddy ya k ura masa ido without saying a word. Su duka biyu shida Hisham kallon juna suke cikin ido.. A hankali Daddy ke bin Hisham da kallo k walla tab idanunsa tin daga fuskarsa har izuwa k afafunsa yanda yaga k afafun Hisham d in Sun jeru da nasa k afafun suna kallon juna. Sai Daddy ya k ura ma yatsun k afafunsu kallo. Babu abinda ya raba k irar halittar k afafunsa da na matashin. K wallan dake kwance cikin idanun Daddy suka d igo suka sauk a saman k afan Hisham. Sai Daddy ya juyo yana duban Hajja dake kuka sosai shid in ma hawaye ke gangaro masa. Yana dubanta yake nuni da Hisham yatsarsa Har rawa take  Is.. Is he my son..? Shi ne D ana.. da kika tafi yana ciki..!

Sai Hajja ta kuma fashewa da kuka ba tareda tace komai ba.

Cikin wane irin yanayi Hisham ke girgiza kai yana duban Hajja. Ya tamke k arafan cell sosai yana kuma girgiza kai mai cikeda nuna rashin amincewa  Hajjah.. Mai nake ji haka..! Mai haka yake nufi..? Mai Mahaifin Haidar yake cewa..? Hajja mahaifin Haidar .. Shine mahaifina..?

Har lokacin ta kasa cewa komai sai kuka yayinda Daddy yaci gaba da duban Hisham hawaye naci gaba da gangaro masa.

Haidar da yai mutuwar tsaye yana duban abin al ajabi cikin wane irin yanayi yake girgiza kai  No.. No.. No way.. This can t be.. No this can t be happening..?

Hawaye suka ci gaba da gangaro ma Hisham. Cikin wane irin yanayi yake furta  Hajja please answer me.. Is he my father..? Da gaske shine mahaifina..? Hajja shekara da shekaru ina tambayarki ina mahaifina..? Ina danginsa.. Ce min kike ya mutu all these years.. Ce min kike baida kowa baida dangi.. Hajjah.. Ta Ya mahaifin Abokina Ya zama mahaifina..? Hajja ki sanar Dani dan Allah.. Hajja zuciyata tana nauyi.. Dan Allah Ki sanar Dani bazan iya d auka ba.!

Hawaye ne ke ci gaba da gangaro ma Daddy yai saurin shigar da hannunsa cikin k arafan cell d in Ya tallafi fuskar Hisham dake kuka sosai. Cikin rawar murya Daddy ke furta  My son.. My son.. You really are my son.. I m your father.. Your father is alive.. He s very much alive.. Mahaifinka na raye D anah.!

Sai Hisham yai bursting cikin kuka yayinda Haidar yaci gaba da dubansu cikin tsananin shock.

 Yansandan ma duk mamaki da al ajabi ne Ya cikasu. Kowa a wajen mamaki yake. Sai babba cikin  yansandan ya fito yana gyara d amararsa yace  Inaga an sami rashin fahimta a nan..! Da alama rikicin na cikin gida ne.. Inaga bai kamata mu bar wann k araffan su zama shamak i tsakanin D a da mahaifi da suka shafe shekaru basu tare. Ya k arashe yana mai bud e cell.

Kaman jira Daddy yake sai Ya shige Har cikin cell d in Ya rungume Hisham sosai cikin jikinsa.

Girgiza kai kurum Haidar yake yana duban Daddy da Hisham yana jin tamkar dai duniyar na juya masa. Ya kasa yarda da abinda idonsa ke gani.. Ta Ya mutumin da yaci amanarsa zai zama D an mahaifinsa.. Ta Ya zai soma kiran wann bak in k umurcin D anuwa. Just what is this.? Meye yake faruwa haka.? Bazai iya jure tsayuwa nan wajen ba. Bai san sanda Ya fice daga wajen cikin wane irin yanayi ba.

**

A can asibiti kuwa an rasa gwani wajen tarairayar sabon jariri da mahaifiyarsa tsakanin Mommy da Mama Tani. Dr ne Ya shigo ya duba jariri da mahaifiyarsa nan yake sanar dasu a ranar zaayi Sallama. Mommy ta kuma daukan jaririn ta mak ale shi cikin hannunta tana fad in zasu fice lambun dake bayan d akin Ya samu vitamin d in dake cikin hasken ranar hantsi a cewarta.

A wasa Mama Tani ke fad in su dai basu saba da jegon turawa ba. Jariri a d aki yake har yai kwanaki bakwai.

Mommy ta murmusa tace gwara dai su fice taji dumin mai gidanta koda na dan lokaci ne tinda gashi har zaayi Sallama.

"Sai jikin Mama Tani Ya d anyi sanyi Har taji ba dadi dan ta kula sosai yaron ya shiga ran Kakar tasa gashi Haidar da Ummu basu tare balle ta Sami kusanci da yaron. Sauken ajiyan Zuciya Mama Tani tai tana addu an samun maslaha a al amarin ma auratan cikin zuciyarta. Musamman idan ta tuno wani rikicin da suka baro gida wato Abba. Ta maido da dubanta ga Ummul bayan Mommy ta fice tace  Yauwa Ke Ummu, nace ba.. Kinga dai a halin yanzu ke uwa ce.. Abinda aka sani ga uwa kuma shine sadaukarwa.. Ummul inaga tinda Allah yasa kin haihu lafiya sann yanzu rabo Ya tsaga tsakaninki da yaron nan Aliyu.. Bakiga yanda Ya shiga damuwa da tashin hankali ba sanda baki nan, yaro mai k aunarki ga dattaku da sanin yakamata ba irinsu mijin Badia Tasi u barawo da mijin Azeema Habibu gantalalle. Ni inaga zaifi kyau a maida aurenku tinda ga rabo a tsakani.. Yaro Ya girma tsakanin iyayensa biyu yafi.. rabuwar sai dole. Idan Har ke d in kika sauko daga dokin fushi kika amince a maida auren Abbanku mai sauki ne.. Bata Kai aya ba ta soma sinkayo kukan Ummul."

Taci gaba da girgiza kai  Ni dai a a dan Allah Mama. Wllhi bani son komawa gidan Haidar.. Ni ko ganinsa bani son yi.. Kuka ya hanata ci gaba da magana.

Mama Tani ta jinjina kai a hankali  Shikenan kiyi shiru Ya isa haka.. Kinji gashi ana Sallama a k ofa. Ta k arashe tana bada izinin shigowa.

Ga tsananin mamakinsu Asshe suka gani.

Mama Tani ta mik e tsaye tana gyara daurin zani tana huci  Toh gayyan tsiya gayyar Allah tsine.. Waye Ya gayyatoki.?

Ga mamakinsu cikin sanyi Asshe ta dubi Mama Tani tace  Kiyi hak uri mu gaisa kafin duk wani tashin hankali.. Hasalima no ban zo nan da wani tashin hankali ba.

Mama Tani ta rakata da harara  Yo ai ke ganinki babu alkhairi Sam Sam.

A hankali Asshe ta jinjina kai  Komai kika fad a akaina bazan mayar Miki ba. Wanda nayi tuba domin shi Ya sani. Ta dubi Ummul dake zaune saman gadon ta kuma duban Tani tace  Wajen Ummulkhair nazo idan kinmin izini.

Mama Tani ta kuma gyara daurin zani  Toh ban miki izini ba.. ki kwashe k afafunki ki fice tin muna mu biyu..

Ummul Tai saurin girgiza kai tana duban Mama Tani  Kiyi hak uri dan Allah Mama.. Kiyi hakuri ki kyale Aunty Asshe.

Shek ek e Mama Tani ke dubanta  Awho na fice na k yaleki da ita a d aki ta shak eki kaman yanda wancan muguwar  yar tata taso kashe ki.

Asshe ta share hawayen da suka gangaro tana mai zama gefen Ummul.

Harara Mama Tani ta rakata dashi Tai mata nuni da k ofa tace  Ba nisa zanyi ba.. Ina nan daga k ofa ina gadinki.! Tana ida fad in haka tasa kai ta fice tana aika ma Asshe mugun kallo.

"Bayan Mama Tani ta fice Ummul ta bud e murya ta gaida Aunty Asshe. Saiga Asshe na hawaye. Ta kamo hannayen Ummul tana rok onta gafara. Taci gaba  Tabbas a wann ranar da za a Miki aure ni da kaina na baki zab i cewa sadakinki shine zai zama kudin jinyar mahaifinki.. Idan akwai Wanda Ya tilasta Miki auren Haidar ba kowa bane face ni.. Ummulkhair, Haidar baida masaniya a duka abubuwan da muka aikata nida mahaifiyarsa.. Kaman yanda mahaifiyarki ma bata sani ba.! "

Cikin wane irin yanayi Ummul ta d ago tana duban Aunty Asshe hawaye na gangaro mata.

Asshe taci gaba da jinjina kai tana hawaye  Haidar baisan da labarin Auren karya sihiri ba kaman yanda mahaifiyarki bata sani ba.! Ummul batada laifi cikin AUREN WATA UKU da muka shirya. Mahaifiyarki uwa ce kawai kaman ko wace uwa. She wants nothing but the best for her daughter. Tana son  yarta takaiga d akin Aure kaman ko wace  ya mace.. Tana so ta sauk e wani nauyi ne kawai da Ya rataya a wuyanta matsayinta na mahaifiya. Tana so ta cike wani gurbi nata na zama uwa a gareki. Da saninta da hankalinta ba mahaifiyar da zata d auki  yarta ta sakata cikin halak a.. Mahaifiyarki tana matuk ar k aunarki Ummulkhair..! Asshe taci gaba da girgiza kai tana duban Ummul  Mahaifyarki Bata san da Auren karya sihiri ba.! Mahaifiyarki bata san da AUREN WATA UKU ba har sai bayan da akai auren. Idan akwai mai laifi ni ce da na b oye mata. Ni nayi amfani da rauninta na shashantar da ita Har ta d auki  yarta ta jefata cikin irin Auren da Babu Uwar da zata saka  yarta. !

Tinda Asshe ta soma magana kuka kawai Ummul take ba k akk autawa. Tausayi da soyayyar mahaifiyarta ya cika zuciyarta.

Asshe taci gaba  Ni na datse soyayya da shak uwa dake tskanin  ya da mahaifiya. Ni nayi umarni ma mahaifiyarki cewa ba ita ba ke Har sai bayan tsawon watanni uku. Ni ce nan na tilasta mata ta sanar dake haka amma ba rad in kanta bane. Ni na saka shamak i a tsakaninku.. Yau gashi  yansanda Sun saka shamak i tsakani na da tawa  yar.. Anisa tana tsare kurkuku.. Da zargi masu nauyi akanta na attempting kasheki da taso yi..! Ta kuma kamo hannayen Ummul hawaye naci gaba da gangaro mata  Zunubaina ke bibiyata.. Tabbas duk abinda ka shuka a rayuwar nan zai dawo gareka. Ya rage naka ka shuka khairan ko sharran. Ummul dan Allah ki yafe mun ki yafe ma  Yata Anisa ko zamu samu sassauci.!

Ummul taci gaba da kuka sharshar da hawaye yayinda Asshe ma taci gaba da zuban hawaye. Ta goge hawayen kafin taci gaba  Anisa tayi yunk urin kashe ki ne sabida soyayyar da take ma Haidar.. Ina sane da duka abubuwan da Anisa take Wanda hankali bazai Kama ba amma na adana a raina sabida soyayyar dake tsakanin Mahaifiya da  yarta.. Na mance ba ayi ma Allah wayo.. Kaman yanda naso raba wata uwa da  yarta gashi nan Nima yanzu za a rabani da nawa  yar.. Nabi son zuciyana Ya rufe mun ido.. Nayi komai ne sabida soyayyar da nake ma yarana Haidar da kuma Anisa. Ki sani Ummulkhair.. Haidar baida masaniya akan Auren karya sihiri.. Eh Tabbas da yarda da amincewarsa

aka k ulla AUREN WATA UKU sabida wani manufa na shi kan iyayensa a baya amma baisan da labarin karya sihiri ba. Ya d auki girman laifin ne kawai domin Ya zamto shield ga mahaifiyarsa.. Ya datse igiyan Auren ku ne ba don yana son yin hakan ba sai don ya zamto garkuwa a idonki dama sauran jama a ga mahaifiyarsa.. Ya d auki laifin mahaifiyarsa ne don ita d in mahaifiyarsa ce.. Ko wane D a na gari zai sadaukar da komai nasa sabida mahaifiyarsa.. Ciki harda soyayyarsa.. Kuma na sani wann shine mafarkin ki da burinki ga ahalin Haidar Tun bayan da kika shigo rayuwarsu.. Kina kwadayin kiga alak arsa da iyayensa ta gyaru tayi kyau.. Toh Tabbas ta gyaru kuma tayi kyau.. Saidai tazo at a huge cost. The cost of your marriage.! Ta kamo hannayen Ummul cikin nata su duka biyun hawaye na gangaro musu tace  Ki yafe ma Haidar domin shi d in masoyinki ne. Ni na raini Haidar da hannuwana Tun yana k uruciya.. Na kalle shi Har tasowarsa.. Kuma ban tab a ganin shi cikin soyayya irin Wanda na gani akanki ba. Sai suka soma sinkayo kukan jaririn daga window.

Asshe taci gaba da jinjina kai tana duban Ummul  A wasu lokutan mukan rufe idon mu ne mu Dole ce kawai da K addara suke sa  ya ya su girma ba tareda iyayensu biyu ba matuk a suna raye.Ki koma d akin mijinki ko dan wann D an k aramin alhakin da baisan hawa ba baisan sauk a ba. Kar ki bari ahalinki ya tarwatse. Kar ki hana ma D anki abinda Haidar Ya rasa lokacin k uruciya.. Kar ki bari tarihin abinda Ya faru da mahaifinsa Ya maimaita kanshi..! Ta sauk e ajiyan zuciya murmushi gauraye da hawaye saman fuskarta. A hankali ta mik e tana gyara fuskarta  Zanje naga jikana.. D an Haidar dina.! Tana ida fad in haka ta mik e ta fice. Yayinda Ummul Tai bursting cikin kuka.

Asshe tana fitowa taci karo da Haidar a lobby cikin wane irin yanayi tamkar Wanda ruwa Ya shanye shi. Cikin sanyin jiki take dubansa. Ta ambato sunansa a hankali  Haidar.!

Bai iya cewa komai ba sai kawai Ya rungume Asshe.

Jikin Asshe ya kuma yin sanyi ganin yanayin nasa. Ta rungume shi cikin jikinta hawaye na kuma gangaro mata  I m here.. I m here

84 / 103