AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   93 / 103

276K to 279K   out of 306.8K words

ba. Iyaka hakuri fah munyi kar kuma a k ure mana hakuri. Dan takaiga mun fara maganar k arin aure.

Galala Mmmy ke duban Aunty Asshe  Haidar d in ne ke maganar karin aure.?

 K warai kuwa. Aunty Asshe tace tana karanto ma Mommy yanda sukai da Haidar d in.

Girgiza Mommy tai had ida tab e baki  Rigima ce kawai irinta Haidar.. Kuje can kuyita auren naku  Yata tana nan sai na tabbata Martabanta Ya inganta.

Daga haka Mommy bata kuma bi takan Aunty Asshe da rigimar Haidar ba.

**

A b angaren Ummul kuwa sosai ta damu da zancen Auren Haidar gashi ta kasa sanar da kowa damuwarta. Ga Haidar kaman ya k ara janye jiki da gidan. Ko ya shigo gaisuwa kawai ke kawosa saiko duba D ansa sam baya bi takan Ummul har kawo wann lokacin. Iyaka damuwa da tashin hankali Ummul ta shigesa. Da kyar ta iya sanar da Hajja halinda take cik. Hajja ta lallasheta da fad in ta cire damuwar Auren da Haidar yace zaiyi a ranta. Ta maida hankalinta ga karan kanta. Ta natsu ta kwantar da hankalinta. Dan ita tama fi so lokacin da Haidar zai ganta ya kasa ganeta. Ga gyara mai aminci da take samu daga Hajja harma da YâGumsu wacce da alama ba don kula da Baba Ali kawai Mommy ta kawota gidan ba harda kula da Uwar Baba Alin. YâGumsu sunada dangantaka da Daddy dan mazaunin Kaka take ga Haidar.

Gyara na kankaro mutunci da dawo da martabar d iya mace bayan haihuwa YâGumsu ke mata. Gyara tin daga ciki Har kawo fatarta daga waje. Kan kace mai Ummul tayi kyau ta k ara haiba. Ga wani haske da shek i na musamman da take ba a maganan wani musulmi k amshi da tuni yabi jikinta Har zuwa suman kanta. Ita da kanta jinta take ta canza kama daga matantakanta har zuwa gangar jikinta. Wasu lokutan sai ta d auki wayarta tana duban layin Haidar kaman zatai dialing sai kuma ta tuno kashedin Hajja na cewa ta maida hankalinta ga karan kanta ta mance da zancen Auren Haidar. Cikin zuciyarta take furta  Toh ma ni ina ruwana.. Ba sai yaje Yata auren nasa ba. Dama ni sabida Abba da Mommy na amince da aurensa. Ta Kai dubanta ga YGumsu da shigowarta kenan rik eda Baba Ali yaron ya girma yayi wayau ga kyau da ya k ara kaman D an turawa bazaka ce d an wata biyu bane. Ga shiga rai wajen duk Wanda ya d ora ido kansa.

A haka suka doshi watanni uku suna samun kula da tarairaya daga ita har jaririnta. Tayi k ok arin kauda tinanin Haidar cikin zuciyarta kaman yanda Hajja ta shawarceta. Ita zama ta iya cewa ta mance da Haidar d in balle wani zancen aurensa. Sosai ta natsu ta kwantar da hankalinta. Idan tana tareda Baba Ali ba k aramin d ebe mata kewa yaron yake ba. Ya shiga ranta yanda baka tsammani. A sama ranan ta stinci hirar YâGumsu da Mommy. Yâ Gumsun na shirya Baba Ali bayan ta masa wanka take jajen uban Babagana kaman yanda take kiran Baba Alin.

Mommy tace  Ai zaman Lagos ya auresa yanzu yana can kudu bai Faye zaman nan d in ba. Abinda Ummul ta sinkaya kenan taji kanta na juyawa. Wai zaman Lagos ya auresa.. Innalillahi wa inna ilaihi raji un.! Toh kodai Haidar aure yai ya aje matar a Lagos ba tareda saninta ba. Toh kodai ya b oye ma Mommy zancen Auren nasa ne kaman yanda yace da Aunty Asshe zata had a masa lefe ko babu sanin Mommy.. Idan ba haka ba maiyasa zai tare garin Lagos.? Sam bama ta kawo tunanin aiki ko wani abu zai iya kaisa Lagos ba. Haka ta yini d aki tana faman sak e sak e. Duk yanda taso ta yakice tunanin ta kasa. Haka ta shige band aki taci kukanta ita kad ai tana mai tausayin kanta.

**

Kwance take da hantsi d akin Mommy. Idanunta a lumshe irin na mai bacci.. Baba Ali na cikin cradle d insa dake nan d akin Mommy shima baccin yake. Haidar da shigowarsa gidan kenan Kai tsaye d akin Mommy ya nufo yana nemanta. Cak yai tsaye yana dubanta zuciyarsa na wane irin fuzga.. Ta masa kyau har ta gaji ga wani k yalli na musamman da fuskarta keyi. Shi zai iya cewa rabon sa da ita ya mance..

A hankali yake takowa cikin d akin kaman mai tsoron kada ya tadasu daga baccinsu.

Yai tsaye akanta yana dubanta sihirtaccen murmushi saman fuskarsa. Ya furta  sleeping beauty a hankali kafin ya zauna nan gefenta yana kuma k are mata kallo tin daga fuskarta har zuwa d an yatsarta. Ga wani musulmin k amshi mai sauk ar da nitsuwa da yai ma k ofofin hancinsa Sallama tinda ya zauna kusanta. Bai san sanda ya rank wafo sosai yana shak an k amshin nata. Idanunsa a lumshe yake shak an dadd an k amshinta Wanda ya sauk ar masa da natsuwar da ya mance yaushe rabonsa da yaji irin haka.

Kaman a mafarki Ummul ke Jin hucin numfashin mutum saman wuyarta. Tai saurin bud e idanunta masu cikeda bacci. Nan kaw sukai ido hud u da Haidar fuskarsu dab na juna har tsinin hancinsu na had ewa.

Zuciyarta yai wani irin yankewa. Dan ita dai rabon ta da Haidar zata iya cewa ta mance.. Ta d anyi yunk urin mik ewa a firgice amma sai Haidar yai saurin rik o ta ya hanata mik ewa. Ya tsareta sosai da rikitattun idanunsa. A hankali ya furta  I ve missed you Khairy.. I ve missed everything about you..! Yai maganar yana mai kuma shigar da Kansa wuyanta  Your smell..! Your skin..! Your lips..! Ya k arashe yana gangaro da bakinsa zuwa labb anta.

Sosai ta rintse ido tana Jin hawaye na ciko idonta sanda ta tuna daga Lagos ya dawo can wajen matarsa. Sai taji kuka ma zuwa mata da gaske. Tai ta maza ta taresa daga jikinta kukanta na k aruwa  Ni dai ka k yaleni.. Ka koma can wajen matar taka.. Nida D ana bamu buk atarka.

Cak Haidar ya dakata yana dubanta cikin rashin fahimtar ina kalamanta suka dosa. Ya dan girgiza Kai kad an  Wait.. What do you mean& Na koma wajen matata.?

Cikin kuka taci gaba  Eh wajen matarka da ka baro can Lagos.. Ni dai kawai ka koma wajenta ka kyalemu.

Izuwa lokacin dariya maganganun nata suka so basa. Yai k ok arin gimtse dariyarsa  Kinga.. Saurareni Khairy.

Ta mak e masa kafad a cikeda shagwab a  Ni dai kawai ka koma. We don t need you here

Ya jinjina kansa  Tinda bazaki saurareni ba shikenan.. Kece dai baki buk atana amma D a na yana buk atana.. I m sure he missed his Dad. Ya k arashe yana nufan gadon Baba Ali.

"Annurin fuskarsa ya k aru sanda ya Ciro yaron daga cikin gadonsa. Yana kissing d insa yake fad in  Hello Son, Wakey wakey.. Dad is here.. Yai maganar sai kissing yaron yake yana mai cillasa sama yana fadin ya tashi daga bacci su gaisa. Haka ya fice da yaron cikin hannunsa sai masa wasa."

Aka bar Ummul da matse matsen k walla.

Ficewar Haidar da Baba Ali da kad an taji sak o ya shigo wayarta. Ta janyo wayar tana dubawa zuciyarta yai wani irin tsinkewa. Kuka ta fashe dashi sosai ta nufo downstairs a guje tana ambaton Mommy cikin kuka.

SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!*

*61*

*©þSameena Aleeyou& *

Mommy taci gaba da jijjigata tana tanbayarta lafiya meke faruwa. Ummul ta kasa furta komai sai kuka da take tana girgiza kai. A haka su Hajja da Yaa Gumsu suka shigo suka taddasu. Sud in ma bakin Mommy suka bi suna tambayar meke faruwa.

Mommy tace  Yanda kuka ganni a nan tambayar da nake mata kenan. Ta kuma duban Ummulkhair  Ina Baba Ali wani abin ne Ya faru.?

Cikin kuka Ummul ke fad in  Baya nan Mommy.

Suka saki baki gaba d aya. Mommy ta girgiza kai kad an  Ban gane baya nan ba.. Wane irin bayi nan.? Inji tare na barku a d aki kuna bacci.?

Murya Har na sark afewa take fadin  Mommy Haidar Ya tafi dashi.

Mommy tace  Haidar kuma..?

Ummul ta kuma jin kai cikin sauri bata daina matsan hawaye ba  Ya shigo ya d auki Baba Ali ya tafi dashi.. Mommy dan Allah Ki kirashi. Ta k arashe cikin shesshek ar kuka.

Da mamaki suke duban juna gaba d aya. Mommy ta girgiza kai tace  Haidar kuma Ya tafi da Baba Ali..? Toh ina zai kaisa.? Yaushe ma ya shigo gidan.?

Yaa Gumsu ta dubi Mommy tace  Ah ah.! wai ba jiya nakeji kina cewa yana birnin ikko ba.?

Mommy tace  Dama akan yau jirgin safe zai biyo yazo shi Abuja. Amma bai sanar Dani ya taso ba.. Sann yaushe ma ya shigo gidan..? Sam banji alamunsa ba.

Yaa Gumsu taceda Ummul K ila dai mafarki take amma basuga shigowan Haidar gidan ba.

Ummul na kuka take fad in ba mafarki take ba a shiga d akin a duba babu Baba Ali Haidar ya tafi dashi.

Mamaki Ya cika su Mommy gaba d aya. Yaa Gumsu da Hajja suka nufi sama duba Baba Ali amma wayam bashi a makwancinsa. Mommy ta shiga dialing layin Haidar amma baya shiga. Neman duniya anyi ma Haidar wayarsa baya shiga. Ran Mommy idan yayi dubu ya b aci k wafa kawai take tana fad in Haidar zaizo Ya sameta. Akan wani dalili zai d auki yaro jariri mai shan nono ya fice dashi Har tsawon sa o i.

Abu kaman wasa ba Haidar ba Baba Ali sann wayoyin Haidar kaf a rufe suke basa shiga.

Lamo Ummul tai saman cinyar Hajja hawaye naci gaba da gangaro mata ga k irjinta da tuni Sun ciko sai ciwo suke sakamakon ba mai sha. Ita bama physical pain d in bane Ke damunta psychological pain din Ke dawainiya da ita. Tana jin Hajja na fad in Tai hakuri haka ta daina kunan nan tinda dai Haidar ba cutar da Baba Ali zai ba.

Cikin zuban hawaye tace  Hajja wa ya sani yaci abinci ko bai ci ba.? Koma kuka yake.? Waye zai hada masa abincinsa.? Waye zai canza masa diaper.? Hajja ni nasan kawai wajenta yakai shi.. Ta k arashe cikin rawar murya irinta mai kuka.

Hajja ta girgiza kai cikin rashin fahimta  Wajen ita wa.?

 Wajen matarsa. Ta bata amsa kai tsaye cikin rawar murya.

Muryar Mommy suka sinkaya tana fad in  Wajen matarsa.? Wace matar kenan.? Haidar d in keda wata matar.?

Ummul taji kukanta na k aruwa sai ta mik e zaune tana jinjina ma Mommy kai  Eh Mommy.. wajenta yakai Baba Ali.

Hajja ta girgiza kai cikin rashin fahimta  Ummulkhair kinkuwa ji abinda kikace yaushe Haidar d in yai aure bamu sani ba..

Cikin kuka Ummul ke fad in  Hajja da gaske aure yai.. Gashi Ya turo mun sako cewa Ya d auke dansa kuma nasan ma matarsa zai kaisa.

Hajja ta girgiza kai kad an had ida murmusawa  Banda abinki Ummulkhair a ina Haidar zai tafi yai aure duk bamu sani ba..? Kuma har ya d auki Baba Ali ya kaishi ma matar .?

Mommy tai k wafa tace  Toh wa ya sani masa ne yanzu. Zai aikata tinda yayi a baya ba da sanin namu ba..

Ta d aga waya da zummar kiran Aunty Asshe ko zata Sami wani bayani gameda Haidar d in tinda tasan d an gidanta ne amma sai Aunty Asshen ta riga kira. Mommy tace da Hajja  kinga ma Asshen na kira

Ta daga wayar tana jin da mai Aunty Asshe ta kirata. Aiko tambaya Aunty Asshe ta soma ma Mommy meke faruwa ne Haidar Ya mata waya yana tambayarta yanda ake had a baby formula da canza diaper.

K wafa kawai Mommy take kafin tace  Zan kira kika rigani.. Kinsan yaron nan zuwa yai Ya d auki D ansa Ya kuma kashe wayoyinsa.. Wato iyakacina yake son nuna min.!

Hakuri ta fara ba Mommy tana fad in  Kinga yace ma I should keep it a secret. Kawai so yake ya kasance da D ansa.

 Dan yana so ya kasance da D ansa shine sai Ya d auke sa yai tafiyarsa Ya kashe wayoyinsa.. Waye Ya tab a hanasa kasancewa da Dan nasa.? Mommy ta kuma fad i cikin fad a.

Aunty Asshe tace  A a Aunty Kwaise banda son kai mana. Watak ila bai Sami breathing space bane a gidan shisa ya fice dashi.. Keda Ummul kun suffocating min yaro. Ni dai dan Allah dake da d iyarki ku daga masa k afa haka nan yasha iska.

Gajeren tsaki Mommy tai tace maza Asshe ta kira mata shi. Daga haka katse kiran Tai. Sai fad a take har saida Ummul taji ba dad i dan bata tab a ganin fushin Mommy irin haka ba.

Har Daddy ya dawo gida ba Haidar ba dalilinsa. Daddy ma fad a yai tayi yana fad in wane rashin hankali ne zaisa Haidar Ya d auki yaro jariri mai shan mama Ya fice dashi. Daddy yasa akai masa kiran Ummul. Duk sai jikin Ummul ya kuma yin sanyi wai yau ita Daddy yake kira sashensa.

Gaba d aya iyayen suna had u parlorn Daddy. Mommy da Hajja ga Daddy daga nasa kujeran.

Ta risina daga can gefe tana goge ragowar hawayen dake gangaro mata tana janyo mayafinta zuwa fuskarta. Ta risina sosai ta gaida Daddy da kyar. Mommy kam har lokacin huci kawai take ba walwal saman fuskarta.

Daddy yaci gaba  Ummulkhair nasan kin d aukeni kaman Abbanki.. Bazan bari wani abu na cutarwa ko rashin adalci Ya faru dake ba.. Kaman yanda nai alk awari ma Abbanki.. Ki sanar Dani akwai wani matsala ne tsakaninki da Haidar.. Tinda nasan ba k aramin abu bane zaisa Aliyu Ya d auki jariri Ya fice dashi Har tsawon lokacin nan.

Ummul bata iya bama Daddy amsa ba sai hawayen dake ci gaba da gangaro mata.

Mommy tai karaf tace  Wai har sako yake tura mata zai kai D ansa ga sabuwar matarsa sabida shi ga shafaffe da mai.!

Daddy ya girgiza Kai cikin rashin fahimta  Sabuwar matarsa kuma.? Yaushe Haidar d in yai aure.?

 Oho masa mana.! Iyakacina yake son nuna min tinda na hanasa matarsa bari yaje yai wani Auren Wanda ban isa da shi ba.! Mommy tace cikin b acin rai.

Hajja tace  A a fah Aunty Kwaise. Auren nan mai yuwa hasashen Ummul ne kawai amma Haidar bazai aikata abu makamancin wann ba.

Mommy tace ba maganar hasashe zai aikata dan ya nuna mata iyakarta.

Daidai nan Haidar yai Sallama rungume da Baba Ali cikin abin goyo dake d aure daga kafad a zuwa k irji. Hannayensa kuwa rik e suke da manyan bags mai k unshe da manyan teddies da dangin kayayyakin wasa na yara.

Zuciyar Ummul yai wani irin tsinkewa. Yayinda iyayen nasa suka zuba masa ido gaba d aya suna dubansa.

Ga dai Baba Ali sai baccinsa yake peacefully rungume cikin k irjin Babansa.

Babu Wanda ya amsa masa gaisuwar nasa cikin iyayensa sai kaw Hajja. Mommy kam mik ewa Tai ta isa garesa fuu fuska a matuk ar tsare ta hau kwance belt din da ya rik e yaron tana fad in  Bani shi nan.!

A hankali Haidar ke furta  Mommy I m sorry.! Ya fad i yana mai shan jinin jikinsa. Bata sami zarafin amsa sa ba ta koma mazauninta tana jijjiga yaron cikin hannunta.

Daddy yai masa alama da hannu yace yazo Ya zauna. Ba musu Haidar Ya isa yanda Daddy ke nuna masa ya zauna a sanyaye.

Daddy yai gyara murya yace  Aliyu.

 Na am Daddy. Haidar ya amsa a sanyaye. Dan yasan idan Daddy ya ambaci sunansa kai tsaye akwai bayani.

Daddy yaci gaba  Have you realized what you ve done.? Wani dalili zaisa ka dauki yaro jariri ka fice dashi ka rabashi da mahaifiyarsa Har na tsawon sa o i.?

Haidar yace  Daddy nayi kuskure Im sorry.. But I just wanted to spend time with my son.

Mommy tai karaf tace  Mu zaka fad a ma kana son spending time da danka.? Ka cire yaro a nono na tsawon sa o i.. Kai ko tausayin uwa da D an bazaka ji ba.! Harda turo sako kana wani cewa ka kaisa ma sabuwar matarka ko.? dan ka nuna min

93 / 103