AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   58 / 103

171K to 174K   out of 306.8K words

ma Inna Dije mugun kallo.

Umma ta girgiza Kai kurum ganin irin kallon da Azeema ke yi ma k anwar mahaifin nasu. Ta sani Sun canza sosai Sun rage wasu abubuwan sosai. Amma wasu abubuwan sai a hankali su daina dan haka ga duk Wanda ya san su waye su a baya dole yai masu uzuri.

Umma ta murmusa tana mai janyo Azeema kusanta  K warai d iyata k ofan mu ya zama k ofan zaman lafiya da lumana cikin yardar Ubangiji. Hakan yasa Innarku shigowa cikin lumana. Ta k arashe tana duban Inna Dije wacce ta koma tamkar salihar mage  Haka ne Dije.?

"Inna Dije tai saurin d agowa ta dubi Umma sai ta jinjina Kai a hankali  K warai Suwaiba. Babu abinda yafi yafiya, zaman lafiya da lumana. "

Umma ta jinjina Kai kafin ta maido da dubanta ga Badia da Azeema  Ku gaisar da k anwar mahaifinku.

Suka dubi juna suna yatsina fuska. Umma ta tsare sosai tana dubansu alamun tana jira su aiwatar da abinda ta umarcesu.

Murya can k asa Badia tace  Wllhi darajan Umma kikaci.!

Zuciyar Dije yai wani irin tsinkewa jin wai yau ita ake ce ma taci darajan Suwaiba shashashar matar D anuwanta. Ta had iyi abinda ya tsaya mata sanda ta sinkayo muryoyin yaran D anuwan nata suna gaidata da k yar. Ta amsa masu a Mutunce da sakin fuska kaman dai ba Inna Dije ba.

Umma tace Badia ta kawo ma Inna Dije abinci sann Salima ta gyara mata d akinsu ta kwana ciki tinda tace washe gari take komawa Dutse.

Sosai Inna Dije ta saki jiki ta nuna musu komai ya shige. An bud e sabon shafin rayuwa na zaman lafiya da k aunan juna tsakani da Allah. Harda ba ma Umma zab i tai idan tana so a dawo da Abba gida cikin ahalinsa.

Umma ta murmusa had ida girgiza Kai kad an  A a Dije zamansa a can yafi. Kinga har yanzu akwai abubuwan da bai sani ba. Kaman auren Ummul da Tani dake tsare. Kuma kinga shi mutum ne majinyaci shiga damuwa ko tashin hankali ba nasa bane. Muryarta ya soma rawa sanda taci gaba da fad in  Yau a k alla watan Ummul guda da aure harda  yan kwanaki.. Dije kinfi kowa sanin auren Ummul mai k ayyadadden wa adi ne.. Nafi so idan wa adin ya cika Ummul ta dawo garemu kaman yanda Hajiya Asshe ta tabbatar mana sann a lokacin Tani ta dawo sai mu fuskanci Malam gaba d aya matsayin ahali.! Ta k arashe cikin murya irinta mai kuka.

Inna Dije ta matso gareta ta dafata kad an  Suwaiba Hak ik a kurakurai mun riga mun taptapka a baya. Gyaran da zamu masu kenan shine mu gyara gaba.

Umma ta jinjina Kai a hankali tana duban Inna Dije itama Inna Dijen Umma take duba ko wanne da abinda yake sak awa cikin zuciyarsa.

**

Hilal yana isa gida kaman jira take ta soma kiransa. Ya murmusa kad an yana mai lumshe ido dukda jikinsa Ya basa ba kalamai masu dad i zaiji cikin wayar ba.

Ya d aga yana jiran da mai zata fara.

 Wai Kai dan Allah a sau nawa zance maka ka daina shiga al amarin ahalina..? Shin bakada wani abin yi ne? Ko kuma dai ka zama wakilin wanzar da zaman lafiya ne.?!

Ya murmusa kad an yana mai relaxing cikin kujerar motar  I d rather become a Peacemaker and a unifier da ace na zama mafad aci..

Kafin yakai aya yaji an finciki marfin motar an fuzge wayar. Ba kowa bace face mahaifiyarsa.

Khulsum wacce batasan meke faruwa ba daga d aya b angaren taci gaba  Ni Khulsum Ina maka gargadi na k arshe da ka daina shiga hidiman ahalina dan zaman lafiyarka da naka ahalin.!

Asshe dake huci ta katseta  Ke mai kika ce.?! Ta fad a da mamaki tana duban Hilal da Ya zuba ma sarautar Allah ido.

Khulsum kaw tinda taji muryar mahaifiyar Hilal cikin wayar sai ta katse kiran a daburce zuciyarta na tsinkewa.

Asshe ta dubi Hilal da tuni ya fito daga cikin motar  Mai ya had aka da yarinyar nan Hilal.? Nace mai ya had aka da ita.? Ta shiga salati tana dafe k irji  Na shiga uku ni Asshe Sun ranste sai Sun lasheka.! Ka amsa min Hilal! Ta k arashe kaman zata rufesa da duka. Daidai lokacin Motar mahaifin Hilal Ya shigo gidan.

Yanda sukaga yanayinsa daga ita Har Hilal d in Ya d aga masu hankali. Musamman yanda sukaga Ya nufosu a zafafe ga wane irin kallo da yake bin Hilal d in dashi.

Yana k arasowa yace su biyosa parlornsa.

Asshe ta dubi Hilal Wanda shima ita ya duba cikin tunanin yanayin da yaga mahaifinsa ciki.

Suna shiga ya nuna ma Hilal saman carpet gabansa  Zauna nan.!

Ba musu ya isa ya zauna yana kokarin gaida mahaifin nasa Wanda ko amsawa bai ba. Abinda bai tab a masa ba tun tasowarsa.

Mamaki ya kuma cika Asshe dan tasan Hilal dan gaban goshin mahaifinsa ne Tun tasowarsa. A Cewar sauran ahalin gidan baya laifi idon mahaifinsa. Jiki a sanyaye tace

 Alhaji lafiya.. Meke faruwa.?

 Ki tambayi wann D an naki.! Ya k arashe cikin huci yana nuni da Hilal.

Ta girgiza kai cikin rashin fahimta tana duban Hilal.

Asshe ta kuma duban mijinta duk hankalinta a tashe da yanayinsa. Ta kuma duban Hilal.

 Hilal.? Meke faruwa ne wai..?

Kafin Hilal yakaiga bude bakinsa mahaifinsa ya katsesa  Meye dalilin da yasa ka bar karatunka.? Meye dalilin da yasa ka bar makaranta wann karon.?!

Salati Asshe ta soma cikin tashin hankali tana girgiza kai  Hilal.! Makarantar ka kuma bari wann karon ma..? Na shiga Uku ni Asshe.. Hilal asirina kake so ka tona.. Meke damun rayuwarka ne.. Abubuwan da bakai a k uruciya ba kake so kayi yanzu.?

 Gwara ki tambayesa idan ma shaye shaye Ya fara. Dan wann karon idan ya watsar da karatunsa sisin kobona bazai sake ciwo akansa da sunan karatu ba. Makaranta na nawa aka canza masa.? Sa anninsa daga masu aure sai masu  ya ya shi Har yanzu baima san ina nasa rayuwar ta dosa ba. Shi ba kasuwa ba shi ba wani sana an hannu ba shi ba karatun ba. Sanin kanki ne sauran yarana sai Sunyi zaman yaran shago kafin na barsu suyi wani karatu amma shi da yake gata Ya masa yawa gashi nan bai san mai yake ciki ba.!

Cikin tashin hankali Asshe take duban Hilal  Kace mun hutu kake Har yanzu.!

 Makarantar su sun jima da soma karatun wann zangon. Daga gidan Alhaji Halilu nake akwai nasa yaran a makarantar nasu. Muna labari yara sunata hutu yake sanar Dani ai Sun tsufa can Cyprus. Gashi nan ki tambayeshi.! Ya k arashe yana nuni da Hilal d in cikin b acin rai.

Asshe ta fashe da kuka ta mik e tana nuna Hilal da yatsa tana fad in bayanta yake son gani.

Sai sann Hilal ya katseta  Ammi I didn t dropout.. Ok.. Ni bar makaranta ba..

 Idan ba bari kai ba mai ya hanaka komawa.?! Ta tambaya tana kuka.

Ya dubi mahaifinsa cikin kwantar da kai  Abba ba makarantar na bari ba.. I Only take.. half a semester off..

Mahaifinsa ya katsesa  Akan mai zaka jingine karatunka na wani lokaci.. Akan mai..? Mai kake yi a nan d in.?!

Zuciyar Asshe ya kuma tsinkewa kar dai sabida matsalolin zuriyan Suwaiba Hilal ya shashantar da karatunsa.

 Tambayarka nake.?! Mahaifinsa Ya kuma katsesa.

 Abba.. Aure nake so a nema min kafin na koma.

Daga Asshe Har Mahaifin nasa da mamaki suke dubansa.

Asshe baki sake tace  Aure.? Aure Hilal.?  Yar wa kake nema.?

"Muryar Mahaifin Hilal d in ne ya katsesu   Yar waye yake nema ba shi bane matsalar. Matsalar shine bazan masa aure bai koyi komai a rayuwarsa ba. Kodai ya koyi san a na basa jari yayi aurensa ko kuma yayi karatu. Amma bazan nema masa auren  yar kowa baida sana a ko aiki ba. Son da nake masa bai kai na sangartasa Har haka ba. Nima nawa iyayen ba haka suka mun ba. Dan haka bazanyi ma nawa d an kisan gwani ba. He must learn to take responsibilities. Kuyi shawari da D anki. Kodai ya kama Sana a ya hakura da karatun yayi auren ko kuma ya ci gaba da karatu kafin yayi auren.! Yana ida fad in haka ya mik e zai fice. Sai kuma ya juyo ya dubi Hilal  Kana jina, ka dawo da duka kud ad en da na baka da sunan makaranta. K wandala ban yarda ka bari wajenka ba. Kar ka bari na sake maimaita maka ka dawo mun da kud ad ena.! Yana ida fad in haka yasa kai ya fice."

Asshe taji duniyar na juya mata. Ta k araso gaban Hilal dake duk e wajen  Ina jinka.. Wace yarinyar ce ta d auke maka hankali haka..?  Yar waye.. Waye mahaifinta a garin nan.?!

Ya d ago yana murmushi mai ciwo yana duban mahaifyarsa  Ammi is that really what matters now.? Kar ki damu kinfi kowa sanin ko wacece ita da kuma ahalinta..! Yana ida fad in haka ta mik e ya fice cikin sassarfa. Zuciyarsa fal damuwan yanda zaiyi Ya maidama mahaifinsa kud ad ensa kafin wa adin da ya basa Ya cika.

Yana ficewa Asshe ta mik e tana tunanin abun yi. Wacece ta d auke mata hankalin D a haka.? Khulsum.! Sunan da zuciyarta ya raya mata kenan. Ta soma girgiza kai tana zagaya parlorn. Suwaiba ta gama da ita da halinta dole ta nemo hanyar da zata raba Hilal da wad ann harababbun mutane kafin su gama da ita. Dije.! Ita ce ta fad o ranta. Dije ce kawai zata zamto makamin da zata yak i Suwaiba da ita.

Saurin ficewa tai ta nufi nata sashen. Saidai tana isa ta tadda wayar Anisa na shigo mata.

Labarin hadarin su Haidar da Anisa ta sanar da ita ya kuma jagula mata lissafi.

Asshe ta shafe goshinta tace  How s my sister doing Anisa..? Yaya  yaruwata take.?

Anisa takai dubanta ga Mommy wacce Daddy ke rik e da ita Sun nufi mota. Da kyar ya shawo kanta zai kaita gida ta dan huta Tai sallah. Saida yai mata alk awarin dawowa da ita asibitin ma kafin ta amince ta bisa.

Ta numfasa daga nan yanda take tsaye tana wayar  Your sister needs you Ammi.. Gata nan ta kasa barin asibiti. Ta kasa cewa komai ta kasa cin komai sai kuka da kiran sunan Haidar take. Ammi ya kamata ko mai kike ki bari ki zo Abuja.. Ki raba Haidar da annobar da kika lik a masa kafin tai ajalinsa.. Dan tinda ta shigo ahalin tashin hankali ne ke kunno kai na yau daban na gobe daban. And worse part d in shine ta lashe Zuciyar Mommy bata ganin laifinta. Tana mata wani irin soyayya da bazai bari ta bud e idonta ta gane cewa ita d in annoba ce kuma had ari ce ga rayuwar Haidar.. Ammi only you.. Ke kad ai ce zaki iya raba wann jarabbabben aure da kika nemar ma Haidar. Dan idan ba kece kika bud i baki kikace Ummul annoba ce Mommy bazata tab a yarda ba.!

Zufa yaci gaba da karyo ma Asshe dan yanzu wani masifan da ya b ullo mata ya wuce gaban tasa k afa ta tsallake. A halin yanzu ba rayuwar Haidar bane kawai akan layi harda rayuwar nata d an Hilal. Dan tayi imani tsautsayi da masifa ke bibiyan Suwaiba da ahalinta.. Bazata tab a bari Hilal dinta Ya fad a cikin wann bala i ba. Nan take ta sanar da Anisa zata kira Mommy amma bata jin zata samu zuwa duba Haidar a daidai wann lokacin domin kuwa wani wutan zata kashe. Dole ta saka ma Suwaiba birki.

Anisa tace da mamaki  Ammi yanzu ita Ummul d in Har tanada  yaruwa da Hilal ya k yalla ido kanta.? Ammi wai mai kika gani so special gameda mutanen nan ne kam da kika jajibo mana su..? Ammi yanzu kina so kice mun Abba yace Hilal ya maida masa kud ad ensa.?

Asshe tace  Wann ba matsala ta bace Anisa. Tinda nasan D anuwanki kobon mahaifinku bazai ciwo ba zai maida masa. Da ace kece sai na damu.

Anisa ta katseta  Ammi you are wrong.!

Asshe tace da mamaki  Mai kike nufi.?

Anisa taci gaba  Ammi.. Bana jin Hilal yanada kud ad en maida ma Abba yanzu. Tai maganar kanta staye.

Da mamaki Asshe tace  Kan mai zaki ce haka.. Kinsan wani abu ne..?

 Ammi Hilal ya tura mun kud ad en dake account d insa.!

Da mamaki Asshe tace  Ke ban fahimceki ba mai kike nufi..?

Take Anisa ta labarta komai yanda Leenah taita karb an kud ad e wajenta ita kuma tana tambayar Hilal.

Asshe ta koma ta zauna gijif saman gado tana dafe kai  Kin kashe ni Anisa..! Take zuciyarta ta soma ayyana mata Yanzu idan Hilal bai maida masa kud ad en ba dole k arshe zai fad i gaskiya cewa ma Anisa ya bada. Idan aka isa nan.. Magana zai fito fili.. Komai zai bayyana. Mijinta zai San ta tafi gidan boka. Aunty Kwaise zata San ta ha inceta akan auren Haidar da Ummul. Wani b angare na auren da  yaruwarta bata san dashi ba zai bayyana. Snn  yarta Anisa zata shiga uku. Gaskiya zai bayyana cewa ita ce sanadin rufe Aunty Kwaise da akai. Ahalin zai tarwatse .. Bazata bari hakan ta kasance ba.. Bazata bari ba.

Gaba d aya Asshe ta daburce ta susuce. Ta yanda take shiga ba ta nan take fita ba. Daga ita Har Anisar kuka suke. Ko wanne na jingine laifi ga d aya b angaren.

Anisa na kuka take fad in  Ammi.. Mommy bazata sake stanata ba ma sai taji cewa had arin da ya samu Haidar inada hannu ciki..!

Cak hawayen Asshe suka k afe  Na shiga uku.! Anisa mai kika zama..? Kin lalata komai kin b ata komai keda nace kar ki aiwatar da komai ba tareda umarni na ba.!

Anisa na kuka take fad in  Har yaushe zan jiraki Ammi.? Har tsawon wani lokaci zaki d iba kafin ki fitar da Ummul daga rayuwar Haidar.. Duk abinda na aiwatar sabida son Haidar nayi. Ammi I couldn t wait for you to act.. I had to do it my way.. And I ended up screwing everything up as always.!

Ta share hawayenta tana huci  But there s no going back Ammi.. Abinda ya faru ya Riga ya faru. Idan kikai wani abu foolish ko kika tona asirina wajen Mommy. Ba ni kad ai Mommy zata yak a ba Ammi..  Yaruwarki will wage a war against you zata tsaneki ne..  Yaruwar da ta rik eki har kawo Aurenki..  Yaruwar da ta d aukeki Aminiya abokiyar shawari. The best solution shine ki bar min komai a hannu na.. Ki tsaya a kano ki kashe wutan da Hilal ya kunna.! Tana ida fad in haka ta kashe kiran.

Wani irin kuka Asshe ta fashe dashi duniyarta tai mata d aurin goro. Ta d aura hannu biyu akai tana fad in  ya yanta biyu zasuyi ajalinta. Cikin duka abubuwan data aiwatar Bata tab a tsammanin zai backfiring da yaranta tsamo tsamo ciki ba.

Mik ewa Tai tana tunanin kuka bai ganta ba. Take ta danna kiran Dije.

Dije tana ganin kiran Asshe tai wata murmushi da gefen fuska. Cikin zuciyarta take ayyana kin kira akan gab a.

Saida ta Lek a ko ina ta tabbata babu mai ganinta kafin ta d aga kiran. Babu b ata lokaci Asshe ta sanar da ita dalilin kiran.

Inna Dije ta sanar da ita tana gari ta tsammaci ganinta washe gari kafin ta juya Dutse tinda dama a washe garin take shirin komawa. Da wann sukai sallama. Washe gari kuwa kaman yanda suka tsara. Bayan Inna Dije tayima su Umma Sallama cikin mutunci ta nufi gidan Asshe..

Asshe ta dubeta ta kuma gyara zama  Ni da ke munsan sirrikan juna.. Haka ne.?

Dije ta murmusa  K walliya munsan abinda muka sani dai.

Asshe ta furzar da huci  And we have common enemy here.

 A a a a yimin da yaren da nafi wayo.. Mai kike nufi.? Ta k arashe tana fiddo idonta waje.

 Ina nufin munada mak iyiya guda d aya.. Ita ce Suwaiba.!

Inna Dije ta murmusa  Anzo wajen.. Ai ni a halin yanzu kallon  yaruwa Suwaiba take min ba mak iyiya ba.

Asshe ta girgiza kai cikin rashin fahimta  Ban fahimceki ba.. Kina so kice mun keda Suwaiba Kun sasanta..? Kin yafe mata duk abubuwan da tai maki a baya.. Ciki harda mutuwan tilon D anki.?

Inna Dije ta murmusa tana kurban soft drink d in da

58 / 103