AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   31 / 103

90K to 93K   out of 306.8K words

jinjina kai tana kuma tabbatarwa. Waima Tani bataga wann daula da Ummul ta shiga ba kenan koda kaw ace na wutin gadi ne. Dole Tani ta zauce ta haukace."

Mommy ta fad ad a murmushinta tana fad in su k araso su k araso bismillah.

Yayinda Zuciyar Ummul yaci gaba da tsinkewa. Har lokacin kanta rufe yake cikin mayafi.

Daga yanda take zaune saman carpet tana jin yanda su Inna Dije dasu Aunty Asshe suke gaisuwa da muryar wata mata mai yanayi da shige dana Aunty Asshe. Nan gaisuwar tasu ta sauya salo zuwa yaren k abilar shuwa arab tsakanin Asshe da  yaruwarta.

Ita dai Inna Dije tinaninta da k wak walwarta sun gaza tantance tsananin kyau da tsarin gidan. Sai juye juye take tana mamakin koda ace auren kwangila na wata uku d ansu zai da Ummul meyasa sai Ummul a wann irin arziki da suke dashi. Meyasa basu nemo mace da Babu aibu tattare da ita ba sai Ummul. Itafa wann aure Sam bata amince iyaka cin gaskiya Asshe ta sanar dasu ba. Dik yanda akai akwai wata a k asa. Tunaninta ne Ya katse sanda taga matar ta k araso gaban Ummul murmushi fal saman kyakkyawar fuskarta.

Zuciyar Ummul yaci gaba da tsinkewa sanda taga hannun matar saman nata.

Lokaci guda Mommy ke ci gaba da fad in  Welcome my daughter. Sannu da zuwa cikin ahalinmu. I can t believe this is happening.. Finally Matar Aliyu na ta iso. Sai ta k arashe tana rungume Ummul daga zaune.

Anisa da Tai mutuwar zaune tana dubansu. Sai ta rausayar da ido cikeda k osawa tana mai aika ma Amminta wani kallo wacce itama jiki a sanyaye take duban Mommy dake rungume da Ummul tana ayyana farin cikinta a fili.

"Mommy kaw cikin zuciyarta take ayyanawa  Zan kula dake a tsawon watanni uku da zakiyi damu. Sabida kin cancanta. You are my son s savior. Kin sadaukar da rayuwarki dan rayuwar nawa d an Ya inganta koda ace bakida masaniya akan hakan. This is the least I can do for you bayan sadaukarwa mai girma da kika mana. Zan baki dukkan soyayya da kulawa Har kawo lokacin da zaki warware mugun k ullin da akai ma D ana harma da ahalina. Ta k arashe tinanin nata idanunta harda guntun k walla. A hankali ta saka hannu ta yaye rufin da akai ma Ummul. Wani ikon Allah Sai Zuciyar Mommy ya kuma karaya. Fuskar yarinyar take kallo.. She looks so innocent and totally naive. She couldn t help but to feel guilty.. Meyasa rauni Ya cika zuciyarta a kallon farko da Tai ma fuskar yarinyar a zahiri. Tai k ok arin saita kanta tana fad ad a murmushinta  Barka da zuwa Ummulkhairi, d ago ki kalleni.. Sabuwar Mamanki..! Ta k arashe tana mai tallafo fuskar Ummul wacce ta kasa d ago idonta ta dubi matar amma jin kalamanta na k arshe yasa ta soma k ok arin d ago idonta masu cikeda rauni hawaye tab cikinsu."

Dubanta Mommy take Har lokacin tana rik eda hab arta murmushi saman fuskarta.

Sai Ummul taji kuka da gaske na zuwa mata musamman da taji matar ta ambaceta da sabuwar Mamanta. Shin tasan Ummanta ta datse alak a da ita ne..?

Mommy ta soma girgiza mata kai alamun banda kuka. Ta shiga share mata hawayen tana fad in ta daina kuka ta saki ranta kaman tana cikin Ahalinta.

Mik ewa Anisa Tai cikeda k osawa tana rausayar da ido. Ta dubi Amminta ta furta a hankali  I m tired of this drama.! Tana fad in haka tasa kai ta shige.

Su Inna Dije Anci an sha an masu tarban girma ta kuma yarda Lallai Ummul gidan girma ta arziki ta shigo dan ko matar nan bata masu tarba da kayan arziki ba tarban fuska da ta masu da yanda ta amshi Ummul kawai sun isa ta shaida gidan girma da arziki Ummul ta shigo. Koda yake amma Asshe ta sanar da ita Auren na wata uku ne sann ga dalilin auren cewa kwangila suke so a bama d ansu a kampanin mahaifinsa mahaifin nasa yace bazai bada ba har sai ya kawo masa mata ma ana Har sai yayi Aure. Shin duk akan AUREN WATA UKU matar nan tai masu irin wann tarba ta kuma karb i Ummul hannu bibbiyu kaman  yarda ta haifa.. Anya kuwa..? Ita fah duka abubuwan dake faruwa Sun fara kwance mata kai. Ji take ta gaza fahimtar komai. Koda sukazo tafiya da Ummulkhairi b angaren Haidar Mommy ce ta rik e Ummul da kanta tace ita zatai ma  yarta rakiya. Kan Inna Dije Ya kuma d aurewa. Suka dubi juna itada Asshe. Asshe ta k ifta mata ido alamun kar tace komai.

A haka dai aka bama Inna Dije ma nata masauk in nan cikin gidan da nufin washe gari idan Allah yakai rai zasu koma Kano itada abokiyar tafiyarta Asshe.

Ita kad ai a d aki sai sak awa da warwarewa take. Ta d au d amarar kafin su bar gidan kafin su koma garin Kano sai tayi yanda tasan ta fahimci duk abubuwan dake wakana. Batai ma Ummul rakiya zuwa garin ba sai don su koma tare da Ummul d in. Amma yanda taga Uwar mijin Ummul na kaffa kaffa da ita tana nan nan da ita bata tsammanin Auren zai Mutu a sauk ak e. Abu guda ne zai kashe auren nan shine kawai ta bud e bakinta ta sanar da matar cewa ajalinta D anta Asshe ta kawo mata cikin gida.

Ta mik e da zummar fitowa nan taga Asshe tsaye gabanta.

Girgiza mata kai Asshe Tai tace  Koma ki zauna Tun muna mu biyu.

Inna Dije ta dubeta da mamaki. Sai kuma Tai  yar bazawarar murmushi  Aw baki so mu kasance mu uku ne. Ina nufin ni da Ke da kuma  yaruwarki wacce kikai mata rufa rufa ki aura ma D anta ajalinsa. Kar ki tausareni da abun duniya dan yanzu na fahimci kema gaban  yaruwar taki almajira ce. Sunan mijinki ne kawai kike tink aho da

tak ama dashi amma da alama Babu abinda auren naki ke tsinana Miki. Da alama yayinki ya k are wajen miji dole ki nemi hanyar neman kud i kota halin k ak a.

A zuciye Asshe ta dakatar da ita  Kar ki kuskura ki bada shaida kan abinda bakida masaniya. Ina shawartanki kar kiyi gangancin shiga tsakanin  yanuwa guda biyu. Ina nufin nida  yaruwata. Ta k arashe maganar nata tana sakin murmushi kamar ba itace ta sha mur ba.

"Lokaci guda Asshe ta k araso ta dafa kad an Inna Dije guda tana sakin murmushi  Ki kwanta a saman gado irin Wanda baki tab a mafarkinsa ba. Ki yada gajiya, kafin ki d auki hanyar gida gobe dan ba Lallai ki sake karo da irin wann gadon ba. Kar ki mance  yarku wata uku kacal zatai a gidan nan.! Ta k arashe tana k irga uku da yatsunsa. Lokaci guda ta zaunar da Dije saman gado sai itama ta zauna a gefenta  Ya kamata mu tab a hira ta k awaye kafin safiya.. Baki tunani.? Ta k arashe tana kashe ma Dije ido. Daidai lokacin Anisa ta shigo da tea cups guda biyu."

Asshe ta fad ad a murmushinta  Yauwa  yar albarka. Kin kawo mana shayin nida k awata.

Anisa ta jinina kai tana mai ajewa gaba garesu.

Asshe ta d auko ta mik a ma Dije  Ga shayin gidan shugaban k asa. Irin wann ganyen shayin a gidan shugaban k asa kawai kike gani ki sha ki kafa tarihi ki goranta ma sirakanki ina nufin Tani da Suwaiba. Ta k arashe tana kurb an wanda ke d aya hannun nata.

Ganin Dije ta k ek ashe ido tana dubanta Ya sanyata sakin murmushi  Aw na zaci k awa kika d aukeni. Kindai san k awar arziki bazata baki guba ba. Ko dama k arya kike da kika kirani k awa.? Ta murmusa tana kurban shayinta hankali  Ashe k aryar gogewa kike Dije. TaI maganar tana kuma kurban shayin. Harda lumshe ido tana fad in  Wani abu sai a fadan shugaban k asa. Ta shanye nata tana k ok arin janyo na Inna Dije da niyyan shanyewa Inna Dije Tai saurin rik e hannunta ta amshe tea d in.

Inna Dije na murmushi tace  Yo Dije nake muricin kan Dutse . Idan baki sani ba ban fito ba saida na shirya. Ba wani barikinki da gogewarki da zai bani tsoro. Ta k arashe tana kafa kai ta soma kurb an shayi tana lumshe ido.

Kan kace me Inna Dije ta zube kan gado bacci yayi awon gaba da ita. Asshe ta kece dariya tana jinjina k ok arin  yarta Anisa da ta kawo wann plan d in. Lokaci guda ta gyara ma Inne Dije kwanciyarta tana furta  K awata ki sha bacci lafiya. Keda bud e ido kuma sai gobe da safe in sha Allahu. Ta k arashe tana kuma kecewa da dariya.

A haka Anisa ta kuma shigowa ta tadda Amminta  Gobe da safe jirgin Daddy zai tashi. Mommy zata masa rakiya zuwa airport. Sai kiyi amfani da wann dama Ammi ki fitar da matar nan daga gidan nan da zaran Mommy ta fice. Kinga hakan na nufin bazata samu zarafin sanar da Mommy abinda kike tsoro ba wanda kika kasa sanar dani. Ta k arashe tana tab e baki had ida rausayar da ido Wanda d abi anta ne.

Bakin Asshe Ya gaza rufuwa dan farin ciki bata tab a tsammanin zata samu solution na yanda zatai da matar nan cikin sauk i ba. Ta dubi Anisa tace  Ni yau kin gama min komai. Ina Miki kallon marar wayau ashe zaki iya had a plan irin wann. Lallai na yarda banyi ganganci ba da nace You d become my eyes here.

"Anisa ta murmusa  I m your daughter after all, Ammi. "

Asshe ta jinina kai  K warai yau kin gama tabbatar min. Kuma na yarda zakiyi kaman yanda nace. Koda wasa kar ki bari D anuwanki Haidar Ya samu kusanci da yarinyar nan. Kiyi duk irin makircin da kikaga Ya dace ki tabbata basu samu kusanci ba a tsakanin watanni uku.

Anisa ta girgiza kai kad an  Amma Ammi meyasa kika canza ra ayinki akan yarinyar bayan da kince mun na zama mabudin k ulla shak uwa tsakaninsu da Haidar.. Ammi what s with all the mystery behind this marriage.. Ke yanzu kin nuna baki so amma a b oye ba tareda kin bari Aunty Kwaise ta fahimci haka ba. Ita Aunty Kwaise tana son auren tana son yarinyar da duka zuciyarta. And at the same time baki so wann matar tayi magana da Aunty Kwaise.. Ta k arashe tana nuna Inna Dije dake zube saman gado tana bacci. Ta kuma girgiza kai  Ammi wai menene b oyeyyen al amarin gameda Auren Haidar.?

Asshe ta sauk e ajiyan zuciya ta kamo hannayen Anisa  Ki yarda dani Anisa. Zan fayyace miki komai amma ba a daidai wann lokacin ba. Akwai lokacin da zaki fahimci duk abubuwan da nayi. Iyakacin abinda zan fad a Miki a k arshe shine zaki mallaki Haidar da izinin Allah. Amma fah sai kinyi aiki tuk uru Anisa. Kar ki bari Ya kusanci yarinyar nan. Daga k arshe zamu nemo mafita.

"Anisa ta sauk e ajiyan zuciya  Shikenan Ammi zanyi yanda kikace. After all, bana son auren tin daga farko. Yanzu zan d auko makaman yak i na da kika sa nai watsi dasu daga farko. Ta kuma murmusawa kafin tace  Tinda inada ke Ammi, I know I m not fighting a losing battle. "

Suka sakar ma juna murmushi a tare kafin Anisa tasa kai ta fice zuciyarta na mata sanyi. Zatai whatsoever it takes dan ta tabbata yarinyar nan ta fita daga rayuwar Haidar duk tsananin son da Mommy ke mata kuwa. Ta kuma rausayar da ido kafin ta shige.

Asshe ta janyo ma Inne Dije k ofa kafin ta fito daga b angaren bak in ta nufi wajen  yaruwarta daketa faman neman layin Haidar bata samu.

Zama tai gefenta ganin damuwa ya nuna k arara saman fuskar Mommy.

" Aunty Kwaise, ya na ganki haka. Allah sa dai lafiya.? "

Mommy ta furzar da huci kad an  Na gaza samun layin Haidar Har yanzu. Ga amaryarsa ta iso.

Asshe ta jinina kai kad an  Relax Aunty Kwaise. Ki kwantar da hankalinki.. Yarinyar nan tana nan a gidan nan har tsawon watanni uku. Ki basa space kar ki tak ura masa da batun a yanzu. Tinda an samu Ya amince kuma yarjejeniya akai dashi so I believe zai zo Har nan kan k afafunsa.

Mommy da har lokacin ta gaza samun sukuni girgiza kai take  What if ya janye fah Asshe.? What if wancan makirar ta kuma jifansa da wani mugun asirin fah..? Asshe what if Malaminta yafi namu..? Asshe I m scared.. Tsoro nake kar duk efforts d ina su tafi a banza.

"Asshe ta kamo hannun Mommy ta zaunarta saman gado  A a Aunty Kwaise ke uwa ce. Da izinin Allah k ok arin ki bazai tafi a banza ba. Haidar zai dawo gareki. D anki zai dawo gareki. Munyi komai kaman yanda Malam yace. Inada yak inin hak armu zata cimma ruwa. Just relax, ki zama calm kuma ki tunk ari Haidar a tsanake. Yanda kike ta rawar k afa akan yarinyar zai k ara tunzura Haidar ne. Kinsan halinsa hasalima kinfi kowa sani tinda ke kika haifesa. Ki bashi gobe zuwa jibi koma satin nan. A hankali sai ki tunk aresa da batun. "

Mommy ta girgiza kai  Sati Asshe..? Toh me zaman me yarinyar zatai a gidan nan idan Har babu wanda tazo domin shi.. Asshe no sati yayi yawa. Kema uwa ce ya kamata kifi kowa fahimtar mai nake ji.

Asshe ta jinjina kai  Na fahimceki Aunty Kwaise. Shiyasa nake k ok arin fahimtar dake abinda na hango.

Mommy ta jinjina kai a hankali tana duban Asshe wacce gaba d aya batada wani kuzari  Asshe. Ta kirawo sunanta in a serious tune.

Zuciyar Asshe Ya tsinke. Kai da ganinta kaga maras gaskiya.

"Mommy taci gaba  Akwai abinda ya kamata na sani ne..? Ina nufin, tinda kuka kawo yarinyar nan kin canza. Kaman akwai abinda ke damunki ba kaman lokacin da muka soma shirya auren nan ba. Tell me, is there something I should know.? "

Asshe tai Shiru zuciyarta naci gaba da yankewa sai tanajin tamkar  yaruwar tata ta riga ta fahimci komai abinka da maras gaskiya.

 Asshe.! Mommy ta kuma ambato sunanta su duka biyun suna duban juna.

Sai Asshe ta fashe da kuka tana girgiza kai.

Hakan yai mugun tada hankalin Mommy. Bata San sanda ta mik e ta k araso wajen  Yaruwar tata ba. Ta dafata tana tambayarta meke faruwa.

Asshe na hawaye take bama Mommy hak uri tana girgiza kai.

Cikin rashin Hajiya Kwaise ke girgiza kai  Asshe meyasa kike kuka irin haka. Kuma meyasa kike bani hak uri.. Wani laifi ne kika min..?

Cikin zuban hawaye Asshe taci gaba  Na miki laifi mai girma Aunty Kwaise..

Mommy ta girgiza kai  Laifi.. Wane irin laifi..?

Anisa da isowarta jikin k ofan kenan nan tai tsaye ta kasa kunne tana sauraron wani laifi ne mahaifiyarta ta aikata ma Mommy. Cikin zuciyarta Addu a take Allah yasa taji amsoshin duk tambayoyin da takewa mahaifiyarta gameda wann murd add en aure da sukai ma Haidar.

Muryar Amminta ta sinkayo tana fad in  An sace komai Aunty Kwaise. Kayan lefe na gani na fad a da kika sa akai ma yarinyar. A lokacin da kayan ya dawo gidana bayan an kai gidansu yarinyar.. A lokacin b arayi suka biyo dare suka kwashe komai.. Maganar millions of Naira ake.. Shiyasa kikaga dik jikina yayi sanyi ko zarafin fad a ma yarinyar ma ban samu ba balle danginta.

Shiru Mommy tai tana dubanta. Sai ta jinjina kai a hankali  Kan haka kika tada hankalinki.. Idan dan wann ne Babu wani matsala tinda kwalliya ta biya kud in sabulu yarinyar ta riga ta shigo hannunmu. Akan auren nan har property na na d aga na sayar a garin nan.. Kwabon Aliyu Maitama baiyi ciwon kai cikin yak in neman auren nan ba. So ko nawa zan kashe akan yarinyar nan bazan Ji ciwo ba Asshe because it worth it. Gobe idan Allah Ya kaimu sai ita yarinyar su

31 / 103