AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   38 / 103

111K to 114K   out of 306.8K words

kai a hankali kafin Tai mata godiya tabi hanyar da budurwar ta nuna mata. Tana tafe taga wani k aton hoto manne a wani madaidaicin parlorn mai kaman waiting. Ta gane Mommy a hoton dukda k uruciya da ya nuna a fuskar Mommyn. Gefe da Mommy wani mutumi ne mai Kamala da bata tantance ba amma tanada tabbacin shine mai gidan kenan. Tsakiya dasu wani yaro ne Wanda duka duka bazai gaza shekaru 10 ba. Kansa an tara masa suma irin mai laushin nan da cika. Ga kamannin iyayensa d auke a fuskarsa. Yanda yaron ya b ata rai cikin hoton ga fuskarsa da Ya buya cikin sumar kansa sosai abun yaso bata dariya musamman da taga kaman ita yake harara. Kai da gani kasan camera yasha harara kaman dai Wanda aka masa dole.

Muryar su Anisa da ta soma jiyowa ne Ya janyo hankalinta. Ta nufi hanyar da take sinkayo muryoyin. Nan ta kuma cin karo da wani hoton a wani dogon corridor. Saidai wann hoton matashi ta gani tsaye gaban wani k atoton zanen gine gine hannunsa rik eda wani k aramin abu kaman kara yana nuna ma mutanen dake zaune saman kujeru bayansa zanen dake gabanshi. Ko ba ace ba zaka fahimci ma aikata ne. Matashin yana sanye da suit saidai fuskarsa bai bayyana cikin hoton ba sakamakon Ya bada baya alamun yana bayani gameda hoton dake gaba gareshi. Bata san dalili ba amma kallo guda Tai ma mutumin dake cikin hoton zuciyarta ya yanke. Ta tsinci kanta da fad uwan gaba dukda ba wai ganin fuskarsa tai ba.

A haka tana nan tsaye su Anisa suka k araso suka taddata. Anisa da Leenah suka dubi juna kafin Anisa ta k araso murmushi saman fuskarta. Tai tsaye gefen Ummul dake duban hoton.

 Aliyu Haidar Maitama. D a d aya tilo ga Engr Aliyu Maitama da kuma Hajiya Kwaise Maitama. Abinda Anisa kenan tace Wanda ya kuma haifar ma Ummul fad uwan gaba. Kenan wann shine Aliyu.. mijinta.? Sai ta kuma jin zuciyarta na bugawa da sauri. Musamman da Zuciyar nata ta ambacesa da mijinta wanda ko shakka babu da kokonta zuciyar nata ta raya mata.

Anisa ta murmusa tana ci gaba da kallon hoton  Mutumin da manyan mujallu ke rubibin hasko fuskarsa yana guje masu. Da matuk ar wahala kiga hotonsa koda cikin mutane saidai a bazata. Ta kuma murmusawa  But If you read papers definitely zaka iya sanin fuskarsa. Dan bana tunanin wann d anuwan nawa has any social media account. Ta kuma murmusawa tana girgiza kai  I guess my cousin is allergic to camera. He is the weirdest person with high standards I ve ever known. Ta juyo ta dubi Ummul  Shall we.. Abinci is ready ke muke jira ranki dad e.

Ummul ta murmusa kad an  Saidai ni Ina azumi yau d in..

Anisa da Leenah suka dubi juna. Anisa tace  Azumi ba cikin watan azumi ba.

Ummul ta kuma murmusawa  Yau d in alhamis ne akwai falala cikin yin azumi a wann ranar.

Leenah ta kauda fuska gefe tana rausayar da ido cikeda k osawa yayinda Anisa ta murmusa  Wow. A gaskiya kin burgeni Ummul. Zan so na koya daga wajenki.

Batace da Anisa komai ba sai murmushi da tai. Anisar ta janyo hannunta tana fad in suje she can wait in her room idan bazata zauna a table din ba. Nan d akin Anisa suka baro Ummul d in yanda Anisar da Leenah suka nufo teburin cin abinci.

Mommy ke tambayarsu ina Ummul d in.

Anisa ta waiga kaman wacce take nemanta  Oh mun fito tare daga d akina.. But where has she gone.? Tai maganar fuskarta d aukeda alamun tambaya.

Leenah tace  I think naga komawarta cikin d akin. Maybe ta mance wani abun.. Or she s Probably using the bathroom.

Mommy bata ce komai ba taci gaba da cin abincinta. Can wayarta yai ruri ta tashi daga table din tabi wani k ofan tana amsa kiran.

Leenah da Anisa suka dubi juna suna murmushi daidai lokacin Ummul ta fito. Su biyu ta tadda a table d in.

Anisa ta fad ad a murmushi sanda taga fitowarta  Har kin fito. Sorry we left you alone. Gashi na mance ban kunna miki Kayan kallo ba. You must be bored.

Ummul ta girgiza kai  A a kar ki damu babu komai. Ina so na koma ne naga garin da hadari na bar wasu Windows a bud e.

"Leenah ta girgiza kai  Haba Ummulkhair kan wann zaki wahalar da kanki. Umarni kawai zaki bawa ma aikata su miki.. Wai ko Har yanzu baki gane matsayinki bane a gidan nan.? Kinga koma abinki kiyi zamanki yanzu zamu shigo nasan kunya kikeji. Bazaki iya zama ki saka surkarki gaba tana cin abinci ba dikda ita Mommy normal ne wajenta abinki da civilized woman. Ta karkato sosai tana duban Ummul  Kinada babban sa a Ummul. Mata da yawa suna burin ina ma ace sune a matsayinki. Wayayyun mata Wanda suka had a komai na rayuwar duniya. If I were you, bazanyi wasa da wann damar ba. Ta kuma murmusawa  Kar ki damu a hankali zaki koyi irin rayuwar. Ta k arashe tana sakar mata murmushi kafin Ta mik e tana fad in  I ll ask one of the maids ta rufe windows din. Bata jira Cewar Ummul d in ba ta wuce b angaren ma aikatan cikin sauri Kai kace itace  yar gidan. Anisa ta dubi Ummul d in da murmushi."

Ummul Tai tsaye kaman mai tunanin wani abu. Magaganun Leenah take kuma nanatawa cikin kanta. Sai tanaji tamkar wani sak o Leenar ke son bata a dunk ule. Allah sarki da ace Leenah tasan ita wann auren ba da son ranta akai ba. sadaukarwa ne kawai ga ahalinta da bata fad i abinda ta fad i ba.. Ta d anyi still a wajen sai kuma ta juya ta koma d akin Anisar dan gabatar da sallar la asar da aka soma kira.

Bayan Sun gama cin abinci suna zaune suna hira nan d akin Anisa gaba d ayan su ukun. Da alama harta Leenah ta saki jiki da Ummul. Har kana iya jiyo shewan Leenah da Anisa alamun hira ta masu dad i. Ita dai Ummul saidai tai murmushi idan an fad i wani abun bakajin muryarta.

Suna tsaka da hiran suka soma sinkayo muryar Mommy tana doka kira ma ma aikatan gidan.

Anisa Tai shiru tana fad in  Kai ku saurara kuji.. Meke faruwa.? Kaman muryar Mommy nakeji cikin fad a.

Gaba d aya suka saurara aiko nan suka sinkayo muryar Mommy tana fad in kaf ma aikatan su hauro parlornta.

Anisa tace maza su tashi suje suji abinda ke faruwa.

Suka mik e gaba d ayansu suka nufo parlorn Mommy yanda suka tadda ta had a assembly ma gaba d aya ma aikata tana tambayar waye ya shigar mata d aki cikinsu.

Wann ya dubi wancan wancan Ya dubi wann. Kowa yace bai shiga ba tin gyaran safe.

Mommy ta d ago wani d an box hannunta. Cikin tsimewa taci gaba da fad in ta tadda jewelry drawers d inta a bud e kuma an d auki sark ar dake cikin box d in hannunta. Waye ya d auka.?

Anisa ta zaro ido waje  Mommy sata cikin gidan nan..? This is something unusual.. Abu ne da bai tab a faruwa ba.

Mommy taci gaba da jinjina Kai  If there s one thing I hate shine rashin gaskiya. Abu ne da akayi shi a cikin gida. And that s why dole a fito da koma waye yayi satan. If it takes ayi searching every angle na cikin gidan nan ne za ayi. Kayan kowa cikinku kaf sai an bincika. Ta k arashe tana duban ma aikatan.

Anisa ta jinjina kai  K warai Mommy a duba ko ina cikin gidan nan. I ll search the employees section myself. Mommy ta dubi babba cikin ma aikatan wacce tafi aminta da ita Tai assigning d inta da suje su duba su caje kaf b angaren ma aikatan. Daga b angaren ma aikata Anisa tace su nufi b angaren Ummul tinda Mommy kaf gidan tace a duba.

Su Mommy da Ummul suna tsaye tareda sauran ma aikatan a parlor wayan Mommy yai ringing. Anisa ce mai kira duk jikinta a sanyaye.

Mommy tace  Ehen I m listening to you. Kun samu sark ar.?

Anisa ta jinjina kai a hankali kaman Mommy na kallonta  Eh mommy mun samu..

Mommy taci gaba da jinina kai  Cikin kayan waye kuka samu tsakanin maids d in. Ki sanar da security guda d aya a kira  yansanda. Wacce duk tai satan must be punished kuma zata bar gidan nan a yau.

Anisa ta kuma fad i a sanyaye  Mommy you need to come see it yourself.. Ban san yanda zan sanar dake ba.. Amma Ya kamata ki gani da idonki.. I m still in shock..

Mommy ta girgiza kai kad an  Anisa.. Ban fahimceki ba.. Mai kike nufi.?

Shiru ne Ya biyo baya alamun Anisa na sanar da ita abinda ke faruwa.

Ta juyo ta dubi Ummul wacce damuwar abuja ke faruwa Ya nuna a fuskarta  Kin tabbata da abinda kike fad a Anisa.?

Jinjina kai Mommy tai a hankali kafin ta nufo k asa.

Sosai taji mamakin ganin sark ar cikin d akin Ummul. Toh amma Ya hakan ta kasance.?

Ma aikaciyar ta girgiza kai  Hajiya gaskiyar kenan. Nima naji mamaki sosai da abinda muka gani.

Mommy ta girgiza kai  Ummulkhair bata jima da zuwa gidan nan ba. Amma inada tabbacin bazatayi abu makamancin wann ba.

Anisa Tai Shiru kaman mai tunani  Nima dai Mommy ban zaci haka daga wajenta ba. Dukda yau ce rana ta farko da ta jima b angarenki..

Shiru Mommy tai tana juya maganganun Anisa. Tabbas yau ne rana na farko da Ummul ta jima irin haka a b angaren ta. Sann lokacin da suke cin abinci batazo teburin cin abinci ta zauna tareda su ba.

Anisa ta kuma duban Mommy kafin tace  Mommy bazanso hakan ta kasance ba.. Yarinyar nan ba saninta mukai ba. Ammi ce kawai ta Santa da background d inta.. I m sorry to say kinsan talakawan nan gold diggers ne. Ammi used to tell me this. Ta kuma duban Mommy sosai  What if Ammi batai bincike mai zurfi kan ahalin Ummul ba.. Kuma d azu da naje zan shigo da Leenah na ganta ta fito ta hanyar parlorn ki na sama. I thought kece kika aiketa wajen or something. Kuma one of the maid ta sanar damu taga Ummul wandering around the house.

Shiru Mommy tai tana juya maganganun. Sai kuma ta girgiza kai  I still find it hard to believe Ummulkhair zata iya aikata abu makamancin wann. But koma menene we ll find out about it. Je ki kira Ummulkhair da ita da maid din da tace miki ta ganta tana zagaya gidan.

Anisa ta jinjina kai  Yes Mommy. Lokaci guda tasa kai ta fice tana sakin muguwan murmushi zuciyarta fal nishad i.

Ba a jima ba Ummul da maid d in da Tai mata kwatancen hanya harma da Leenah suka k araso. Anisa na tafe gaba garesu.

Zuciyar Ummul yaci gaba da tsinkewa ba don tsoro ba sabida tasan akan gaskiya take ba abinda zai bata tsoro saidai a duniyarta ba abinda ta tsana irin a danganta ta da sata. Sata abu ne mai ciwo ace an danganta ka dashi. Koda ace ta fito gidan da basuda arziki Allah ya masu arziki da wadatan zuci wanda shine babban arziki. tayi imani basuda abinda zata sata. Sanda Mommy ta d ago sark ar tana nuna mata sai taji kuka yazo mata.

Mommy ta k araso ta dafata  Bance kin d auka ba Ummul. So nake kawai ki amsa min tambayata dan haka ne zai wanke ki. An samu sark ar a cikin d akinki.. Ta Ya haka ya kasance.?

Ummul ta girgiza kai  Ki yarda Dani Mommy. Ni ba b arauniya bace. Ban kuma d auka ba. Sann bansan Ya akai ya zo d akina ba. Gaba d aya ranar ina zaune cikin gida ban ma shigo b angarena ba.

Leenah tai kaf tace  But wait kince zaki zo ki rufe Windows d inki sabida hadari da kika gani gudun kar ruwa ya shiga miki.. Kodai lokacin ne kika fito kika kawo sark ar kika ajiye a d akin ki.

Ummul ta dubi Leenah cikeda mamaki dan ta ma kasa cewa komai yayinda Anisa Tai karaf tace  A a Leenah. Ai Ummul bata zo ta rufe Windows d in ba.. D aya daga cikin ma aikata ne tazo ta rufe Windows d in.

Leenah ta tab e baki  But samun sark ar a nan proves otherwise.

Ummul taci gaba da girgiza kai tana hawaye take fad in ita ba b arauniya bace.

Leenah tace  Prove it then.. So kike a d aura ma wani sharri bayan ga abinda aka gani.

Mommy ta aika ma leenah wani kallo ganin irin kukan da Ummul keyi.

Hannayen Ummul Mommy ta kamo tace  Idan kina son sark ar Ummul zan baki ita kyauta. Kar wann yasa ki d aga hankalinki. Ni ban kawo a raina zaki min sata ba. Duk abinda kika d auka nawa tamkar naki ne. Ke matar Haidar ce idan har zance kin min sata kaman nace Haidar ya mun sata ne. Duk abinda kika d auka gidan nan ba sunansa sata ba. Case closed. Ta k arashe murmushi saman fuskarta tana goge ma Ummul d in hawayen dake gangaro mata. Cikin zuciyarta cewa take ke d in makarin asirin d ana ne ko mai zaki min zan shanye har na samu Haidar ya dawo gareni.

Da mugun mamaki Anisa da Leenah suke duban juna baki sake. Wai shin wane irin makahon so Mommy ke ma yarinyar nan Wanda hankali bazai d auka ba. Wai Hajiya Kwaise ce ta zama very soft haka. Matar da sunyi imani irin sanin da suka mata yanda ta kama b arawon nan sai Ya d and ani kudarsa. Matar da sam bata yarda da wani shit ba.

Ummul ta girgiza kai ba don bata d auki maganganun Mommy da mahimmanci ba sai don bazata bari a mata shaidan sata ba. Amma ta ya zata wanke kanta. ta ina zata fara hakan.? D agowa Tai tana dubansu gaba d aya da idonta mai zuban ruwa. Sai ta dubi Mommy ta kuma girgiza kai  Ban d auka ba. Kiyi hakuri Mommy ban raina k ok arin ki na kula dani da bani duk wani kariya ba. Amma hankalina zaifi kwanciya idan har aka tabbatar banida laifi.

Leenah da Anisa suka kuma duban juna suna mamakin ta Ya za ai ta fidda gaskiyar.

Ummul Tai tsaye tana k are ma gidan kallo. Cikin zuciyarta kaw addua take  Ya Allah banida wani wayo sai abinda kayi dani. Ya Allah ina tawassili da azumin dake bakina Wanda nakeyi dan neman yardarka. Allah ka wanke baiwarka mai rauni daga wann sharri da aka k ulla mata.

Anisa ta katseta da fad in  Ummul Mommy ta aminta dake inaga ya kamata ki bar zancen a haka. I think You don t need to prove your innocence.

"Mommy ta girgiza kai  No, if she wants to prove her innocence bazan dakatar da ita ba. After all, I want to know who the real culprit is. "

Zuciyar Anisa Ya kuma tsinkewa. Leenah ta dubeta a tsorace itama. Nan ta fara wak an tafiya gida. Mommy tace babu mai tafiya sai gaskiya ya fito. Ta dubi Ummul tace suna sauraronta. Ta bayyana gaskiyarta.

Ummul ta jinjina kai a hankali kafin ta d aga kai tana k are ma gidan kallo.

Can k ofan shigowa sashen ta hangi security camera.

Leenah ta rausayar da ido tace  Ummul bakida wani hujja please don t waste our precious time here. I really need to leave now. Is getting late already.

Juyowa Ummul tai ta dubi Leenah tana murmushi  A a inada hujjar da zan kare kaina.

Leenah ta girgiza kai  So.. Where is your proof then.?

Ummul ta girgiza kai  Kiyi hak uri ban fahimci mai kike nufi ba.

Leenah tai murmushin rainin hankali tana duban Ummul a wulak ance  Common English bakiji har kina tunanin kinada wani intelligence da zaki iya canza abinda idonmu ya gani.? Is this a joke or something.

Jinjina mata kai Ummul Tai  K warai inada shi koda harshena bai iya furtawa ba. Ta d aga hannu Tai mata nuni da cctv camera. Taci gaba  Na tabbata shi zai tantance na fita daga

38 / 103