AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   75 / 103

222K to 225K   out of 306.8K words

babu Wanda ta sanar dashi. Nima abinda yasa naji tana waya ne na lab e na saurara nan naji da Addarmu Ummulkhairi take waya.

Mama Tani ta mik e tana duban Khulsum  Ke Khulsumu meke faruwa..? Yanzu dik irin d aga hankalin nan da kikaga munyi munata neman Ummulkhairi dama kinsan yanda take.. Shine kika kyalemu cikin duhu.. Muna nan muna tunanin Har yanzu fushi kike da ita Shiyasa baki tada hankali wajen neman ina take ba Ashe kina sane..

"Kuka Khulsum take tana girgiza kai   Yaruwata bata sanar Dani yanda take ba.. Amma nayi waya da ita kuma ta sanar dani cewa tana nan lafiya kar na damu ta kuma tambayeni jikin Abba.. Sann tace na kula da Umma kuma na nemar mata yafiyar Umma.. Sann.. Sai ta dubi Haidar da yai mutuwar tsaye yana dubanta, taci gaba  Sann tace ko ka zo nemanta kar na sanar dakai cewa munyi waya.. Dan har abada bataso ta sake ganin ko mai kamanninka.. Ta k arashe tana mai fashewa da kuka."

Cikin wane irin yanayi Haidar ke furta  No please.. Don t do this.. Please tell me.. Tell me idan ta sanar dake yanda take.. Ko kuma.. Ina layin da ta kiraki dashi.. Duk a daburce yake.

Khulsum ta girgiza kai  Ta rufe lamban bai fito ba..

Ya lumshe idanunsa yana dafe kai  No.. There has to be something.. Just think please.. Or maybe we can try to retrieve all the calls from your line.. And see if we can track the number..

"Ganin duk ya daburce yana neman ficewa hayyacinsa yasa Daddy d an yin gyaran murya yace  Haidar, taho nan ka zauna.. Abi komai a sannu.. Ya dubi Khulsum yace   Yanmata jeki abinki ko. Khulsum ta risina ta tana mai jinjina kanta kafin ta shige tana share ragowar hawayen da suka zubo mata. Azeema na take mata baya."

Tani ma ta dawo mazauninta ta zauna.

Daddy ya dubi Haidar yai gyaran murya  Haidar ina so ka natsu ka kuma natsa zuciyarka. Yanada kyau mubi komai cikin lumana dan tada hankali bazai tab a kawo mana maslaha ba. Idan har Ummulkhair tana cikin k oshin lafiya wann ma abun mu gode ma Allah ne. Kuskure ne an riga anyi shi dama kuma shi gyara sai a hankali.

Tani ta jinjina kai  Wann gaskiya ne.

Daddy ya kuma jinjina kai kafin yace  Amma yaya jikin Maigidan..? Yana asibiti ne Har yanzu kokuwa..? Mai likitoci suka ce gameda rashin lafiyar nasa.?

Tani ta dan gyara mayafinta  Toh jiki Alhamdulillah zamu ce. Sann asibiti kuma sai jikin ya d anyi tsanani ake zuwa.. Yana nan a gida. Saidai maganar ne ba sosai ba.. Amma yakan fahimci wasu abubuwan.. Rahotannin asibitin nasa duk yana wajen d iyarsa Khulsumu dan kusan tareda ita akai jinyar nasa gaba d aya. Ba abinda zamuce ma yarinyar saidai Allah shi mata albarka.

Daddy ya jinjina Kai yana fatan lafiya ga Abban kana ya mik e yace  Ko zamu iya ganin shi.?

Tani ta jinjina kai  Eh yana d aki yana kwance. Mu k arasa. Bismillanku.. Tai gaba Daddy da Haidar na biye da ita suka nufi wata  Yar k aramar k ofa da zai sadaka da d akin Abba.

Suka d an tsaya daga waje kafin Tani ta shiga ta tadda Umma ciki nan take sanar da Umma su Haidar da mahaifinsa zasu shigo su gaida Abba dama tuni Tani d in ta sanar da ita zuwansu.

"Umma ta gyara zamanta ta dan gyara Abba ma kafin ta rufe kanta da mayafi, Har rabin fuskarta saida ta rufe sabida surkunta."

Tani Tai masu iso. Daddy ya soma d an rage tsawonsa ya shige d akin Haidar na biye dashi.

Suka gaisa da Umma suka tambayi mai jiki kafin Tani ta d an matso kusan Abba tana sanar dashi ga Surkin Ummul da mai gidanta zasu gaishe shi.

Allah sarki Abba sai ya soma k ok arin mik ewa jin an ambaci Maigidan Ummul d insa da surkinta. Daddy yai saurin taimaka masa yana masa sannu da jiki dukda muryar Abban ba wani sosai yake fita ba.

Bayan sun gaisa da Daddy sai ya fice amsa wayarsa dake ruri.

Cikin muryarsa da bai fita sosai irinta majinyaci mai Jin jiki Abba yace  Ina Maigidan Ummulkhairina.?

Haidar ya k araso cikeda risinawa yana gaida Abba zuciyarsa ya kuma cika da tausayin Khairy da ahalinta. Sai Abba ya soma k ok arin d ago hannu yana mik a ma Haidar alamun yana so suyi masabaha. Haidar yai saurin tallafo hannun Abban ya rik e cikin nasa suka gaisa. Sai yaji Abba ya rik e hannunsa gam yana fad i da kyar  Kaine Aliyu mijin Ummulkhairi na..?

Sai Haidar ya jinjina kai a hankali  Eh.. Eh Abba ni ne..

"Abba yaci gaba  Ina matuk ar son  Yata Ummulkhairi, tanada zuciya mai kyau.. Ka rik e mun.. Ita da amana kaji koh.. "

"Dukda tausayin Abba had ida wani abu mai kama da rauni da Haidar keji yana taso masa tin daga can k asar zuciyarsa bai hanasa jinjina Kai cikin sauri, ya soma furtawa cikeda k warin gwiwa  In sha Allah Abba.. Zan rik eta& Zan rik e Khairy amana.. Na maka alk awari.! "

Abba ya murmusa had ida jinjina kai sai kuma yace  Ina Ummulkhairi.. Maiyasa bata biyoka ba..? Na jima ban ganta ba. Ina kewar..  Yata sosai.

A nan ne kuma jikkunansu gaba d aya yayi sanyi. Babu ya Haidar Wanda ya gama d aukar ma majinyacin mutumin alk awarin kular masa da  yarsa wacce baisan ina take ba.

Sai Tani Tai karaf tace  Ai.. ai laulayi take& K aramin juna gareta shiyasa bata samu zuwa ba. Ita kanta Tani da tai maganar saida taji banbarak wai. Yayinda Umma tai saurin dubanta da idanunta masu cikeda rauni. Shi kaw Haidar sai ya sadda kansa kad an.

A haka dai Har suka fito zasu tafi. Baffanin Ummul guda biyu da suka amshi kud ad e hannun Asshe suka bada Auren Ummul d in nan suka jeru suna jiran fitowar su Haidar ganin hamshak iyar motar da ke k ofar gidan nasu. Sai jinjina lamarin suke suna fad in albarkacin bakinsu gameda mijin Ummulkhairi da mahaifinsa Wanda Tani ta hana su gana dasu a cewarsu.

Ai ko suna ganin fitowar su Haidar suka k arasa kaman zasu kwanta suna mik o ma Daddy hannu alamun musabaha. Daddy da Haidar suka tsaya suna gaisawa da mutanen cikeda girmamawa. Nan sukai introducing kawunansu matsayin K annen Mahaifin Ummulkhairi kuma Wanda suka bada Auren ita Ummulkhairin. Nan suka sake sabon gaisuwa na musamman suka kuma cikasu da goma na arziki daga Daddy har Haidar din babu wanda aka bari baya. Kowa kokari yake yayi alkhairi daga aljihunsa. Alkhairin da ya bar su Baffah Ado cikin tsananin al ajabi. An masu kyautan ban girma sai kawai suka fara wasa Ummulkhairi cikin gidan suna cewa ta kawo alkhairi. Wacce a baya suka kyamaceta da k addararta Har cewa suke tana bata sunan zuri a da muguwar bak ar k addararta yau sai gasu nan suna rigen kiranta jininsu. Rabon da su shiga sashen su Ummul su duba D anuwansu tinda Abba da Khulsum suka dawo daga Jigawa can gidan Inna Dije. Yau sai gasu nan tsamo tsamo suna kiran Abba Yayansu. Tani kaw ta masu d add aya tana fad in maza aci arziki. Ummulkhair da suke ambato da Ummulsharri a baya yau sai gashi suna k aryata harsunansu dan cewa suke ta amsa sunanta Uwar alkhairi.

**

Bayan Haidar ya kai Daddy masauk i nan suke tattaunawa da Daddyn gameda ciwon Abba. Daddy yace  Inaga ko zakaje Asibitin ku tattauna da Likitocinsa na nan. Sai a duba hospital report din nashi kaji shawarwarinsu.. Idan yaso ko can Abuja ko dan ta kama a fitar dashi abroad ne sai su sanar dakai.

"Haidar ya jinjina Kai  Ina da wann plan din Daddy.. Hospital din da na kwanta lokacin da na samu had arin mota is a prestigious hospital, sunada likitoci k wararru daga k asashe da dama sunada advanced technology.. In fact is a foreign hospital.. Because a yanda naga jikinsa ba Lallai Likitoci su bamu shawarin a fita dashi kai tsaye matuk a akwai solution a nan.. Duba da process din da za a bi. Dan Ga dukkan alamu yana jin jiki sosai. Amma zan tuntub i Likitocin nasa kaman yanda kace. "

Daddy ya jinjina kai  Good.. Yayi kyau.. Toh ai inaga ni zan bi jirgin yamma na koma. Zan turo Sadis (Daya daga cikin trustees d in Daddy ne a wajen aiki) sai ya tayaka ku kula da al amran.

Haidar ya dan murmusa yana risinawa  A a Daddy da ka barshi. Zan kula da komai by myself.. Financially da dik wani abinda ya kamata.

"Murmusawa Daddy ya d anyi yana jin dad in yanda D an nasa ya zama responsible. Sai yace  Even so, Sadis zaizo ya tayaka da wani abin. Jirgin yamma nake son bi. Ya k ara maimaita ma Haidar d in."

Sai Haidar yai saurin jinjina kai  I ll call the airport right away Ya fad i yana mai ficewa. Daddy ya jinjina masa kai.

Haidar bai bar garin ba saida ya tabbata an shirya duk wani abinda ya kamata gameda tafiyan Abba zuwa prestigious hospital din da za ai treating d insa. Umma tace fir saidai Mama Tani ta tafi tareda Abba ita zata zauna da yaran.

Haidar ya musu goma na arziki dukda cewa da Umma take ya daina d awainiyar nan musamman idan ta tuna abinda ke faruwa na rashin Ummul. A cikin zuciyar Haidar kaw cewa yake baiyi rabin abinda Khairy ta musu shida ahalinsa ba. Cikin zuciyarsa yana kewarta sosai.. A koda Yaushe k aunarta k aruwa masa yake.

Kafin ya bar garin da yamma yana zaune saman tabarma a haraban gidan dan tuni ya zama D an gida. Azeema sai zuba masa surutu take ta d auko wani tsohon album d in Abba tana nuna masa hotunan Ummulkhairi harda Wanda take sanye da uniform na makaranta. Ya jima yana kallon hoton. Sihirtaccen murmushi saman fuskarsa.

Azeema taci gaba da basa labarin k uruciyarsu Har ta gangaro kan samarukan Ummul da ake saka musu rana a fasa. Har kan Zubairu da su Alhaji Kamilu da yanda kowa ya zata Zubairu zata aura sabida yanda Zubair d in yaso Ummul. A nan ne fah sukaga Haidar ya had e rai tamau. Badia sai mintsilin Azeema take tana fad in Tai shiru haka nan amma inaa Azeema sai zuba take yawa kurna.

Mama Tani ta kawo masa abinci tana fad in su Azeema su kyalesa haka nan yaci abinci.

Azeema ta dubeta ta dubi tuwon. Tuwon gero ne da miyar yauk i.

 Haba Mama ya zaki bashi irin wann abincin. Na tabbata bai ma tab a gani ba.

Haidar kam ma iya cewa baima abindake faruwa ba. Dan tinda Azeema tai mentioning Zubair tsohon saurayin Ummul ya rasa sukuni.. Sai ya dan dubi Azeema ya girgiza Kai kad an yace  Amma ina Zubair yanzu.. Yayi Aure.?

Azeema ta saka ma bakinta sakata tana Zare ido. Badia ta rankwafo had ida rankwashin Azeemar kad an ta rad a mata  Kin gani koh. Ke baki san kishi irin na maza bane kinzo kina labarin tsaffin samarukan Ummul. Yanzu gashi kinsa mutumin na miki wasu tambayoyi. Haba Azeema mutumin nan fah ji yake kaman Ummul ta kufce masa kenan tinda sun rabu.. Idan baki basa k warin gwiwa ba bazaki basa dalilin rura wutan tashin hankalinsa ba.

Azeema tai murmushin da yafi Kama da yak e ta dubi Haidar tace  Wann ai tsohon labari nake sanar dakai Yayanmu. Zubairu ya jima da auren  Yaruwarsa wacce ake so a had asu tuntuni.. Ta shiga tura foodflaks din abincin da aka kawo masa tana fad in  Kaci abincinka Sirkinmu. Tuwon nan idan yai sanyi babu dad i.

Badia ta harareta tana girgiza Kai ta janyo Azeema suka bar wajen tana rad a mata  Kedai wacce tai jegonki bata farse wann bakin naki ba.

Azeema ta kuma kame bakin ta tana fad in  Wllhi na sani& Duk yanda akai Inna Dije ce. Suka dara a tare Badia tana fad in Allah ya shiryi Azeema.

*

Kafin ya tafi saida ya k ara tuntuban Khulsum ko ta sake samun kira daga Ummul. Khulsum tace bata sake kiranta ba. Su kansu saida Haidar ya basu tausayi. K arshe haka ya hak ura ya bar garin ba don yaso ba.

**

"Idanunsa na duban window yake ci gaba da fad in  It s been three months Hisham. Wata uku babu Khairy.. And Dareen is nowhere to be found. I feel lost, tiny and insignificant in this world.. "

"Hisham ya sauk e ajiyan zuciya  I believe everything happened for a reason. Ya dan furzar da huci had ida girgiza Kai  I have never met your wife Haidar.. Amma abinda na kula shine kana k aunarta sosai, because ban tab a ganinka cikin yanayi na soyayya irin haka ba.. Ya dan numfasa  Kuma koda ka kasance mutum da bai cika bud e al amransa ba jikina yana bani ba k aramin abu bane ya shiga tsakaninku. "

Sai Haidar ya dubesa amma baice komai ba.

"Hisham ya jinjina Kai kad an  Whatever is the case Haidar, know that I m here for you.. And you can always count on my support. Ya jinjina Kai alamun tabbatarwa.  Idan zakaje kaci gaba da Neman matarka ni zance naci gaba da"

"nemar maka Dareen. Ko ba don ka hukunta Dareen ba sai dan D anka dake cikinta. Ko ya kayi Haidar, that child she s carrying is still yours.. Kuma baida laifin komai.. Bazaka hukunta shi da laifin mahaifyarsa ba. "

Haidar ya tsaresa sosai da ido wann karon sai ya girgiza Kai yace  Are you even sure that child is mine.? Shiru Hisham bai amsa shi ba saima tunani da ya soma cikin zuciyarsa  Bastard! Zaka sheganta wann D an kaman yanda Ubanka ya shegantani a ciki.! Kai din baka rage ma Ubanka komai ba Haidar.

"Hisham ya sinkayo muryar Haidar sanda yaci gaba  Wha if babu wani ciki. What if k arya take, tinda iyakacin tarayyata da ita k arya ne kawai.! "

"Hisham ya dan furzar da huci yana mai d aga gira sama  Bazan k i maka ba. Kuma bazanga laifinka ba.. Because you ve been fooled and betrayed. Amma Kai tunani Haidar.. Kayi rayuwa na Aure da Dareen koda ace rayuwar ta k arya ce. You were once husband and wife.. You cannot deny that. So ba abin mamaki bane idan tana d auke da gudan jininka.. I mean, if you neglect that child zai tashi ne da tsanar koma waye mahaifinsa.. Meyasa  ya ya zasu biya kuskuren da iyayensu suka aikata..? Hakan ba adalci bane. Yanda yake maganar tamkar yana digging ma Haidar past d insa ne."

Hisham yaci gaba  You can t let that child pay the price Haidar.. You know exactly how it feels mutum ya girma babu soyayyan iyayensa. You can t make that child a victim. You can t let that happen to your own child.! Ya k arashe cikin tsananin k warewa tareda tono ma Haidar bayansa. Yanda ya girma da tunanin iyayensa basa sonsa duk sabida wani kuskure da mahaifyarsa ta aikata. Ya rintse idanunsa yana jin kamar dai duniyar ta dad a juye masa. Sann gaskiya ne abinda Hisham ke fad i. Because shi Kansa Haidar d in was once a victim. Bazai bari tarihi ya maimaita Kansa cikin ahalinsa ba.

Hisham ya tsaresa da ido cikin zuciyarsa cewa yake  Kai da ahalinka bakuda daman yin wani farin ciki

75 / 103