AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   23 / 103

66K to 69K   out of 306.8K words

yin b aranb arma ya sata sassauta murya tace  Anisa ni mahaifiyarki ce, kuma ki yarda dani I want nothing but the best for you. So idan nace ki yarda dani ma ke nake wann yak in ki yarda kawai. Zaki mallaki Haidar. Zai zama naki Watak ila nan da watanni k alilan kinji koh. So ki kwantar da hankali ki and trust your Ammi. "

"A hankali Anisa ta sauk e ajiyan zuciya  Shikenan Ammi, if you say so. I trust you, hundred percent. "

Bayan sun Ida wayar zama Anisa tai tana tunanin maganganun mahaifiyarta. Ta ya zata goyi bayan wann auren.? Abun da kamar wuya. Ta mik e jiki babu wani k wari ta shiga unpacking kayanta.

**

"Yana tsaye k asan shower ruwan na sauk owa tin daga cikin sumarsa har zuwa jikinsa, saurin bud e idanunsa yai Wanda suke a lumshe sakamakon hoton fuskar yarinyar da ya gaza b acewa a kwanyarsa da kuma k wayar idanunsa. Ba wai fuskar nata yake gani cikin k wayan idanunsa ba. Dan bazaice ga kamanninta ba. A a kwantattun hawayen da shi kad ai ne yai noticing a hoton yake gani. Sau d aya tak ya kalla, maiyasa ya kasa cire hoton cikin idanunsa, meyasa duk rufe idanun da zai sai yaga idonta masu d auke da hawaye.. Maiyasa ta amince da aurensa.. Meyasa hawayenta kawai ya iya noticing.? Shin dole aka mata.? Shin Wacece ita ma.? Shin tasan shirin Mommy Akan auren cewa AUREN WATA UKU zasuyi kuma dalilin auren shine mahaifinsa ya mallaka masa project. Shin tasan duka wad ann ta amince da aurensa.? Is she that lowlife.? Wacece zata amince da irin wann wulak antaccen auren. Does she have any idea who he really is.? Does she even know what she s getting herself into.? Tambayoyi da yawa Wanda idan ba ita ba babu mai amsa masa. Take yaji zuciyarsa ta soma raya masa  Maybe she s aware of everything.. Maybe kaman yanda Mommy tai deal dakai Akan auren haka itama tai deal da ita.. Mommy zatayi komai dan abinda take so. He knows his mother har cinikin auren zatayi. What if wann yarinyar cinikin aurenka tayi"

da Mommy.? Take yaji zuciyarsa na masa wani irin zafi. Ji yai ya kuma tsanarta. Ya tsani mutumin da zaiyi komai sabida kud i da abin duniya. Sauri sauri ya fito daga shower d in dan baiso yaci gaba da tunanin.

Yana fitowa ya tadda Dareen har ta kwanta. Ya k arasa shirinsa kafin ya isa gefe ya kwanta. Saidai kwanciyar sa da kad an ya soma sinkayo sautin Dareen a hankali kaman na mai kuka.

"Ya d an mirgino yana dubanta, nan yaga har kaman shesshek a take. Side lamp ya kunna ya mik e daga kwamcen da yake  Hey. Ya furta a hankali."

"Jin bata amsa ba ya sanya shi matsawa kusanta ya mirgino da ita, nan yaga hawaye Sun wanke mata fuska. Baison ganin hawaye tin yana yaro. Watak ila hoton yarinyar can da ya gaza b ace masa a k wayar ido ma sabida hawayen da ya hango ne cikin idonta. He hates to see people cry.. A nashi tunanin ba abu k arami bane zaisa mutum kuka. A lokacin yarinta duk irin abubuwan da yai going through baya iya kuka koda yana son yi. So he believes idan har baiyi kuka lokacin yarinta lokacin da ya kamata ace yayi ba dukda irin abubuwan da ya fuskanta a rayuwa Lallai ba Abu k arami bane zaisa mutum kuka."

 What s wrong.? Ya tambaya cikin kwantar da murya idanunsa tar kanta.

"Dubansa tai sai kuma ta girgiza Kai  Haidar I don t know.. Ban sani ba, I.. I just feel like I m losing you somehow.. "

"Zuba mata ido yai tausayin ta fal k irjinsa. She s right, a kwanakin kaman ya nesanta Kansa da ita. Above all, wann auren shirin ko yace auren yarjejeniya da Mommy ke yunk urin yi masa yasa ya d auke masa hankali da tunani.. He feels like he s not being fair to her.. Koda ace bai mata irin son da take mishi. She s still his wife kuma ta cancanci kula na musamman daga wajensa. Hannayenta ya rik e cikin nasa suna fuskantar juna. Yayinda Dareen taketa addu an Allah yasa tarkonta ya d anu. Bata isa tace ga weak point d insa ba tinda tasan shi mutum ne da ba kasafai ake iya karantar yanayinsa ba. What she s sure about shine shi Mutum ne mai tausayi wanda ta fahimci haka from his actions, especially towards mutane masu rauni. Yanada tsananin zafi saidai a wasu lokutan tausayin masu rauni da yake dashi yakan rinjayi zafin sa. Da wann takanyi amfani ta tatsa duk wani information gameda rayuwarsa. Ta kula yanzu kaman ya daina sanar da ita abubuwa da dama. Ya fara komawa kaman dai Haidar d in da ta soma sani daga farko kafin aikin aisiri yai tasiri akansa. Muryarsa ta sinkayo yana fad in."

 I have been dealing with so many things lately& That I even lost sight of what s more important.. I mean you..! Gajeren murmushi saman fuskarsa ya kuma rik e hannayenta cikin nasa yaci gaba da fad in  But I ll make it up to you.. Just choose a place from the map.. Let s go for a vacation.

"Surprisingly take dubansa  Really, vacation..? Na zab a duk yanda nake so from the map.? "

Murmushin bai bar saman fuskarsa ba yake jinjina mata kai  Just mention the place.. Any place you have in mind.

 OMG.! I love you.. I love you so much.. Ta fad i tana mai fad awa jikinsa sabida murna.

 I ve never been to Cuba. Let s go to Cuba. Zan duba mana best Resort da sukeda shi. Ta fad i murmushi saman fuskarta.

"Shid inma murmushin yai kafin ya jinin Kai  Alright Cuba, Lets explore Cuba then. "

Rungumesa ta kumayi zuciyarta na raya mata ta mance komai ta daina binciken komai tabi mijinta suje su sha soyayyarsu.

"A b angaren Haidar kaw cikin zuciyarsa yake ayyana wann shine maslaha. A daidai lokacin da Mommy zata kawo masa yarinyar can matsayin mata zata shafa ne taji baya nan.. Bazai dawo ba sai bayan wani lokaci, zai timing lokacin da zasu fara gudanar da project d in kafin ya dawo k asar."

**

Kano

Da tsananin mamaki Hajjah Fannah ta dubi agogo Jin da gaske buga mata k ofa ake. K arfe shad aya na dare har ta gota. Ta fito da kyar dan har kawo lokacin bata wani Jin k arfin jikinta.

Khulsum ta gani tsaye k ofar gidan ga alamun hawaye saman fuskarta.

 A ah! Khulsum. Lafiya? Ina kika fito cikin Daren nan..?

Khulsum bata iya amsa mata ba sai ma wani sabon kukan da ta fashe mata dashi. Hajja Fannah tai saurin kamo hannun Khulsum suka shige cikin gidan.

Ruwa ta soma kawo mata tace ta sha ta samu natsuwa. Ta d an dubeta  Khulsum ina Ummul..? Meke faruwa ne wai.. Inji ba wani Abu bane ya kuma faruwa.?

Khulsum ta saka bayan hannunta ta share hawayen  Hajja Adda Ummul ta tafi.. Umma ta saida ita.. Tabi Umma.. Ta amince da auren da Umma ta shirya mata.. Ta zab i tayi biyayya ma Umma bisa auren da ta shirya mata a bayan idon mahaifinmu.. Su d in basuda wani banbanci da Mama da yaranta masu burin ganin bayan Abba..! Ta k arashe tana mai kuma fashewa da kuka.

Hajja Fannah ta dubeta da mamaki  Aure kuma Khulsum. Aure Ummul zatayi.?

Khulsum ta jinjina mata Kai har lokacin jikinta a mace yake.

Sai Hajja Fannah ta nemi duk wani ciwon da takeji ta rasa. Taci buri ma d anta Wanda ko shakka babu shima ya auka ma soyayyar Ummulkhairin. Saidai kana naka Allah na nashi kuma na Allah shine daidai.

Jiki a sanyaye ta dubi Khulsum  Wanene mijin da zai auri Ummul.?

Khulsum ta girgiza mata Kai tana mai tab e baki  Bana tsammanin ko ita kanta Umma da ta had a auren ta sansa.

"Sauk e ajiyan zuciya Hajja Fannah tai, wani irin batu ne ita kanta Umman nasu bata san mijin da ta nemo ma Ummul ba. Ta yaya haka zai kasance.? Ummul ta wahala a rayuwa bazataso ta kuma fad awa wani wahalar ba. Lokaci yayi da za a dakatar da mahaifiyar Ummul. Idan ahalin su Ummul bazasu iya dakatar da Suwaiba ba zata nemi taimakon manyan Unguwa musamman mai Unguwa da commette d insa asan halinda ahalin Malam Isubu ke ciki ayi k ok arin dakatar da Suwaiba tun kafin mai aukuwa ya auku."

Ta dubi Khulsum tace  Kici abinci ki kwanta ki huta na Miki alk awari in sha Allah zanyi iyaka abinda zan iya dan naga mahaifiyarku bata salwantar da rayuwar Ummul ba da izinin Allah.

Khulsum ta jinjina mata Kai ba tareda ta iya cewa komai ba.

Hajja Fannah dai mamaki ne ya kasa saketa. Sai sak awa da warwarewa take tana tinanin toh waye mijin da Suwaiba ta kawo ma Ummul Wanda ita kanta bata sanshi ba. A haka ta kwana cikin daren tareda zullumin idn har auren Ummul ya tabbata batasan ta yanda zata soma sanar da tilon d anta Wanda ta jima tana binsa da batun aure yana kaucewa sakamon k azafi da mahaifinsa ya jefasa dashi tin yana d an watanni uku a ciki. Daga k arshe Hisham ya samu macen da take tunanin zasu samu daidaito sai ga kuma abinda ke shirin faruwa. Tabbas Zuciyar D anta zai karaya.

Washe gari ma Khulsum wajen mahaifinta ta yini dan ko ta kan ahalinta bata kuma bi. A cewarta dukansu basuda banbanci da juna.

*

Washe gari masu kawo lefe Sun samu isowa gidansu Ummulkhairi. Tin daga bakin layin ake k irga motocin dake shigowa domin kawo lefen Ummulkhairi.

Su Azeema sukai layi suka jeru nan tsakar gidansu suna duban masu shigo da lefe.

Tin suna k irga akwatuna har dai suka hak ura da k irge suka zuba ma sarautar Allah idanu.

Azeema ta tab a Salima tace  Yaya Salima anya wann ba kwari suka saya gaba d aya ba..!

Salima ta sauk e ajiyan zuciya  Ni na ma rasa abin fad i.

Gajeren tsaki Badia tai  Mtseww aikin banza.. Wann da gani kasan kayan haya ne ba lefe ba.. Tana ida fad in haka ta d age labulen d aki ta shige.

Azeema ta dubi Salima tace  Kin ganni nan wallhi baza ayi hidimar nan babu ni ba.. Gwara na shiga a dama Dani dan nasan duk rintsi sai an sallameni da atampa da jaka da takalmi na samu na yak an dangin Habibu.

Salima ta tab e baki  Amma Azeema matsalarki kad an ce..! Tana ida fad in haka itama ta fad a d akin mahaifiyarsu. Duk suka zuba tagumi suna Jin yanda hayaniya ke ci gaba da tashi. Zancen guda d aya ne Ummul tayi dace.

Azeema kaw tuni ta nufi bakin farandar Umma yanda ake baje kolin kayan lefen Ummul. Sai zuzuta kyaun kayan take tana fad in  yaruwarta tayi goshi..

Umma ta dubeta tace  Kar ki damu Azeema dake za a tafi kai amarya.

Azeema ta daka tsalle tana fad in  Wllhi Umma ni har zaman d aki ma sai na mata ai.. Irin wann kayan bajinta kayan alatu haka. Kai ina ma nice mai sa a irin Ummul..

Anzo yanda Umma take so. Taji ana ambaton Ummul d inta da mai sa a.. Umma ta shiga washe baki tana jin yanda mutane ke fad in K warai Ummul tayi goshi ita d in mai sa a ce.

Haka akaita shigo da zuk a zuk an akwatina da sunan lefen Ummulkhairi. Kan kace me labari Ya karad e unguwa.

"Umma naku fah ba a sama ba a k asa, uwar amarya da kanta. Duk magulmatan unguwar masu tsegumin Ummulkhairi ta kasa auruwa Sun dawo b angaren Umma. Mama taga tijara a wann ranan, dan tuni Umma ta amshe girman nata kama daga cikin gida har zuwa wajen mutanen unguwa Wanda a baya suke aibata su."

Uwa uba da sukaga su Hajja Asshe matsayin iyayen mijin da zai auri Ummulkhairi dan tuni d aya daga cikin kawayen Asshe ta soma bada bayanin ko su waye su. Hakan ya kuma sanyar ma kowa gwiwa dan mijin Asshe dai ba b oyayyen mutum bane a birnin Kano da kewaye. Hakan Ya kuma tabbatar masu Umma dai ba hark ar shan jini ta fad a ba kaman yanda duk sukai zato a baya. Allah ne ya kashe ya basu. Lokacin su ne yayi.

Azeema sai kallon Hajja Asshe take sanda taji tana yabon surkarsu Ummul. Sai duban dank ara dank aran gwal d in dake zube wuyarta da awarwaron dake hannunta take. Ga wani k amshin  yan gayu na musamman da matan suke. Dan Asshe ita da K awayenta suka kawo lefen.

**

Yanda Mama taga rana haka taga dare. Ko asibiti wajen mijinta ta kasa komawa tinda taga an kawo lefen Ummulkhairi. Ta mik e ta shiga safa da marwa a d an tsukikin d akinta tana neman hanyar da zatabi ta hana yuwan wann aure.

Wani tunani ya fad o mata. A fili ta furta Dije. Dije ce kawai zata sa wann aure Ya watse.

Cikin sauri ta isa tana bubbuga k afar Badia wacce tinda Tasi u Ya b ace ta dawo kwanan gida.

" Badia, ke Badia.. Tashi mana..! "

Badia ta mik e tana mutsuka idanu da kyar  An fara shagalin bikin ne..?

 Shagalin bikin Ubanki..! Mama tace tana danna mata dak uwa.

Badia taja tsaki tana turo baki gaba  Haba Mama ni wllhi na zata shagali aka soma inata mafarkin mun tafi Kai amarya an raba mana motoci matsayin tukwici kin wani kama kin tashen.

Mama ta kuma danna mata harara  Dan ubanki murna kike wann annobar zatai aure bayan ke ga naki auren yana sama yana k asa. Allah kad ai yasan yanda wann macucin mijin naki ya gudu.. Ba abun muyi k ararsa ba mu tona ma kanmu asiri& 

Badia tace  Mama Tasi fah ba guduwa yai ba. Ni na tabbata yana can yana juya mana kud ad enmu sai yayi arziki kaman mijin da zai auri Ummul kafin ya dawo. Na fad a Miki ko jiya fah Munyi waya dashi.

Katseta Mama tai tana mai kuma danna mata wani ashar d in  Ashe ke babbar shashasha ce. Yacce kika san Suwaiba ce ta haifeki.. Ba dan ina tsoron tonuwar asirina ba ace na saida gadon mijina tun kafin ya mutu wllhi da na maka k arar wann d an iskan mijin naki a Kotu..

Badia ta shek e da dariya  Toh ai saidai ki maka k arar wofi Mama. Dan Tasi dai ba ganinsa zakiyi ba sai Ya zama hamshak in Mai arziki ya dawo mana da kud ad en mu.. Wai baki so muyi arziki kaman nasu Ummul ne..

 Idan kika sake kira mun Ummul a nan zan zagi gawa ka k i kabarin uban nan naki dake kwance. wann aure kuma ba yinsa za ayi ba dan alwashi na d auka. Bani wayarki.. Ta k arashe tana mik a mata hannu.

"Badia ta dubeta sai kuma ta mik a mata  Mama me zakiyi da wayata, ni dai dan Allah kar ki kira Tasi ki zagesa dan nasan halinki.. "

Bata amsata ba sai ta mik a mata nata wayar  Ungo nemo min lambar Dije.. Allah Sa dai bata canza layi ba..

Badia ta dubeta galala  Mama Inna Dije kike nufi ko wa..?

 Dije k anwar Ubanku Isubu kira mun ita..

Badia tace  Mama me zaki fad a mata a tsohon daren nan.. Sanin kanki ne Inna Dije da Abba harma da ahalinsa sun raba gari tun da jimawa..

Mama ta jinjina kai  Waye sila..?

Badia tai k uri tana dubanta.

Mama taci gaba  Suwaiba da bakinta ta fad a cewa  Yarta Ummul ita tai sanadin barin Fa iz duniya dan haka zan kira Dije na sanar da ita komai na kuma kunna mata recording d in da kikai a wayarki lokacin da Suwaiba ke fad in Ummul ce tai Sanadin Fa iz.. Sai muga ta yanda za ayi ai wann aure tinda naga su  yan uwan mahaifin naku an rufe bakinsu da kud i.. Dije ita kad ai ce zata

23 / 103