AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   36 / 103

105K to 108K   out of 306.8K words

nadamarta a fili Har dai Suwaiban Tai mata hanyar fita..

Dum!! Haka k irjin Umma ya buga dan ita kanta bata isa tace ga kalan sirakan Ummul ba. Uwa uba rabuwar da sukai da Asshe Wanda Asshe tai mata iyaka da gidanta.

Tani ta tsare Umma da ido. Cikin zuciyarta take ayyana tinda na sauko da kaina Suwaiba dole kimin abinda nake so. Ta haka ne kawai zan samu na fito har na fahimci mai kike b oye min gameda auren Ummul.

" Ke nake sauraro Suwaiba, zaki min wann alfarmar.? Mama tace tana tsareta da ido."

Zuciyar Umma ya kuma tsinkewa. Ta d ago tana duban Mama cikin sanyin jiki&

SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!*

*27*

*©þSameena Aleeyou& *

Umma ta girgiza kai a hankali  Kiyi hak uri Yaya.. Bazan iya Miki alk awarin komai ba a halin yanzu. Tai maganar ba tareda ta iya duban fuskar Mama Tani ba.

A dak ile Mama ke dubanta  Suwaiba.. Kina nufin bazaki taimake ni ba..? Kenan kema kin zab i a tura ni kurkuku kaman Dije.?

Umma tai saurin d ago kai tana girgizawa alamun a a.

Tani ta gyara zama  Toh idan ba haka ba yaya ne.? Bakida wani maraba da Dije Suwaiba.. Banyi zaton haka daga wajenki ba Suwaiba.. Sai ta fara hawaye  Bayan ke banida kowa Suwaiba..  Ya ya na Sun guje ni.. Mijina na kwance jinya ta cinyesa.. Ke da nake zaton zamu taru mu rufa asirin juna kema kin juya mun baya Suwaiba.? Sai ta fashe da kuka tana fad in bata zaci haka daga Umma ba.

Lokaci guda Mama ta mik e tana huci  Tinda haka kika ce Suwaiba.. Shikenan kije abinki.. Kije kici arzikin sirakanki ke kad ai. Ni kuma in sha Allahu babu ni babu Ke Suwaiba. Kar ki sake tako inda nake idan har ba taimako na zakiyi ba. Tasa kai zata shige Umma tai saurin mik ewa ta tareta  A a Yaya. Dan Allah kar kice haka.. Ni ahalin yanzu banida kowa nima sai ke. Bamuda kowa sai mu biyun.. Amma..

Katseta Tani tai  Amma me Suwaiba.? Tai maganar tana tsare Umma da ido.

Gaba d aya Umma ta daburce bata San mai zata sanar da Mama Tani ba. Bata san ta yanda za ayi ta sanar da ita cewa itama ta riga ta k are mata ba. Tai saurin jinjina kai  Toh. Toh.. Yaya.. In sha Allah zan nemo hanyar da zaki fita..

Mama ta jinjina kai  Yanzu naji batu Suwaiba. Kar ki mance fitowa zanyi muyi yak in k wato mijinmu daga hannun azzalumar  yar uwarsa wacce babu komai cikin zuciyarta face burin fansa dan nayi imani ba tsakani da Allah Dije ke ma Isubu jinya ba. Shi kansa yasan halin Dije Shiyasa tun yanada lafiya ya mata iyaka da yanda yake. Ko dan wann Suwaiba bazamu bari Dije ta rab esa ba. Ki nemo kud ad en bak auye a biyasa na fito mu k wato mijinmu uban  ya yanmu. Ta haka ne kawai ahalinmu zai kuma samun daidaito. Kin fahimta.

Umma tai Shiru kaman mai nazari sai kuma ta shiga jinjina kai  Na fahimta Yaya. Nima zanso muyi jinyar mijinmu mu samu ladansa. Kuma kuskure ne mun riga Munyi amma munyi nadama. Kuma Allah mai afuwa ne mai yawan gafara.

 Yauwa dai Suwaiba ko ke fah. Nasan kinada fahimta Shiyasa munafukai basu tab a samun nasaran shiga tsakaninmu ba. Ni  yaruwa na d auke ki Suwaiba ba kishiya ba. Kuma  yan sa insa da sab ani da muke samu a baya zama ne Ya kawo haka. Dama shi kansa rayuwar zo mu zauna ne zo mu sab a. Harshe da hakori ma suna samun sab ani ballantana mu  yan adam.

Umma ta jinjina kai  Haka ne Yaya. Zanyi iyaka kokari na in sha Allahu. Allah ya mana jagora.

Mama ta murmusa had ida amsawa da  Yauwa yanzu naji batu Suwaiba. Ina nan ina saka tsammani. Na d aura duka yardana akanki Suwaiba. Ta k arashe cikin yanayi na tausayawa.

"A hankali Umma ta jinjina kai duk jikinta a mace haka sukai Sallama da Tani. Tana ficewa Tani ta kece da dariya. A fili take furta  Saidai ba Suwaiba matar Malam Isubu ba. Muje zuwa, da kanki zaki fiddani ni kuma na fidda  yar naki a gidan auren nata. Tinda  ya yana basu zauna d akin miji ba naki  yarma bazata zauna ba. Abun yazo gidan sauki dan da alama akwai abinda kike b oyewa gameda auren. Bazan yi k asa a gwiwa ba har sai na shak a iskar  yanci dan na cimma burina. Ta kuma murmusawa daidai sanda wata  yar sanda tazo maidata cell dinta."

Umma tana tafe tana lazimi da tinanin ta yanda zata b ullo ma al amarin Tani. Zatai iyaka yinta dan ta taimaki Tani tinda ta tabbata idan yau mijinta ya farka Ya gansu sun had e kawunansu kuma sunyi nadaman duk abubuwan da suka aikata a baya zaifi kowa farin ciki kuma Watak ila fushin da yake dasu ya gushe. Watak ila hakan ya zama silan yafe masu duk wasu kurakuren da sukai sanda yake kwance. Toh amma ina ta nufa..? Ina zataje .? Wajen waye zata je ta samo kud ad en da za a fidda Tani.? Asshe kawai ta fad o ranta. Dan idan ba Asshen ba bata kuma san wajen waye zataje ba. Toh amma sanin irin rabuwar da sukai da Asshe sai ya kuma haifar mata da sanyin jiki. Asshe ta bada umarni ma masu tsaron gidanta cewa ko mai kamanninta suka gani kar su bari ta shiga. Uwa uba had e kan da Dije da Asshen sukai mata kafin a tafi da Ummul. Ta tabbata idan Har Dije ta k ulla aminta da Asshe zuwa wajen Asshe had ari ne. Dan idan har Dije ta fahimci Matan Isubu Sun had e kai. Wato ita Suwaibar da Tani wani sabon wuta zata kunna masu. Snn abinda take k ok arin b oye ma Tani gameda auren Ummul kuma shikenan ya tashi daga sirri. Dan tayi imani Dije bazata so taga wann had in kan ba Wanda yake nufin rugujewar shirin duk wani fansarta akansu. Dole tai taka tsantsan. Dole tabi komai a tsanake idan har tana so ta taimaki abokiyar zamanta Tani ta fita daga kurkuku. Da wann tunanin ta sallami mai adaidaita ta shigo gida. Saidai tana shigowa abinda Tai karo dashi ne Ya mugun bata mamaki. Dije ta gani tsaye tsakar gidan ga kayan abinci da kwanaki Suwaibar ta kawo lokacin sunayi da Asshe lokacin yak in auren Ummul jirge gaban Dije ta kirawo yara tana fad in maza su fidda mata kayayyakin su kai mata cikin adaidaita dake jiranta k ofar gidan.

Umma ta saki baki tana kallon ikon Allah  Dije.. Lafiya mai nake gani haka..? Ina zaki kai mana kayan abincin.?

Kallonta Inna Dije Tai daga sama zuwa k asa  Makauniya ce ke.? Bayan shahshanci kuma idonki Ya rufe ne Suwaiba.? Tafiya dasu zanyi. Tinda na tabbata da kud ad en da kika saida d iyar D anuwana kika sayi kayan abincin nan. Ko ma ince su suka baki. Kaman yanda kika sani da zaran an sallamesa daga asibiti ko gidan nan bazai taka ba balle yayi karo da wani tashin hankalin da tsautsayi. Dutse zan wuce dashi ya samu hutu da jinya a can. Kayan abinci kuma zamu buk ata. Ta k arashe tana d aura ma yaro guda kwalin taliya akai.

Umma ta girgiza kai  Amma Dije mai zamuci.? Kar ki mance ba ni kad ai ce a gidan nan ba. Akwai Badi a sann akwai Azeema. Idan kika kwashe komai mai zaki barmu dashi.?

Dariya Inna Dije tai harda shewa kafin tace  Lallai Suwaiba. Yau kece mai fafutakan abinda yaran Tani zasu ci.? Saikace ba kece Tani ke hana naki yaran abincin da ubansu Ya kawo ba. A cewarta bazata girka ma k artan banza Wanda suka ki aure abinci ba.? Ikon Allah sai gashi yau ke Suwaiba kece kika nemo abinci kika ba ma yaran Tani da suka k i zaman aure harma girka masu kike. Yaran da ko ganin mutuncinki basayi. Lallai na yarda kin tabbata shashasha Suwaiba.

Umma ta girgiza kai  Dije rayuwar duka nawa take. Ciyar da rai lada ne dashi balle  ya yan mijina Wanda jarabawar rayuwa ya fad a kansu suka baro gidan mazajensu. Babu mahaifinsu a gidan Babu mahaifiyarsu. Gatansu Allah sai ni kad ai da na rage masu cikin gidan kuma in sha Allahu bazan wofantar dasu ba. Idan Allah ya bani dama da iko na

zama mahaifiya a garesu zan zama. Idan ban samu daman gyara kura kuran da nai a baya kan nawa  ya yan Ummulkhairi da UmmuKhulsum ba zan kwatanta gyara akan Azeema da Badia cikin yardar Ubangiji Dije. Ki kirani da duk sunan da kikaga dama amma in sha Allahu ni Suwaiba bazan sake maimaita kura kuren da nai a baya ba.

Inna Dije ta murmusa ta matso kusan Umma sosai  Idan dai Tani da iyalanta ne gaki gasu. Sai ki fita ki nemo ki dafa ki basu. Idan ma aikatau zakiyi ki nemo masu wann ke ta shafa. Amma kinga wann abincin Ya haramceku daga ke Har su. Ta k arashe tana sunkuman kwalin taliya. Kaman daga sama taga Azeema da Badia kanta ko wacce tana sakin huci. Shigowarsu gidan kenan.

Azeema ta nuna mata kwalin taliyar  Ajiye. Ta fad i cikeda gargadi.

Inna Dije ta dubeta da mamaki  Ke Azeema ni zaki ma rashin kunya.

 Zaki ajiye ne ko zaki jira na tayaki ajewa. Cewar Badia tana shan d amara.

Inna Dije ta saki baki da mamaki  Ke Badi a.. Ni zaku ma d iban albarka ina kanwar Ubanku.?

 Allah yasa k anwar uban kikace ba uban ba. Rashin kunya kuma ai mai sauk i ne wann. Billahillazi akan abincin nan sai mu tara Miki na jaki a nan mu bama idon mak ota abinci dan kinsan dai wann ba bak on abu bane a wann k ofar. Azeema tace tana kuma shan d amara.

Har lokacin mamaki take baki bud e  Ni Dije zaku daka ke Azeema.! Eh Lallai! Ai idan bakuyi ba baku cika jinin Tani ba. Ba laifinku bane Kunsha a nono.

 Wllhi Inna Dije zakici bugu a banza dan kin fad a da bakinki nida kunya dama munyi hannun riga. Ke d in banza tinda na tafi na tari fad a da budurwar Habibu mai tak ama da uniform da bakin bindiga banga uban da bazan taresa ba. Ke mu fah fad a ma rancenta muke ko ya kikace Badia.?

Badia ta dubi Inna Dije da bakinta ya gaza rufuwa sabida mamaki  Inna billahillazi idan baki kira yaran nan sun maido da abincin da suka fitar ba wllhi Kinji na ranste Miki kaf takaicin duniya da Tasi u Ya juye mun zan juyesu akanki. Dan wllhi yanzu a haka hannayena k aik ayi suke.!

Inna Dije ta jinjina kai  Eh na yarda dole ku kasa zaman gidan aure dan babu Wanda zai zauna da shed anu Irinku. Me za a tsammata daga wajen yaran da uwarsu ke tsare a gidan gyaran hali.

 Saki nawa aka Miki.? Yaji sau nawa kikayi da wayonmu kafin ki zauna gidan auren.?da wayonmu muna rakaki kome. Naga gado mukai wajenki Badia tace tana fincikan kwalin taliya dake hannun Inna Dije.

Inna Dije ta jinjina kai tana duban Umma da ta zuba ma sarautar Allah ido. K wafa tai tasa kai zata wuce Badia da Azeema suka shiga janyota suka nufo waje suna fad in saita maido kayan abincin da ta sace ta saka a keke napep.

Haka Azeema da Badia suka tirsasa ma Inna Dije ta dawo masu da kayan abinci.

Suka k araso da kayan suka jirge gaban Umma. Har lokacin ko waccensu da d amara a kunkuminta. Azeema taci gaba da nuna ma Umma kayan abincin  Kema kiji da kyau bamu k wata abincin nan sabida Ke ba sai don yunwar cikinmu. Kici gaba da girkawa kina bamu.

Umma bata ce komai ba har suka gama maganganun da zasuyi. Dan tun bayan abubuwan dake faruwa kaman abun nasu k aruwa yai. Cikin Zuciyarta tabi su da addu ar shiriya. Ta d au alwashin zatai hak uri dasu kuma bazata fasa masu nasiha ba har lokacin da abubuwa zasu daidaita da taimakon Allah.

**

Abuja&

Anisa taci gaba da juya kwalaben turare da Mommy ta bata tace ta kaisu ma Ummul.

Waya ta d aga ta kira Amminta. Asshe na ganin wayar Anisa Tai saurin d agawa  Ina sauraronki Anisa meke faruwa.? Shin Haidar yazo gidan.?

Anisa ta rausayar da ido  No Ammi he hasn t shown up until now. And I don t think zaizo gidan anytime soon.

"Asshe ta jinina kai  Toh ina sauraronki, wani abun ne Ya faru.? "

Anisa taci gaba da juya kwalban turaren  Ammi Kince duk abinda ake ciki na dinga sanar dake.

Asshe tace  Eh K warai. Remember you are my eyes there.

Anisa taci gaba  Ammi Mommy ta bani wasu kwalaben turare guda biyu.. Kaman turaren black khumra amma banaji suna k amshin khumra.. Tace na bama Ummulkhair.. Lallai Lallai na bata na kuma sanar da ita had in khumra ne na musamman Mommyn Tai mata kyautar su.

Ai Asshe bata San sanda ta mik e daga zaunen da take ba. Ta soma tuna lokacin zuwansu wajen boka sanda za a masu aiki akan makarin asirin Haidar. Boka Ya basu wani turare mai launin bak i ya kuma ce lallai lallai duk matar da za a karya asirin jikin Haidar da ita sai ta zamto tana amfani da wann turaren domin kuwa turaren tamkar shine kuran k arfe da zai janyosa zuwa gareta Har dai sihirin Ya lalace. Idan kuwa haka ne bazata bari Ummulkhairi Tai amfani da turaren ba tinda ita d in barazana ce ga rayuwarsa.

Baki na rawa Asshe tace  Turaren humra.? Kar ki bata su Anisa..!

Anisa tace  Meyasa Ammi.?

 Na fad a Miki no asking questions Anisa. Just do as I say. Ki zubar ki zuba turaren Khumra cikin kwalban ki bata. But koda wasa kar ki bata wann turaren idan har kina son ki mallaki Haidar.

Anisa ta kuma juya ido  But Ammi what if Mommy ta ba ma Bagidajiyar nan turaren da zata mallaki Haidar ne since she wants her for her son. What if I use it instead.. Kinga sai ya soni bai sota ba..

K iris Ya rage Asshe bata kurma kururuwa cikin waya ba jin nata  yar zata zama makarin asiri  Ke Anisa. Zan tsine miki albarka idan kikai amfani da turaren nan.. Wai ke wace irin shashasha ce. Nace duk abinda nace kiyi kawai kiyi zan miki bayanin komai daga baya.. Just dispose it and replace with natural Khumra. Kin fahimceni.? Ta k arashe cikeda gargadi.

Anisa ta furzar da huci dan ta gaji da wann mysteries d in  Ok fine Ammi. As you wish. Ta k arshe tana katse kiran.

Taci gaba da juya turaren kafin ta nufi d aki ta nemo wani kwalban ta juye turaren ciki ta wanke kwalban kafin tai yanda Amminta tace. Can k asan kayanta ta b oye turaren da Mommy ta bata Wanda zuciyarta ke raya mata turaren da zaisa Haidar yaso Ummul Mommy ta bayar a kai ma Ummul d in tinda tana mata makahon so. Idan kuwa Har hunch dinta ya zama gaskiya ita ce wacce zatai amfani da wann turaren dan Haidar ya so ta.

**

Gaba d aya Ji take bata kyauta ba tin bayan abinda Ya faru tsakaninsu da Anisa. Musamman da taga yanda fuskar Anisar Ya b aci. Ita a halin yanzu ba abokin fad a take nema ba. Hasalima Tun farko batada abokin fad a dukda kuwa masu nemanta da fad an sunada yawa kama daga cikin gidansu har izuwa mutanen unguwa. Khulsum ce ta fad o ranta wacce a ko yaushe idan an taresu da fad a ita ke d aukan fad an. Tayi nata Tai na Ummul d in. Ta murmusa a hankali. A fili ta furta  Nayi kewar ki fitananniyar  Yaruwarta. Ta share hawayen da Ya gangaro mata. tunanin mahaifinta ne Ya fad o mata sai ta tuna alk awarin Inna Dije gareta a lokacin da suka kawota cewa kar ta saka damuwan mahaifinta a ranta domin kuwa zata kula dashi cikin yardar Ubangiji. Umma ta fad o ranta. Sai ta lumshe ido a hankali tanajin kuka na zuwa mata. Kalaman Umma na k arshe a gareta su take tunawa cewa kar ta nemeta kar ta nemi kowa cikin danginta Har na tsawon watanni uku koda kuwa

36 / 103