AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   87 / 103

258K to 261K   out of 306.8K words

zata haihu.. Naji da kunnuwan kana cewa baka damu ba koda za a rasa jaririn matuk a Ummul zata zama safe.. Kalamai be da ban tab a jin makamancin su daga gareka ba.

Sai Ya dan jinjina Kansa a hankali  K warai nayi wann furucin.. Watak ila cikin dimauta da ganin irin yanayin da Ummul ke ciki.. Ya kamata ki min uziri a nan.. Sabida zuciya batada k ashi.. Kar ki mance irin soyayyar da nai ma Ummul.. A lokacin da take yunk urin haihuwa tsakanin rayuwa da mutuwa take.. Hajja ko kece aka baki zab i tsakanin Ummul da jaririn dake kokawan fitowa nasan Ummul zaki zaba ba jaririn ba..! Yaci gaba da jinjina Kai yana dubanta  Hajja kema zargina kike kaman Haidar..? Na kasa yarda Hajja.. You raised me yourself.. Kinsan komai akaina.. Ni din tarbiyarki ne kuma rainonki.. Ta Ya Daddy da muka hadu yau d aya tak zai yarda dani amma mahaifiyar da ta raineni ta kasa yarda dani.?

Furzar da huci kad an Tai tana kauda fuska gefe. Ta soma girgiza kai  Ban sani ba Hisham.. Ban sani ba ko na tauyeka ta wani waje.. Ban sani ba.. Ko dai nayi kuskure da na zab i nisantaka da mahaifinka..! Sosai muryarta ke rawa sanda take maganan.

 Ban sani ba kodai na gaza.. Ban sani ba Kodai wani abu daban na raina..! Ta k arashe muryarta na rawa irin na mai kuka.

Zuciyar Hisham yai wani irin tsinkewa. Hawayen da ya gani na fitowa daga idon mahaifyarsa Ya haifar masa da shiga tashin hankali. A duniyarsa ba abinda baya so kaman b acin ran mahaifiyarsa. Zaiyi komai sabida ita. Hasalima duk wani fansa da Ya jima yana dauka sabida ita ne sabida soyayyar da yake mata ne Har saida Ummul ta shigo cikin picture d in.

Saurin k arasawa yai ya rungumeta  Hajja ki daina kukan nan.. Baki san hawayenki sunfi komai tsada a Duniyar nan ba. I ll set whole world on fire just for your tears.. Dan Allah Ki daina kuka Hajjata..

Ta d ago tana dubansa shima ita yake duba. Ya kamo hannayenta  Na Miki alk awari zan wanke kaina Hajja.. Kuma ki yarda dani dan halak kika raina. Zan fito da evidence da zasu tabbatar da iyakacin gaskiyata. Ya k arashe yana jinjina kai alamun tabbatar da kalamansa. Daga nan bud e mata marfin mota yai ya taimaka mata ta shige kafin suka d auki hanyar Asibiti.

**

Suna isa asibiti suka iske ana shirin sallamar su Ummul. Hajja ta mak ale Ummul cikin jikinta tana fad in  Ki yafeni

 Yata na tafi na barki a lokacin da bai kamata na tafi na barki ke kad ai ba.

Ummul ta murmusa  Nasan babban al amari ne zaisa ki tafi ki barni. Na gode ma Allah da yasa kuka kasance cikin k oshin lafiya.

Hajja ta kuma rungumeta tana amsar jaririn. Duk wann abin gaban su Mommy ke faruwa. Sai mamaki suke suna fad in ashe Ummul ce zatai sanadin sake had uwarsu. Mommy ta kuma kamo hannayen Ummul tace Lallai ta cancanci sunanta Uwar Alkhairi kuma element of Union. Gashi dai duk dad ewa da sukai suka shafe shekara da shekaru suna neman Hajja basu sameta ba sai ta dalilin Ummul. Tabbas ita d in alkhairi ce ga ahalinsu. Nan Su Mama Tani suke ta mamakin al amarin harma da Ummul d in musamman da sukaji cewa Haidar da Hisham  yanuwan juna ne da suka had a uba d aya. Mama Tani tace ashe abin duk ahali ne. Mommy ta karada  What a small world. Addu a sukai gaba d aya kafin suka d unguma suka fito dan tuni an sallamesu. Hajja Fannah ta rok i alfarma a bar Ummul ta kwana d aya can gidanta idan yaso washe gari sai su d auki hanyar kano tinda ga almuru Ya sako kai ga kuma jariri danyen haihuwa. Bai kamata su d au hanya cikin dare ba.

Mommy tace eh gaskiya ne hakan yayi Mama Tani ma duk sunyi na am da shawarin idan ka dauke Haidar Wanda sam ba hakan yaso ba musamman idan Ya tuna cewa gidan mahaifiyar Hisham Khairy and his Son zasu.

Aka zo shiga Mota Hajja na rik eda Ummul suka nufi motar Hisham yayinda Mommy ke rik eda jaririn. Ga kuma Haidar Ya k araso da bak ar Land Cruiser din da Sadis ke ja tin zuwansu garin. A daidai gefen motar Hisham Haidar yai parking. Ga Ummul tsaye tsakiya hannunta cikin na Hajja. Mommy na daga bayansu rungume da jaririn.

Ummul ta kalli motar Hisham da tin fitowarsu ke jiran karasowarsu ta kuma dubi Motar Haidar da k arasowarsa wajen kenan. Sai kawai tasa kai ta nufi motar Hisham.

Daga nan cikin mota Hisham da Haidar ke aika ma juna kallo ta tsakankanin glass. Sai Hisham Ya sakar ma Haidar sihirtaccen murmushi alamun shi Ummul ta zab a tinda gashi ta nufo motarsa. Idanun Haidar suka kad a sosai sanda yake duban Hisham.

"Mommy ta waiga ta dubi Haidar, ta kuma dubi Ummul da tuni ta nufi motar Hisham. Sai ta dubi jaririn dake cikin hannunta. Ta kuma duban Haidar. Sai taji tausayin D an nata sosai. Kawai sai ta nufi motar Haidar da jaririn."

Har ta isa jikin motar Hisham sai ta waigo ta dubi Mommy wacce tuni ta nufi motar Haidar. Tausayin Mommy ne taji sosai cikin zuciyarta. Ta dubi Hajja tace  Kiyi hak uri Hajja.. Zan taho tareda Mommy.

Hajja ta murmusa had ida jinjina mata kai  Ba komai  Yata Allah hadamu a gida lafiya.. Je ki taho tareda Mommyn ki.

Ummul ta jinjina mata kai kafin ta nufi motar Haidar zuciyarta na tsinkewa.

Hisham Ya had iyi abinda ya tsaya masa a mak oshi.

Ummul tana isa jikin motar Asshe taceda Azeema ta shigo su zauna tare. Aiko kaman jira Azeema take ta shige bayan motar ta zauna tsakiyar Asshe da Mommy. Sai wage baki take yau gata zaune tsakiyar gogaggun mata wayayyu yan boko.

Ba yanda Ummul ta iya dole ta shige front Seat gefen Haidar.

Su Mama Tani dasu Badia harma da Khulsum suka shige motar Hisham tareda Hajja gaba d aya suka dunguma suka nufi gidan Hajja dake nan cikin garin Bauchi.

"Koda suka iso gidan, su Mommy na ficewa kafin Ummul Tai wani aune tana k ok arin ficewa saiji Tai Haidar ya locking motar."

Ta lumshe idonta kad an had ida sauk e ajiyan zuciya. Ba tareda ta dubesa ba tace  Ka bud e min mota na fice.

"Shima a dake yace  And who s holding you.? Go ahead.. get out.. After all, bani na kawoki cikin motar ba. "

A kufule ta juyo tana dubansa da mamaki  Karma kai tunanin wani abu daban. Sabida Mommy kawai na shigo motar nan.!

Murmushi yai da gefen baki  Really.. Sabida Mommy.? Toh Mommy ta fice kema sai ki fice.

Kaman zatai kuka take dubansa  Wai mai keke nema wajena..?!

A fusace ya matso da fuskarsa dab kusan nata  You..! Ke nake nema Khairy..! You and my Son.!

Muryarta ya soma rawa tana girgiza kai  Duk abinda ka mun bai isheka ba.? Kayi AUREN WATA UKU dani.. Kuma ka cika Wa adin Auren kuma..

Bata kai aya ba ya katseta  Kar ki sake nanata min wann kalmar. AUREN WATA UKU.!

Tai murmushi da yafi kama da murmushin takaici. Sai ta d ago hulan sanyin jaririn dake rike cikin hannunta  Kaga wann shi zai dinga tuna maka da kalmar AUREN WATA UKU..! Ta k arashe tana kuma fincikan marfin motar. Har lokacin motar a rufe take ta kuma juyowa a kufule. Sai ta sassauta murya tace  Dan Allah ka bud e min na fice.. Please..! Tai maganar kamar mai shirin kuka.

Har lokacin muryarsa a dake  Khairy.. Look up.. Look here.. Look into my eyes and tell me you don t love me.. Ki kalli cikin idona ki fad a mun baki sona..!

Kasa d agowa tai ta kallesa saima shesshek ar kukanta da Ya soma jiyowa.

"Haidar ya sassauta murya wann karon  You can t.. Bazaki iya ba.. Because you too love me.! I know you do.! Stop punishing yourself.. Stop punishing me.. Stop torturing our love.. Stop being stubborn Khairy..! Look, Our life will be good as it was.. I promise you.! Those days.. Those beautiful days kin tuna..?! Ya k arashe cikin sigan rad a sihirtaccen murmushi saman fuskarsa."

Katsesa ta da fad in  Dan Allah ka bud e min na fice.. Na rok eka. Ta k arashe tana had e hannayenta biyu alamun rok o hawaye naci gaba da gangaro mata.

Hisham na daga gefe yaga fitowar kowa daga cikin motar amma baiga ta fito ba. Duk ya damu. Sai tambayar kansa yake cikin zuciyarsa uban mai Haidar yake mata da zai kulleta cikin mota Ya hanata fita.

Yana tsaka da tunanin yaga ta fito ta nufi cikin gidan tana matsan hawaye.

Yabi bayanta da kallo Har ta shige kafin Ya maida dubansa ga Haidar da fitowarsa kenan shima daga motar.

Hisham Ya nufosa yana tambayar mai Ya ma Ummulkhair.

Dubansa Haidar yake without saying a word sanda Ya jingina jikin mota had ida folding hannayensa saman k irjinsa.

"Hisham Ya dan furzar da huci ganin irin duban da Haidar d in ke masa. Sai Ya sassauta murya ya soma fad in  Look Haidar, don t think otherwise& Ummulkhair kaman k anwa take a wajena.. Kasan yanda big brothers suke.. So protective.! Ka kira hakan da kulawa na Babban Yaya. Ya k arashe yana daga masa gira d aya."

Har lokacin Haidar bai daina dubansa ba. Ga mamakin Hisham murmushi yaga Haidar ya sakar masa.

 You are a coward.! Wanda yake aikata laifi sann Ya b uya a bayan mace. Ta Ya zaka daura nauyin zunubanka akan Anisa. What kind of a coward are you.?! Ya k arashe cikin k unan rai.

Hisham ya murmusa kad an  You know what your problem is.. You are being jealous for no reason.. Bazan tilasta maka ka yarda dani ba.. Amma na maka akawari zan wanke kaina.. Dear Brother.!

Sosai wann karon Haidar ke huci Ya matso da fuskar sa dab kusan na Hisham  You can fool them all you want.. But you can t fool me. Zan kama ka a cikin hannuna Hisham ka yarda dani.!

Hisham Ya dan lumshe ido  Haidar& 

Dakatar dashi Haidar yai  You might be my father s Son.. But you will never.. Never be my Brother..! Yaci gaba da jinjina Kai still yana duban Hisham d in  And let me make this clear to you.. You will stay the hell away from Khairy and my Son..! Bai tsaya sauraron amsar Hisham ba yasa kai ya shige.

Hisham yabi bayansa da kallo muguwar murmushin nan saman fuskarsa.

**

"Koda suka isa gidan sallah sukai kafin suka hadu gaba d aya tsakar gida gwanin ban sha awa sai hira ake kowa Ya yafi kowa an zauna inuwa guda. Mai yafi yafiya da zama lafiya dadi a duniya. Gaba d aya  Yanmatan kitchen suka shige sanda sukaga Hajja ta mik e zata daura girki. Nan suka karbe ragamar girkin daga hannun Hajja sukace ta huta zasuyi komai.Azeema, Badia harma da Khulsum idan ka d auke Ummul mai jego dake daga d aki."

Aunty Asshe ce ke tsaye daga k ofan tana duban  Yanmatan yanda suke ta k ok arin daura girkin sai raha suke tsakanin junansu suna tuno lokutan k uruciya sanda suke kwaba girki a gida. Sai Tai tsaye tana dubansu tunanin nata  yar dake tsare ofishin yansanda Ya fad o mata. Tasa bayan hannu ta goge hawayen. Jiki a sanyaye ta shige wajen Mommy da Mama Tani yanda Mama Tani d in ta cikata da labarai na barkwanci.

Wayar Mommy na parlor saman kujera yayinda suketa fira saman darduma a veranda. Daddy sai kiran Wayar yake Mommy kam bama ta sani ba tana can Tani ta cikata da hira.

Hajja ce ta fito daga d aki wajen Ummul nan ta hangi wayar sai ruri. Taje da zummar dauka ta kai mata wayar nan taga mijinta ke kira wato Daddy. Zuciyarta yai wani irin yankewa..Sai tai saurin matsawa da baya. Saima ta fice daga parlorn cikin sauri ba tareda ta tab a wayar ba sabida zuciyarta da Ya tsananta bugu.

Koda Daddy bai samu wayar Mommy ba sai ya kira na Haidar dake tareda Sadis daga waje saman wani d an dakali. Nan Daddy ya buk aci ya hadasa da mahaifiyarsa idan suna tare. Haidar ya mik e Ya nufi cikin gidan yanda Ya taddasu gaba d aya kasan rumfar dake tsakar gidan. Mama Tani da Ummul na daga ciki tana taimaka ma Ummul d in da wanka. Jaririn kaw na rik e cikin hannun Hajja shima an masa nasa wankan Mommy tana fad in a kwantarsa cikin mosquito net d insa. Hisham tsaye daga gefen Hajja yana kallon jaririn da murmushi saman fuskarsa lokaci guda yake tambayar  Hajja wai an masa suna kuwa..? Ya kamata dai na samu takwara.

Muryar Haidar suka sinkayo yana fad in  Aliyu..! Gaba d aya suka juyo suna dubansa.

Haidar yaci gaba daga nan yanda yake tsaye  Sunansa Aliyu..!

Gaba d aya sai murna Ya kacame waje Ya dauka ana Allah Ya raya Aliyu. Another Aliyu in the Family.. Aliyu the 3rd. Hajja Fannah ta mik a shi ma Mommy tana fad in Allah Ya raya musu BABA ALI.

Haidar Yaci gaba da takowa Har gaban Hisham da takaici Ya nuna k arara a fuskarsa. Yayinda hankulan mutanen dake wajen Ya tafi ga murnan sunan Aliyu da aka sake sakawa cikin ahalin Haidar kaw yai tsaye gaban Hisham da tuni yayi mutuwar tsaye wajen like a loser. Kyakkyawan murmushi saman fuskar Haidar hannayensa sakale cikin aljihun jeans d insa. Ya dan rank wafo da Kansa saitin kunnen Hisham  He s named after his Dad.. He will grow up like a Lion.. Just like his Dad.!

Hisham ya had iyi abinda yai masa tsaye a mak oshi yanaji kaman ya shak o Haidar amma ba hali.

Haidar yaci gaba  I had a great Victory.. Like a Lion& I beat you Hisham.! Yaci gaba da murmushi yana jinjina kai  I won.. You are the loser.. Ya gyara tsayuwarsa Ya tsaya k yam gaban Hisham Har lokacin da murmushi saman fuskarsa. Har ya juya zai soma tafiya sai kuma ya juyo yace  You should change your last name.. You must be eager to bear the name Aliyu Maitama.! Ya k arashe still da murmushi lokaci guda ya tsime had ida sa kai ya bar wajen. Ai Hisham bai kuma k ara Minti d aya tsaye wajen ba ya fice a gaggauce zuciyarsa na masa d aci.

Ummul ma a sama taji wai Haidar yayi ma jaririnta suna ya kumayi ma Kansa takwara. Takaici ya cikata.. Sabida tsaban gadara ko sanar da ita bai ba yama kansa takwara. Tana Jin sai shelan sunan suke a tsakani bata ko bi takansu ba.

Bayan Mommy da Haidar Sun keb e nan yake sanar da ita Daddy nata nemanta a waya baya samunta.

Mommy tace  Af aiko inaga na baro wayar can yanda nai sallah.. Aiko batai shiru ba Daddy ya sake kiran layin Haidar.

 He s calling again. Haidar yace yana kokarin daga kiran. Ya sanar da Daddyn suna tare da Mommy sann Ya mik a mata wayar yana mai bata privacy.

Bayan sun gaisa Daddy ke tambayarta ina ta shiga yaketa nemanta duk a dame yake maganar.

Murmushi Tai kafin tace yai hak uri hira ce tai dad i.

Daddy yace  Ya kamata ki taho masauki haka nan.. Is getting late already.

Daidai lokacin Hajja Fannah ta taho da abincin da ta kawo ma Haidar sai ta aje gefen Mommy ganin ba Haidar wajen.

Mommy ta dubi Hajja Fannah sai tace  Nidai idan ka min izini zan kwana nan gidan Fannah.

Cak Hajja Fannah ta dakata da abinda take sanda ta jiyo abinda Mommy tace. Bata ida mamaki ba saida ma taji Mommy ta saka wayar a speaker. Tana jin sanda Daddy ke fad i daga d aya b angaren  Shikenan ni kuma sai ki barni gauro a nan.

Mommy ta murmusa kad an  Toh ka k ara mana kawai Engr& Kaga idan bani nan inada mataimakiya..

 Aw haka ma kika ce.. Shikenan

87 / 103