AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   62 / 103

183K to 186K   out of 306.8K words

komai acan.. Ki saka mana ido kan Haidar da Ummul kiga ina relationship d insa ya nufa.. Sann ki saka mana ido Akan Kwaise Maitama.

Anisa ta jinjina Kai  Kar ka damu da wann.. Zan kula da wann b angaren.

Ya jinjina Kai suna Sallama da Anisa.

"Bayan Anisa ta fice shid in ma gidansa ya nufa ya isa jikin hotunan Haidar da Ahalinsa Wanda yai crossing da red pen gaba d aya. A fili yake furta  Ban jure duk wani wahala a banza ba..! Banyi duk wani fad i tashi na ganin na zama cikakken architect a banza ba.. Nayi haka ne to easily invade your lives.. Nayi haka ne domin na fanshe duk wani k uncin da kuka jefamu ciki nida mahaifiyata..! Ya kuma gyara tsayuwarsa yana huci  I m resourceful today because you rejected me Aliyu Maitama.! Yai maganar yana duban hoton Daddy Wanda shima yayi crossing. Yaci gaba  I m who I m today sabida na girma cikin wahala, k unci da takaicin zama D anka..! Ka yarda dani wann D an da ka sheganta da bakinka tun yana ciki baizo duniya ba shi zaiyi ajalinka da duk wani farin cikin da kake tunanin ka samu a wann duniyar.! Ya maida dubansa kan hoton Mommy Wanda shima anyi crossing da red pen. You re the one who instigated all this chaos.. Kece kika tada duk wani k ura.. Daga k arshe kin kawo Ummul d ina ciki.. Saidai d iyar  yaruwarki Anisa ta mutu amma ba Ummul dina ba.. Sai na raba wann D an naki da Ummul d ita duk wuya duk rintsi.. Ummulkhair is mine.. Wllhi na ranste sai na d auketa daga wajenka Haidar.!! Ya k arashe yana huci yana duban hoton Haidar dake daga tsakiyan na iyayensa Wanda shima anyi crossing anja layi da jan alk alami."

**

Su biyu ne cikin d akin yana kwance daga saman gadon yayinda Ummul ke tsaye gefe tana fito da shirts daga cikin suitcase d in da suka shigo dashi itada Anisa. Mommy ce ta d aureta nan wajen tace Lallai ta nema ma Haidar rigar da zai canza dan tasan halinsa tinda Ya farfado bazai taba yarda ya zauna da kayan asibiti ba.

Sai fito da t-shirts din take amma da alama Wanda take fito da Kayan dan ya gani yai selecting baida niyyan yin hakan. Dan ko kallo bata ishesa ba balle kayan da take cirowa.

Ta lumshe idonta a hankali tana tunani cikin zuciyarta  Mai zanyi yanzu ni Ummul. Bai kallon b angaren da nake.

D ago idon da zatai sukai ido hudu. Sai ta daburce gaba d aya.. Ta suri t-shirt d aya ta d ago sama tana nuna masa  Wann yayi.? Yanda tai maganar fuskarta d aukeda murmushin da yafi kama da yak e sosai zai baka dariya. Kai da gani kasan maganar zuwa mata kawai yai ba tareda ta shirya yinsa ba.

Bai bata amsa ba Har lokacin dubanta yake da rikitattun idanunsa.

Ganin bai daina kallonta ba bai kuma ce komai ba Ya sanyata aje rigar ta kuma d auko wani ba tareda ta kalla mai ta d auko ba ta shiga nuna masa  How about this one..? Duba kaga.

Wann karon sosai ya dad a tsarewa yana duban abinda take nuna masa Wanda da alama ita kanta bata San mai take nuna masa ba.

Ta kasa daina murmushin yak en da take sai juya abin dake hannunta take idanunta naga Haidar Wanda yai k ok arin mik ewa alamun zai nufo yanda take. Bugun Zuciyar Ummul Ya k aru ta yunk ura zata nufosa tana fad in  A a ka dakata.. Zan taimaka maka. Bata rufe baki ba abinda ke cikin hannunta tana nuna ma haidar wanda a tunaninta riga ce ta fad o k asa.. Dubawan da zatai nan taga shorts ne ashe take ta faman nuna masa. Bama tasan da gajeren wandon cikin jakar ba. Anisa ce ta saka a sace dan kawai ta had a Ummul d in da Haidar fad a tinda tasan Haidar mutum ne da baya so ana kutsa masa kai cikin rayuwa without an invitation.

Ummul ta runtse idonta sanda ta d auko gajeren wandon cikin hannunta.. Tai saurin b oyesa a bayanta tana tuhumar kanta  Daga ina wann yazo. Mai kika aikata Ummul.?

Bata Ankara ba sai jin hannayen Haidar tai ya kewayeta. Bakinsa kusan kunnenta yake furta  Who gave you the right to touch my things.?

Ta kasa cewa komai sai zuciyarta dake ci gaba da bugu. Jin tayi shiru bata ce komai ba yasa Haidar ci gaba sanda yake Zare shorts d in daka cikin hannunta har lokacin tana rungume cikin jikinsa  I hate it when others invade my private space.! k arashe yana zare wandon cikin hannunta.

Daidai lokacin Anisa ta turo k ofa ta shigo Mommy na biye da ita. A tunanin Mommy Anisa ta nemi izinin shiga an bata Shiyasa ta kutsa kai.

Anisa tai saurin cin birki had ida cewa  Kuyi hakuri na shigo kaina tsaye. I m sorry.!

Mommy tai saurin janyota suka nufi k ofa tana fad in  Ke ai bansan Randa zaki bar wann shashancin naki ba.

Haidar ya dan matsa baya kad an yana dafe garu had ida ciza labbansa kad an sabida raunin da suke jikinsa Har lokacin. A hankali ya furta  It s fine Mommy.. You can come in. Ya k arshe maganar sanda yake kishingid a saman gadonsa ta majinyata.

Ummul ta rintse idanunta tana jin kaman k asa ya tsage ta shige. Ko d agowa ta dubi Mommy ta kasa. Yayinda Anisa ke ta faman aika mata harara cikeda k iyayya k asa k asa.

Mommy ta karance yanayin da Ummul ke ciki sai ta bata aike wajen nurses d in dake reception dan tana son magana da Haidar alone. Ta dubi Anisa ma ta aiketa can waje wajen driver d inta.

D akin ya rage saura ita da Haidar.

Mommy ta tsaresa sosai da ido. Duba irinta ta tuhuma. Ya d an dubi mahaifiyar tashi sai ya d an sadda idonsa kad an ba tareda yace komai ba.

Sosai Mommy taji dad in hakan da Haidar yai alamun dai gradually yana sauyawa tinda tasan girmamawa ce yasa shi sadda idanunsa.

Ta janyo kujera ta zauna kusan gadonsa gefen kansa.

 Haidar.!

Ya d ago ya dubeta jin ta kirasa in a serious tune.

Mommy taci gaba  Kar kaga laifin Ummul dan an had o kaya an kawo maka.. Ni ce na sakata yin hakan.

Ya d anyi shiru sai kuma yace  But Mommy ba sai anje cikin kayana ana bincike ba.. You could ve sent your driver ya saya ko a boutique.. Since I won t be staying here for too long..

Mommy ta murmusa jin yanda yake ta kwanakwana yana maganar. Wai Haidar ne bai fad a mata magana kai tsaye ba yaketa faman kwana.. Hakan na nuna mata Ya fara gudun b acin ranta.

Ta d aura hannunta guda saman nasa tana murmushi  I know Haidar.. Zan iya yin hakan amma na zab i matarka taje ta bincika cikin kayanka ta d auko maka kaya.. Kasan dalili.? Sabida ita d in matarka ce.. Bata da wani shamak i da duk wani sirri naka.

Sai ya dan lumshe ido kad an ba tareda yace komai ba.

"Mommy ta kuma gyara zamanta  Aliyu, my son. "

Haidar Ya d ago Ya dubeta.

"Mommy taci gaba  Kaman yanda Ubangiji Ya bamu daman kasancewar D a da mahaifiya a karo na biyu.. Ina so ka nuna godiyarka ta hanyar kasancewa miji ga Ummulkhair.. Bani so na kuma tilasta maka wani abu musamman abinda ya danganci yanke hukunci ga rayuwarka.. Amma na maka alk awari wann shine zai zamo abu na k arshe da Ya danganci yanke hukunci cikin rayuwarka Wanda zan buk ata daga gareka, in sha Allah.. Please do this for me Haidar.. For the last time.. Ka bama kanka dama da Ummulkhair.. Just this once.. Na maka alk awari.. Daga k arshe idan bai working ba I won t force it.. Ta dan murmusa tana dafa hannunsa  Inada yak inin ma Khair in sha Allah. Ta k arashe tana duban D an nata."

Haidar ya dan dubeta cikin yanayin da bazaka iya fasalta abinda ke cikin zuciyarsa kai tsaye ba.

Mommy ta kuma murmusawa kafin ta mik e  Ni zan wuce gida na duba Aunt d inka Asshe da gajiyan hanya.

Haidar baice komai ba sai jinjina mata kai da yai. Yai mata fatan kasancewa lafiya. Da haka Mommy ta fice zuciyarta fari sol. Cikin buwayar Ubangiji D anta Ya soma dawowa kan turba.

Bayan tafiyar Mommy daga bisani Ummul ta shigo. Aiko tana shigowa saiga Anisa ta take mata baya. Tai Sallama ma Haidar kafin ta juyo ta dubi Ummul  Ummul kema ya kamata mu tafi koh.. You know they don t accept visitors here.

Kaman wanda aka zaburesa haka ya juyo yana duban Anisa jin tana fad in Ummul ta tashi su tafi.

Anisa tai murmushin da yafi kama da yak e ganin irin duban da Haidar ke aika mata  Hos..Hospital rules.! Ta fad i cikin sauri da k ok arin kare statement d inta.

Har lokacin wani irin duba Haidar ke aika mata  She s not a visitor.. You can leave. Ya fad i a tak aice.

Cikin sanyin gwiwa Anisa ke jinjina kai  Haka ne na mance..She s your wife.. I.. am the visitor here. Tai maganar cikin k ok arin danne k uncin dake taso mata ga murmushi mai ciwo saman fuskarta.

Ummul dai ta dubi Anisa ta dubi Haidar.

Anisa taima Ummul saida safe had ida fatan samun sauk i ma Haidar.. Tasa kai zata fice Haidar Ya dakatar da ita

" Do yourself a favour and quit coming around. As you mentioned, visitors ain t welcome.! "

Da mamaki Anisa ke dubansa jiki a matuk ar sanyaye yayinda Ummul ma ke binsa da kallon mamaki.

Anisa ta k ak aro murmushi mai ciwo tana jinjina Kai  As you wish..Dear Cousin. Ta k arada  Get well soon. Ta k arashe tana Kai dubanta ga Ummul wacce sosai damuwa ya nuna saman fuskarta.

Anisa na ficewa tai bursting cikin kuka. Gudu gudu ta fice daga asibitin.

Ummul ta maidoda dubanta ga Haidar Wanda ke k ok arin zame rigar dake jikinsa sai faman tamke fuska yake sabida zafin rauni da basu gama sake shi ba. Sam bama ta kula da abinda yake ba dan sosai korar da yai ma Anisa yai mata zafi.

Kaman zatai kuka. Cikin sanyinta ta soma fad in  Haba mana.. Mai ka aikata ne ..? Meyasa zaka Kori Anisa. Laifi ne dan an nuna damuwa akanka.? Kallan Yanda tai da fuskarta kaman mai shirin kuka Haidar yake.  How dare she interferes! Who does she think she is? Cikin zuciyarsa yake zancen saidai Ya kasa furta komai.

Bai ce da ita komai ba sai k ok arin sauk owa daga gadon da ya soma. Sai sann Ummul ta kula babu riga jikinsa. Ai sai ta d an daburce ta soma k ok arin kare idonta da tafin hannunta tana sadda Kai k asa ga Haidar dake nufota. Ta soma matsawa baya tana fad in  Wai mai kake aikatawa ne. Da.. Da cewa Kai na baka waje zaka canza..

Bai amsata ba bai daina nufota ba har suka isa jikin gini. Hannu yasa ta bayanta Wanda ya sanyata saurin d agowa a matuk ar tsorace tana dubansa zuciyarta bai daina bugawa da sauri ba. Sun d an d auki lokaci a haka kafin Haidar ya mik a hannunsa sosai ya d auki riga cikin suitcase d insa dake daga gefen Ummul saman drawer.

Ganin ya d auki rigar ya soma takawa a hankali ya sanyata lumshe ido had ida sauk e ajiyan zuciya a hankali.

Shi kaw Haidar na hankalce da ita yana kallonta ta wutsiyar ido. Murmushi ya saki da gefen bakinsa kafin ya dan saki k ara yana rik e gefen ribs d insa Wanda yasa Ummul saurin Ware idonta. Bata san sanda ta nufosa da sauri ta mik a hannayenta ta tallafosa tana masa sannu had ida tambayarsa ko ciwo yake ji.

Haidar bai daina ciza labb ansa yana tamke ido had ida sakin k anan k ara alamun yana jin pain har saida suka isa saman gadon.

Ummul ta kuma dubansa a kid ime bayan ta taimaka masa ya d an kishingid a  Kana jin ciwo ne.? Kana so na kiraka maka Likita.? Kaga barin kirawo su. Ta k arashe tana k ok arin dirowa daga saman gadon amma sai taji Haidar ya rik o hannunta.

Cak ta dakata da abinda take ta juyo a sanyaye tana dubansa.

Ya d an sha mur ganin tana duban fuskarsa kafin ya sakar mata hannun  Why would you call them.? Bayan gaki nan a nan.! Ya k arashe maganar yana d aura mata rigar saman hannunta.

Ta dubesa ta dubi rigar da ya saka cikin hannunta da mamaki. Sai ta d an girgiza Kai kad an alamun bata gane mai yake nufi ba. Mai zatai da rigarsa.

Sai shima ya d aga mata gira had ida yi mata alama da ido da ta saka masa rigar.

Sai Ummul ta soma girgiza Kai  A a bazan iya ba.. Ka saka rigarka da kanka.

"Bata Kai aya ba ya bata amsa da  But I can t move my arms.. It hurts.. And since you are my caretaker, Ke yafi kamata kiyi. Haka ne.! Ya k arashe yana tsareta sosai da ido."

Sukai shiru su duka biyun suna duban juna kafin Haidar ya k ara da  I thought kin d auki alk awari ma Mommy.. Cewa zaki iya shiga cikin rayuwata..? Here.. Do it.! Ya k arashe cikin sigan rad a yana mai kuma dank a mata rigar cikin hannunta.

Ummul tai rau rau da idanu tana dubansa kaman zata sakar masa kuka tace  Amma..Toh.. Amma ya akai ka cire wancan.?

Har lokacin muryarsa k asa k asa  It s just a patient wear.! Hakan na nufin zan iya cirewa cikin sauk i.. Ya k arashe yana tsareta da ido.

D an rausayar da ido kad an tai tana mai satan kallonsa. Har lokacin idon Haidar na kanta alamun yana jiran ba asinta. Sai Ya kashe mata ido guda alamun yana jira.

Ta d an gyara zamanta tana duban gefe da gefe. Ta kai idonta kan hospital gown da ake sanyawa wa marassa lafiya Wanda Ya cire. Tace  Amma.. amma Na zata saka rigar asibitin ma dokace.

Kafin tai shiru ya bata amsa da fad in  You should understand by now that I don t follow rules.! Ya k arashe yana mai tsareta da ido. Wanda hakan Ya kuma sanyata maida idonta k asa.

D akin Ya d anyi shiru banda lugude Babu abinda k irjinta keyi. Ta Ya zata soma sanya masa riga.?

Haidar ya soma k ok arin saka rigarsa yana hankalce da ita sai faman juya yatsun hannunta take. Sarai yasan tunani take.

A hankali yake zira hannunsa still yana kallonta.

Out of nowhere ta sinkayo muryarsa  Kenan k arya kike da kika ce kin dau ma Mommy alk awarin shiga rayuwata.?

Shiru batace komai ba sai sadda kanta k asa da tai kaman wata maras gaskiya.

Dak ik ai suka gifta babu mai cewa komai cikinsu.

 Zamanki a nan baida amfani.. You shud also leave please. Ya fad i yana k ok arin saka rigar da kansa.

Ta soma girgiza kai tana dubansa cikin d an daburcewa. K ara ya saki kad an alamun ya fama ciwonsa.

Ba shiri Ummul ta k araso da sauri ta rik e hannunsa da rigar tana masa sannu had ida tambayarsa ko ciwo ke masa. Duk ta daburce a hankali take zira masa rigar Har saida ta fitar masa da hannunsa. Idonsa kyam a kanta Har ta gama zira masa rigar ta gyara masa pillow ya kishingid a.

Zata mik e Ya rik o hannunta. Ta kaikaito suna duban juna.

 You should.. also change.. You can t sleep with& those cloths.! Yai maganan yana nuni zuwaga kayan jikinta da idonsa.

Ta k ak aro murmushi  Kar ka damu.. Zan iya.

Bai kuma cewa komai ba sai tab e bakinsa da ya d anyi.

Tana kallonsa daga nan yanda take zaune ya tada sallan isha har ya sallame. Can wani ma aikacin asibitin Ya nemi izinin shigowa Ummul tai masa iso. Nan ya shigo yana turo wani keke irin Wanda ake d aura abincin majinyaci.

Iyakacin k ayaddajen abincin da majinyacin zaici aka shigo dashi harda dose din maganin da zai sha na wann lokacin.

Mutumin zai soma b alle magani Haidar ya dakatar dashi  Just leave it from here. Kana iya tafiya.

Ya jinjina masa kai kafin ya dubi Ummul Ya bata wani k aramin card Wanda zata karbi abincinta dashi a cafeteria.

Ita dai Ummul sai juya card d in take tana mamakin asibiti kaman a turai. Dole ma ace ba a buk atan d an tayin jinya tinda duk wani kula za a baka. Ga na ura dake indicating musu abubuwa da dama Wanda daga yanda suke zasu fahimci hakan.

Haidar yai gyaran murya kad

62 / 103