AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   19 / 103

54K to 57K   out of 306.8K words

enta.

Badi a tace  Kud in jinya ake nema ko zaku biya ne tinda wancan karan ma ku kuka biya. Sai aje a sake saida jiki a kawo kud i. Ko mazan ne babu.?

Khulsum ta dubeta Har lokacin mamakinsu bai saketa ba  Da dai a kiramu b arayi marassa imani masu saida k addaran mahaifinsu da ransa gwara ace jikinmu muka saida muka biya kud ad en jinyarsa. Kin fahimta B arauniya matar b arawo.!

Badi a ta nufota a zafafe tana fad in  Ke ni sa anki ne dan ubanki.. Sai na gurje bakin ki yanzu a nan..!

Saida aka shiga tsakanin Khulsum da Badi a.

Nurse yace  Yanzu haka Dr zaizo babu abinda aka buk ata.. Shin ba hanyar da za a bi a samu a saya magungunan..?

Kaman daga sama suka sinkayo wata murya  K warai akwai hanyar da za a saya!

Mama dake shirin barin wajen dan batada lokacin cecekucen rashin kudin jinyar Malam da malaman asibiti burinta kawai ta isa ta cimma Tas u. Nan tai birki jin wann murya dai tai ma me muryar farar sani. A hankali take k ok arin juyowa har dai ta karkato gaba d aya.

Mama ta daskare. Ta shiga mutsuka idanunta tana duban wacce take gani gaba gareta  Suwaiba.! Ta furta cikin tsananin mamaki.

Suwaiba ce fah.. Suwaiba Amaryar Malam Isubu nata take gani sanye cikin tufafi na alfarma. A gidan Uban wa Suwaiba tayi arziki dare d aya. Karfa hausar nan da ake cewa dare d aya Allah kan yi bature ta tabbata kan Suwaiba. Ta kuma mutsuke idanunta dan har lokacin gani take kaman gizo ne ba gaskiya ba. Wai Suwaiba shashashar matar Malam Isubu ce haka kaman wata matar shugaban k asa ko gwamna.

"Khulsum da Ummul ma da mugun mamaki suke duban mahaifiyar tasu wacce kaman an canzata. Suka dubi juna suka kuma duban Umma shaye da tsananin mamaki, cikin tsananin shock suka furta  Umma.! "

Umma taci gaba da takowa gaba garesu. Azeema da Badi a ma da mugun mamaki suke duban Umman.

Kai tsaye nurse d in Umma ta nufa tace  Nawa ake nema..?

Nurse d in Ya d ago takardan na list d in abubuwan da ake buk ata Ya soma karantowa.

Kafin Ya gama karantowa Umma ta d aga masa hannu alamun dakatarwa lokaci guda ta bud e tsadadden handbag d in dake rik e hannunta ta Ciro sabbin kud ad e  yan dubu dubu sai walk iya suke. Mama ta zaro ido waje ganin dubabe bugun habuja suna walk iya suna kashe mata ido. Wai Suwaiba ke fiddosu.

"Ko k irgawa batai ba ta mik a ma nurse d in  Ungo nan.. A saya duk abinda ake buk ata, idan yayi canji ka rik e canjin idan kuma akwai abinda bai isa ba ka sanar Dani.. Ko menene.. Ta k arashe tana gyara zaman tsadaddan mayafin dake bisa kanta."

Nurse ya murmusa  A a Hajiya saidai na Miki jagora ki biya da kanki.

Umma ta jinjina kai yayinda Umma ta take masa baya.

Tin daga k afafu Mama ke dubanta Har zuwa tsadadden leshi da yan kunne da sark a dake kwance wuyanta. Wann ko taron manyan matan gwamnoni Suwaiba taje a haka ai ta cinye taro.

Akan idonsu Umma ke gudanar da komai da taimakon nurse d in kafin daga bisani ta amso receipts ta dawo yanda ta baro ahalin mijin nata Wanda kowa shock Ya hanasa aiwatar da komai. Baga Mama da yaranta ba baga Yaran Umma ba wanda zasu iya cewa Har yanzu basu tabbatar idan mahaifiyarsu bace.

Ko takan Mama batabi ba ta dubi su Ummul wacce suma kansu ta koma masu tamkar bak uwa. Kallon rashin sani ne ko na mamaki suke bin mahaifiyar tasu dashi. Tsakiyan yaranta ta shiga wato Ummulkhairi da Ummukhulsum ta kamo hannayensu tace  Mujenku kuga mahaifinku..

Tamkar rak umai da akala haka Umma ke janyo su Ummul da Khulsum. A haka suka zo suka shige gaban Mama da yaranta wanda suka koma kaman an dasa su.

Har suka shige cikin ward d in Mama da yaranta basu daina binsu da kallo ba.

Suna shigewa Mama ta dubi Azeema tace  Ke wanke ni da mari dan ubanki.

Azeema ta dubeta a yatsine  Ban gane na wanke ki da mari ba Mama..

 Nace ki mareni na tabbata ba mafarki nake ba.. Ba Suwaiba bace Ke min gizo ba. Inji ba itace yanzu ta shige gaba na ba ko.? Ku amsa min mana.. Na shiga uku ni Tani..

Bata kai aya ba taji zafi Ya tsunkuri  yar yatsarta na k afa. Badi a ce ta take mata  yar yatsar cikin k ok arin dawo da Mama hayyacinta.

Mama ta saki k ara tana d ingile k afarta  Wayyo kunama ta cijen.!

"Badi a tace  Ba kunama bane ta cijeki, take maki k afar nai ki tabbata ba mafarki kike ba.. "

Azeema tace  Mama wllhi Umman su Ummul ce. Amma nima nafi zaton canzata akai.. Mama ina ta samo kud ad e irin haka dare d aya.. Kinga Har fari da shek i ta k ara dare d aya. Mama kin kaw ga suturan dake jikinta. Wllhi iriinsa matar Gwamna ta saka ranan da za a rantsar da mijinta.. Mama Ina matar nan ta samo kud i haka wai.?

 Yo Ina zan sani ina tareda ke a nan.. Mama tace tana kuma lek en bayan Umma a tsarace.

Badi a ta tab e baki tace  Kar canzawarta ya zautar daku. Abu ne a bayyane matar nan dama barikinta kawai take son yi auren mahaifinmu ya taka mata burki.. Yanzu da take ganin zai Mutu shine ta baje kolinta da kyau zatai barikinta mai dalili..

"Azeema tace  Kai wllhi amma fah ta mun kyau, kinga shegen mayafin da ta watsa. Irin mai walwalin nan fah da ake talla online.. Inama ta bani aro naje dashi Bikin k anwar Habibi na yak i shegun danginsa. "

Bata kai aya ba Mama ta hamb are bakinta  Kud in shan jini da tsafin zakije a baki.. Toh Idan shaye shaye kike kije Azeema.. Kije Suwaiba ta shanyeki.. Ni nayi imani itace ta asirce Ummul mazan dake nemanta ke gudu sabida Allah Ya rufa masu asiri da sauran kwanakinsu. Shi Fa izu dake kwanansa Ya k are gashi ta lashe kurwansa. Yanzu kuma abun yazo kan Malam Shiyasa data mik a sa gashi a kwance kafi gawa.. Kuma yanzu ba sai anjima ba zan fiddata daga cikin asibitin nan..

Fiuuu Mama ta shige ta nufi ward d in yaranta na biye da ita.

Bata damu da majinyata dake kwance wajen ba Mama ta shiga kururwa tana fad in Suwaiba mayyace yar K ungiya asiri ne na shan jini.. Ta tsafe  yarta Ummul tana amfani da ita tana cinye mutane kaman yanda Fa izu d an  yar uwan Malam Isubu ya mutu. Bai isheta ba yanzu ta mik a mijinsu zata cinye.. Sai dukan k irji take tana fad in wllhi bazaayi ma mijinta amfani da dukiyar  yar shan jini irin Suwaiba ba.

Sauri sauri wasu nurses da cleaners suka tafi kiran securities. Hango securities d in da Mama tai ya sanyata had iye kalamanta.

Securities suka k araso suna muzurai suna fad in waye zasu fidda.

Take Mama ta shiga masu nuni da Umma tana fad in  Ga Suwaiba ita zaku kama ita zaku fidda.. Yar shan jini ce..

Ai sai Mama taga securities sun isa gaban Umma suna duk awa suna kwasan gaisuwa lokaci guda suna tambayar ko da abinda kike so a miki Hajiya.

Mama sai ta saki baki tana duban ikon Allah. Suwaiba.? Suwaibar ne Hajiya..?

Umma ta murmusa tana gyara zaman mayafinta  A a babu komai Kar ku damu. Haukar wancan Matar ne Ya motsa inaga b allewa tayi daga b angaren masu jinyar hauka.

Mama jin an ambaceta da Mahaukaciya ya sanyata kuma hayyak owa. Jikinta Har rawa yake.

Sauran mutanen dake wajen Wanda dama fitinan Maman a ishesu sukace da gaske ne batada saiti kullum fama ake da ita.

Aiko nan take securities suka fidda Mama da k arfin gaske sai ihu take tana tsine ma Umma. Yaranta suka bi bayanta a guje suna ambato sunanta.

Umma ta zuba masu idanu har aka fice dasu kafin ta sauk e ajiyan zuciya ta juyo tana duban yaranta Khulsum da Ummul Wanda Har lokacin kallon mamaki ko muce kallon tsoro suke binta dashi musamman bayan da Mama ta gama fad e fad enta.

Umma ta kuma dubansu sai ta k arasa ta rungumesu. Basu iya maida mata martanin rungumar ba.

" Ummul, Khulsum.. Ni ce fah mahaifiyarku Ummanku.. Meyasa kuke dubana kaman bak uwar fuska. Shin ko baku shaida mahaifiyarku bace.? "

Girgiza mata kai Ummul tai  Mun shaida kamanninki Umma amma yanayi ki yafi kama da bak uwar Fuska.. Umma mai ya canza ki cikin kwanaki k alilan..?

Murmushi Umma ta saki kafin ta dafa Ummul  K addararki itace ta canza ni cikin kwanaki k alilan Ummul.. K addaranki Wanda a baya naita Allah wadai dashi shine ya zamto mabud in Alherinmu..

Girgiza kai Ummul tai cikin tsananin sanyin jiki  Umma ban fahimceki ba..

Umma ta kuma murmusawa  Kar ki damu  Yata da sannu zaki fahimci komai.. Kuzo muje.. Ta shiga janyo hannuwansu suka nufo waje yanda suka hangi Mama har lokacin huci take bayan an tilasta mata yin shiru.

Mama ta zabura zata nufo Umma amma sai taga wata jibgegiyar jeep taja tayi parking gaban Umma. Mama taja wani wawan birki tana dafe k irji.

Mamaki da sanyin jiki Ya kuma sauk ar masu Ummul.

"Umma ta dubesu  Toh yarana ni zan tafi, in sha Allah zan kuma dawowa nan bada jimawa ba. "

Da tsananin mamaki suke duban mahaifiyarsu. Tasa kai kenan zata shige mota Ummul tai saurin kamo hannunta. Hawaye na gangaro mata take girgiza kai  Umma.. Ina zakije ki bar Abba cikin halinda yake ciki..? Umma ina kikaje kika barmu mu nata nemanki.. Shin Kinsan abubuwan dake faruwa a nan.. Umma wai meke faruwa.. Umma meke faruwa ne..?

Dafata Umma tai  Da sannu zaki fahimci abinda ke faruwa Ummul.. Zan rok i alfarmarku. Kar ku bar kusan mahaifinku.. Ku zauna ku kula dashi.. In sha Allah daga yanzu duk wani abinda za a kashe sabida jinyar mahaifinku bazai zama matsala ba. Na barku lafiya yarana..

Ummul na kuka ta kuma kamo hannunta  Umma shin kinsan kalan tashin hankalin da muka shiga na rashin ganinki.. dan Allah kar ki tafi ki barmu.. Umma.. saidai tuni Umma ta cire hannunta daga rik on da Khulsum tai mata ta shige mota. Ummul ta kuma yunk ura tana ambato Umma amma saiji tai Khulsum ta rik on hannunta had ida dakatar da ita  K yaleta Adda.. Wann ba Umman mu bace.. Idan ma itace banida haufi an canzata dare d aya.

Fad awa jikin Khulsum Ummul tai wani irin kuka na kufce mata.

Mama kaw zuba masu idanu tai tana mai kuma tabbatar da zarginta cewa Suwaiba dai K ungiyar asiri ta fad a.

Umma tana shigewa cikin motan ta dubi Asshe dake zaune gefe. Ta d an yi adjusting mayafin  Hajja Asshe Ya kikaga k warewata..? Kinga kaw yanda na razana Tani na haukata ta na gigitata.? Gaba d aya fah ta birkice..

"Asshe ta murmusa tace  Ai ma fah bama ayi komai ba, wann ai sharan fage ne. Sai randa aka kai lefen Ummulkhairi, ranan ne zaki kashe kishiyar ki da k unci. Dan ina mai tabbatar miki sai ta had iyi ranta. Kaf abinda ta miki kan Ummulkhairi sai kin rama. Ranan biki kuma a fice da gawarta. "

"Umma ta zaro idanu  Na shiga uku, bazan so Yaya ta Mutu ba ai&  "

Asshe ta d an murmusa kad an had ida dafe kafad ar Umma guda  Bazata Mutu ba ma sai taga Nasaranki da na Ummul. Kuma ko yanzu kin tauna tsakuwa aya kuma taji tsoro.. Ni so nake ki kece raini a kamfatanin layinku.. Duk masu aibata Ummul d inki sai Sun shaida auren gata da za a mata..

Nan fah Umma ta shiga wage baki zuciyarta na mata dad i. Karfa ku mance mijin Umma na kwance gadon asibiti tsakanin rayuwa da mutuwa. Amma Har yanzu burin Umma shine Ummul d inta tayi aure kota halin k ak a ko ba dan komai ba sai dan ta birge Mama da sauran jama an unga sabida abinda suka jima suna mata kan Ummul.

**

A b angaren su Ummul kuwa tinda Umma ta shige bak ar Jeep d in nan mai lullub e da tint suka kasa komawa cikin asibiti wajen Abbansu dan haka su Mama da Azeema sukai caa a haraban asibiti suna nunasu suna cewa ga  ya yan mayya. A dole suka fice daga asibitin suka dawo gida.

Ummul ta zuba tagumi Khulsum ma da kalan nata tagumin.

 Adda anya ba gaskiya Mama take fad i kan Umma ba.. Anya Umma ba wani k ungiyar asirin ta shiga ba..! Tai maganar kaman mai tsoron furtawa.

Ummul tai saurin d agowa tana dubanta  Haba Khulsum ta ya zakiyi irin wann tunanin..?

 Adda abinda idanun mu suka gane mana fah kenan& Ina Umma ta samo dukiya irin wann tsakanin kwanakin nan..? Sann meyasa ta tafi ta k yalemu..? Meyasa bata damu ta bar Abba cikin halinda yake ba.. Adda kifa duba kiga yanayin da Abba yake ciki amma Umma tana a matsayin matarsa ta saka k afa ta tsallake shi har da shigewa shirgegiyar Jeep d in nan. Ga ado da tayi irin wanda bata tab a yi ba. Wata matace zatayi wad ann abubuwan alhalin mijinta na kwance cikin tsananin jinya. Wllhi ko baki fad i ba Kema kanki nasan zuciyarki bai kwanta ba Adda kuma akwai irin tambayoyin da nakeyi kwance cikin zuciyarki.

Sauk e wani irin ajiyan zuciya Ummul tai sai kuma ta jinjina kai tace  Kinyi gaskiya& Akwai tarin tambayoyi k unshe cikin zuciyata Wanda zanso Umma ta amsa min su.. Amma ko ma menene kar muyi gaggawan yanke hukunci da abinda idanu mu ka iya gani.. So tari abubuwan da idanun mu ke iya gani a zahiri ba haka suke a bad ini ba.. Mu tsaya Har muga gudun ruwan Umma mu kuma ji abinda ke faruwa.

Khulsum taja wani irin gauron numfashi ba tareda ta kuma furta komai ba.

**

Abuja.

Laptop ne gabansa waya manne kunnensa yana duban wasu sketches na manyan bridges iri daban daban. Ko ba ace ba da Hisham yake wayan. Da alama shi ya turo masa sketches d in da suke tattanawa akai. Bayan Sun gama magana shiru yai yana nazarin abinda ke gabansa. Sai kuma ya rufe laptop d in ya k ura ma waje guda idanu.

Dareen da waya ke mak ale kunnenta ta kuma lek ensa kafin ta koma da baya tana rage murya had ida matse wayar jikin kunnenta sosai  How would I know.. He s been acting strange lately..

Daga d aya b angaren muryar mutumin ya katseta  What are you there for idan har bazaki iya karantar yanayin da yake ciki ba..?!

"Ta d an rausayar da idanu had ida furzar da huci  Look, I see him everyday but I can t grasp his mood. Ba ko yaushe asiri yake tasiri ba. Kar ka mance Shi mutum ne Wanda tun kafin sihiri ya jefesa yakeda wahalan sha ani. "

Mutumin yace cikin tsawatarwa  Kalla Dareen. Ban kawo ki cikin rayuwar Haidar dan kiyi holewarki dashi ba. Kinfi kowa sanin dalilin da yasa kike tare dashi. Idan Har bazaki min amfani ba. Zan tarwatsaki da kaina.. Kinsan inada makamin da zan tarwatsaki a hannuna tinda har yau baki san yanda na bisne sirrin da Ya rufe Aurenki da Haidar ba.

"Lumshe idanunta tai had ida bud esu  Fine, zanyi iya k ok arina na fahimci mai yake shiryawa. Amma karkayi gangancin rabani da Haidar domin zan tashi wutan da kaima baka isa kashewa ba.! "

Ya murmusa  Kar ki mance I m the one calling the shots here. Kibi umarnina ki zauna lafiya.! Yana ida fad in haka ya katse kiran.

Furzar da huci ta kumayi kafin tai k ok arin kintsa kanta ta fito parlor yanda Haidar ke zaune.

Murmushi saman fuskarta ta zauna gefensa  Love.. Ta fad i tana shigewa jikinsa. Sai kuma ta d ago fuskarta tana dubansa  Is something bothering you..? You seem preoccupied& Is it about work..? Ko kaje duba Mommy ne..?

Tambayan da ta masa na k arshe yasa ya dubeta sai kuma ya maida dubansa wani b angaren  I m fine.. Ya fad i a tak aice ba tareda

19 / 103