AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   34 / 103

99K to 102K   out of 306.8K words

Kun fuskanci k alubale na lalacewar neman aure kafin akaiga auren. Toh amma a ko yaushe shi mutum ya zama mai d aukan k addara da hak uri da jarabawar Ubangiji a yanda tazo masa. Duk iyaye burinsu kenan. Farin cikinsu kenan suga  yarsu ta natsu a gidan aure. Haka zalika idan namiji ne suga yayi archiving a rayuwa sann ya zama mutum mai cikan kamala yayi aure. Shi aure abun so ne ba abun gudu bane ba abun k i bane. Hasalima ya inganta a hadisin Anas dan Malik wanda Bukhari da Muslim sukai ittifak i akai. Cikin hadisin Manzo SAW ya tabbatar Aure sunnarsa ce kuma wanda ya k yamaci sunnarsa baya tare dashi. Toh kaga kuwa aure sunnah ce mai girma kuma koyi ne da Manzo SAW. Yayi umarni ma samari da suyi aure ga Wanda Allah ya bama ikon yi. Domin shi aure yana tsare gani da kuma kamewa. Ga Wanda baida hali kuma yayi azumi domin shi azumi garkuwa ne. Hadisin Abdullahi bn Umar wanda Bukhari da Muslim suka rawaito shi. Ta d an numfasa  Toh kaga duk wad ann hadisan suna nuni da aure ba abun k i bane aure ginshik i ne na ko wani Al umma. But you can t force it. Kuma ka nemi zab in Allah cikin duk abinda ka sa gaba. Kana so kana buri kana kuma fatan kayi. Cikin aure akwai tarin albarka kuma ibada ne. Allah ya halicci  yan Adam jinsu biyu domin su samu natsuwa da juna. Kaga wann natsuwar sai ta hanyar aure za a samu. Kai hak uri d ana, Kai hakuri da jarabawarka. Kai hak uri da Ummulkhair. Ka cireta a zuciyarka ka nemi wata daban. Allah yasa haka shi yafi zama maka alkhairi da mu baki d aya. "

Sauk e ajiyan zuciya Hisham yai yana mai shafe fuskarsa da tafukan hannayensa. Sai ya kifa Kansa na d an lokaci. Ya d ago yana duban mahaifiyarsa broken  Hajjah.. Hajjah wanene Ummul ta aura.?

Tambayar da ya haifar mata da fad uwan gaba. Ta girgiza Kai kad an  Shin baka d auki k addara bane.? Are you having doubts kan abubuwan da na sanar dakai.?

Girgiza mata Kai yai a hankali ba tareda da ita cewa komai ba.

Hajjah Fannah ta jinjina Kai  Sanin waye Ummul ta aura baida wani alfanu wajenka. She s someone s wife now. Ka cireta gaba d aya a ranka kuma kar ka waiwayi baya.. Ka min wann alk awarin D ana.

D agowa ya kumayi ya dubeta. Sai yai murmushi mai ciwo  Kamar yanda kika ce Hajjah.. Zanyi kaman yanda kikace.. Ya mik e yana kuma shafa fuksarsa  Inaga zan koma bakin aiki ko zuwa& Gobe idan Allah ya kaimu. If that s with you. Ya k arashe jiki a mace.

Sosai tausayin shi ya cikata. A hankali ta jinina masa Kai  Hakan yayi D ana.. Allah ya tsareta da tsarewarsa ya baka dukkan kariya. Ya saka maka albarka cikin duk abinda ka sa gabanka.

Ya k ak aro murmushi ya sakar mata kafin yasa kai ya shige.

Sauk e ajiyan zuciya tai tana jin ciwon da D an nata ke ji har cikin zuciyarta. Shin har yaushe zata ci gaba da b oye masa.? Shin sai yaushe zata sanar dashi gaskiyan lamari gameda mahaifinsa.? Shin rufe masa da tai tayi daidai..? Shin yaushe zata sanar dashi gameda Ahalinsa.? Shin Anya wann ba alama bace a gareta na cewa ya kamata ta fayyace ma D anta komai. Musamman da yanzu d an uwansa ya auri Ummul.? Anya ba baya bane yake hunting d inta..? Bayan ta datse duk wani alak ar da take da tabbacin zaisa su waiwaya.. Meyasa kwatsam abubuwa ke neman sauyawa..? Shin Ummul zata iya kasancewa dalilin da zaisa su waiwayi baya.? Ta kuma girgiza kai cikin sauri. A fili take furta  Bana fatan hakan. Allah ya gani tsakani da Allah naso Ummul tamkar  yarda na haifa a cikina. Watak ila iyaka lokacin da zamuyi kenan a tare. Tabbas ya zama dole na datse alak a da Ummul da duk wani abinda zai had a d ana da Aliyu Maitama.

**

Abuja&

Tsaf suka fito cikin shirin fita. Doguwar rigar abaya Anisa ta bata ta saka. Da shike kaf dogayen rigunan Anisa ta rage fad insu hakan yasa ya kama Ummul sosai sai yafi kyau a jikin Ummul d in saidai tsawo da ya d an mata yawa sakamakon Anisar ta fita tsawo.

Sai faman yatsina fuska Anisa take tana mata kallon wulak anci.

Mommy kaw suna fitowa ta mik e ta isa ga Ummul wacce tuni ta sadda kanta k asa.

Murmushi saman fuskar Mommy take fad in  Ki saki jikinki  Yata. Ki zabi duk abinda kike so. Ko menene. Ta dubi Anisa  Ki tayata ta zab i kaya masu kyau Wanda zasu k ara fito da kyaunta. And make sure you take good care of her.

Anisa ta kauda Kai gefe tana rolling ido. Kuji Mommy fah wani wai ta kula da ita saikace watchdog d inta or something.?

 I m talking to you Anisa kina kallon wani wajen. Kinsan bana san shashancin nan naki.. Mommy tace ba walwala.

Anisa ta juyo fake smile saman fuskarta  Ok Mommy. Kaman yanda kikace .. I ll take good care of your daughter in- law for you. I promise.

"Mommy tace  She s my daughter, not daughter in-law.. "

Anisa ta kuma kauda Kai tana fuzar da huci. Sai yanzu ta yarda da kalaman Haidar idan ya kira Mommy good actress. Tayi imani ba a banza take ma wann kucakar makahon so irin haka ba. Yarinyar da gaba d aya duniyarsu ya banbanta. Su d in gaba d aya ma ba d aya bane. Wai Hajiya Kwaise Maitama ke treating  Yar talaka haka. Wllhi idan za a Mutu bazata tab a yarda auren nan na Allah da Annabi akayi ba. Kuma ko menene ke rufe cikin auren she vowed to find out about it. Sai ta binciko to the core.

Credit card Mommy ta mik a ma Anisa bayan ta tambayeta zatai driving ko driver ya kaisu. Anisa tace no zata tuk asu.

Murmushi Anisa ta sakar ma Ummul harda bud e mata front Seat gaban Mommy. Dan Mommy ta tabbata zata kula mata da sirkarta. Cikin zuciyarta kaw cewa take  I ll play your little game Mommy har na gano bakin zaren komai.

A haka suka d auki hanya.

Suna tafe Anisa ta d aga waya ta k ara a kunne  Hello Girlfriend kina ina..? Ta murmusa  Toh ki bar duk abinda kike let s go shopping. Ta kuma darawa  Ok just wait there yanzu zaki ganni. Tana Ida fad in haka ta katse kiran.

Tai parking ta dubi Ummul  Ke koma baya zan d auki k awata

Ummul ta dubeta sai ta murmusa. Kaman zata fita sai kuma ta fasa. Ta juyo ta dubi Anisa  Amma ba a gidan baya Mommy tace na zauna ba. Kiyi hak uri bazan iya sab a umarninta ba. Ta k arashe murmushi mai k untata ma Anisa saman fuskarta.

Hararta Anisa tai kafin taja motar. A haka suka k arasa kusan wani k aton gini mai gidaje iri guda a jere.

Can wata budurwa ta fito cikin shigar Wando sai top bajajje wanda bai matseta ba sai d ankwali d aure kanta.

Tana k arasowa Anisa ta bud e motar ta fito suka tafi a guje suka rungume juna suna kiran juna Girlfriend.

Da mamaki budurwar ta tsaya tana kallon wacce ke zaune gaban motar.

Ta juyo ta dubi Anisa  Neesa wacece kuma wann..?

Anisa ta rausayar da ido  Kinsan a duniya ba abinda ke burge bakauye irin zaman gaban mota. Kedai shige muje Leenah we gonna shop the entire city.. Ta k arashe tana d aga mata card d in mommy dake hannunta.

Leenah ta shige backseat sai labari suke itada k awarta Anisa. Tanata k are ma Ummul kallo wacce batabi ta kansu ba.

Can Leenah Ta bangaji Ummul ta mik a hannunta jikin radio na motar ta k ure kid a. Har lokaci Ummul batabi ta kansu ba. K arshe hannu tasa ta cikin mayafi ta toshe kumnuwarta dan ita dama ba mai sauraron irin wad an wak ok in na turawa bane.

Sanda suka isa ma gaba sukai suka barota baya. Har sun d an yi nisa kafin Anisa ta rausayar da ido ta juyo ta dubeta. Nan ta hange Ummul na kokawan d alewa escalator. Sai kuma ta dubi Leenah  I can t believe this is happening to me. I can t believe we are hanging out da bagidajiya irinta. Dubi abinda take neman wani ya mana video yace tare muke. Anjima mu ganmu ana tagging d inmu. Nidai yau Mommy ta kashe ni. Wann da kyar idan ba daga kauye aka d aukota ba dan ba dai cikin birnin Kano ba. Ta k arashe tana furzar da huci. Daidai sanda Ummul ta k araso  Kuyi hakuri takalmin ne nakeji kaman zai kadani.

Leenah da Anisa suka dubi juna suka dara a tare. Kafin Anisa tace  Malama karkiji Mommy ta ce na kula dake. If you go missing babu wanda zai b ata lokaci wajen nemanki dan da alama this is your first time in a place like this.

Leenah ta tab e baki sai kuma ta nufi wani wajen cikin sauri tana ambaton sunayen designers.

Anisa ta rausayar da ido tana duban Ummul da Leenah ta barsu nan tsaye tare  Baiwar Allah. We are here already. Select what you want.. Ko shima sai na tayaki.? Ta k arashe tana kuma rausayar da ido had ida furzar huci.

Tuni Anisa ta tafi wajen k awarta Leenah. Suka kyale Ummul ita kad ai.

Saida suka jida kaya nik i nik i suka tadda Ummul tsaye da wasu dogayen riguna da basu wuce uku ba.

Duban juna suka kuma yi kafin Anisa tasa hannu ta finciki Kayan dake hannun Ummul. Ta d aga kayan sama ta Ware tana gani Leenah na tayata  What.! Are you kidding me..? Wann shine iyakacin abinda kika iya zab a tuntuni.? Ta girgiza Kai tana kuma duban Kayan.

Leenah tace  Wai zallan jallabiya ta zab a. Ina zata dasu.. Ba azumi ake ba balle nace ittik afi zata shiga.

"Anisa ta girgiza Kai tana duban Ummul take d aga rigunan  Baiwar Allah. We are shopping with Hajiya Kwaise Maitama s card, we can buy the whole mall if we want.. And hello! You are married to Haidar Maitama. So get used to spending a lot. "

Leenah baki sake take duban Anisa Jin ta kira budurwar da suke tare matar Haidar. Saurin janyota tai suka matsa daga kusan Ummul.

"Leenah ta dubi Anisa  Wait, did I hear that right..? Wann d in matar Haidar.. Haidar Maitama da na sani. Our long time crush..? "

Anisa ta juya ido  You heard it right. Wai wann d in matarsa ce. Amma bana tunanin auren mai d orewa ne dan dai tin jiya da aka kawo masa ita gidan he didn t show up. Mommy ce kawai mai son Auren Amm Wanda akai domin shi baisan anayi ba da alama.

Leenah ta jinina Kai  No wonder. Dan dai wann hanyar da Haidar yabi ma bata isa bi ba. Sai ta kuma gyara tsayuwarta tana duban Anisa  But what about you girlfriend. I know you love your cousin so much. Does that mean.. You give up..

 Giving up is not in my vocabulary Leenah. You should know better. Kawai lokaci na d ibar masu. I have to study my target well before I strike.! But trust me sweetheart hakan zai faru ne kafin ta samu kusanci da Haidar. Ta k arashe makirin murmushi saman fuskarta.

Leenah ta murmusa  Then do it fast sweetheart. Kinga irin wadnn makiran babu wuya sun saye Zuciyar namiji.

Dubanta Anisa take fuska a yatsune. Tai nuni da Ummul wacce mata me kula da kantin keta faman nuna mata wasu kalolin designs din. Anisa ta murmusa ta kuma duban Leenah  Haidar Maitama ya fada soyayya da wann bagidajiyar. You know what Leenah. I hate to burst your balloon but what you re imagining is never ever going to happen. Ta k arashe tana kuma rausayar da ido.

Leenah ta murmusa  Lallai Neesa toh barikiji na fad a miki. You ll remember this moment idan baki tashi tsaye tun yanzu kin kawar da ita ba. Ina nufin tun kafin Haidar ya zame Miki k alubale wajen kauda ita.

Shiru Anisa tai sai kuma tace  I don t want things to reach the point where I have to stain my hands.

Leenah ta murmusa  Then hire someone to do the job for you.. I can t wait to get my hands dirty.. Ta k arshe tana kashe mata ido.

Juyawa tai ta kalli wani cream yanda aka rubuta do not apply on face. It contains strong fragrances that might irritate your facial skin. Ta murmusa ta kuma duban Anisa  Hey Girlfriend. Daga nan ya kamata mu ziyarci beauty Spa. Tai maganar tana d auko cream d in ta nuna ma Anisa. A tare suka dara kafin suka k arasa wajen Ummul suka ci gaba da tayata shopping kaman babu abinda ke faruwa. Har cewa Anisa take ita tasan taste d in Haidar so zata zab a ma Ummul kaya to taste d insa. Ita dai Ummul bata tankasu ba amma jikinta ya bata wani abun suke shiryawa.

Daga nan Beauty Spa suka tsaya. Ummul ta dubi Anisa  Mai zamuyi a nan.

 Face treatment sweetheart. Ta bata amsa tana unbelting kanta daga cikin kujeran.

 Amma ba abinda ya samu fuskata ni.. Ummul ta bata amsa.

Gajeren tsaki Anisa tai  Beauty treatment ake magana ba sai kinji rauni ba. Dan Allah bani son stinginess naku na talakawa. Mommy card ta bayar mu k arar dashi akanmu idan munso.

Ummul ta murmusa had ida girgiza Kai ganin Anisa ta fice zata rufeta a mota.

Koda suka shiga Ummul na hankalce dasu. Anisa da Ummul ake ma gyaran fuskar yayinda Leenah ke tsakani tana jira ta cika aiki kaman yanda suka tsara itada k awarta Anisa. Ana fara face massage cikin dabara Leenah ta dauko wann cream din ta zuba cikin bowl din da aka kwaba kayan gyaran fuska na Ummul. Tana gama zubawa ta fice dama idon Anisa a lumshe suke sakamakon abinda aka daura mata saman idon.

Ummul ta murmusa a hankali dan taga sanda Leenah ta matse tube din ciki. Aiko nan Ummul ta soma kokawan mik ewa a birkice jin ana juyata mata fuska alamun bata saba ba. Aiko nan bowls d in suka fado k asa saidai basu zube ba. Ummul tai saurin d aukan na Anisa wacce idonta ke lumshe sai faman tsaki take Bagidajiyar nan na bada ita. Ummul ta mik a ma mai mata gyaran fuskar robar gyaran fuskan Anisa yayinda mai gyaran fuskar Anisa ta Sunkuya ta d auki na Ummul dake k asa tana ce da ita ba komai ta daina basu hakuri.

Anisa ta rausayar da kwayar idonta dake rufe. Takaicin Ummul fal zuciyarta wani b angare na zuciyarta kuma cikeda farin ciki zata toya ma Bagidajiyar Amaryar Haidar fuska tun kafin ya ganta.

Bata Ida tunanin ba taji wani k aik ayi mai gauraye da k una saman fuskarta. Aiko nan Anisa ta saki k ara tana tsalle tana ihu tana tambayarsa mai suka saka mata a fuska.

**

Royalton Cayo Santa Maria resort. Cuba&

Tana kwance tana facing view na ruwa. Zuciyarta na mata sanyi. Rayuwar Jin dadi da bata fata wani abu ya katse mata shi. Nan ta bud e WhatsApp dinta da ta kwana biyu bata waiwaya ba. Sak onni ne sukaita shigo mata daga wani number da tai saving da . *Shadow.* Kaman jira yake ta kunna nan k ira ya soma shigowa. Dareen taja garen tsaki. Tasan babu abinda zai tambayarta face mai suke Cuba a daidai wann lokacin bayan kwana biyu bata basa wani update kan Haidar d in ba. Ganin bazai daina kiraba yasa ta d aga ba don taso ba.

Tana d agawa ta fara

34 / 103