AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   102 / 103

303K to 306K   out of 306.8K words

irin duba  That s just it.. Shikenan.?

Haidar ya jinjina mata kai yana fadin  Umhum..!

Sai ta matso sosai saitin kunnensa ta rada masa  But I love you more than love itself..And when I tell you I love you.. I m not saying it out of habit.. I m reminding you that& You are my life..!

Baisan sanda ya rufe bakinsa da nata suka lula wata duniyar.

**

Months later&

"An fara shirye shiryen auren Hilal da Kulsum, Azeema da Sadis da kuma Badia da Alhaji Gimba. Dan Alhaji Gimba bai k asa a gwiwa ba har saida ya tabbata ya samu soyayyar Badia da amincewar ta. Matarsa ta jima da rasuwa kuma d a d aya gareshi Wanda tinda Ya tafi turai karatu bai kuma waiwayowa gida ba aure ma can yayi. Ya auri baturiya  yar k asar Poland. Suna can da yaransu har biyu saidai shi Alhaji Gimban yaje Ya duba su idan yaji kewa amma sam basu zuwa Nigeria Shiyasa a lokacin da Daddy yake nuna halin ko inkula akan Haidar Alhaji Gimba yake ganin kuskuren abokin nasa. Mu zamto masu godiya ga d imbin rahamar Ubangijinmu garemu domin abinda kake rainawa wani shi kawai yake fata da burin Allah Ya basa. Bamu gane mahimmancin wani ni ima da Allah yai mana sai mun rasa wann abin. Allah kasa mu zamto bayinka masu godiya a gareka da kuma karban k addara a duk yanda tazo mana."

**

Khulsum ta rok i alfarmar iyayenta da su bari ta tafi can Jigawa wajen Dije. Koda aka fara bikin ma Abba da Umma basu nemi ta dawo ba sai Inna Dije Tai mata nata bikin a can. Aure kawai aka d aura a Kano amma tana can wajen Inna Dije. Sosai Inna Dije taji dadin hakan Har saida tai hawaye sabida farin ciki. Hak ik a Khulsum ta girmamata ta bata darajan uwa taji dadin wann karramawa sosai. Taita godiya ma abba da Umma tana hawaye. Umma tace ta daina godiya Hak ik a ita d in ta zamto uwa ga Khulsum a lokacin da ta gaza zama uwa gareta. Abin farin cikin shine Allah Ya dad a had e kan ahalinsu kuma ya cikasu da alkhairi.

Umma da Mama Tani suka had e kawunansu suna kukan farin ciki. Yau yaransu gaba d aya sunyi aure. A baya lokacin da sukaci musu buri na ganin sunyi ko wani irin aure ko ta halin k ak a sai Allah Ya barsu da wayonsu. Yanzu da suka fawwala masa al amarinsu sai Ya zamto majib icin al amarinsu. Ya kawo ma  ya yansu mazajen aure na gari a lokaci guda. Lallai Ubangiji Ya cika abin godiya.

An sha biki lafiya a lokacin cikin Ummul Ya tsufa Baba Ali nada shekara d aya da wata uku a duniya.

Tai zaune a playing room d in Baba Ali tana duban yanda Haidar Ya baje ma yaron kayan wasa dangin building block da motoci irin na construction.. Harda helmet ya d aura masa yana fad in  Da kyau my little Engr let s build a house for Maama..

Ummul ta kuma dubansu tana sakin sassanyar murmushi.

Wayan Haidar ne ta soma ruri Ya daga yana amsawa. Da alama wayar nasa aiko ya Shafa. Tinda Ummul taga haka sai ta d anyi kicin kicin da fuska dan tasan bazai wuce kira na gaggawa Ya samu daga Lagos ba sabida taji sanda ya ida wayan Ya kira Sadis yace ya masa shatan PJ a ranan zai tafi Lagos d in bazai jira jirgin safe ba.

Ya k araso gabanta ya dan langab e kai yana duban yanda ta cika Tai fam. Ya duka gabanta hadida d aura hannayensa saman laps dinta  Maman Biyu.. What s wrong.. Why the long face.?

"Ya dan hararesa kad an bakinta a ture, kaman zatai kuka tace  Nasan tafiya zaka kumayi.. Bayan duka duka yaushe kazo. "

Haidar ya dan murmusa yana mai kamo yatsun hannayenta cikin nasa  Duk sabida haka ake fushi ana bata kwalliyan da aka mun.?

Sai Ya bata dariya ta dan murmusa tana mai kuma turo baki  Amma ai baka jima da zuwa ba.. Kuma kace wann karon zaka jima kafin ka koma.

Jinjina mata kai yai  Kiyi hak uri.. Dole ce tasa zanje suna buk atana a can. But I ll only be there for a while.. Bazan jima ba In sha Allah. Da zaran na gama abinda yakaini zaki ganni.. Tashi muje ki tayani i shirya jaka. Ya k arashe yana mai taimaka mata ta mik e da kyar. K arasawa yai Ya d auki Baba Ali suka nufi dakinsa gaba d aya dan shirya jaka.

Ummul tana fiddo masa kayan yana shiryasu a suitcase ta d an dubesa. Kaman bazatai magana ba sai kuma tace  Dazu Munyi magana da Anisa a waya take ce mun basu ganka ba har yanzu.. Yau kuma satinsu guda kenan da dawowa daga Germany.. Kowa yaje Ya duba Hisham saura kai..

Haidar Ya katseta  K arata ta kawo miki banje na duba mijinta ba..?

Saurin girgiza kai Ummul Tai  A a ba haka bane Ta bar abinda take ta matso yanda yake  Dan Allah ka yafe ma D anuwanka.

Ya dubeta kad an sai Ya girgiza kai  Na yafe masa tuntuni.

"Ta jinjina kai  Kai kokari ka mance komai ku gyara alak arku.. Haka ne kawai zai tabbatar da yafiyarka a gareshi.. Ina so ka min wann alfarmar mijina, kaje ka duba D anuwanka kafin ka wuce Lagos.. Please mijina.! Ta k arashe cikin sigan lallashi tana kuma kamo hannayensa."

"Haidar Ya dan furzar da huci kad an  Fine, zan biya na duba shi.. Yayi miki..? "

Ta murmusa cikeda jin dadi tana jinjina kai  Yayi min.. Na gode sosai.

Tsareta yai da ido. Sai Ya tallafo fuskarta da tafukan hannayensa.. Ya kannare ido sosai yana dubanta  What have you done to me Khairy..? You convince me on most impossible things..

"Ta murmusa tana kashesa da wani irin kallo mai kashe masa jiki. Ta sakala hannayenta saman kafad unsa, ta langab e kai  You love me so much that you can t say no to me. Tai maganar tana kashe masa ido.. Sai Ya janyota jikinsa Ya lumshe ido  Of course I do.. I do love you..! K arshe duk awa yai saitin zungureren cikinta ya soma zance da cikin  Hey twins, Papa is going on a short trip.. While I m away, be good kids and don t give too much stress to Maama& I love you. Ya k arashe yana sunbatan cikin. Ummul kaw sai dariya take dan so tari idan Haidar na zance da cikin jikinta sosai abin ke bata dariya. Sai ka rantse da wani cikakken mutum yake magana. Ba wai taga banbancin rainon cikinta na farko lokacin bata tareda Haidar da wann da take tare dashi. Taga gata da soyayya irin wana batai zaton na faruwa da gaske ba. Ita kam ba abinda zatace ma Ubangijinta sai godiya. Fad insa ne tsanani yana tareda sauk i sann duk Wanda ya dogara gareshi toh ya isar masa. Tafiyan Haidar da kwanakin da basu shige biyu ba ta fara labour. Ai kaw koda aka tafi asibiti cikin ikon Allah bata d auki dogon lokaci tana labour din ba ta haifo d iyarta ma sha Allah. Ba a kuma jimawa ba namiji Ya biyo baya. Ma sha Allah tabarakallah. Allah mai kyauta da k ari, buwayi gagara misali."

Zo kaga farin ciki wajen d aukacin ahalin. Abin baa cewa komai sai son Barka. Shi kansa Uban gayyan wato Haidar kai kace ba a tab a masa haihuwa bane. Kowa na farin ciki da son Barka. Wann karon Umma da kanta saida ta wanko k afa tazo Abuja. Tsaban farin cikin da Abba ya shiga ma tuni yace Umma da Mama Tani duk su shirya su tafi. Yara biyu lokaci guda ba k aramin kyauta bane. Taron suna yaga jama a . Harta da Inna Dije saida tazo.. Su Badia da Azeema dake a nan Abuja gidajen su yake tuni akai komai dasu. Khulsum ce dai aka sha fama da Hilal dan ciki gareta kuma karami irin mai saka laulayin nan. Da kyar dai saida Aunty Asshe ta saka baki Ya amince suka biyo jirgi suka taho gaba d aya. Gaba d aya dangi duk sun hallara. Abin fah ba a cewa komai sai son barka.

Ranan suna da safe Hajja ta had e kan  Yanmatan gaba d aya dan d abbaka wani al ada na ahalinsu.  Yanmatan a gida da sirakai sukan hadu su girka ma mai jego abinci wana zata ci.

Aka had a Anisa da yanke Albasa. Idon Anisa sai hawaye yake sai mita take tana fad in ita bata saba da wann aikin wahalan ba. Fad i take  Wayyo idona yaji.. I can t open my eyes.. Wai dole dai sai mu zamuyi aikin nan gida cikeda ma aikata.

Azeema ta harareta  Ni fah gaskiya duk kin cika mana kunne. Masu abin mita ma basuyi mita ba sai ke.? Tai maganar tana nuni da Khulsum da Badia dan dukansu biyu juna garesu.

Anisa ta galla mata harara da idonta da yai jazir Ya jik e da hawaye  Ina ruwanki dake nake.? Ai duk laifinki ne. Sabida kinajin haushina kika sa aka hadani da yanka albasa. Toh ai sai kizo ki karisa.. I m not doing it again..! Ta k arashe tana aje wukar had ida goge ido.

Azeema ta tabe baki  Toh ke me zaki iya ma idan ba yanka albasa ba. Ba iya girkin kikayi ba balle ace kiyi. Dan haka dole ki yanka albasa.

Badia ta lallashi Anisa da fad in kar ta biye ma Azeema k ila itama fitinar masu k aramin ciki take bata sani ba.

Azeema ta zaro ido tana fad in ita batada komai.

Aunty Asshe ce ta lek o tana musu sannu da aiki. Ta dubi Khulsum tace kar tayi stressing kanta musamman da yake cikin jikinta na sakata laulayi sosai.

Kawai sai Anisa ta fashe da kuka tana fad in  Wayyo Ammi idona.. Wayyo yaji..

Aunty Asshe ta galla mata harara  Meye haka ke kuma.. banson sakarcin banza.

Anisa ta kuma turo baki tana fad in  Ammi wllhi bakiji ba kaman idona zasu fice.

 Toh su fice din mana. Haka dai zakiyi.

Ta kuma fashewa da kuka tana fad in  Why are we torturing ourselves.. Is there not a machine for doing this..?

Aunty Asshe tace  Machine din kenan hannunki.. Ta dubi su Azeema tace su karo mata lawashin duk ta yanka. Kuma Mijinta na ida jin k arfi zasu tattara su tafi gidansu kuma zata hana ya d aukar mata wata mai aiki.

Anisa tace  Ammi kawai kice baki sona.. Dama Hilal kikafi so gashi kin hana matarsa aiki.

Aunty Asshe tace eh d in ba a sonta d in. Ta dubi Khulsum tace maza ta fito kitchen din haka Anisa ta had e aikin Khulsum d in da nata duk tayi.

Khulsum tana fad in zata iya Azeema na turota waje tana fad in  Wllhi Ammi dazu ma bakiga ba yanda take tangad i kaman zata fad i k asa saida na tarota.

Aiko nan Aunty Asshe tace maza maza ta fito haka ta huta.

Anisa sai ta kuma fashewa da kuka tana ma Azeema Allah ya isa data sa aka had ata da wahala. Dan ko bayan aurensu da Hisham a SouthAfrica ba girki take ba. Sann da suka tafi Germany jinya ma ba girki take ba. Yanzu da suka dawo ma gidan Daddy suke.

Azeema da baki baya shiru ta galla mata harara ta karo tulin albasa ta dangwala gabanta tana fad in  Allah dai yasa surkarki ce ta sakamu. Kuma baa isa ace baza a ayi aikin sirka ba. Ta kekace da dariya tana fad in  Maza ayi biyayya aci gaba da yanka albasa aci gaba da murza ido aci gaba da hawaye. Gaba d aya saida ta basu dariya. Kawai sai Anisa ma ta fashe da dariyar ga ido jazir fuska sharkaf da hawaye.

"Yara sunci sunan Mommy da Abba. Ta ko wani b angare farin ciki ke circulating. Da yamma aka sha walima na alfarma a nan gidan Daddy. Bak i maza da mata. B angaren mata daban na maza daban. Musamman aka d auko babban malami yai wa azi sosai kan mahimmanci tarbiya da kula da yara.  Ya ya rahama ne kuma kyauta ce da babu mai yinta sai Allah. Sann duk Wanda aka danka masa kiwon d a Tabbas amana aka dank a masa Wanda Allah zai tsayar dashi Ya tambayesa gameda wann amana da aka basa. Yaya ya tafiyar da amanar.? Ya sauk e nauyi da hakkoki da suke kansa.? Mu sani kafin mu samu nagartattun  ya ya Tabbas sai mun zama iyaye masu nagarta kuma ababen koyi. K addarar mu tana tafiya da jarabawar mu. A lokacin da muka kamanta namu k ok arin muka kuma had a da neman taimakon Allah sai kuma mukaci karo da jarabawa, toh fah mu sani wasu mutanen Allah yakan k addarosu cikin rayuwarmu ne matsayin jarabawa. Ya Allah kasa mu zama  ya ya masu biyayya ga iyayenmu sann ka sanya mu cikin iyaye masu nagarta. Ka azurta Al umman Mamzonka (SAW) da samun  ya ya na gari wad anda zasu zamto"

sanyin idaniya kuma sadak atuljariya a garemu baki d aya. Allah ka iyar mana abinda mu bamu iyawa. Ya Allah duk wata uwa da take nema ma  ya yanta shiriya Allah ka shirya mata su. Masu neman haihuwa Allah ka azurtasu da salihan  ya ya wad anda zasuyi alfahari dasu dama Al umma baki d aya. Ameen thumma Ameen.!

**

"Haihuwan  yan biyu yazo ma Haidar da tarin nasarori na rayuwa. A lokacin Daddy yai stepping down daga matsayinsa na kasancewa shugaban kampani kuma mai jagoranci kampanin. Yanda Ya d aura D ansa Aliyu ya zamto shugaba kuma mai jagorancin Kampanin. Sann Ya bar zab i hannun Haidar gameda aikin Hisham under his company. Idan har Haidar ya amince zai iya barin Hisham yai aiki a company, idan kuma bai amince ba Hisham bazai koma company ba. A Cewar Daddy bayan yafe masa da yai wann shine hukuncinsa."

Gagarumin taro aka gudanar yanda Haidar ya karbi lambobin yabo da karramawa dama. Ciki harda aikin da ya gudanar na bridge project da ya jagoranta a lokacin da yai yarjejeniyar AUREN WATA UKU da Ummul. Wann gadar ta zamto kaman itace mafarin komai. Sanda ya fito domin bada speech d insa bai k asa a gwiwa ba har saida ya fad i mahimmancin wann project d in a garesa da yanda Ya zamto silan canza direction na rayuwarsa harma da Company s future. Wann project d in zai tabbata na musamman cikin jerin ayyukan da yayi.

Daddy ya k araso sukai masabaha bayan zauren taron ya kacame da tafi da fatan alkhairi.

"Murmushi saman fuskar Daddy yake furta  Congratulations Son, ina tayaka murnan d imbin nasarori da ka samu. Ka cancanci fin haka. Nasan bazanyi danasanin dank a maka ragamar company ba. Inada yak inin zaka kai Company zuwa matsayi mai girma cikin yardar Ubangiji. Ya kuma duban Haidar sosai yana jin k walla na ciko idonsa. Sai ya kuma tuno lokutan baya yanda yaita nuna gazawar Haidar d in da kasawarsa. Muryar Daddy yaci gaba da rawa sanda yake furta  Today I want to tell you this Son. I am so proud of you.. Ina alfaharin zama mahaifinka Aliyu..! Ya k arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarsa."

Haidar ma murmushin yake sai yai hugging Daddy  Thank you Daddy.. Thank you for trusting and believing in me. In sha Allah bazan baka kunya ba.

Daga nan manema labarai sukaci gaba da hasko Haidar as the New President of Maitama Builders suna neman ji ta bakinsa.

Daga bayansa Ya sinkayo murya na fad in  Congratulations brother..! Ka cancanci wann matsayin.!

Juyowar da zai sukai ido hud u da Hisham dake dogara sanda alamun ya fara takawa da sanda bayan da Ya dawo jinya daga Germany.

Murmushi Haidar Ya saki sai ya mik a Hisham hannu suka gaisa  Thank you& Brother.! Haidar yace

102 / 103