AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   20 / 103

57K to 60K   out of 306.8K words

ya kuma cewa komai ba. A  yan kwanakin ta kula magana ma sai ya zama dole yakeyi. Ya koma mata tamkar bak o cikin gidan dukda dama a iya zamansu bata isa tace ta sansa kaman yanda tasan tafin hannunta ba dukda kuwa Auren sihiri da tayi dashi. Mik ewa yai ya nufi sama ba tareda ya kuma ce mata komai ba. Hannayensa sakale cikin aljihun sweatpants d in dake jikinsa.

Tabi bayansa da kallo har ya haye sama kafin tai saurin janyo laptop d in ta bud e. Sannu a hankali take bin duk wasu abubuwan dake fuskan computer d in tana karantawa.

Aiki yake sosai kan project d in da takeda masaniya yanata fad i tashi akai. Toh kodai mahaifinsa ya basa go ahead ne.? Idan har mahaifinsa ya amince ya jagoranci aikin dole akwai wani abu a k asa. Ba yanda za ayi mahaifinsa ya amince masa cikin sauk i.. She needs to find out meke faruwa.

**

Yau kwanaki biyu kenan Umma bata kuma waiwayowa ba. Hankalin Mama kaw gaba d aya ya gaza kwanciya. Damuwarta kawai shine tasan yanda Suwaiba ta samo irin wann arziki da ta gani tareda ita. Gaba d aya ta ma mance da batun Tasi u da halinda kud ad en shagon Abba ke ciki.

Yau d in ko asibiti wajen Abba ta gaza komawa. Tare take da yaranta Badi a da Azeema yayinda suka baro Salima can wajen Abba. Tunanin Mama d aya idan ta fice Suwaiba na iya zuwa gidan wajen  ya yanta Shiyasa ko k ofa ta gaza fita.

Mama da yaranta Azeema da Badia Suna tsaka da aibata Suwaiba  yar k ungiyar asiri gaban su Ummul suka soma jiwo hayaniya daga waje. Wann Ya dubi wancan wancan ya dubi wann.

Azeema tai saurin tare wani yaron cikin gidan da ya shigo a guje rik eda gudan dubu a hannunsa yana ihun murna. Azeema ta rik esa tana tambayarsa meke faruwa waje.

Yaron yace  Umma ce.. Umman su Khulsum itace tazo da k atotuwar mota tanata rabon kud i a waje..

Mama dasu Azeema suka dubi juna. Babu shiri suka nufi waje a fujajan yayinda su Ummul ma duban junan sukai itada Khulsum. Take suma suka take ma su Mama baya.

Mama da yaranta suka wani irin birki Har saida ya rage saura k iris Mama bataci tuntub e da wani yaro da ya nufo gida a guje yana ihu yana d aga kud insa sama.

Daskarewa Ummul da Khulsum ma sukai suna duban kayan al ajabi. Ikon Allah. Da gaske Umma ce ta fito cikin wann bak ar shirgegiyar mota tana rabon kud i ma Al umman unguwar. Mutane kaw sai fitowa suke kusufa kusufa daga lungu da sak o suna amsan kud ad en da Umma ke rabawa.

A haka Umma ta k araso gaban Mama. Ta murmusa tana dubanta  Tani ya muka sameku..

Mama ta kuma bud e baki tana duban Umma jin irin gaisuwan rainin da tai mata. Wai Tani ya muka sameku.. Tani fah.. yau Suwaiba bata kirata da Yaya kaman yanda ta saba ba. Tani fah ta kirata dashi gatsau. Waima Yaushe

"Suwaiba ta sami  yanci cikin gidan. Dan lokacin da aka aurota daga rugarsu babu kalan uk uban da bata gallaza mata ba ga wauwauta ga shashashanci had ida mugun k auyanci da sukai mata dabaibayi.. Wai har Suwaiba ne ta waye yanzu.. Lallai ta yarda da hausar nan da ake cewa Shege na k auye.. Idan bak auye ya samu faraga yafi d an birni iya shege.. Eh Tabbas yanzu ta shaida wann da idanunta.. Dan barikin da Suwaiba take a yanzu ko goggan d an birni Wanda aka haifesa tsakiyar wayayyu bazai ba. Ko ita kanta bata tasa k afa ta tsallake mijinsu dake kwance yana jinya ta tafi ta barsa ba. Sai yanzu take ganin ashe ita jaririya ce a bariki tinda ita saida shagon Isubu kawai tayi, tanata kumfan baki tana fad i tashi ta raba gadon Isubu tun yana raye dan kar Suwaiba da yaranta su samu. Ashe Suwaiba kallon k aramar  yar iska take mata. Ita a daidai wann gab ar ma ta baje Rumfar barikinta."

Muryar Umma ne Ya kuma dawo da ita daga duniyar tunanin da yai nisa ciki  Yauwa Tani nace ba ga wann ki kula da Abban Ummul sosai.. Naga Salima wajensa. Bansan mai kike a nan ba da har yanzu baki tafi wajensa ba. Idan akwai abinda ake buk ata kina iya sanar Dani dukda dai duk wani abinda ya kamata a bayar an bayar. An canza masa d aki ma ya koma b angaren kud i. Kira Salima zata sanar dake komai tinda tareda ita akayi duk wasu sauye sauyen. Tai maganar tana mai Ciro kud ad en cikin hamshak in jakanta. Yacce kasan matar gida na bawa  yar aikinta sak o.

Mama tai sakare tana duban Suwaiba.

 Ungo amshi mana..! Umma tace tana mai kamo hannun Mama had ida damk a mata kud ad en ciki.

Lokaci guda Umma tasa kai tana taku d add aya sai juya ma Tani mazaunai take.

Kusan silalewa wajen Mama tai har saida Azeema ta tallafeta.

Kasa motsawa Khulsum tai har Umma ta shige ta nan gabanta rik eda hannun Ummulkhairi wacce ke biye da ita tamkar rak umi da akala. Bata iya dawowa hayyacinta ba saida ta sinkayo muryar Mama na fad ida Azeema ta rik eta sosai bata iya tsayuwa kan k afafunta.

Cikin sauri Khulsum ta nufi bayansu Umma k afafunta Har hard ewa suke.

Tana shigowa ta sinkayo muryar Umma dake rik eda hannun Ummulkhairi tana fad in  Ba sai Kin d auki komai ba. Maza tashi muje direba yana jiranmu..

Katseta Khulsum tai da fad in  Ina zaki Kai  Yaruwata Umma..?

SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!*

*17*

*©þSameena Aleeyou& *

Katseta Khulsum tai da fad in  Ina zaki kaita Umma..? Muryarta Ya soma rawa sosai sanda take ci gaba da furta  Umma shin abinda mutane ke fad i gaskiya ne..? Umma dan Allah wacece ke..? Ina asalin Ummanmu da muka sani..?

 Banida lokacin Miki bayanin komai a yanzu Khulsum.. A halin da ake ciki  yaruwarki nazo d auka.. Ta k arashe tana mai janyo hannun Ummulkhairi.

Cikin azama Khulsum ta rik e Ummulkhairi tana girgiza mata kai tana hawaye  A a Adda kar ki bi Umma.. Adda dan Allah kar kije..

Dubanta Umma tai a yatsine kafin direba ya bud e mata owners corner saida ta dubi yaranta na d an lokaci kafin taceda Ummul idan kin gama kya shigo muje. Daga haka ta fad a mota kayanta.

Khulsum ta kuma share hawayen da suka gangaro mata. Hannayenta cikin na Ummul take fad in  Adda dan Allah kar ki bi matar nan.. Bamu san Ina zata kaiki ba.. Watak ila rad erad in da mutane suke da gaske ne Adda.. Kinga Umma dai an canzata gaba d aya bamu San Wacece ita ba a halin yanzu.

"Khulsum na hawaye take girgiza kai lokaci guda taci gaba  Adda Ummul, Mai zai faru idan da gaske wajen matsafa zata kaiki.. Mai zai faru idan wani abun ya sameki.? "

"Ummul ta zame hannunta daga cikin na Khulsum tabi bayan Umma aka bud e mata mota ta shige. Tana kallon Khulsum dake tsaye wajen hawaye na gangaro mata yayinda itama Ummul d in hawaye ne ke gangaro mata. Ta rintse idanunta cikin zuciyarta take furta  Kiyi hak uri  Yaruwata. Ya zama dole nayi wann. Babu abinda zai sameni face Allah ya k addari faruwan hakan.. Dani dake mun San yanayin Umma a d abi a da halayya. Munsan matsalan mahaifiyarmu, Abu ne mai sauk i a rud eta.. mahaifiyarmu ce, ya zama dole na bita na gano hak ik anin abinda ke faruwa da ita. Domin kaw bazamu bari ta auka ma halaka ba munaji muna gani. In sha Allah komai zai daidaita K anwata.. Ta k arashe tuanin nata wasu hawayen na kuma gangaro mata."

A daidai gate d in wani gida mai matuk ar kyau da tsari motar tai horn.

Khulsum da tuni ta d ale acab a tabisu a baya ba tareda saninsu ba. Tana ganin gidan da akai parking tace ma me mashin ya ajeta daga can nesa dan sai ta karanci gidan kafin ta danna kai ciki. Allah ya gani bazata bari mahaifiyarsu ta bada  yaruwarta ayi tsafi da ita ba.

Driver na Ida parking Ya fito ya bud e masu k ofofin. Zuciyar Ummul sai tsinkewa yake tana duban Umma wacce ta koma mata tamkar bak uwa.

Umma ta dafata tana murmushi  Ki saki jikinki Ummul d ita. Ban kawo ki yanda za a cutar dake ba. Domin kaw ni mahaifiyarki ce. Tin haihuwarki burina shine rayuwarki ya cika da d imbin alkhairai kaman dai yanda sunanki yake. Ta d an numfasa kafin taci gaba  Kinga nan gidan.. Gidan da za a share mana hawaye ne.. Gidan da za a cika mana burinmu da yardar Ubangiji. Kukanmu yazo k arshe Ummul.. Taho muje.. Ta k arashe tana mai janyo hannun Ummul. Amma sai Ummul ta tarje.

"Umma ta juyo tana dubanta  Ummul ya kika ja kika tsaya, kinga nasan damuwarki bai wuce tafiya da mukai muka k yale  yaruwarki Khulsum ba. Sanin halinta, sanin duk abinda aka saka da ita sai ya lalace shisa bamu taho da ita ba.. Shige muje kinji. "

Hawaye sukaci gaba da gangaro ma Ummul. Cikin rawar murya take furta  Umma gidan da za a cika mana buri fah kikace& Umma Ashe har akwai mahaluk in da zai cika ma wani mahaluk i burinsa..? Umma idan kinga burin d an adam ya cika ya bar duniyar nan ne..

Bata Kai aya ba Umma ta hanb are mata baki  Ke ke meye haka.. Daina kira mana mutuwa a nan.. Nidai bazan Mutu ba sai burina ya cika in sha Allahu. Shiyasa nace da yardar Ubangiji. Kuma burina shine na ganki a d akinki dik rintsi.. Koda k arshen abinda zan aiwatar kenan a rayuwana..

"Jikin Ummul ya kuma yin sanyin Jin kamar mahaifiyarta ta riga ta zauce. Cak tai tsaye tana duban mahaifiyarta, ta rasa tausayin kanta ne ko tausayin mahaifiyarta take. Muryar wata mata ce ya dawo da Ummul daga duniyar tunanin da ta tafi  Ummul d inmu ta iso..! Ta fad i kyakkyawan murmushi saman fuskarta."

Ummul ta karkato tana duban matar wacce keta faman fad ad a murmushinta. Kafin tai wani aune ta k araso ta rungumeta tana fad in finally sun had u. Lokaci guda kuma ta shiga janyo Ummulkhairy tana fad in maza ta shigo ta shirya mai hoto yanzu zai iso bada jimawa ba.

Tambayarta kanta take Wacece wann matar..? Ina Umma ta santa..? Hoto kuma..? Wane irin hoto..? Meke faruwa ne wai..? Anya zata iya jurewa..? Anya batai gangancin biyo Umma ba kaman yanda Khulsum tace.. Amma idan mutanen suka cutar da mahaifiyarsu fah.. Zuwanta shine daidai ko dan tasan wani hali Mahaifiyarsu ke ciki.

Jikin Ummul sai rawa yake yayinda Asshe taci gaba da janyota Har suka shige cikin gidan Umma na biye dasu baki har kunnenta.

*

A b angaren Khulsum kaw tinda ta shigo gidan ta rasa wani b angare suka shige. Nan ta hangi wani section daga farko. Ganin k ofan wajen a bud e Ya sanyata nufan k ofan cikin tunanin nan su Umma suka shige. Saidai tana shiga wayam bataga kowa ba. Shiru alamun babu kowa. A hankali cikin sand a ta soma jada baya zata fice. Saidai tana cikin sand an da baya da baya taji ta bangaji mutum. A tsorace ta juyo zuciyarta na tsinkewa dukda bata bari tsoron Ya nuna saman fuskarta ba saima sauk e huci da take.

"Wani matashin saurayi ta gani ya zuba mata ido, hannayensa hard e. Yana binta da kallo mai d aukeda alaman tambaya."

Taci gaba da huci tana hura hanci basu daina duban juna ba.

 Ina  yaruwata.. Mai kuka mata.. Su waye ku.?

"Hilal ya girgiza kai kad an  Excuse me, what are you talking about..? Wait, Who are you..? And what exactly are you doing in here.? "

Gajeren tsaki tai had ada sa kai zata shige. Hilal ya kuma tare gabanta Yana girgiza yatsa alamun bazai barta ta fice ba har sai ta amsa masa tambayoyin sa  Oh wait. Dakata dakata. Ai bazaki fita ba sai kin sanar dani wacece ke. Daga ina kike..? Kuma mai ya shigo dake b angare na.?

Ya d an girgiza kai ganin har lokacin hararsa kurum take. A tunaninsa sabuwar mai aikin Amminsa ce a gidan. Ya katse shirun da fad in  You must be new here? Basu fad a miki masu aiki basa shigowa b angarena ba saida izinina.?

Kallonsa tai daga sama zuwa k asa jin ya kirata da mai aiki  Kaga Malam ka bani hanya na wuce. Banida lokacinka balle na tambayoyinka. Watak ila ba kai nazo nema ba.! Ta k arashe kaman zata bangajesa ta shige.

Ya d an matsa Ya bata hanya ganin da gaske bangajesa zatayi. Lokaci guda yabi bayanta da kallo  Who s she.? She doesn t sound like mai aiki. Ya d an girgiza kai har lokacin yana duban k ofan  She s so tough. Ya fad i yana mai tab e baki had ida girgiza kai.

*

Suna shigewa d akin Ummul ta juyo ta dubi matar amma bataga Umma tareda ita ba. Nan fah tsoronta Ya ninku.

Asshe ta murmusa ganin har lokacin jikin Ummul bai daina rawa ba  Ki kwantar da hankalinki Ummulkhairi. Ki saki nan gidanku ne kinji.. Ga bathroom ki shiga kiyi wanka duk abubuwan buk ata zaki samu cikin band akin.

Asshe tasa kai zata fice kenan Ummul tai saurin kamo hannunta  A a dan Allah kar ki cutar dani.. Dan Allah kar cutar da mahaifyata.. Na San tanada nata irin matsalar amma ita d in ba mai kwad ayin abin duniya bace.. Bansan mai ya sameta ba har ta mance damu da mahaifinmu dake kwance gadon asibiti ta zab i wann rayuwar.. Kiji tsoron Allah kar ki cutar damu.. Na rok eki..! Ta k arashe tana mai duk awa gaban Asshe tana kuka sosai.

Tallafota Asshe tai ta d agota cikin k ok arin kwantar mata da hankali take fad in  Ki kwantar da hankalinki Ummul banida wani k ulli cikin zuciyata taimakonku nai niyya.. Kar ki min mummunan fahimta..

Ummul taci gaba da kuka har lokacin jikinta rawa yake  Dan Allah kar ki cutar damu kar ki cutar damu..

Ganin gaba d aya ta birkice yasa Asshe daka mata tsawa da fad in  Ke ki mun shiru.. Yi mun shiru dallah.. Kar ki mun shashashanci a nan.. Shige maza kiyi wanka kafin masu kwalliya da mai hoto su iso.. Tai maganar tana k ok arin tura Ummul cikin bathroom Ummul tana tarjewa tana fad in  A a dan Allah.. Dan Allah a a..!

Daidai lokacin Khulsum ta k araso ta finciki hannun Ummul daga rik on da Asshe tai mata  Sakar mun  Yaruwata.!

Ta fad i da k arfin gaske tana fincikan Ummul.

Asshe tai tsaye tana duban Khulsum wacce tuni ta soma tambayar Ummul koda abinda ya sameta  Adda sun Miki wani abu ne.. Muje zo mu gudu.. Zo mu tafi..!

Kaman daga sama suka sinkayo muryar Umma tana fad in  Babu yanda zaki kaita.. Sakar mun  ya..!

Da mamaki Khulsum da Ummul suke dubanta.

Khulsum tace  Umma Allah bazai baki damar cutar da  Yaruwata ba sabida tin tasowarta biyayya take Miki. Dani da  Yaruwata zamu tafi.. Zamu fice daga rayuwarki Umma idan Har haka kike so.. Muryar Khulsum ya soma rowa sosai  Umma me ya sameki..? Su waye wad ann..? Menene gaskiyan rad e rad in da mutane suke akanki.. Umma shin kin manta da k alubalen da ahalinmu suke fuskanta..? Shin har akwai abinda Yafi Miki ahalinki mahimmanci..? Umma Abba yana kwance a asibiti tsakanin mutanen da suke mafarki da burin ganin bayansa.. A daren da kika zab i ki tafi ki barmu Har kusan kwana nayi a police station.. Duk ina kike Umma.. Ina kike sanda mahaifinmu yake tsananin buk atarki kusan shi.. A kullum muna fita mu fuskanci mutane da maganganun da suke jifanmu dasu.. Yanzu kin zagayo kin d auke  Yaruwata kin kawota nan ayi tsafi da ita.!

Bata kai aya ba taji sauk an mari a k uncinta. Ta d ago tana duban Umma dake sakin huci.

Lokaci guda take nuna Khulsum hawaye na gangaro mata  Ke baki san

20 / 103