AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   89 / 103

264K to 267K   out of 306.8K words

wajena. Ta k arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarta. Ta k arasa ta sumbaci Baba Ali dake bacci kafin ta kuma yima Ummul Sallama. Har Mommy takai k ofa Ummul ta mik e cikin sauri tana duban Mommy. Ta ambaci Mommy a hankali."

Mommy ta juyo tana dubanta. Sai Ummul ta isa da sauri bata san sanda ta fad a jikin Mommy tana hawaye.

Mommy ta rungumeta sosai tana bata baki tareda mata fatan alkhairi. A haka dai suka sake wani sallaman.

Ummul ta kuma yarda kaunar dake tskaninta da Mommy daga Allah ne ba wai dan ta kasance mahaifiyar Haidar ba. Dan ita dai tin farkon haduwarsu tin kafin ta saka Haidar a idonta Allah ya jefa mata k aunar matar.. Matar da tai defending dinta a gidan da babu kowa nata cikinsa gidan da mijin da taje domin sa ya gujeta. Koda ace Mommy da manufa ta nuna mata so a fari itakam bataji son da take ma Mommy ya ragu ba ko kadan.

**

Abuja&

Isowan Mommy gidan ta hangi sashen Haidar a bud e ana fiddo da wasu kayayyaki. Mamaki ya cika Mommy. Ta dubi d aya daga cikin ma aikatan ta tambayesa lafiya meke faruwa meyasa suke fiddo da wasu kayayyakin.

Kafin ma aikacin ya bata amsa ta hangi Hisham ya fito daga sashen sai stretching hannayensa yake yana Ware su alamun duniya tana masa dad i.

Mommy ta zuba masa ido tana duban ikon Allah. Daidai nan Hisham ya k araso yana mata sannu da zuwa. Bata iya amsa shi ba sabida mamaki da ya daure mata Kai. Can ta hangi Daddy na k arasowa da murmushi saman fuskarsa. Ganin Daddy sai Hisham ya koma ga ma aikatan yana ci gaba da nuna masu abubuwan da yake so da Wanda baya so a sashen.

Daddy na mata sannu da sauk a bata iya amsa shi ba sai nuni da tai da sashen Haidar cikin tsananin shock  Engr. Meke faruwa..? Ya naga ana fidda wasu kayayyakin Haidar daga sashensa.?

Sai Daddy ya murmusa  Banda abinki Kwaise Haidar kam ai yanzu bak o ne a gidan nan.. Ko kin mance tin bayan bikin tariyarsa saidai yazo mana bak unta..

 But still.. Sashen sa ne.. Akwai sections da yawa a gidan nan.. Meyasa na Haidar..? Cewar Mommy har lokacin a shock take.

"Murmushi Daddy ya kumayi  Haba Kwaise is just a section.. Ba wani abu bane dan D anuwansa ya zab i ya zauna a nan. Hisham da Kansa ya zab i wann section d in.. Ni kuma ganin yanzu Haidar ba mazaunin gidan nan bane yasa nace zai iya amfani da wann b angaren. After all, nan ne ya kamace shi ba b angaren bak i ba. "

 Amma Engr.. Haidar ya sani.? Kasan yanda yake. Kasan yanda baya so ayi invading space d insa ba tareda saninsa ba..

Muryar Haidar ta sinkayo daga bayanta yana fadin  Is ok Mommy.. Yai maganar kyakkyawar murmushi samar fuskarsa.

Ta waigo tana dubansa murmushin ne saman fuskarsa. Yana k arasowa ya bud e mata hannaye alamun hug. Sai ta fad a da murmushinta suka rungume juna yana fad in  welcome Mommy.. Ya hanya.. Ya kika baro Little Haidar.?

Daga Mommy har Daddy murmushi sukai Mommy tana fad in ba ko kunya D ansa kawai yake tambaya. Su duka ukun raha ne saman fuskokin su yayinda Mommy ta Ciro wayarta tana nuna musu hoton littile Haidar yanda Ya k ara wayau. Daddy na fad in dashi yake Kama ga hancinsa da sumarsa ya d auka. Mommy na cewa hasken fatanta da manyan idanunta ya d auka. Haidar ya saka iyayen nasa gaba yanda ko wanne yake fad in jikan nasu dashi yake kama. Sai murmushi kurum Haidar yake. Hisham na tsaye daga gefe rik eda hoton Haidar da Ummul Wanda aka musu ran bikin tariyar su ya fito dashi daga sashen Haidar d in. zuciyarsa sai faman tafarfasa yake.

Basu Ankara ba sai karan fashewan abu sukaji. Hisham ya saki hoton ya fad i k asa ya fashe.

Suka juyo gaba d aya suna duban Hisham Wanda tuni ya d uka yana k ok arin tattare hoton yake fad in Haidar yai hakuri bai sani bane. A garin k ok arinsa na tattare hoton glass ya yanka masa hannu. Daddy ya k arasa da sauri ya

rik o hannun Hisham d in yana duba yankan da yai. Hisham yana fad in Daddy ya bari ba komai it s nothing serious. Tuni Daddy ya rikosa ya nufi cikin gidan dashi yana fad in  You are bleeding Son.. Are sure ba sai anje asibiti ba. Come We need to clean your wound. Ya k arashe suna nufan cikin gidan.

Mommy da Haidar suka bi bayansu da kallo kafin Mommy ta kamo fuskar Haidar  Son..

Saurin girgiza mata Kai yai ya kamo hannayenta murmushi saman fuskarsa  I m fine Mommy.. Don t stress yourself.. Ya rik o hannunta yana fadin  You just arrived.. Ki shiga ki huta..

Saida ya tabbata ya mata rakiya har cikin gidan kafin ya dawo yana duban hotonsu shida Khairy Wanda Hisham ya fasa. Duk awa yai ya d auki fasasshen hoton yana kallo. Daga bayansa ya sinkayo muryar Hisham  I m sorry Haidar.. It wasn t my intention to break your photo.. Sai yai aya har lokacin Haidar bai tankasa ba.

"Hisham ya zira hannayensa cikin aljihun jeans d insa  Koda yake dan na breaking hotonku bazai zama matsala ba.. After all, kayi breaking auren naku da kanka. "

Haidar ya had iyi abinda ya tok are masa mak oshi. Ya mik e tsaye ba tareda ya dubi Hisham ba. Yayinda Hisham yaci gaba da sakin muguwar murmushinsa silently dan ya tabbata ya tarwatsa Zuciyar Haidar da kalamansa kaman yanda ya tarwatsa hoton aurensu. Ga mamakin sa murmushi yaga Haidar ya sakar masa. Ya tako zuwa gaban Hisham d in k adan. Saida dak ik a ya gauta Haidar na duban Hisham na sakin murmushi kafin yace  You can do your worse Hisham. Amma bazaka tab a iya raba tsakanina da Khairy ba.. Kasan dalili..? Sai ya nuna masa fuskar wayarsa dan D ansa ne Akan fuskar wayar.

 Wann kawai ya isheka amsa. Kuma ka yarda dani.. Zan kawo k arshen karyarka da fuska biyunka.. Sai nayi unmasking dinka.! Yai maganar yana jinjina Kansa alamun tabbatar da kalamansa kafin yasa kai ya shige.

Hisham ya bisa da kallo yana shafa hab arsa muguwar murmushinsa saman fuskarsa.

Washe gari da safe Haidar da ya fito cikin shirin fita Office kaman yanda Daddy ya buk aci yaran nasa da su shirya da wuri sabida gabatarwa na musamman da zai musu a company nan ya iske iyayensa saman dining table. Ya k araso ya gaishesu Mommy tace ya zauna suyi breakfast.. Ba musu Haidar ya zauna.. Zai soma serving Kansa Daddy yace ya jira D anuwansa ya shigo. It would be rude a fara breakfast ba tareda an jirasa ba musamman da yake bak o ne shi a gidan.

Da mamaki Haidar ya dubi Daddy sai ya aje serving spoon din cikin sanyin jiki. Mommy ta dubi D anta cikeda tausayawa tasan an fara kaisa mak ura da al amarin sabon D an mahaifinsa. Hannunta ta d aura saman nasa cikin k ok arin calming d insa. Sai ya murmusa yana girgiza mata Kai alamun ba komai she shouldn t worry.

Time Haidar ya duba saman agogonsa dake daure hannunsa na hagu. Ya dan furzar da huci kad an.. Yana tapping yatsunsa a hankali saman table d in.. Ba jimawa gogan ya shigo cikin shirinsa tsaf irin shirin da bai tab a irinsa a baya ba idan zai tafi office. Da ka gansa kaga D an manya. Ga wata expensive suit da ya saka da wata tsadaddiyar cover shoe bak a sai shining take. Ga k amshin turaren TomFord dake tashi jikinsa. Irin dai turaren Haidar yau shi ya saka. Haidar ya kauda fuska gefe yana sakin murmushin takaici. Ba shakka wann banzan competing yake dashi a halin yanzu.

Daddy ya mik e da murmushi yana tarban D ansa sanda Hisham d in ya duka yana gaida Daddy cikeda ladabi. Daddy ya kamosa ya mik arsa tsaye yana tambayarsa how was his night. Hisham ya amsa yana wani sadda Kai k asa yawa mutumin arziki. Haidar ya kuma yin murmushin takaici yana kauda fuska. Hisham ya k araso ya duk a yana gaida Mommy.. Ta amsa masa da sakin fuska tana fad in bismillah ya zauna suyi breakfast.

Hisham ya zauna a kujera mai kallon na Haidar murmushi saman fuskarsa yake fad in  Good morning bro& I hope I

didn t keep you waiting.?

Mik ewa Haidar yai yana fad in  I ll.. Go ahead..

Mommy ta dakatar dashi  Haidar ka tsaya kaci abinci mana.. You can t go to work with an empty stomach.

Haidar ya dan girgiza Kai  Kar ki damu Mommy zanci a Office.

Daddy yace  Koma ka zauna Haidar..

Ba don yaso ba ya komo wajen zamansa.

Hisham ya murmusa yana duban Haidar sanda yake cakalan chips da fork  You shouldn t be skipping your breakfast

"Brother.. Because, they say breakfast is the most important meal of the day& Haka ne Daddy.? "

Daddy ya jinjina Kai da murmushi saman fuskarsa  K warai haka ne. Gwara ka dinga fad a ma wann D auwan naka dan bai son abinci tuntuni.

Hisham ya murmusa yace  K warai ni zan bada shaidan hakan.. Dan baida abokin da ya fini..

Banda murza fork and knife din dake hannunsa ba abinda Haidar keyi sabida takaicin da ya turnikesa. Bai tunanin zai iya hakurin zama waje d aya da mayaudari irin Hisham. Washe gari ma Daddy yasa yaran nasa su shirya cikin manyan kaya wann karon. Cikin su biyun babu Wanda yasan nufin Daddy. Bai kuma sanar dasu ina suka nufa ba.. A haka dai suka d auki hanyar Airport cikin shiga ta manyan kaya.

Basu zarce ko ina ba sai birnin Maidguri yanda sukai rakiya wa mahaifin nasu ya amso aurensa da tsohuwar matarsa a karo na biyu. Saidai amarya bata biyosu Abuja ba ta buk aci ango ya bari sai daga baya ta tare dan abubuwan komai ya faru ne cikin sauri. Ga dangi da bata gama zagawa ba. Taso Hisham Ya zauna nan Maiduguri tareda ita amma sai Daddy ya nuna yana buk atan Hisham d in can Abuja kusansa.

Farin ciki wajen Hisham baya misaltuwa. Shidai Haidar bai um bai um um.. Sam baijin haushin matar amma yasan D anta bak in k umurcin maciji ne. Snn koda suka dawo gida ya jaddada wa mahaifiyarsa tana tareda goyon bayansa duk abinda zai faru. Mommy ce ta kwantar masa hankali da fad in babu abinda zai faru da izinin Allah sai alkhairi domin Auren da mahaifinsa yai ma zabinta ne.

Bayan ficewar Haidar daga wajen Mommy Daddy ya shigo. Duban Mommy yai da murmushi saman fuskarsa. Zatai magana yai saurin daura d an yatsarsa saman lips dinta. Yai gyaran murya kad an sanda ya rik o hannayenta cikin nasa  You don t have to say a word Kwaise. Yau d in ni zanyi maganar.

Murmushi ne saman fuskokinsu suna duban juna hannayensu cikin na juna. Daddy ya dan sassauta murya kafin yace

 Do you know that.. you are the pillar of this family..

Murmushi Mommy tai had ida girgiza Kai kad an  Kai Engr.. Kar fah ka mance ni fah matar Engr ce so nasan matsayi da amfanin pillar a gini.. I might be the scaffolding that keeps the pillar upright.. But you are the pillar my Engr.

Daddy yai murmushi mai bayyana hakwara kad an kafin yace  Lallai na yarda ke matar magini ce. Amma a wann ahalin you are both the scaffolding and the pillar Kwaise..

Behind every successful man is a woman. Do you think I'd be Aliyu Maitama that I am today if it weren't for you..? Yaci gaba da murmushi yana dubanta  Hak ik a Allah Ya gama min duk wani gata da Ya bani mace  yar aljannah irinki. Thank you for everything Kwaise.. Allah ya miki albarka..

Ta sadda idonta kad an tana mai amsawa da Ameen mijina.

**

Washe gari sassafe a station ya musu. Idan kaga Anisa sai ta baka tausayi. Ta fice a hayyacinta ta shiga makarantar ta natsu. Ga mahaifinta yace ba ruwansa ya cire hannunsa akanta sann idan Asshe ma ta taka k afa taje yanda Anisa take a bakin Aurenta. Asshe tanaji tana gani an mata farrak u da  yarta kaman yanda tai ma Umma da  yarta Ummulkhair a baya. Tabbas sharri d an aike ne. Duk yanda ka tura shi zai dawo gareka.

Hisham dai Ya gama k ulle Anisa cikin case din ko ta ina. Sam bai bar wani k ofa da zargi zai hau kansa ba.

K arshe Daddy da Haidar suka buk aci belin Anisa Daddy ya bada umarni da a rufe case din gaba d aya .. Saidai ana tsaka da processing release papers d in Anisa sukaji sauti daga bayansu na fad in  Bada garaje ba. Babu yanda wann macuciyar zataje har sai ta biya kisan yar mu da tai.!

A tare Daddy da Haidar harma Hisham suka waigo suna duban mutanen da suka shigo station d in.

Daddy ya girgiza kai yana dubansu cikin rashin fahimta  Su waye ku.?

Mutumin yace  Mune iyayen Dareen da  yarku ta kashe.!

Sabon tashin hankali da ba a saka masa rana.

Ga dai iyayen Dareen Sun bayyana Sun kuma d au alwashin sai an karb ar ma  yarsu hakkin kasheta da akai wanda hakan ke nufin ba ranar fitar Anisa daga gidan kasu babu kuma ranar rufe case. Sann ba ranar yanke hukuncin shari a har sai angano gawan Dareen.

Anisa ta amsa laifin ta na cewa ita ta bige Dareen da mota sabida soyayyar da take ma Haidar dan ga shaida an samu a gidan Aliyu Maitama motar da Anisa tai amfani dashi ta bige Dareen.

A halin yanzu case ake na kisan Dareen Wanda duk wani evidence yake pointing zuwa ga Anisa. Itace prime suspect. Ita keda babban dalilin kashe Dareen sabida son da take ma Haidar kaman yanda ta tassama kashe Ummulkhair.

Allah sarki Anisa dole ta baka tausayi dan ba wanda zai fiddata daga cikin wann masifa da take ciki sai Allah. Ta saduda ta koma ga Ubangiji. Shi kawai take ambata da ya kawo mata d auki.

SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!*

*59*

*©þSameena Aleeyou& *

Safiyar ranar Alhamis Haidar ya fito cikin shirin fita Office. Can wajen motoci ya hangi Hisham na zab en motar da zai d ale. Saida ya hangi fitowar Haidar kafin yai murmushi ya isa jikin farar SUV da Haidar ke hawa time to time ya dafa motar yana duban Haidar murmushin nan nasa saman fuskarsa  How about this ride.. Baka tunanin zai dace Dani..? Dear brother..!

"Haidar baice dashi komai ba ya nufi motarsa. Har ya isa jikin motar ya d ago yana duban Hisham da murmushi saman fuskarsa  Bazaka tab a zama kaman Haidar Maitama ba, no matter how hard you try.. Kasan dalili..? Ya tsare Hisham sosai da ido  You are nothing like me.! Yana ida fad in haka ya saki murmushi kad an kafin ya juya zai shige motarsa. Sai kuma ya juyo kaman Wanda ya tuna wani abu. Ya dubi Hisham yace  Make sure you don t"

lose track of time.. You don t want your Boss to arrive first before you.! Ya k arashe yana nuni da agogon dake daure hannunsa. Lokaci guda yasa kai ya shige mota yaja motar ya fice daga gidan.

Takaici ya cika Hisham. Ya bigi tayar motar da k afarsa guda tsanar Haidar na kuma ruruwa cikin zuciyarsa musamman idan ya tuna yana sama dashi wajen aiki. Da takaicin Haidar ya nufi Company. Yana tafe hanya Daddy ya kirasa ya sanar dashi ya zama in charge bazai Sami shigowa company ba ranar. Haba nan fah kan Hisham ya kuma fashewa yana jinsa sama da Haidar.. Alla alla yake ya isa Company ya nuna ma Haidar kasawarsa tinda gashi Daddy shi ya k ira ya bar masa ragamar komai a hannunsa. Yau sai ya wulak anta Haidar ya k ask antar dashi a company. Allah yasa ya Riga Haidar isa ya wulak anta sa.

Haidar kaw bai isa Company ba Daddy ya kirasa yace ya juyo zuwa gida. Ba musu ya dawo ya tadda mahaifin nasa.

Farar shadda mai dankaran kyau da tsada Daddy ya basa yace ya sauya shiga zasu wani wajen. Ba musu Haidar ya amsa yai yanda Daddy yace duk a tunanin Haidar Maiduguri zasu sake komawa tinda bai jima ba sukaje suka amso auren Daddyn.

Wann karon ma airport suka nufa saidai ga mamakin Haidar maimakon Maiduguri wann karon Garin Kano suka nufa. Suna isa Sadis ya isa ya d aukosu. Shidai Haidar sai aika ma Sadis kallon tuhuma yake yayinda Sadis ke ta faman

89 / 103