AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   79 / 103

234K to 237K   out of 306.8K words

sai an sallamesa sun koma can gida Kano ta yanda ba wani tashin hankali da zai bullo mana. A tsanake zamu tunk ari lamarin. Kedai kawai ki kwantar da hankalinki kiyi duk abubuwan da na umarceki tinda kinada yarda da amincewata ki k addara tamkar kin Auri Haidar an gama.

Anisa ta danyi jim sai kuma ta jinjina Kai tace  Gaskiya ne Mommy. And its a once in a lifetime in sha Allah. Kuma so nake Aurenmu Ya karad e ko ina dan babban biki nake so Mommy.

Mommy ta jinjina Kai tana duban Anisa murmushi saman fuskarta.

**

A haka Anisa taci gaba da mafarkinta na kasancewa matar Haidar cikin kwanciyar hankali sanin cewa tana tareda yarda da amincewar Mommy. Ba abinda yake gabanta a halin yanzu tamkar taga wann mafarki nata Ya zama gaskiya. Dole ta dad a daure belt dinta da kyau dan ta tabbata Ummul bata dawo ba. Burinta bai wuce taga wann ragwababben uban Ummul d in Ya bar garin ba.

A can b angaren su Ummul ma Hisham yanata samin lafiya saidai da yaga hankulansu zai karkata zuwa wani abin daban sai ya b ullo da wani abin wanda zai dauke hankulansu.

A haka aka kwashe kwanaki satuttuka Har aka soma k irga watanni. Kowa da abinda yake burin cimmawa. Ummul na nan tana rainon cikinta. Hisham bai fasa kudirinsa da shirinsa ba. Haidar bai fasa neman Ummul ba. Mommy ta maida hankali kan Anisa yayinda Anisa taci gaba da mafarkin cikan burinta. Abba yanata samun lafiya. Daddy nata zarya tsakanin SouthAfrica da Nigeria kasuwancinsa na dad a bunk asa a k asashen k etare.

Cikin Ummul nata girma cikin k oshin lafiya. Saidai tinda cikin Ya fito ta kuma rok on Hajja da cewa dan Allah ta barta tai rainon cikin gabanta ko dan guje ma abinda zaije yazo cikin ahalinta.

A b angaren Haidar kuwa dukda ayyuka da suka sha gabansa bai fasa k udirinsa na nemanta ba. Dan tinda tafiye tafiyen Abba ya k aru Sai ayyukan cikin gida Nigeria suka dawo wuyan Haidar gaba d aya. Kusan shi yake kula da ragamar Kampanin.

*

Watan Abba uku a Abuja aka sallamesa daga asibiti. Tuni Haidar Ya kira Sadis ya sanar dashi tinda dama duk wani hidindimun asibitin Sadis d in keyi.

"Kai tsaye gidan Daddy suka taho. Abba har tafiya yake da sanda, idan ka gansa bazaka gane sa ba ya samu lafiya da kula cikin ikon Allah. Sai son barka. Mama Tani da Abba ne a bayan motan yayinda Azeema ke zaune mazaunin mai zaman banza Sadis na tuk awa."

Koda suka iso gidan Mommy da kanta ta tarbesu. Tuni tasa an shirya musu sashen bak i sai haba take dasu Anisa kaw sai cika take tana batsewa dikda cikin zuciyarta fal annashuwa ne an sallami nakasashen uban Ummul zasu fice daga rayuwarsu gaba d aya su huta.

Suka raka juna da mugun kallo itada Azeema dan dukansu basu mance karonsu da juna ba.

Anisa taja dogon tsaki ta juya Azeema ma Tai shigewarta tana kad a kai.

Tinda suka iso gidan jikin Abba ba a sake bane. Ya kuma duban Mama Tani yace  Tani wai shin bazai yuwu mu tafi gida a yau d in nan bane sai mun kwana gidan sirakanmu. Ni fah sabida naga Ummulkhairi na amince na taho.. Amma ina ganin rashin dacewar hakan. Abin zai yawa ai.

Dukda k irjin Mama Tani dake bugawa sai tai k arfin halin cewa  Haba Malam.. Daga sallamanka asibiti sai ka hau hanya.. Ai dai ka jira ka d anji k arfin jikin.

Shiru yai kaman mai nazari sai Ya girgiza kai  A a Tani.. A Ina kika taba jin Uba yaje gidan sirakansa Ya saki jiki.. Wann ai bai tsari ba& Iyakacin karamci da duk wani taimako mutanen nan Sun mana. Kuma na shaida Ummulkhair tayi sa an miji da iyayen miji masu dattaku da sanin darajan d an Adam. Kinga bazan so ni kuma suga namu rashin dattakun ba.

Tani ta d an murmusa  Haba Malam. Kamawa fah take. Ba don jinya da Allah ya jarabceka dashi ba da hakan bazai kasance ba. Fatanmu Allah ya k ara maka lafiya su kuma ya biyasu Ida mafificin alkhairi.

Sai Ya dubeta kaman Wanda Ya tuna wani abu  Na shafe watanni banga Suwaiba ba..

Wai ance kishi dole saida Mama Tani taji zuciyarta ya d an sosu. Sai Tai kokarin kauda tunanin tace  Malam a yau kawai sau uku kai waya da Suwaiba.. Kai hakuri zaka ganta ne da zaran mun koma gida. Kasan Suwaiba da kunya da

surkunta bazata iya zuwa nan ta duba ka ba Shiyasa bata zo ba amma ai nakan had aku a waya tin bayan da likitoci suka ce zaka iya amsa wayan talho haka ne.

Abba ya jinjina Kai a hankali sai kuma yace  Ummulkhairi fah.? Kince bata iya fita ko k ofa sabida junan da take d auke dashi. Likita yace mai tattare da had ari ne.  Ya d anyi fasali  Amma ai zan iya ganinta yanzu.. Zan iya zuwa Har yanda take ko Tani. Ya fad i yana k ok arin mik ewa da sandarsa.

Mama Tani ta rasa ta ina zata b ullo masa. Mai zata sanar dashi gameda Ummul da Aurenta.?

Ganin yana k ok arin mik ewa yasa Tani saurin kamo hannunsa  A a Malam ka dakata ka dan huta kaci abinci.. Ai.. Ai nan gidan sirakan Ummulkhairi ne.. Ba.. Ba nan bane Gidanta Shiyasa baka ganta ba. Ta fad i cikin k ok arin had o kalaman tanayi tana kauda fuska gefe.

Abba ya tsareta sosai da ido dan yasan matar tasa sosai. Ya sani idan tana had o zance.

 Tani. Ya kirawo sunanta cikeda kulawa.

Ta d ago ido a sanyaye ta dubesa  Na am Malam.

 Ina Ummulkhairi..? Ya jefo mata tambayar.

Tani ta d an sosa keyarta  Tana gidanta Malam. Dan Allah ka kwantar da hankalinka. Kaji mai likitan nan yace sam shiga tashin hankali ko damuwa ba naka bane& Kaga lokacin sallan la asar ta gabato barin taimaka maka ka d auro alwala. Ta fad i tana mik ewa.

Bayan ta masa rakiya ban d aki ta nuna masa yanda zaiyi nan ta dawo d akin tana waya da abokiyar zamanta Suwaiba. Ko shakka Babu matsalan suke tattaunawa.

Sam Tani bataji fitowar Abba daga Band aki ba sai muryarsa ta saurara yana fad in  Tani& Mai nake ji kina cewa?

Za a sami Ummul da izinin Allah..? Tani meke faruwa..? Ina Ummulkhairi& ?

Ya k arashe tambayar jikinsa na rawa daga nan yanda yake tsaye. Har sandarsa rawa take.

Murmushin da yafi kama da yak e Mama Tani tai. Ta k araso tana fad in  Wai Har ka fito bakai kirana ba.

Abba ya girgiza Kai ba alamun wasa  Baki amsa min tambayata ba Tani. Da waye kike magana a waya? Sann meyasa kikace za a samu Ummulkhair.?

 Da Suwaiba nake magana Malam. Kuma tambayata take ko kun gana da Ummul tinda tasan kana matuk ar son ganin Ummulkhairin.. Shine take ce min an sameta a waya nace za a sameta in sha Allah. Ta k arashe cikin k ok arinta na gamsar dashi.

Abba yai shiru kaman mai nazari dan Sam baijin zuciyarsa ta natsu da maganganun Tani d in.

Bayan yayi sallah Tani ta taimaka masa suka fito parlor yaci abinci Ya sha magani.

Nan Mama Tani ta soma waige waigen neman Azeema. Ta mik e tana fad i ma Abba bari ta nemo Azeema cikin gidan. Dan Sam zuciyarta bai kwanta ba da rashin ganin Azeemar tinda tasan sam ita da Anisa d iyar k anwar Hajiya Kwaise had uwarsu baya dad i.

Ficewar Mama Tani da kad an aka soma k wank wasa k ofar.

Abba ya mik e kad an daga kishingid en da yake. Ya bud e idanunsa yana duban k ofan yake fad in  Bismillah.

Wata budurwa ce ta turo k ofan da Sallama saman bakinta.

Abba ya gyara zamansa yayinda murmushin Anisa Ya k aru tana tambayar Abban ko zata iya shigowa.

Abba ya jinjina Kai yana bata izinin shigowa had ida amsa gaisuwarta.

Anisa ta risina yawa mutumiyar arziki tana kuma yima Abba sannu da jiki had ida fatan samun lafiya. Harda addu o i ta jero masa. Abba ya amsa cikeda jin dad I musamman da yaga yanda yarinyar ke girmamasa sai ta tuna masa da Ummul d insa.

"Anisa taci gaba da risinawa tana fad in  Abba ni sunana Anisa, kuma k anwa nake ma sirkin ka Aliyu.. Sann munyi zaman dad i da Ummul dan har mun k ulla k awa ce da Ya zarce Ya koma tamkar  yanuwan juna.. "

Abba yace  Allah sarki.. Toh.. Ma sha Allah.. Ai ga dukkan alamu halayyanku ne yazo d aya da Ummulkhair.. Dole kuyi abota.

Anisa taci gaba da murmusawa tana kuma sadda Kai.

Sai ya dan gyara zamansa kad an yace  Amma.. Nace ina ita Ummulkhairin.. Har yanzu ban ganta ba& Ina so naga

d iyata.. Ina so naga yanayin jikin nata.

Anisa ta waro ido tana dubansa. Sai ta d an waiga baya kad an tace  Ban gane baka ganta ba Abba.. Wai har yanzu basu sanar dakai ba.?

Abba ya dubeta da mamaki  Akwai wani abinda Ya kamata na sani ne gameda Ummulkhairina..?

Anisa ta soma girgiza kai  Abba ai Ummul ta jima bata nan.. Idan ban b ata lissafi ba mun d ebe a k alla watanni shida bamusan yanda take ba..

Abba ya girgiza Kai cikin rashin fahimta yana dubanta  Ban fahimceki ba yarinya.. Kina nufin b acewa Ummulkhairi tai baku san yanda take ba.?

Anisa sai ta fara hawaye murya na rawa take fad in  Abba Auren Ummul da D anuwana Aliyu Ya k are& Ta tafi

babu Wanda yasan ina ta tafi..

Daidai lokacin Mama Tani da Azeema suka shigo suka tadda Abba na dafe k irjinsa ga Anisa duk e wajen tana kuka.

Mama Tani ta soma salallami ta isa ta tallafi Abba dake k ok arin kaiwa k asa yayinda Azeema ta tafi a guje ta shak o Anisa tana tambayar mai tai ma mahaifinta.

Tani taci gaba da jijjiga Abba tana fad in  Malam meke faruwa..? Lafiya na Barka.. Innalillahi wa inna ilaihi raji un. Malam.!

Ita kuwa Azeema tuni ta shak e Anisa tana fad in sai ta sanar da ita mai tai ma mahaifinta..

Hayaniyar yaja hankulan mutanen gidan. Mommy ta shigo a fujajan tana tambayar meke faruwa.?

Azeema taci gaba da mak ura Anisa tana fad in ko ta fad a mai tai ma mahaifinta ko itama ta shak eta sai ta daina numfashi.

Jikin Anisa yaci gaba da karkarwa. Fad i take  Mommy ki yarda dani wllhi babu abinda nayi.. Gaishesa na shigo yi Ya tambayeni Ummulkhair ni kuma na sanar dashi bata nan.. Mommy bansan Mahaifin Ummulkhairi baisan meke faruwa ba.. Wllhi iyakacin gaskiyata kenan.

Azeema ta kuma yowa kanta tana fad in  K arya kike bak ar munafuka shak esa kikayi..

Mommy ta daka musu tsawa da fad in  Ya isheku dukanku..! Ta dube Azeema tace  Maza kirawo Sadis a koma asibiti.

"Sai suka sinkayo muryar Abba yana fad in  A a ba sai an koma asibiti ba.. Magana guda nake son ji! Ya dubi Tani dake hawaye yace  Tani, ina Ummulkhairi..? Shin gaskiya ne Aurenta Ya k are ta tafi babu Wanda yasan ina take.? Shin wann ne dalilin da yasa na kasa ganin Ummulkhair.? Shin wann ne abinda kuketa b oye min keda Suwaiba.? Wann ne dalilin da yasa Suwaiba ta kasa zuwa ta dubani tsawon watannin nan.? Tani mai kuka aiwatar lokacin da nake kwance..? Wane irin Aure Suwaiba da  yanuwana sukaima Ummulkhair da zaisa ta guji gida bayan mutuwansa.? "

Sai kukan Tani ya k aru yayinda jikin Mommy yai sanyi. Tai k arfin halin k arasowa. Ta dubi Abba sai ta dubi Tani.. Tace  Abban Ummul.. Dan Allah kar ka yanke hukunci Har sai ka saurareni& Duk abinda ke faruwa ko ince abinda Ya faru.. Babu wani mai laifi face ni.. Duka laifina ne& 

Daidai lokacin Haidar Ya shigo. Kafin Mommy ta k ara furta wani kalma Haidar yai karaf yace  Abba duka laifi na ne.. Ni nayi AUREN WATA UKU da Ummulkhair.! Ni nayi Aure mai k ayadadden wa adi da ita. Auren da zai Wanzu na tsawon Watanni uku. Ni na tilasta mata ta Aureni dan ta Sami damar biyan kud in jinyarka.! Na saka sadakin Ya zama kudin da za a maka aiki dashi muddin ta amince da Aurena.. AUREN WATA UKU.. Dan na cimma burina na mallakan wani aiki k ark ashin kampanin mahaifina.. Muryarsa ya soma shaking  It is all my fault.! Duka laifina ne ni Aliyu.. Umma da Mommy duka basuda laifi.. Laifin nawa ne& Da nai irin wann wulak antaccen Auren da Ummulkhair..

Cikin tsananin shock Abba ke dubansa. Ya soma takowa yana dogara sandarsa Har ya k araso gaban Haidar Wanda tuni ta sadda idanunsa k asa.

Abba yaci gaba da girgiza Kai yana ma Haidar kallon k iyayya  Kai.. Har ka isa.. Har ka isa ka saka rayuwar  Yata a matsayin farashi.?! Hawaye suka soma gangaro ma Abba sanda yaci gaba  Waye kai..? Wa ya baka ikon wulak anta rayuwar  Yata irin haka.! Ka amsa min waye ya baka dama.!

Haidar ya rintse idanunsa rad ad in da yakeji a zuciyarsa na ninkuwa.

Abba yaci gaba da jinjina kai  Shiyasa ka d aukoni ka kawo ni nan.? Dan ka goge zumubinka ne.? Ka amsa min.!

"Parlorn yai shiru sai hawayen dake gangaro ma Mama Tani, Mommy harma da Azeema."

"Abba yaci gaba da jinjina Kai yana duban Haidar dake tsaye gabansa kansa kife. Yaci gaba da nuna Haidar da hannunsa mai rawa  Ka sani, rayuwar  Yata baida farashi.! Gwamma ace na rasa nawa rayuwan.! Yata tana da daraja.. Tanada k ima.. Kuma ta wuce ayi irin wann wulak antaccen Auren da ita. Zan tabbatar maka da hakan.! Yaci gaba da jinjina kai yana haki da kyar. Lokaci guda ya dubi Tani yace  Ki shige mu tafi bamuda wajen zama a wann gidan.! "

Jiki a sanyaye Mama Tani da Azeema suka nufi hanyar d aki yayinda Mommy ke k ok arin shawo kan matsalar amma ko kallo basu ishi Abba ba daga ita Har Haidar d in balle Ya tanka musu.

A haka suka fito zasu wuce Haidar yai saurin kiran Sadis a waya ya sanar dashi Ya d aukesu komin dare ya tabbata sun isa kano cikin k oshin lafiya da izinin Allah.

Bayan tafiyarsu a waje Mommy ta iske Haidar. Ta zauna gefensa su duka biyun ba mai cewa komai.

A hankali Haidar Ya furta  It s so painful and tiring Mommy& 

Ta janyosa jikinta tana Shafa sumarsa kadan  This too shall pass

Haidar yace  Yaushe ne duka wad ann zasu wuce Mommy.? It s one challenge after another.

Mommy ta jinjina kai  Wann sunnar rayuwa ce Haidar. Haka rayuwa ta gada. You cannot expect life to be hundred

percent perfect.. Dole yau idan anyi dariya wataran zaayi kuka& Yau gareka gobe ga waninka.. Tsanani yana tareda

sauk i.. Duka wad ann zasu zo su wuce.. All you need to do is put your trust in Him.. Ka saka yardarka wajen Allah shi kad ai. Da sannu zai yaye mana duka matsalolinmu Ya cika ahalinmu da alkhairi.

Anisa ta hangesu daga saman bene tana murmushin cin nasaran kauda iyayen Ummul daga cikin picture d in. Tinda taga Mommy bata nuna mata b acin ranta gareta ba ya kuma tabbatar mata Mommy ta aminta da ta d ari bisa d ari. Yanzu ta tabbata zatai maganar Aurensu da Haidar dan dama tayi hakan ne dan ta samu ta kauda su a wuce wajen.

*

Koda su Abba suka isa Kano bai gane gidansu ba. Dan tuni an sauya fasalin gidan an d aga gini na zamani gaba d aya gidan hasken lantarki irin manyan fitilun

79 / 103