AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   68 / 103

201K to 204K   out of 306.8K words

e idonki.

Ta soma k ok arin mik ewa yayi saurin kamo hannayenta  Ina kuma zakije bayan kin riga kin jik e.

Baki a ture tace  Ba kaine ka jik ani ba... Kuma kasan Mommy ta gayyacemu cin abincin dare. Ya kamata naje sashenta da wuri dan na taimaka da wasu abubuwan..

 Kar ki damu Mommy bazata ce komai ba..

Ta d an hararesa baki a ture  Kuma na riga na shirya.. kasa na jik e gaba d aya.

Ya dan tab e baki kad an had ida lifting shoulders d insa  Shikenan sai ki sake wani wankan. Ya matso saitin kunnenta yana mai rage murya  Let s bath.. Together..

Turasa tai da duka k arfinta ta tashi . Murya na rawa ta shiga nuna masa forehead d insa da hannunta  Kaga duba kaga.. akwai abu kusan idonka.. Yakai hannunsa goshinsa sai Ummul tai amfani da damar ta tashi a guje ta zille masa. Wann karon itake masa dariyar.

" Don t worry, I ll get you next time. Ya k arashe yana mai mata alama da yatsarsa."

Anisa da tin shigowarta sashen ta soma sinkayo kaman sautin mutane nan ta sad ad kaman mai shirin satan wani abu. Ta lab e yanda take sinkayo sautin. K iris Ya rage Zuciyar Anisa bai buga ba. Kasa jurewa tai dole ta fice daga sashen.

Tana ficewa ta d auki waya ta kirawo Hisham. Cikin tsananin huci take fad in  No way Hisham. I can t wait till that day.. I m losing my patience here. Na tsani wann kucakar.. She s driving me crazy.. Ji nake kaman naje na shak eta.

 You will not do anything foolish.

Ta katsesa  Na gaji Hisham.. Bakaji yanda suke dariya cikin nishad i ba. They were having a good time. Ta saki kara tana fad in  It s so irritating.. Ka gane we can t let those two be happy while we are stuck here.. just freaking miserable. We need to act fast.!

Hisham dake ci gaba da sakin huci Ya katseta cikin tsawa  Just shut up Neesa.! Na gaya Miki bazaki aikata komai ba ba tareda umarnina ba. Na dan lokaci ne. Haidar bazai taba samun dama akan Ummul dita ba. So just trust me.! Ya k arashe idanunsa ba kuma kad awa in rage.

A fusace ta katse kiran tana kuma ci gaba da zagaya d akin zuciyarta naci gaba da tafarfasa. Sautin nishadin Haidar da Ummul Ya kasa barin kwanyarta da kunnuwarta. Ta saki k ara kad an tana durk usawa wajen. A hankali take furta  I hate you.. I hate you Ummul.!

*

Koda Ummul ta koma nata d akin murmushi ne Ya kasa barin fuskarta. Ta Tina sanda sukai juyi cikin jacuzzi tub tare sai ta lumshe ido a hankali tana sauk e sassanyar ajiyan zuciya. Wata doguwar riga silk kalan peach da ya zauna a jikinta sosai ta d auko ta saka ta yane kanta da mayanin rigar. Ba makeup a fuskarta sai d an man leb e amma sosai tai kyau. Fatarta da bai cika haske ba sann bai cika duhu ba ya k ara murjewa yayi kyau. Kwantattun sumarta irinta asalin k abilar fulani da ta d auko daga mahaifiyarta sun kwanta sunyi luf tin daga gaban goshinta Har zuwa gefen fuskarta. Kallo d aya zaka mata kaso sake kallonta. Kalan rigar sosai ya tafi da Kalar jikinta. Abinda bata saba ba sai ta tsinci kanta da duban kanta a madubi. Kunya da dariyar kanta suka zo mata lokaci d aya. Harga Allah zata iya cewa ta mance da wata damuwar gidan duniya da batun Anisa. Shi d in kawai take hangowa a duniyar ta Wanda takeji tamkar su biyu ne ciki. Parlor ta sauko tana jiransa dan yace ta jirasa zasu shiga sashen Mommy tare.

A b angaren Haidar kuwa bayan Ya d auki file din ya jima yana juyawa yana tinanin maganganunta kai tsaye sashen mahaifinsa Ya nufa.

Daddy yana zaune study Haidar yai Sallama Ya shigo.

Daddy ya d ago ya dubi Haidar da idanunsa dake rufe cikin farin gilashi na k ara k arfin gani ga wad anda shekaru Ya d an ja masu.

Tin daga yanda Daddy ya amsa masa Sallama jikin Haidar Ya d anyi sanyi. Dan yanayin amsa masa da yai yasha bambam da irin yanda yake amsa masa a baya.

Sun d auki lokaci suna duban juna kafin Daddy ya nuna masa kujera mai kallon table d insa yace ya zauna.

Haidar ya k arisa ya zauna.

Shiru Ya dan ratsa tsakani kafin Haidar yai k arfin halin cewa  Daddy.. Barka da dare.

Daddy ya amsa masa had ida jinjina Kai.

Sai Haidar ya aje folder d in saman table din Daddy.

Daddy ya girgiza Kai kad an kaman Wanda yake avoiding k wayan idon Haidar d in  What s this for.?

Haidar yai clearing throat d insa  Yarjejeniyar project d in ne Daddy.. Tareda resignation latter.. Na janye ragamar kula da kwangilar.. Sann.. Na aje aikina na company.

Daddy sai Ya d ago yana dubansa sosai wann karon.

Haidar sai Ya mik e kansa a kife  I.. I m sorry idan ban kasance wann d an da kake fata da buri na zama ba..

Ya soma k ok arin ficewa daga study d in mahaifinsa ya dakatar dashi.

 Aliyu.! Daddy ya ambaci sunansa.

Ya d ago Ya dubi Daddy.

Da ido Daddy yai masa nuni da kujeran  Koma ka zauna.

Haidar ya komo ya zauna har lokacin Kansa a kife.

Cikin tsawa da fad a kaman yanda ya saba masa a lokutan baya ya soma fad in  Ni kake ce ma ka aje aikinka..? How dare you.? Who do you think you are...! Kai har ka kai ka dubeni kace min ka aje aikinka.? Kai har ka isa.?!

Da a lokutan baya ne da ya amsa ko ya maida ma mahaifinsa martani cikin daga murya. Amma ga mamakin Daddy sai yaji ya soma magana a natse  I m sorry.. But I can t do it Daddy.! Ya fad i k walla suna ciko idanunsa. Cak mahaifinsa ya tsaya yana dubansa.

Haidar yaci gaba da girgiza Kai  I can t destroy you.!

Daddy ya koma ya zauna yana duban Haidar d in sosai cikin tsanani shock.

 My plan was& To use this so called project and destroy you.. I wanted to show you the kind of monster you created in me.. But then I couldn t.. I couldn t destroy the hands that raised me koda ace mun kasance munada alak a mai rauni cikeda tarin k alubale. Yaci gaba da girgiza kai. Sai murmusa kad an wann karon  I just want to be free from this prison. I.. I don t want to keep on living my life tied to all this rage and hatred.. I want live a normal life.. To start a family of my own.. Muryarsa yaci gaba da rawa  I.. I m sorry Daddy.. I m sorry idan ban kasance wann d an dake fata da burin samu ba.. I m sorry idan ban kasance wann D an da zakayi alfahari dashi ba.. Believe me.. I truly.. am sorry..

Baikai aya ba Daddy dake ta k ok arin danne hawayensa sai ya zame farin gilashinsa ya kauda fuskarsa kadan yana goge hawayen da suka mak ale masa a ido.

"Kaman daga sama Haidar ya sinkayo muryar mahaifinsa  Aliyu, my son.. "

Da mamaki Haidar ke duban Mahaifinsa Jin ya ambacesa da D ansa abinda bai taba ji daga mahaifin nasa ba.

 Shin ka tambayi kanka koda ka farka daga coma meyasa baka ganni wajenka ba.?

Shiru Haidar baice komai ba.

Daddy yaci gaba da jinjina Kai har lokacin bai kalli b angaren da Haidar d in yake ba  Sabida bazan iya kallonka a ido ba.. Bazan iya ambatan kaina da mahaifinka because I.. I haven t been a good father to you.. And I treated you badly.. Daddy ya kifa Kansa hawaye na gangaro masa  Fad an da kaji ina maka a yanzu borin kunya ce kawai sabida ni d in ban sauk e wani nauyi da hakki na mahaifinka dake rataye wuyana ba. Hadisi ne guda cewa ko wannen mu mai kiwo ne kuma za a tambayemu gameda wann amana na kiwo da aka dank a mana. Bazan iya duban idanunka na nemi gafararka ba Haidar& Bazan iya ba..! Saiga alamun kuka cikin muryar Daddy.

Haidar ya mik e jikinsa a matuk ar sanyaye ya tako har zuwa gaban kujeran da Daddy ke zaune bisa. Duk awa yai gaban Daddy Wanda har lokacin Kansa na kife yana d igar da hawaye.

Haidar ya daura hannayensa biyu saman hannayen Daddy dake bisa laps d in Daddyn. Shiru ne ya ziyarci wajen baka iya jin alamun komai face motsin zuciya.

Daddy ya rik e hannayen Haidar tsam cikin nasa  I m sorry son.. I m sorry.. Please forgive your Dad& 

Hawaye suka gangaro ma Haidar dake duk e gaban Daddy hannayensu cikin na juna.

"Mommy da ta nufo k ofan dan ta sanar da mijin nata gayyatar D ansu da matarsa dinner matsayin maraba da dawowa gida ma Haidar d in koda bazai nuna kulawarsa kaman yanda ta tsammata ba, nan ta riski wann babban al ajabi. Rana mai d inbin tarihi.. K afafun Mommy suka kusan gaza d aukarta.. Hawaye suka shiga zarya a k uncinta.. Sai Mommy ta fad i k asa tana mai sujada na godiya ga Ubangijinta. Tama rasa mafarki ne take kokuwa dai a farke take. Haidar dinta da mahaifinsa take gani cikin yanayi da bata tab a tsammanin zata gansu ciki ba. Allah buwayi gagara misali. Mommy ta kuma yarda cewa lallai duk Wanda ya dogara ga Allah toh fah Allah ya isar masa. Itakam babu abinda zata ce saidai taci gaba da gode ma mahaliccinta Wanda ya yaye duhun dake cikin gidanta da ahalinta ya yalwatasu da haskensa. Ta saki turban boka da suka d auko daga fari ta rik e turba na gaskiya sai gashi komai yana gudana cikin sauk i. Lallai wann wani rahama ne daga Ubangijinta. Lallai wann izna ce ga tababbu masu bin hanyar b ata. Wanda ya gane Allah shi yake yi ba boka ko Malam ba shi keda babban rabo duniya da lahira. Bata san sanda ta koma da baya ba ta nufi d akinta ta maida k ofa ta rufe ta fad a saman gado tana kuka sosai. Kukan farin ciki wann karon. Kukan da ya goge Wanda ta jima tanayi a baya Kama daga zuciya har k wayan ido. Alkhairin Allah yaci gaba da haska gidanta da ahalinta."

Haidar yaci gaba da girgiza Kai yana rik eda hannayen Daddy gam cikin nasa  Daddy ka daina bani hak uri. We are all human beings.. We make mistakes. What s important is that we learn from those mistakes. Yaci gaba da jinjina kai a hankali  Ni yafi cancanta na nemi yafiya a gareka Daddy. Idan inada hakki akanka hakkinka dake kaina yafi girma. Duk yanda naje nazo banida madadinka.. I should ve been more understanding with you. Cikin zuciyarsa yake tuno sanda Ummul take fad a masa  A rayuwa wasu lokutan Allah yakan saka mana jarabawarmu ya zamto people that are tied to us by blood. Sai Haidar ya mik a hannu ya d auko folder d in project da ya shigo dashi. Ya daura saman hannun Daddy suna kallon cikin fuskan juna. Murmushi gauraye da siraran hawaye saman fuskar Haidar yake fad in  Daddy I can walkway from this Business because it s my choice.. But I can t walkway from you. Do you know why.?

"Sosai Daddy yake kallonsa yana hawaye. Haidar yaci gaba da jinjina Kai  Because you are my Father.. Allah chose you for me& We are tied to each other by blood because haka Yake so ya kasance. Yaci gaba da jinjina Kai yana murmushi  Daddy jininka shi yake circulating cikin jikina daga farko.. A karo na biyu Kai ka bani jininka, you couldn t walkaway from me either. Sabida ni d in D anka ne. "

Daddy sai ya janyo kan Haidar ya rungume cikin jikinsa. Muryarsa na rawa yake fad in  Allah ya maka albarka Aliyu.

**

A lambum dake bayan sashen Mommy aka shirya cin abincin daren. Hasken wutan lantarki ya karad e ko ina tamkar ba dare ba.

An shirya teburin gwanin ban sha awa ga barbecue stand daga gefe.

Suna cikin shirya plates saman teburin itada Anisa Anisa tai excusing kanta sakamakon kira da ya shigo wayarta. Nan Ummul ta hangosa na tahowa. Sassanyar murmushi saman fuskarsa. Ta shagala sosai da kallonsa kaman yanda shima ya shagala da kallonta dan sosai tai masa kyau.

Yana k arasowa sai ya tsaya daga bayanta ya dan rungumota had ida rank wafo da kansa kusan kunnenta  You look.. Gorgeous.! Ya fad i cikin sigan rad a.

Ummul ta soma k ok arin turesa daga jikinta tana  yan waige waige  Mai kake aikatawa ne wai.. Idan wani ya ganmu fah.?

Bai saketa ba ya kuma rad a mata  So what.! Can t I hug my wife.?

Ta waiga ta dubi Anisa dake can gefe tana amsa waya. Ta kuma duban ma aikatan kitchen guda biyu dake gefe gaban BBQ stand.

Kaman zatai kuka tace  Dan Allah ka bari akwai mutane wajen nan fah nan..

Juyawa yai ya dubi kitchen staff d in. Sai ya dan murmusa  Is that problem.? fine. Zo muje. Bai jira amsarta ba ya shiga janyo hannunta. Suka nufi yanda ma aikatan ke gashin naman.

Haidar yace musu suna iya tafiya zasu kula da barbecue d in.

Ma aikatan suka amsa masa cikeda risinawa suna duban yanda Haidar ya janyo Ummul dake fad in ita fah bata iya amfani da irin wann abin gashin ba. Yace kar ta damu tare zasuyi.

Sosai suka birgesu kaman kar su daina kallonsu. Abu ne da zasu iya cewa basu tab a ganin ya faru gidan ba. Basu tab a ganin Haidar cikin farin ciki irin wann ba. Su dai kam Sun shaida zuwan Ummulkhair gidan Alkhairi ne.

Anisa ta juyo baki sake tana duban ikon Allah Haidar da Ummul gaban barbecue stand sai zuba soyayya suke. Gwiwoyinta taji sun sake kamar wata maras laka. A haka Mommy ma ta k araso wajen ta taddasu. Farin ciki maras misaltuwa ya kuma gauraye zuciyarta. Zuwan Mommy wajen yasa Ummul janye jiki ta kyale Haidar shi kad ai.

Haidar na fad in ta mik a masa bbq cutting board sai sann ya kula ta silale ta bar shi shi kad ai.. Ba kowa wajen ma sai shi kad ai. K ila Sun shige yin wani abin cikin gidan. Ya dan tab e bakinsa kad an.

Amma sai yaga wani hannu na mik o masa abinda yake nema. Haidar yabi hannun da kallo. Ga mamakinsa Daddy ya gani. Kyakkyawan murmushi saman fuskar mahaifin nasa. Haidar yasa hannu ya amshi board d in had ida godiya ma Daddy. Jinjina Kai Daddy yai. Sai Haidar yaga Daddy na nad e hannun long sleeve shirt din dake jikinsa alamun zai tayasa.

Sai Haidar ya girgiza Kai  No Daddy you don t have to.. Ya kamata kaje ka zauna.. I.. I ll serve you some. Ya fad i awkwardly dan abu ne da bai saba faruwa ba koma bai tab a faruwa ba tsakaninsu.

"Murmushi ne saman fuskar Daddy ya dafa kafad an Haidar din  No Son, let s do it.. Together. "

"Haidar yai murmushi yana tuna lokacin yarantarsa wann shine mafarkinsa. To make memories with both his parents& To strengthen their bond. Ya samu kusanci sosai da mahaifinsa. To have some quality time together.. To build something together. To play sports, video games, go horse riding da dai sauransu. Sai ya murmusa yana duban mahaifin nasa sosai. Kaman mafarkinsa ne yake zama gaskiya. Yana k ok arin yanka naman saman board din Daddy ya dafa hannunsa wana hakan Ya dakatar da Haidar. Suka dubi juna sai Daddy yace  Be careful Engr, this is not a construction side. "

"Su duka sai suka d an dara kad an. Daddy yace  You know Son, if I were to turn back time.. Da munyi aiki tare hand in hand.. Like professional Engrs. "

Jikin Haidar Ya d anyi sanyi Ya fahimci abinda sukeyi a yanzu d in Ya K wadaitar ma mahaifinsa inama lokacin da sukeda damar kasancewa tare a company sunyi ayyuka tare tare babu tsangwama babu hantara. Gashi yanzu Ya

68 / 103