AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   70 / 103

207K to 210K   out of 306.8K words

Ta kashe mata ido guda tana fad in a d auke su tare."

"Mommy ta k araso tana dubanta kwalla kaman zai zubo mata ta k arasa ta rungumeta  Kinyi kyau daughter.. May yours be among the best. Ta k arashe murmushi saman fuskarta. Nan aka d auke su hoto. K wallan da Ummul take makalewa ya gangaro. Mommy tai saurin goge mata tana girgiza Kai  A a Ummul, yau fah ba ranan kuka bane.. Bana so hawayen nan ya bata Miki kwalliya. Ta waigo cikin k ok arin danne nata kukan tana tambayar wai ina Haidar d in ne.?"

Anisa da takaicin acting Mommy ya isheta sai ta juya ido tana furzar da huci. Tana k ok arin barin wajen ta hango Haidar na shigowa cikin shiga ta farar shadda k al babbar riga harda hula. Shigan da zata iya cewa bata tab a ganinsa ciki ba. Sosai ya amshe sa dan ba Anisa kawai ba harta ita Ummul d in saida ta shagala da kallonsa.

Ya k araso aka musu su uku da Mommy. Ta shige tsakiyar su ta rungumesu su duka biyun akaita kashe musu pictures.

Daga bisani aka soma yima amarya da ango. Masu hoto suna bada direction. Aka ce ta d aura hannunta guda saman chest d insa sai ta d an d ago tana dubansa. Duban irin na mai yake nufi.? Ita fah har kawo wann lokacin bai mata magana ba gashi duk yanda aka ce ya rik e jikinta kafin ma ace yayi. Wann fah shine mutumin da a baya he s allergic to cameras. Ummul bata Ankara ba saiji tai ya d ago hannunta ya d aura saman chest d insa.

Anisa taji wani k atutun bak in ciki ya tokare mata makoshi. Ga wani kallo da suke bin juna dashi. A hankali take calming kanta cikin zuciyarta  Patience Neesa.! Patience.!! Na yau ne kawai.. Daga rana mai kaman ta yau ta zama tarihi a rayuwar Haidar dinki. Ta kuma murmusawa  I can t wait for things to get chaotic.

**

A can waje kuwa zabga zabgan bak aken jeep d in sukai parking. Motar farko Hajiya Asshe ce ta fito sai Inna Dije daga d aya b angaren. D ayar motar kuwa daga can seat din  yanuwan Ummul guda biyu ne Badi a da Azeema yayinda Umma da Mama Tani ke daga tsakiya. Suka neri suka fito sahu sahu.

Kallo guda zakai ma Umma ka fahimci tsananin tashin hankalin da take ciki. Tayi tsuru tsuru da ido ko motsi mai kyau bata iyawa. Badia da Azeema kuwa kasa rufe baki sukai ganin irin gidan da Ummul wai take aure ciki.. Ummul fah. Wacce kowa ke gudunta cikin ahalin su. Wann maras sa an.. Wacce ake mata lak abi da mai farar k afa.. Wann wacce maza da yawa ke guje ma Aurenta.. Allah mai iko. Gashi daga sauk an su wasu ma aikata masu uniform suka taho suna masu sannu da zuwa cikin harshen turanci cikeda ladabi suna amsan jakkunansu. D aya daga ciki tai directing nasu zuwa masauk i. Sukaja suka tsaya wann ya dubi wancan wancan ya dubi wann. Asshe ta furzar da huci kad an ganin duk sunja sun tsaya suna duban tsoro ma juna  Ku taho muje mana. Wai ko Baku gaji bane.?

Sai Inna Dije ta murmusa da shike ita ta tab a zuwa lokacin auren Ummul. Tace  Kunga ba masu yankan kai bane ko Shan jini. Ku taho muje..

Sai Mama Tani wacce ta kasa gasgata wata duniya ma tukunna take ta janyo Inna Dije tana rad a mata  Ke Dije.. Da gaske kike.? So kike kice min nan shine gidan da Ummul take ko kuma dai matar nan ta shanshantar damu ne gaba d aya Kama Suwaiba. Dije nan fah fadan shugaban k asa ne. K ur ani shine a talabijin nake gani.! Ta k arashe harda dangwala yatsa saman harshe.

Inna Dije taci gaba da janyo Mama Tani tana fad in  Kin dai gani da idonki.. Na tabbata bazaki so ki bar Ummul cikin wann daula ba. Duk bala in da za ayi bazamu fice daga gidan nan ba saida Ummul. Cikin sigan rad a suke ma juna magana.

Duk maganar da sukeyi ita dai Umma bama tasan mai ke faruwa ba jefa k afafunta kawai take tana tuna kalaman Asshe a gareta tana tuna a daidai wann rana sukai AUREN WATA UKU da tai ma Ummul da d ansu zaizo k arshe.

Azeema da abin ya fara bata tsoro ta dan jada baya tana janyo  yaruwarta Badia. Tai k asa da murya  Badia nifah wllhi naga gidan zama.. Wllhi bazan koma Kano ba ina nan tareda  Yaruwata.!

Badia ta dara kad an tace  Toh kiyi yaya da Habibinki kuma idan ya dawo miki.?

Azeema ta galla mata harara  A a Mak iyi dai ba Habibi ba. Ai ni idan kinga na fice a gidan nan saidai idan fadan shugaban k asa zan tafi..

Badia ta kuma darawa daidai sanda suka isa guest section din.

Asshe ta dubesu tace su saki jiki su huta ga abinci dama tuni an jere musu idan da akwai abinda suke buk ata ga ma aikata zasuji dasu. Zata shiga cikin gida ta sanar da isowarsu. Inna Dije ne kawai ta amsa mata yayinda Mama Tani ta rakata da harara duk cikin acting ne da suke dan su shashantar da Umma. Badia da Azeema kam basu tsaya sauraronta ba suka tashi suka soma zaga gida suna kallon aljannar duniya a cewarsu.

Bayan ficewar Asshe jikin Umma yaci gaba da rawa. Ba tareda ta dubesu ba take fad in  Yau ne.. Yau ne tai alk awari.. Wa adin auren zai cika.. Yau d ansu zai sakar mun Ummul d ita.. Zan d auki Ummul d ita mu tafi.. Shine kawai abinda ya kawoni..!

Mama Tani da Inna Dije suka dubi juna.. Tani tuni shiga bud e buden kayayyakin abincin da aka jere musu Wanda da yawa ma bama ta tab a ganin irinsu ba. Da ta ga dai bata gane wasu abun ba sai ta d auki Wanda takeda tabbacin naman kaza ne ta soma gwagwiya dama Tani da kaza. Tana ci tana Zare ido kaman za a k wace. Ta dafa Umma  Shiyasa na rakoki  Yaruwata. Kinga wann mata mai zubin akwati (Wai Asshe) kina ganinta kinga makira.. Wani abin take shirya Miki.. Ni da tuni kin sanar Dani ga yanda auren Ummul ta kasance ai da tuni anyita da wajewa an gama komai.. Haba Tani fah nake.! Ta k arashe tana kurban wani abu da bata tabbata kunu ne ko madara mai  yan yan itatu ciki ba. Ta lumshe ido tana fad in  Dole ace masu kudin nan kunci rabonku na Aljannah ehe.!

Inna Dije ta harareta sai ta dafa Umma tace  Suwaiba mu duka muna nan tare da ke bazan bari aci zarafin  yard anuwana ba. Kafin su wulak anta Ummul zamu d auketa mu tafi dan kinsan masu kudin nan su wulak anta D anadam ba komai bane wajensu. Tinda auren ma a wulak ance suka nema dan haka a wulak ance zasu nemi rabuwa bacin haka meye dalilinsu na gayyato mu a wann rana da sukai alk awarin kashe Auren. Kinga Suwaiba tashi ki shiga band aki kiyo alwala.. Muje na nuna miki yanda ake amfani da irin bandakinsu kinsan ni na tab a zuwa. Ta k arashe tana mai kamo Umma suka nufi band aki. Ta nuna mata yanda zatayi kafin ta dawo ga Tani. Ta kafe ta da ido  Ke kuma Tani ba sallah ba salati kin fara ciye ciyen abubuwan da cikinki bai saba da irinsu ba.. Idan cikinki ya

tsure kika kasa zuwa wajen shagalin bikin tozarta Suwaiba da  yarta saidai na kulleki a d akin nan dan nidai billahillazi bazaki b ata min shiri ba ehe..

Mama Tani ta saki gyatsa mai k arfin gaske tace  Yo ka iya ibada ciki bai d auka ba. Ibadanki ma maje ina Dije.. Yo naga k eta ce da fansa ya kawo ki nan..

Inna Dije ta galla mata harara yayinda Mama Tani ta shek e da dariya.

**

"Jikin Mommy ya d anyi sanyi. Ta kuma duban Asshe  Asshe kika ce harda Mahaifiyar Ummul akazo..? Asshe ina Jin nauyi.. Ina matuk ar Jin nauyin bayin Allahn nan.. Mu ya kamata mu fara zuwa musu ba su ba.. Kuma a yanda na shirya da anyi bikin tariyar zamu d unguma mu tafi gaba d aya mu gaida iyayen Ummul da danginta musamman iyayenta.. Mu kuma musu godiya sann a k ulla alak a da zumunci mai kyau.. Munada shirin zuwa gaba d ayamu.. Ni, Haidar harma da Engr da Kansa. Sun cancanci haka Asshe.. Dama kawai na buk aci wasu daga cikin danginta suzo ne dan itama taji dad i kar taga ba danginta ko d aya wajen shagalin. Dan farin cikin Ummulkhair. Duk jikin Mommy a sanyaye take maganar."

Asshe ta furzar da huci kad an tana mamakin dan dai Mommy batasan waye Suwaiba ba. Da bazata d aga hankalinta kan wann shashasahar matar ba.

Ta dan girgiza Kai  Aunty Kwaise ke ya kamata ki musu godiya ko su ya kamata su Miki godiya.? Yau kece zaki duk a kiyi godiya ma talaka Aunty Kwaise.? Aunty Kwaise Anya kece kuwa ba a canza ki ba.? Asshe ta k arashe tana bin Yaruwar tata da kallon mamaki.

"Sai Mommy ta dubeta ta shiga jinjina Kai  K warai kuwa ni ce Asshe. Saidai ba Kwaisen da kika sani a baya bane.. Wancan Kwaise da kika sani capitalist, maison mulki, izza da d agawa ta tafi kuma bazata sake dawowa ba. Wann Kwaise ce da ta fahimci duniya da rayuwa. Kwaise ce mai Neman dacewa da tsira duniya da lahira. "

Asshe ta furzar da huci kad an sai kuma tace  Aunty Kwaise nidai.. Da an kashe auren nan kawai mu basu d iyarsu kaman yanda muka tsaro daga farko kawai a huta.. Aunty Kwaise wa adin ya cika.. Kawai mu basu  yarsu kawai and save Haidar.. Ta k arashe cikin rawar murya.

Mommy sai ta d an girgiza Kai kad an cikin rashin fahimta  Save Haidar kuma Asshe. Kaman ya save Haidar.. If there s someone to save here is Ummul. Balle ma boka makaryaci ne kinga dai yanda Al amra suka kasance bayan mun bar hanyar b ata mun kama hanyar gaskiya. Kinga bana ma so ana d ago wann maganar kije ko da akwai abinda suke buk ata sann kizo kimin iso na gaishesu.

Asshe ta kuma fruzar da huci  Wai Suwaibar zakije gaisarwa Aunty Kwaise.? Matar nan fah ko a  yar aikatau d inki bata isa tazo ba.

Izuwa lokacin Zuciyar Mommy ya soma tunzura. A fusace ta dubeta wann karon  Matar da ta haifo Ummulkhairi idan ta kama na duk a gabanta na mata godiya ne zanyi haka Asshe. Domin kuwa tinda Ummulkhair ta shigo rayuwarmu banda alkhairi babu abinda muke gani. Ke shaida ce a gabanki komai ya faru Asshe.. For years ina kuka kan ahalina.. Ahalin da na ruguza da hannu na.. Akan idonki Haidar da baisan hawa ba baisan sauk a ba ya d auki burden din da ba nasa ba tsawon rayuwa. Shin ba Akan haka bane muka tassamma kauce hanya.? Yau sai gashi cikin ikon Allah Haidar ya zauna da iyayensa lafiya. Ahalin da na jima ina mafarki ya dunkule waje d aya. Ummul ta shigo ta farfado da duk wasu kyawawan d abi u da muka mance dasu ta cika gidan da nargartanta da alkhairanta.. Kinga kuwa ko duk awa nai na mata godiya ban fad i ba. Mahaifiyar Ummul ko wace iri ce Asshe tanada k ima da mutunci a idona. Danginta ko yaya suke mun zama d aya irrespective of our social differences. I expect you to do the same with them. Kin fahimta.! Ta k arashe cikeda umarni like a big sister.

Zuciyar Asshe yaci gaba da tafasa. Ta kula Aunty Kwaise tsaf zata iya zab en dangin Ummul ta mance ita ce danginta ta asali. Gaba d aya itakam kaman an canza mata  Yaruwa.

 Magana nake Miki Asshe..! Mommy ta kuma tsawatar mata.

Sai Asshe ta jinjina Kai da kyar tana k ok arin k wak ulo hawaye. Cikin muryar kuka take fad in  Aunty Kwaise yanda kike magana kin fara bani tsoro.. Aunty Kwaise karfa k warin gwiwar da kike dashi Akan yarinyar nan yasa ki mance komai.. Aunty Kwaise ni fah amana ce wajenki.. Iyayenmu Sun bar Miki amanata.. Banida wacce ta fiki kaf fad in duniya.. Aunty Kwaise dan Allah kar ki tab a mance hakan.. Idan kika rabu dani bansan ya zanyi ba& Duk abinda nakeyi kawai dan na damu dake ne.

Jikin Mommy ya d anyi sanyi. Sai taji dan dafa Asshe  Haka ne Asshe. Idan ba mutuwa ba babu abinda zai rabamu  Yaruwata. Likewise banida wacce ta fiki. A lokacin kuka da lokacin dariya duk muna tare. Ta dalilinki Ummulkhairi ta shigo rayuwarmu Asshe.

Bata k arasa sauraronta ba zuciyarta ya shiga tafarfasa. Dole dai sai ta ambaci wann mayyar yarinyar. Gaskiya ta fara yarda da batun su Dije yarinyar mayyace dan gashi ta lashe Zuciyar  yaruwarta.

Sauri sauri Asshe ta nufi kiran Dije da Tani. Suka keb e tana sanar dasu tsarin yanda zasu tarwatsa wann biki.

Asshe ta rik e kunne tana duban Tani da Inna Dije alamun kashedi  Kunaji biki ne na manyan mutane. Biki ne da zai samu halartan manema labarai. Dole  Yan jarida zasu sanin  yar gidan wane hamshak i tilon D an Aliyu Maitama yake Aure. Inaso da zaran manema labarai sun soma jefo muku tambayoyi ku fara amo duk abinda muka shirya.

Tani ta chab i zancen da fad in  Zan fed e musu daga buzu Har fata. Zasuji wacece Ummul da kuma yanda auren Ya kasance. Wayyo wayaga Tani cikin talabijin tana bayani.

Asshe ta furzar da huci had ida yin gajeren tsaki. Ta dubi Inna Dije alamun tana jiran nata ba asin.

Dije ta murmusa  Ita ce tayi sanadin mutuwan tilon D a na Faizu sabida bala in farar k afarta. Maza bila adadi sun mutu ta dalilinta.

Asshe taci gaba da jinjina kai tana sakin murmushin cin nasara.

**

Su Badia tuni Sun nufi cikin gidan suna fad in a kaisu wajen Ummul. Da kyar Anisa ta kyale su suka shige wajen Ummul d in a Cewar Anisa ana gyara mata kwalliyarta dan tuni ta canza zuwa wani shigan.

Sai kallonsu take tana yatsina fuska tana toshe hanci wai dik warin talauci suke.

Azeema tana hankalce da ita jira take su fito daga wajen  yaruwarsu Ummul suji da ita.

Suna shigewa katafaren bedroom d in suka tafi a guje suka rungume Ummul.

Ummul wacce ta gansu a bazata sai ta mik e cikin tsananin shock tama rasa mafarki take ko gaskiya.  Yanuwanta take gani. Sai ta rungumesu ta k ank ame tana mai fashewa da kuka.

Saida tai mai isarta suna bata baki suna fad in kar ta bata kwalliyarta.

"Ummul ta kuma dubansu dan ta kasa yarda  Azeema, Badia.. Wai dan Allah kune.? "

Azeema ta murmusa tace  K warai kuwa mune  Yaruwa. Kawo hannunki ma ki kuma tabbatarwa. Ta had e hannuwansu su duka uku waje guda. Ummul ta murmusa tana share guntun hawayen da ya digo mata da tissue  Ina Abba na.. Ya jikinshi..? Ina Khulsum da Anty Salima.? Meyasa basu biyoku ba..? Ina Mama da Umma.?

Azeema da Badia suka dubi juna sai Badia ta kamo hannun Ummul tace  Abba jikinsa da sauk i sosai Ummul.. Yana tashi yana zama saidai maganar ne da sauki. Sann har fita dashi waje yasha iska anayi. Abubuwa ne dai har yanzu ba kasafai yake ganewa ba. Likitoci sunce sai a hankali..Kinsan ciwo idan ya had u da shekaru.

Ummul ta jinjina Kai a hankali tana addu an samun lafiya ga mahaifinta.

Azeema taci gaba  Anty Salima tana tana gidanta yaranta ba lafiya kyanda suke gaba d ayansu. Amma tace muce Miki tana tayaki murna kuma taso zuwa Allah bai nufa ba. Mun taho da Mama da Inna Dije.. Da..

Sai Badia ta dan dubeta dan Umma ita ta rokesu cewa ko sunga Ummul cikin gidan kar su sanar da ita zuwanta tukuna. Basu kawo wani abu ba dan Umman ta kwana biyu cikin wane irin yanayi.

Ummul sai bata tambayesu Umma ba dan tinda sukace Mama ta taho sai tayi tunanin Umma ke tare da

70 / 103