AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   21 / 103

60K to 63K   out of 306.8K words

komai ba.. Baki san abinda ke faruwa ba.. Zo

ki fice& Shiyasa tin farko ban gayyatoki ba dan nasan ke dai kam ba a k ulla alkahiri dake.. Zo ki fice..

Muryar Asshe ne ya katse su. Ta dubi Khulsum tace  Kar ki Fad i abinda baki Sani ba yarinya. Duk fad i tashin da mahaifiyarku keyi akanku ne da mahaifinku. Ina kuke a lokacin da kishiyar mahaifiyarku ta koreta tace taje ta nemo kud ad en da za ayi ma mahaifinku jinya..?

Khulsum ta kaikaito tana mata wani irin duba  Wacece ke..? Me kike nema daga wajen mahaifiyata..?

 Ki kirani Sirkar  yaruwarki Ummul.. Domin kaw nan bada jimawa ba Ummulkhairi zata zamto matar D ana.!

Da mugun mamaki dukansu suke duban matar da kuma Umma.. suka kuma juyowa suna ma Umma wane irin duba Wanda su kansu basu san duban me suke mata ba a halin yanzu.

 Sirka..! Matar D ah..! Khulsum ta nanata tana duban Asshe da Umma kafin ta kuma juyowa ta dubi Ummul wacce ita kanta cikin rud ani da duhu take.

"Umma ta jinjina kai  K warai kinji da kyau.. Wann matar da kike gani k anwa take wa mahaifiyar mijin Ummul d ita.. Wnn karan bazan bama wani k ofa Ya lalata auren Ummul d ina ba, ba ke ba Khulsum ba Tani da  ya yanta ba ba kuma sauran munafukan mutanen layinmu ba.. Dan haka zo ki fice..! "

Ta k arashe tana k ok arin rab a hannun Khulsum dana Ummul amma sai taji wann karon Ummul ta rik e hannun

 yaruwarta k am tak i saki hawayen dake idanunta sun kafe sun daina zuba.

Ummul ta girgiza kai tana duban mahaifiyar tasu cikin rashin yarda  Har yanzu wann ne damuwarki Umma.. Ki aurar Dani kota halin k ak a..? Shin Umma rashin aurena ne kawai k alubalen da muke fuskanta a rayuwa..? Muryarta Ya soma rawa sosai  Abba yana cikin wann yanayi.. Ahalinmu suna cikin wann jarabawa amma ke damuwarki har yanzu guda d aya ne Umma.. Shin Umma bakida sauran matsaloli na rayuwa ne sai wann..? Umma iyakacin kiman da nake dashi kenan a wajenki a matsayina na  yarki..? Iyakacin kiman da mahaifina yake dashi kenan a wajenki matsayinsa na mijinki.. Umma ina zaki kai girman hakkin Abba.. Ta Ya zaki shirya aurar da  yarsa yana kwance cikin wann hali.

Khulsum na hawaye ta katseta  Ta Ya zata shirya sayar masa da  Ya dai.. Adda dan Allah kizo muje.. Muje mu nemi agaji daga hukumar hisba wllhi Umma bata a hayyacinta.. Ta k arashe tana kuka sosai.

Ummul na hawaye take girgiza kai  kiyi hak uri Umma.. Ki yafe mun amma.. amma Bana tunanin wann karon zan iya Miki biyayya.. Kiyi hak uri zanbi  Yaruwata mu tafi.! Tana ida fad in haka ta janyo hannun Khulsum  Muje Khulsum..!

Umma ta dubi Asshe hawaye na k ok arin ciko idanunta  Kin gani ko kinga abinda nake fad a Miki.. Wann  yaruwar tata ta kora mata mazan aure sunfi abinda suka fi da wann bak ar Zuciyar nata. Kin gani hassada take da ita.. Toh wllhi wann karon ban shirya jin kunyan duniya ba.! Tana huci take duban su Ummul da k iris Ya rage basu fidda k afafunsa daga cikin d akin ba.

Umma ta bud e murya tace  Ummulkhairi.! Idan kika saka k afa kika fice daga d akin nan.. Ki mance kinada mahaifiya Suwaiba..! Wllhi wllhi idan Har ki kai sanadin da mutanen nan zasu ce sun fasa auren nan toh Babu ni babu Ke kuma ke ba  Yata bace daga wann lokacin.. Ki nemi wata mahaifyar amma ba ni ba..! Ta k arashe tana sakin huci.

Cak Ummul ta tsaya ta kasa koda motsa k afarta guda.

"Gani haka yasa Asshe bud e murya  Ba sai kin mata baki ba! Baza kuma a mata dole ba. Yardarta da amincewarta shi zaisa ayi wann Auren. Ta maidoda dubanta ga Ummul  Har yau ba a biya kud in surgery da za ayi wa mahaifinki ba. Anyi masa komai, an canza masa d aki. Yana samun duk wani kulawa saidai kud in aiki ne kawai yai saura.. Kinsan dalili..? "

Ummul ta dubeta cikin tsananin sanyin jiki  Sadakin ki shine kud in da za a biya ai ma mahaifinki aiki Ummulkhairy..

"Asshe taci gaba da takowa gaban Ummulkhairy, su duka biyun suna duban juna  Nasan za a iso wann gab ar. Shiyasa ban bari an biya kud in aikin ba. Har sai nida Ke mun gana da juna. A halin yanzu, ki sani Aurenki shi kad ai ne zai ceci mahaifinki. Domin kuwa sadakinki da zamu biya shine kud in da za a masa aiki a ceci rayuwarsa.. Wuk a da nama na hannunki... Yanzu idan kika ce baki amince ba. Ni kuma zan janye komai ku nemi wani hanyar da za ayi wa mahaifinki aiki.. "

Umma ta kuma bud e murya ganin Asshe tayi nasaran dakatar da Ummul.

 Wacece matsalar ahalinmu Ummul. Kece matsalar mu. K addararki shi yai silan kwanciyar mahaifinki.. Idan Har akwai wacce tafi cancanta tai sadaukarwa mai girma wa mahaifinku.. Toh ki sani kece kika fi cancanta Ummul.!

"Khulsum ta soma girgiza kai tana duban Ummul  A a Adda, dan Allah karki amince.. Akwai na gari da yawa. Na Allah basa k arewa.. Dan Allah kar ki amince da wann auren na rashin galihu Wanda ko sanin mijin bakiyi ba. Ta k arashe tana ci gaba da janyo hannun Ummulkhairy alamun tazo su tafi. Amma sai taji Ummulkhairy ta doge. Lokaci guda take girgiza kai tana duban Khulsum  Kiyi hak uri Khulsum.. Na zab i ceto rayuwar mahaifina koda shine abinda zanyi na k arshe a rayuwata. Zanyi auren.. Zan auri ko waye Umma ta kawo dan na ceci rayuwar mahaifina.. Gaskiyar Umma ne. Watak ila idan nayi auren komai zai zo k arshe. Watak ila matsalar ahalinmu zai k are. Watak ila ni ce matsalar kaman yanda Umma tace. "

Khulsum na hawaye take girgiza mata kai alamun a a.

Cikeda k osawa Umma ta dubi Khulsum. Kinji abinda tace  Ita d in  ya mai biyayya ce ba irinki ba. Sakar min hannun  ya kafin ki mata sanadin abun alheri da ya sameta.

Khulsum ta girgiza kai tana duban Umma. Lokaci guda ta soma jada baya. Tana duban Ummul hawaye na gangaro masu su duka biyun.

**

A can gida kaw Mama tana zaune tsakar gida ta rapka tagumi ga su Azeema da Badia sai dadd age Kayan masarufin da Suwaiba ta kawo suke. Yaran Salima suna gefe an had asu da Kayan mak ulashe. Babu yanda Mama batayi ba kar su tab a Kayan Suwaiba Kayan Shan jini amma babu wacce ta kula mama cikinsu sai Salima wacce ta tayata da tagumi. Gashi Salimar ta basu labarin irin kud ad en da Umman ta kashe a asibiti. Amenity ma aka maida Abba executive room kula ake basa na musamman. Su Azeema kam har so take washe gari yayi ko Umma zata sake zuwa ta rok eta Aron tufafin kece raini taje bikin dangin mijinta da suke dashi a satin.

Mama ta kuma sauk e kakkauran ajiyan zuciya tana tuna Suwaiba a baya Suwaiba fah data maidata bora cikin gidan farkon aurota wai itace yanzu duniyar nan ta juya akeyi da ita. Gashi har  ya yanta na cikinta sun fara son Suwaiba da tarayya da ita. Ikon Allah Lallai ta yarda babu mayaudariyar aba irin duniya. Yanzu zata rud eka ka zata tanayi dakai anjima kad an ta sake ta Kama wani a Barka bakin Tasha. Ita yanzu haka tanaji tana gani Suwaiba zata ci gaba da zuba mata bariki a gida. Lallai bataci ta zama ba. Ya zama dole ta san abinyi.

**

Abuja

Saukowa yai cikin shirin fita waya manne kunnensa  Family dinner?

Ya d an girgiza kai yana ci gaba da sauk owa  This is not part of the agreement Mommy. You know we can t stand each other.

"Shiru yai alamun yana sauraro daga mahaifiyarsa  Fine, I m on my way there. Amma wann zai zama na k arshe. Daga haka katse kiran yai."

Dareen ta k araso tana dubansa  Going somewhere.? Tace tana mai kamo hannayensa murmushi saman fuskarta.

 To my Mom s Ya fad i a tak aice sai kuma ya k ara da  Don t wait for me for dinner.. Maybe I ll be back late. Ya fad i yana shafan b angaren fuskarta guda.

"Ta d an jinjina kai  Haidar, don t you think it s high time you introduce me to your family. After all, we ve been married for months now. "

Hannayenta ya kamo cikin nasa  I don t think it s necessary. Those people mean nothing to me. I don t even consider them family.. Na rubuta yarjejenyar rabuwa dasu. Rabuwa ta har abada.

"Tai masa k uri tana dubansa, Ya d an janyota cikin jikinsa suna fuskantar juna sosai  You.. And only you.. You are the only family I have. "

Murmushi ta saki zuciyarta zallan k aunarsa. Ta shafi gefen fuskarsa tana fad in  And I ll love you till my last breath.

Ya murmusa had ida manna mata light kiss. Lokaci guda Ya kuma mata Sallama kafin ya fice.

Tabi bayansa da kallo cikin d aurewar kai. This is not like him. Ya canza gaba d aya. Mutumin da ya tsana ai masa zancen iyayensa shine yanzu yake zuwa wajensu akai akai.. Sann mai yake nufi da ya rubuta yarjejeniyar rabuwa dasu..? Shin Wai meke shirin faruwa ne..? Haidar ya canza gaba d aya wani sabon kusanci na neman shiga tsakaninsa da ahalinsa.. At the same time yana cewa ya kusa datse duk wata alak ar dake tsakaninsu. What exactly is going on..? Kasa nemo amsar da Tai ya sanyata k arasawa saman kujera ta zauna tana kuma fad awa duniyar tunani.

**

Ita dai tana Jin yanda makeup artist d in keta faman zuzuta kyaun da tai amma bata tanka ba. Dan physically ne kawai take wajen amma tinaninta da hankalinta basu a wajen. Duban fuskar nata take cikin madubi Wanda dukda makeup d in ba mai tsanani bane. Amma abinka da wacce bata saba ba sai take ganin kaman an canza mata kamanni ne . Dama tin can ita ba gwanar kwalliya bace balle yanzu da take tsaka mai wuya. Bata tab a tsammanin Umma zata

"tafi da nisa har haka ba. Tana jin sanda su Umma da Aunty Asshe suka shigo sai faman zuzuta kyaun da tai suke. Lafaya ne Wanda kallo guda zaka masa ka tabbata Ya amsa sunansa kalan peach Wanda Ya dace da skin color d inta da bai cika haske ba haka nan kai tsaye baza a kirata bak a. sai black long sleeve shirt daga ciki, an kwantar da lallausar bak ar sumarta da Ya sha gyara daga gefe."

Asshe ta k araso da sauri ta mik ar da ita tsaye  Wow! lallai za a haifo mana Fulata shuwa. Yauwa  yar albarka Uwar alkhairi.. Maza muje masu hoto suna parlor suna jiran fitowarki.

Ummul ta d ago ta dubi Umma amma sai taga Umma ta kauda kanta gefe alamun bazata saurare ta ba. Cikin sanyin jiki ta soma jan k afafunta tana biyeda Asshe wacce ke rik e da ita. Can k asar zuciyarta bata komai sai ambaton Allah domin ya shiga lamuranta.

Suna fitowa parlorn suka tadda masu d aukan hoto har kusan mutum uku. Tai tsaye tana duban masu hoton wanda k arasowarta kawai suke jira komai nasu ya zama ready. Ji tai kaman kar ta k arasa wajen amma sai maganar Aunty Asshe ya fad o mata  Kud in Aurenki shine kud in aikin mahaifinki Ta d an d aga k wayan idanunta sama cikin k ok arin hana hawayenta zuba. Tamkar kazar da k wai ya fashe ma a ciki haka take takowa cikin parlorn. Ta k arasa ta zauna yanda masu d aukan hoton ke nuna mata. Lokaci guda zuciyarta na karanto mata  Komai da kike gani na faruwa akwai dalilin faruwarsu Ummulkhairi.. Ita rayuwa jarabawa ce gaba d ayanta. Allah yayi tanadi wa masu hak uri kaman yanda yayi alk awari.. Watak ila kasancewar Umma a matsayin mahaifiya a gareki shine babban k alubalenki a rayuwa.. Kiyi hak uri kiyi mata biyayya.. Har abada bazaki tab e ba. Da wann batu na zuciyarta taji k warin gwiwa na d an zuwa mata.

Umma ce mai nuna mata styles d in da zatayi har gyara mata zama take tana fad in tai murmushi kyaunta ya bayyana. Kuji fah.

Izuwa lokacin Ummul ta daina mamakin Umma sai addu a da take wa mahaifiyar nata cikin zuciyarta.

Aka d auki hotuna aka gama dikda cikin idanunta akwai alamun hawaye a duka hotunan amma kam tayi kyau TabarakAllah ma sha Allah inji Aunty Asshe. Fad i take d ansu yayi dacen mata.

Bayan Asshe da Umma sun keb e Umma tace  Toh yanzu meye abu na gaba Hajja Asshe.?

Asshe tace an tura ma mutumin da zai wanke hoto can Abuja ya kai ma  yaruwata. Yau zasuga Amaryarsu Ummulkhairy a hoto kafin su ganta a zahiri.

Umma ta lumshe idanu had ida sauk e ajiyan zuciya. Lokaci guda ta d aga hannuwa sama  Ubangiji kasa an dace.. Allah yasa Ummul d ina ta dace.. Allah na rok eka ka jefa k aunarta cikin zukatansu a kallon farko..

Asshe ta murmusa ta dafa Umma  Anma dace in sha Allahu. Kinsan dai ance wai gani ya kori ji Shiyasa za a aika masu hotunan Ummul su gani su shaida amma  Yaruwata da D anta basuda matsala. Yanzu Abu na gaba sai maganan kai lefe da saka rana.. Inaso duka ayi su a gobe ne. Amma kafin nan dole mu samu magabatan Ummul ayi magana.. Kinaga dangin mahaifinta zasu amince su bamu aurenta.?

"Umma tai shiru kaman mai nazari. Cikinta ya bada wani sauti k uuu.! Ita sai yanzu ma ta Tina da za azo wann gab ar. Ta soma  yan kame kame. Sai kuma ta nusa tace   yanuwansa basa jituwa dashi abinki da gidan da  yanubanci ya raba kai. Yaruwarsa mace ce guda d aya tak, kuma itama Sun raba gari tinda jimawa. Kuma mace ai bata bada aure. Kaf  yanubansa ne gidan Wanda ba wani ganinsa da gashin ido suke ba.. Idanun Umma suka kawo ruwa murna na Neman komawa ciki take duban Asshe  Toh.. toh.. Yanzu mai zai faru idan suka k i amincewa su bada auren Ummul..? "

Saurin katseta Asshe tai  Haba Suwaiba kin faro abu da zafinki kar ki badani mana& Keda kike da babban makami.. Bakiga yanda kika aje Kishiyarki a yanda ya Kamaceta bane..? Ai kud i Sune jigon rayuwar nan Suwaiba. Idan kud i na aiki toh na tabbata Miki zasu bada auren Ummul ba tareda wani b ata lokaci ba dan nayi imani kaf d insu fama suke da rayuwar nan ta yau..

Umma ta jinjina Kai  Kuma fah kince wani abu dan ko yau d in nan da naje nai rabon kud in ina ganin Baballe ya amshe Wanda na bawa D ansa ya soke a aljihu.. Kunya ce ta hanasu nasan suma da Sun shiga layin rabon kud in..

Asshe tace  Ah toh kin gani ko. Ke fah yanzu sai abinda kika ce a wann gidan. Ta k arada  Ita kuma Ummul zata zauna a nan a mata  yan gyare gyare na amare.. Mai gyara na musamman na d auko daga can gida Maiduguri.Kuma kinga dai yaro ne d an gayu Wanda rabin rayuwarsa turai ne Ya saba cin karo da matan turawa da wayayyun

21 / 103