AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   6 / 103

15K to 18K   out of 306.8K words

kwashe ladan. Wataran bazaki huta ba.. Jiki da jini Ummul kink i ayi maku roster da kowa tasan ranan nata aikin.

Ta murmusa  Hajja ai nafi son na tara ladan da albarkan ni kad ai ne..

Hajja Fannah ta murmusa  Ai kuwa da izinin Allah albarka na bibiye dake.. Kinci sunanki uwar alkhairi..

Murmusawa ta d anyi kad an jikinta na kuma yin sanyi da kalaman Hajja sakamakon tuno tashin hankalin da ta baro a gida. Ta mik e da sauri gudun kar Hajja ta fahimci yanayinta ta d auko tsintsiya zata soma shara Hajja da tuni ta karanci yanayinta ta dakatar da ita.

" Zo nan Ummul, zo ki zauna magana zamuyi kafin sauran d aliban su k araso. Bar sharan nan. Tai mata nuni da gefenta saman tabarma."

Jiki a sanyaye Ummulkhairi ta isa ta zauna.

"Hajja ta gyara zamanta  Fad a mun me Ya faru.? Hajja Fannah ta jefo mata tambayar dan dama tana sane da halinda Ummul d in ke ciki. Gidanta na bayan layin su Ummul layin da ke babban kwalta. Hajja Fannah tanada shagon d inki da yara maza masu d inki a shagon ta dake gaban gidan nata yayinda take koyar da  yanmata sana ar d inkin a cikin gidanta. Sunyi sabo mai tsafta da Ummul tin sanda ta soma koyon d inki wajenta. Tana bata shawarwari had ida kwantar mata da hankali hakan yasa Ummul ke samun sanyi wajenta, takan kai mata damuwarta su zauna su tattauna ta kuma bata shawarwari masu amfani a gareta had ida nitsa zuciya."

Ummul ta d an share hawayen da suka gangaro mata  Hajja wllhi na gaji.. Harga Allah na gaji.. Ita fah Umma ko wanne irin mutum so take na aura babu ruwan ta ko ina san wann mutumin ko bana so.. Ita burinta kawai nai aure da farin ciki ko babu. Ni kuma a halin yanzu wllhi batun auren nan ya fita kaina ni sana ar nan da nake nafi samun kwamciyar hankali cikinsa fiyeda komai. Shin wai ita mace ba a mata uzuri ne a rayuwar nan..? Hajja ba biye biyen maza nake ba.. Allah shine sbiadana ina k ok arin tsare mutuncina.. Sann azumin litinin da Alhamis duk basa wuceni ba wai dan na Gaza rik e kaina ba sai dan sabida nasan shi azumi garkuwa ne Hajja.. Amma ita Umma duk fah bata ganin wann. Ita kawai damuwarta mutane da abinda suke Fad i.. Shin Hajja menene laifin wacce Allah ya jarabceta da JINKIRIN aure..? Ta k arashe damuwa fal fuskarta hawaye na kuma gangaro mata.

"Girgiza kai kad an Hajja Fanna tai, cikeda tausayi. Ta kuma gyara zama tana duban Ummulkhairy  Ummul, shi fah d an Adam a koda yaushe bai rasa abin Fad i.. Sann har abada bazaka tab a Iyar masa ba.. Mutum sai Allah.. Ta kuma gyara zamanta  Wato muna cikin wani irin Al umma ne da k addararka take iya zama zunubi a gareka.. Mai nake nufi da k addararka tana zama zunubi a gareka? Macece Allah zai jarabceta da JINKIRIN aure sai kiji mutane suna cecekucen cewa ta zauna a gida tak i aure. Idan wacce take karatu ne sai kiji ance ta rungumi boko tak i aure.. Idan ma Sana a take dan ta rufa ma kanta asiri sai kiji ana cewa maza ke bata kud i ta Kama Sana a ne dan ya zame mata garkuwa kar a zargeta.. Ita dai mace wai bazata rayu ba saida tallafin namiji. Mace ce Allah zai jarabceta da mutuwar aure sai kiji ana cewa ta kashe aurenta ta dawo gida bazaki tab a Jin ance miji ya kashe mata aure ba sai k alilan a a itace dai Sarkin laifi. Kuma babban abin takaicin mutanen da tafi kusanci dasu Sune mutanen da take soma fuskantar k alubale daga wajensu. Kowa sai ya tsangwameta a cikin gidan baga iyayenta ba baga  yanuwanta ba a wasu lokutan. Kinga a nan k addararta ya zama kuskurenta. Ta d an numfasa kafin taci gaba  Ummul ba ina fad a Miki haka bane dan kiga laifin iyayenki ko wani abu mai Kama da haka. A a ko d aya, burin ko wasu iyaye shine da zaran  yarsu ta isa aure su ganta a d akin mijinta. Kuma babu iyayen da zasu so suga auren  yarsu ya Mutu. Toh amma idan jarabawan Ubangiji ya shigo ciki sai ayi hak uri a fawwala masa lamuran. Ka tsara rayuwarka yanda kake burin Ubangiji ya tafiyar maka da ita tareda fatan mafarkan ka su cika ba laifi bane hasalima Wanda baya planning rayuwarsa baisan ina ya dosa a rayuwar ba. Toh amma wasu lokutan yanda muka tsara ba haka rayuwar take zuwa mana ba. Dalili kuwa shine ba muke da hakkin tsara rayuwar ba iyakacin namu mafarkai da burika had ida fata na gari. Ubangijin duka shike tsara mana rayuwar yanda yaso. Kuma tsarinsa a koda Yaushe shine daidai. Idan ya amsa mana addu anmu ya tabbatar mana da burinmu da fatanmu sai muyi farin ciki mu kuma gode masa. Sann idan ya jarabcemu ya janye wann fata daga garemu bamu samu abinda muke mafarki da buri ba shima sai mu masa godiya sabida shi yasan abinda yasa ya hana mu kodai abin mai cutarwa ne a garemu. Ko kuma ya mana tanadin Wanda yafi wann. Ta kamo hannun Ummulkhairy cikin nata  In every delay, I believe there s khayr.. Just like your name Uwar alkhairi. In sha Allahu JINKIRINki zai zamto cikeda d imbin alkhairi.. Babban abinda zan Miki wasiya dashi shine biyayya ma iyaye. Kar ki kuskura koda wasa ki fasa musu biyayya matuk a bazasu ce ki sab i mahaliccinki ba.. Idan kika rik e biyayyan iyaye alkawarin Allah ne rayuwarki zai cika da d imbin alkhairi kinji ko.. "

Ummulkhairy ta jinjina mata Kai a hankali kyakkyawan murmushi saman kyakkyawan fuskarta. Hak ik a tana samun relief da kalaman Hajja Fannah. Inama Ummanta zata kasance mai fahimta kamar haka. Sallaman wasu daga cikin d aliban yasata k ok arin saita kanta Hajjah Fannah na fad in ta kwantar da hankalinta komai zai shige ya zama

tarihi da izinin Allah. Ta mik e tana amsa gaisuwan  Yanmatan da suka shigo tana fad in yau dai Ummul d inta zata huta Sune zasuyi shara su gyara waje.

Daga can bakin Layi Alhaji Kamilu Ya aje motarsa Mama na biye dashi tana fad in  Kai dai muje ka bama idonka abinci Alhaji.

SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!*

*06*

*©þSameena Aleeyou& *

K ofan gidan Hajja Fannah Mama ke nuna masa  Yauwa Alhaji. Nasan Kai mutumin kirki ne. Ance matanka ma ko fita unguwa basayi tsaban yanda kake kaffa kaffa da iyalanka. Toh kaga can yanda kaga mata da maza suna safa da marwa.

Alhaji Kamilu ya kuma duba k ofan gidan wanda shaguna suka saka a tsakiya ga samari sai kai komo suke tsakanin shagunan can gefe harda shagon aski ga  yanmata masu sana an koyon d inki suna Kutsawa suna shiga gidan Hajja Fannah.

Mama taci gaba  Toh wann gida dai dake gani Ummul tana ciki da ita ake wann kai komo tsakanin wad ancan samari marassa tarbiya masu aski irin na shed an. Idanun Alhaji Kamilu ya sauk a samarin da Mama Ke nuni dasu wanda suka fito shagon Aski gana ganinsu kaga samari marassa tarbiya ga wani aski da aka musu an kwashe gefe d aya an bar d aya. D aya saurayin ma harda sark a a wuyansa.

Alhaji Kamilu yai Shiru kaman mai nazari. Sai kuma yace  Da zaran na aureta ta dena fita ko k ofa dan mata na ko taron biki da suna basa zuwa babu yanda suke zuwa sai asibiti da ya zama dole.

"Mama tai  yar bazaurar murmushi  Toh ai Alhaji ba a nan gizo Ke sak an ba. Ta kuma gyara tsayuwarta  Kaga wann gida da Ummul Ke zuwa da sunan koyon Sana a. Matar gidan ba kowa bace face gasunk umar kawaliya. Wllhi nake fad a maka Alhaji ta addabi kowa ta fitini kowa a unguwar nan. Mata take tarawa cikin gidanta maza kuma suna daga waje a shago. Maza take had awa waje mata kuma cikin gidan ayita aikata masha a ana aikata alfasha. Kuma ba zallan  yanmata harda matan aure a wann bad ala da take had awa. Na tabbata bazaka so ka auri yarinyar da ta gama watsewa wajen wann hatsabibiyar Matar wacce ko aure bata dashi zaman kanta take zaman daduro.. Wann shago da koyar da sana a da take cikin gidanta ba komai bane face rufa rufa gudun idon mutane. Amma mu da mukaga jiya mukaga yau a unguwar kowa ya kwana da sanin Kawaliya ce. Amma idan baka aminta da abinda nake fad a maka ba zaka iya tare mutanen unguwar nan ka tambaya Kaji idan ba zaman kanta take ba. Ko aure bata dashi babbar Magajiyar karuwaice. Kaf  yanmata da matan aure dake zuwa wajenta da sunan koyon sana a, karuwanci suke fitowa su fake da san a. Meyasa Ummul tak i aure..? Kai bakai ma kanka wann tambayar ba. Mace har mace kyakkyawa irin Ummulkhairy ta gaza samun mijin da zai aureta.. Ai kaima kasan da walakin wai goro a miya. "

Ganin Alhaji Kamilu ya kifa kansa had ida maida hannayensa baya irin yanda manya suke idan suna tunani yasa Mama ci gaba  Ni wllhi ganin mutuncinka ne kuma ganin Malam zai yaudareka ya lik a maka  yarsa da ta gama yawon ta zubar a kororo yasa nai wann shahadar nace bari dai na sanar dakai gaskiya ka gane dalilin da Ke sa ko wani namiji mai kamala da mutunci Ke guje ma aurenta. Malam bai dubi amanar dake tsakaninku ba. Ba kalan suturan da baka masa ba amma ya zab i ya maka lumbu lumbu dan dai kawai shima ya rabu da alk ak ai.. Yo shima ya gaji da ita.

Birki tai da kalamanta ganin Hajja Fannah ta fito biyeda ita Ummulkhairi ce rik e da kayan d inki suka shige shagon d inki ga wani matashi ya fito daga cikin shagon ya gifta ta gefen Ummulkhairi.

"Mama tai kabbara tana hamdala  Ka gani ko.. Ka tabbata ba sharri nake ba. Wai ance gani ya kori ji.. Kana nan kanata rawar k afa zaka angwance toh aikin banza kake wai rufin d aki da b arawo dan k artai bila adadi sun rigaka.. Ta numfasa had ida gyaran murya  Toh Alhaji ni na gama nawa, Allah ya gani na fita na sanar dakai. Kuma ka gani ma idanunka. Ya rage maka ka amince ka sai ma kanka da iyalanka tikitin mutuwa dan k anjamau ne zai maku sallama. Ka taimaki kanka kaman yanda saura suka taimaki kawunansu. Ni na Barka lafiya Alhaji.. "

Tana ida fad in haka tasa kai ta shige zuciyarta fari tas.

Alhaji Kamilu kuwa sai kallon k ofan shagon yake yana jira yaga ko Ummulkhairi zata fito amma shiru. Zuciyarsa sai tafarfasa take haka yaja k afafunsa yana sab a babbar rigarsa da take  yar duk unaso ya nufi motarsa.

**

Mama tana shigowa gidan ta cire mayafi ta soma zuba ruwan bala i

 Iyi.. Kan wani dalili za a tare ni a hanya ana mun cin mutunci kan laifin da banji ba ban gani ba.. Babu wanda ya huta a gidan nan duk akan rai guda.. Baga yarana dake gidan mazajensu ba yanzu abun har ya tsallako kaina& Toh wllhi bazan d auki cin mutunci daga kowa ba kan  yar da ban haifa ba..!

Umma ta fito daga kitchen afujajan tana goge idanunta da hayak i ya sanya mata su hawaye  Yaya lafiya.. Meke faruwa..? Wani abu ne aka miki..?

Mama taci gaba da tururi  Yo uban meye ma ba a mun ba.. Gashi can Alhaji Kamilu yake ko ya tareni a hanya ta yanda yake shiga ba ta nan yake fita ba saikace alhakin tarbiyan Ummul a hannuna yake.!

Cikin Umma ya bada wani irin sauti k uuuu  Wani abu ne Ummul d in tayi Yaya.?

 Meye kuwa batayi ba bayan ganinta a gidan Matar nan da yayi wacce kowa ya kwana da sanin Gasunk umar magajiyar karuwai ce.. Ai bansan shashashancinki ya kai har haka ba Suwaiba.. Ni na zata da kika samu wanda zai rufa ma Ummul asiri ya aureta kinyi mata iyaka da gidan wann Kawaliyar mai zaman kanta ashe saketa kikai kamar tinkiya tana ci gaba da zuwa.. Yo a haka ne kike buri da fata ta samu mijin aure bayan kowa ya kwana da sanin ga hark ar da Matar take d aura  yanmata. Ai gashi can Alhaji Kamilu dik yanda akai yaji daga bakin mutane. ya tareni yana sanar dani dama munsan  yar mu yawon ta zubar take waye ya mutu waye tashi.. Ta kafe Umma da tuni duniya ya shiga juya mata kafin taci gaba  Bari kiji Suwaiba nidai ban haifi Karuwa ba Allah ya gani ehe..! Ta k arashe tana mai shigewa fuuu.

Umma ta soma girgiza kai tana dafe kai ta shiga bin bayan mama tana  Na shiga uku ni Suwaiba..! Yaya kar kiga laifina.. Wllhi laifin Malam ne na mata iyaka da wann koyon san a amma shi ya k yaleta yace dole ya koyi san a tinda ba karatun take ba.. Amma anyi na farko anyi na k arshe bazan bari Ummul ta kuma jaza mun ba..! Ta k arashe tana zaran mayafinta. Ta nufi waje a fujajan.

Mama ta bud e murya tana fad in  Miyar tuwonki fah.. zai k one..

 Yaya ki rik e min ni nayi nan..! Ta fad i takalma a hannu ta nufi waje kaman zata tashi sama.

Tana ficewa Mama ta kece da wata irin muguwar dariya. Har ga Allah shashancin Suwaiba na saka ta nishad i. Wai Malam ya rasa da wa zai had ata su goga a kishi saida wann shashasha ballagaza lamba d aya wacce sam wayau da hankali basu isheta ba. Indai kishiya irin Suwaiba ne a kawo mata gomansu ma. Ta kuma kecewa da dariya tana

kwaikwayon gudun Umma takalma a hannu. Ta bud e murya tana fad in  Kiyi a hankali dai kar ki fad i ayi haihuwar guzuma uwa kwance  ya kwance.

**

Abuja.

Hisham ya kuma girgiza kansa a karo na biyu yana duban Haidar dake zaune calmly kaman babu abinda Ke faruwa saima d an tapping table din dake gaba garesu da yake da yatsarsa guda fuskarsa na duban wani b angaren.

 Haidar kamata yai muyi suing news outlet da sukai publishing labarin nan for defamation of name..

"Kaikaitowa yai yana duban Hisham, ya d anyi still kafin ya girgiza kai  Seriously Hisham..Are we going to waste our time going against the media..? Ya d an girgiza kai  Don t you think we should focus on finding the traitor that leaked the video..? "

Hisham ya d anyi Shiru kaman mai nazari. Sai kuma ya jinina kai  Yeah you are right.. Gaskiyanka ne fad a da media ba riba.. Wann b eran na cikin company zamu kama sai ya sanar damu wanene uban gidansa. And I m pretty sure shine wanda ya fitar mana da bayanan sirri na company. Rufe bakin Hisham keda wuya wayarsa ta soma ruri. Daga Company ake kiransa.

Hisham ya d aga suna gaisa nan ya fahimci aminin mahaifin Haidar ne Alhaji Gimba mai kiran. Bayan sun gaisa ya tambayesa ko suna tareda Haidar.

Saida ya dubi Haidar d in wanda hankalinsa ya koma kan wayar salular salulansa kafin ya d an matsa gefe ya sanar dashi eh suna tare. Magana suka d anyi na lokaci kafin daga bisani sukai sallama.

Hisham ya dawo wajen zamansa ya zauna yana tunanin ta yanda zai soma sanar da Haidar abinda Alhaji Gimba ya sanar dashi.

 That was Alhaji Gimba. One of the board of directors.. Aminin Dad..

Haidar ya murmusa da gefen bakinsa kad an jin yanda Hisham Ke masa bayanin mutumin da ya masa farin sani

 What s with the introduction..? Yai maganar yana tsare Hisham da idanu.

Hisham ya gyara zamansa cikin kujeran  He called to say ya shirya maka interview with the media tomorrow by 10am at the company.

Haidar ya kuma

6 / 103