AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   47 / 103

138K to 141K   out of 306.8K words

she realises that I m no longer useful to her. That I stoped being her weapon. She couldn t use me to get what she wants. So she decided to get rid of me&  Yaci gaba da jinina kai  When I was a child she used to call me& A useless child. Yes useless.! D ah maras amfani. Haka kike kirana Mommy& Banida amfani cikin rayuwarki.. Yanzu da kika tabbata banida wani amfanin da zan miki.. I couldn t be what you wanted me to be.. I couldn t make you proud.! I couldn t be just like him. Haka ne.?! Ya k arashe yana nuni da Daddy hannunsa har rawa yake jijiyoyin jikinsa na kuma mik ewa.

Daddy ya katsesa  Enough.! I ve had enough of you and your Son Kwaise. I won t allow your problems to affect my business in any way.!

Haidar na huci yake dubansa  Is this about your business again Daddy..? Yaci gaba da huci yana duban mahaifin nasa  This is about me and my life Dad..!

 Of course I do not give a damn about you and your chaotic life.! Daddy ya katsesa da fad in haka cikin tsananin huci.

"Haidar na girgiza Kai cikin rashin yarda yake duban mahaifin nasa. Ya saki murmushi mai ciwo  Those words ain t new to my ears. But I want you to keep this in mind. You can use all the power and influence you have. Amma ina mai tabbatar maka, your wife won t get acquitted until she answers all my questions.! Until she pays for all the crimes she s committed.! "

Bai Kai aya ba Daddy ya daura masa Mari maiji da lafiya su duka suna huci yayinda Mommy tai saurin mik ewa ta shige tsakaninsu tana kuka sosai.

Haidar na jinjina Kai yake duban iyayen nasa  All I ever wanted is a quite and happy life. Away from all this chaos. Yana maganar Mommy tana dubansa hawaye na gangaro mata. Ta rasa tausayin waye take ji cikinsu gaba daya.

Haidar yaci gaba  Amma Idan wann shine Abu na k arshe da zanyi a rayuwata zanyi. Na ranste sai na isa k arshen komai. Mark my words.! Yana ida fad in haka yasa kai ya fice daga room d in.

Mommy ta dubi Daddy  Engr we need to stop him. Da gaske yaron nan ba cikin hayyacinsa yake ba.

 Ki min shiru Kwaise. This is all your fault you know. I ve warned you.. Na Miki gargadi amma bakiji ba. I knew nothing good would come out of this marriage da kika dage sai kinyi ma d anki. Ga abinda nake Miki gargadi akai amma bakiji ba.

Mommy ta girgiza Kai  Ka yarda dani Engr wllhi ban saka guba ma yarinyar ba.

 Just shut up Kwaise.! Meke tsakaninki da wann yarinyar is absolutely none of my business.. Ya kuma matsowa yana nunata da yatsa yana sakin huci  Na gargadeki cewa idan har wann watsattsen auren da kikai ma wann D an naki ya shafi Kasuwanci na ki kuka da naki auren.!

 Har yanzu barazana kake mun da Aurena. Mommy ta katsesa. Taci gaba da jinjina Kai tana hawaye  Shin meye matsalar.? Auren da nai ma Haidar ne matsalar kokuwa dai har yanzu akan Fannah ne da abinda ke cikinta.!

Cak Daddy ya tsaya ya dago yana dubanta yana jinina kai  You are right Kwaise. You are absolutely right. You should be grateful ban miki korar kare ba bayan abinda kika mun.!

Mommy taci gaba da hawaye tana duban mijinta nata yanda yaci gaba  Bayan abinda kika min nayi hakuri na zauna dake da abinda kika haifa tsawon shekarun nan.!

 Nasan albarkacin Haidar naci kake zaune Dani kawo wann lokacin.!

 Will stop with your guilt tripping Kwaise.! Idan kinsan da haka kar ki bari na tuna Miki abinda kika aikata mun a baya.!

Mommy na hawaye taci gaba  Meyasa baka barmu munyi tafiyarmu ba nida Haidar idan har zaka rik esa ka kasa accepting dinsa tsawon shekarun nan.?! Taci gaba da hawaye  Na sani nayi kurakurai da dama a baya. Kuma babban kuskuren da na kasa yafe ma kaina shine k iyayyar da na nuna ma Haidar a lokacin da na haifosa ka k i accepting dinsa.

Daddy Yaci gaba da jinina kai yana huci yayinda Mommy taci gaba da hawaye.

 How do you expect me to accept your child bayan kinsa na sheganta D an wata.? Ta ya kike zaton zan rayu da naki D an na bude ido na ganshi yana girma bayan akwai wani D an nawa can Wanda na sheganta sa da bakina. A kullum na bude ido naga D anki Kwaise ba komai yake tuna mun ba face mummunan kuskuren da na tapka. Kuskuren da na zartar da hukunci akansa ba tareda bincike ba.! Ya jinjina kai kafin yaci gaba  Dik randa naga Haidar sai na tuna akwai D anuwansa can wanda naki accepting d inshi tun yana ciki. Ta ya kike zaton naki D an zai girma da soyayya na.? Ki gode ma Allah da na bama D anki sunana.

Cikin kuka Mommy tace  Haidar D anka ne dole ya amsa sunan ka.

 Amma kin haramta ma wani D an nawa Ya amsa sunana Kwaise.! Ya katseta da fad in haka jikinsa Har rawa yake.

Hawaye yaci gaba da gangaro ma Daddy  Na tuna miki zaluncin da kika mun ne.?! Kwaise kin kawo wani k ato yayi fyade wa Matana a cikin gidana.. Da aurena akanta da cikina a jikinta Wanda kika sa na Sheganta shi tin yana ciki baizo duniya ba. Kinsa na rabu da matata a WATA UKU na farkon aurenmu. Kinsa na tura Fannah gidan Yari ta raini cikinta a can ta kuma haifesa a can. A gidan Yari ta haifi D ah na da na sheganta sabida son zuciya irin naki Kwaise.!

Mommy tai bursting cikin kuka tana girgiza kai take fad in  Wllhi Allah shine shaida na ban basa umarnin ya aikata ma Fannah wani abu ba. Sharri kawai nace Ya mata. Allah shine shaida na babu fyad e a plan d in.

 Just shut up already.! Kar ki sake ambatan sunan Fannah da wann bakin naki.! Daddy ya katseta.

Haidar Ya banko k ofar Ya shigo cikin wane irin yanayi yake duban iyayen nasa  Wacece Fannah..?!

SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!*

*34*

*©þSameena Aleeyou& *

"Kallo daya Daddy yaima Haidar ya watsar. Kaman dai baiji tambayan da yai ba. sai kuma ya kalli Mommy  Kina iya sanar da D anki zunubanki idan kinso. I ll send our lawyer to handle your case. As you know, I have a reputation to protect bazan bari ke ko D anki ku min sanadi ba . Yana ida fad in haka yasa kai ya fice."

Haidar yabi bayan mahaifinsa da kallo kafin ya maidoda dubansa ga mahaifiyarsa. Ya dauki lokaci kadan yana tsaye wajen yana dubanta kafin daga bisani ya soma janyo k afafunsa ya zauna saman kujera mai fuskantar nata  Tell me Mommy. Wacece Fannah.?

Mommy ta dago idonta masu zuban ruwa tana duban D an nata kafin ta jinina Kai  She& She was your Dad s wife.. Matar mahaifinka ce kafin su rabu.

Haidar ya jinina Kai a hankali  So Daddy yanada wata matar a baya.?

Mommy ta jinina Kai a hankali.

" What happened then, mai ya faru da ita..? Ina take yanzu.? "

Mommy ta girgiza Kai a hankali  I have no idea Son. Bansan yanda take ba a halin yanzu.. Kuma na nemeta shekara da shekaru ban sameta ba.

 Meyasa kika nemeta.? Ya kuma jefo ma Mommy tambaya.

Ta d ago tana dubansa  Dan na nemi yafiyarta.

Ya kuma jinjina Kai  So tell me Mommy. Mai kika aikata mata.?

Mommy tasa hannayenta biyu ta share hawayen da suka zubo mata. A hankali take jinina Kai  Zan sanar dakai komai Haidar. Abinda ya faru a wancan lokacin& Watak ila ka samu gurbi cikin zuciyarka ka yafe min D ah na. Ta k arashe cikin tsananin rawar murya yayinda Haidar ya zuba mata ido.

Waiwaye&

Years back..!

"Borno State, Maiduguri."

Hajiya Kwaise zaune saman kujera a madaidaicin parlorn ta Wanda ya tsaru iyaka tsaruwa a wancan lokacin. Kuka take sharshar da hawaye a lokacin da taji sautin wayar landline na gidan na kururuwa. Ta mik e da kyar ta isa ta daga wayar. Daga d aya b angaren muryar Aliyu Maitama ta sinkayo  Kwaise an d aura auren.. An daura auren.. An daura aurena da Fannah.. Yanda yake maganar zaka fahimci kaman Wanda aka saka shi dole haka yake maganar. Bata k arasa sauraro ba ta saki wayar ya fad i kasa tana mai kuma rushewa da kuka. A haka Asshe ta k araso ta sameta. Asshe k anwarta da tin bayan da Kwaise tai aure rik on Asshe ta dawo hannunta dama ba wani girme mata sosai tai ba kuma su biyu iyayensu suka Haifa.

Mommy ta dago tana duban Asshe cikin rawar murya  Asshe Aliyu yayi aure.. Aliyu ya auri d iyar leburan dake aiki k arkashinsa Wanda block na gini ya fado ya fasa masa Kai ya rasa ransa dalilin haka. Asshe Aliyu na ya aure  yar wann mutumin..! Ta kuma rushewa da kuka.

Asshe ta dubeta cikeda tausayawa  Aunty Kwaise mijinki loves you. Wllhi koda ace yayi aure bazai daina sonki ba. Ni fah ban taba ganin wacce mijinta ke mata irin Son da Uncle Engr ke Miki ba. He loves you dearly. Zai komai dan farin cikin ki Aunty Kwaise. Keda kanki kin fada Aurensa da wann yarinyar Fannah k addara ce kawai batada kowa bayan mahaifinta da ya Mutu ta dalilin aiki k ark ashin ma aikatan mijinki da yake. Wllhi na tabbata dan ya taimaketa ya aureta. Ba wai dan yana So ba ko dan ya daina sonki. Idan ba so da mijinki ke Miki ba. Mutum kaman Engr Aliyu matashi mai tashen kud i ga k uruciya ga dama na rayuwa da ya samu ai da tuni ya cika gidan nan da mata sai yanzu da k addarar hakan tazo. Dan Allah kar ki saka wani Abu a ranki.

Mommy ta dago tana share hawaye  Asshe bazaki taba ganewa ba. Namiji Akan mace sunansa namiji bazakiyi shaidarsa ba. Nidai bazan iya sharing Mijina da wata ba balle wann bagidajiyar  yar lebura.

Asshe ta furzar da huci  Toh ya kike so ai yanzu.?

Mommy bata iya bata amsa ba sai mik ewa da tai ta shige k uryar daki wani sabon kuka na taso mata.

Haka ta yini a daki bata aikin komai sai kuka. Asshe ke Lek ata lokaci zuwa lokaci. Ko abinci Mommy ta kasa ci ranan.

Can dare taji shigowar motar mijinta. Nan ta Mike da sauri tana lek en window. Hangosa tai tareda Amaryar sa tana biye dashi kanta a k asa. A haka suka shigo har parlorn gidan.

Koda Daddy ya shigo ya tadda Mommy juya masa baya tai. Ya k araso jikinsa duk a mace  Kwaise. My love.. Sai ya kasa ci gaba da magana yayinda kukan Mommy ya karu.

A hankali ya isa ya rungumeta ta baya. Su duka biyun hawaye na gangaro masu. Cikin kwantar da hankali yake furta  Wann shine k addarar mu Kwaise. Allah ya k addari Fannah zata shigo cikin rayuwarmu. Yarinyar abun tausayi ce bata da kowa sai mahaifinta da ya rasu sakamakon aikin da yake k ark ashina.

Mommy na hawaye take girgiza Kai  Ba hurumi na bane na tuhumeka dan ka k ara aure Aliyu. Addini ya halatta maka auren mata d ai d ai har hudu idan kanada hali. Kawai alfarmar da zan rok a daga gareka shine Kai Adalci tsakaninmu.

Ya murmusa yana dubanta. Ya saka hannunsa ya share hawayen da suka gangaro mata  I love you Kwaise.. So much..! Ban tab a son wata mace sama dake a rayuwata ba. Ki tayani addu a Allah ya bani ikon yin Adalci tsakaninku because.. I m not sure idan son da nake Miki zai barni na kamanta adalci.. Kwaise ba kece cikin tashin hankali ba. Ni ne cikin tashin hankali.. Because son da nake miki baida match da ko wace mace. When it comes to you wayona baida yawa Kwaise.

Mommy ta tsaresa da ido kafin ta k ak aro murmushi ta riko hannayensa  You can do this in sha Allah mijina. I m here for you.. Tashi na shiryaka amarya tana jira.

Kaman rak umi da akala haka Daddy ya Mike Mommy ta shiryawa tsaf harda su fesa turare kaman ba ita ce ta yini kuka a daki ba.

Koda suka fito suka tadda amarya ma Mommy bata nuna komai ba. Asshe taita mamakin canzawan  Yaruwar tata. A haka rayuwa ke tafiya masu Mommy bata nuna komai ga Daddy ya saki jiki ganin hankalin Kwaise ya kwanta. Ya maida hankali kan bunk asa k aramin kampaninsa a nan birnin Maiduguri da Kewaye.

Watan Fannah biyu a gidan ta fara nuna alamun masu juna biyu. Kwaise da kanta ta dauketa ta kaita asibiti akai mata gwaji aka tabbata tana d aukeda karamin ciki na tsawon watanni biyu. Sosai Mommy ta nuna marnanta har kaman tafi Fannah murna. Lokacin Daddy na cuku cukun Kai Kasuwancinsa tsakanin Abuja da wasu jihohi Mommy da kanta tai masa Albishir na cikin da amaryarsa ke dashi sanda sukai waya tinda shi a wann lokacin ya rage zaman Maiduguri. Farin ciki wajen Aliyu Maitama baya misaltuwa. A wann lokacin yai ma matan nasa kyauta ta sabuwar mota dal  yar yayi a wancan lokacin. Ya kuma d ebesu gaba daya suka tafi Umra suka gode ma Allah da kyautar da yai masu dan a lokacin aurensa da Kwaise kusan shekaru biyar kenan babu rabo saida Fannah ta shigo sai gashi ta samu daga shigowarta.

Bayan dawowar su daga Umra Daddy ya tafiya ta kasuwanci da zai d aukesa kusan wata guda.

Asshe ta dubi Mommy wacce keta faman sakin murmushi tana gustiran Apple. Ta d an girgiza Kai tace  Kenan kin yarda ta rigaki Haifa masa Magaji Aunty Kwaise.? Ni fah kirkikin da kike ma matar nan tai yawa. Ke kaman bakijin kishi irin na mata da ake fad a.

Murmusawa Mommy tai  Asshe kenan. Sarai nasan abinda nake kuma lokaci yayi da zan executing plan dina. Trust me.

Asshe ta girgiza Kai  Toh amma Aunty Kwaise mai zakiyi yanzu.?

 Wann cikin da Aliyu Maitama ke rawar k afa akansa da Kansa zai sheganta sa tin a ciki kafin a haifosa. Zai ma Fannah korar wulak anci. Wann cikin kuma Engr Aliyu Maitama bazai taba accepting dinsa ba.

Asshe ta girgiza Kai  Amma ta ya zakiyi hakan.?

Mommy ta kuma gyara zama  Uban Fannah labourer ne a kampanin Maitama. Bincikena ya tabbatar min akwai wani lebura matashi kuma abokin aikin mahaifinta dake mutuwan sonta. Hasalima saurayinta ne kafin iftila ain da ya samu mahaifinta ya samesa. Zuwa Kai ma mahaifinta abinci da take site a can Saurayin nata ya ganta ya fara sonta. Da uban ya Mutu mijina bai san da labarin tanada wani saurayi da suke soyayya ba Wanda shima yake aiki k ark ashin sa. danginta sukai wuf suka nuna masa batada kowa saidai ya aureta sabida tinanin zasu sami kudi. Ance sadaki suka yanka masa kaman dai mai biyan diya. Saida masa ita sukai. Fannah batada say ga danginta Wanda bayan rasa mahaifinta da tai ba rike ta zasuyi ba dole suka tilasta mata auren mijina dukda tanada Wanda take so. Dashi zanyi amfani na fitar da Fannah daga gidana dan ance har gobe yana mutuwan sonta.

Asshe ta sauk e ajiyan zuciya  Toh ya abin zai kasance.?

Mommy ta kuma murmusawa  Abin shine kece zaki taimaka min har komai ya kankama K anwata.

Asshe ta girgiza Kai cikin rashin fahimta  Kaman ya kenan Anty Kwaise.? Ki sanar Dani wane irin taimako zanyi dan nafi kowa burin matar nan ta fice daga gidan nan.

Mommy ta jinjina Kai suka tsara yanda zasu aiwatar da komai cewa Asshe ta tafi ta samu wann Saurayin suyi ciniki dashi da Mommy yazo gidan a ranan da Engr Aliyu Maitama zai dawo gari ya kamasa a d akin matarsa zai hau kan dik abinda ya gani ya zauna tinda su biyun tsaffin masoya ne. Ta k arashe tana sakin murmushi.

Da taimakon Asshe Mommy ta tsara komai har shigowa gidan da Auwalu tsohon Saurayin

47 / 103