AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   18 / 103

51K to 54K   out of 306.8K words

bai damu yaji waye zasu aura masa ba. Dan yayi imani da zaran an basa jagorancin wann project d in sun aura ma banza ne da wofi dan ko kamanninsa bazai tab a bari matar ta sani ba."

" Fine Mommy.. Na amince,na amince da AUREN WATA UKU kaman yanda kikace.! "

Mommy jin abun tai a bazata. Wai Ya amince zaiyi wann Auren Wanda bata sanar dashi k udirinta da mak asudin Auren ba. Ta tabbata a nasa tunanin ta zab i yayi wann Auren ne sabida project d in da yake matuk ar so ya jagoranta. Ta tabbata kafin ya saki Matar tama riga ta jima da rabuwa dashi idan har aikin Malaminta ya cika. Zuwa wann lokacin kuma asirin ya karye hankulan ahalinta zai dawo jikkunansu. Daga nan sai su bud e sabon babin rayuwa mai dad i ita da ahalinta.

Ta k araso ta rungume Haidar tana hawaye tsananin farin ciki da Ya lullub eta.

"Anisa dai sai lek ensu take, tana mamakin yau Mommy ce harda rungumar Haidar haka. Lallai something s going on.. She needs to find out. Saurin sauk owa tai sanda Mommy da Haidar suka kuma shigewa sashen Daddy."

"Mommy bakinta har kunne take duban mijinta  Engr, Haidar Ya amince.. Ya amince da sharad inmu. Ya amince da batun Auren. "

Zuciyar Anisa dake daf k ofan katafaren parlorn yai wani irin tsinkewa. A fili ta furta  Aure.? Aure kuma..?

Daddy ya d ago yana duban Haidar Wanda ke tsaye gaba gareshi cikin parlorn Ya nad e hannayensa kansa a karkace. Shid in ma mahaifinsa yake duba. Irin duban nan na your days are numbered.

"Cikin zuciyarsa yake furta  This is the beginning of an end for you Daddy.. K arshenka and your so called company.. Komai zaizo k arshe a tsakanin wata uku. This project will turn out to be a great disaster for you and your company. On the day of launching the project, a wann ranan zan gayyato maka manyan bak i Daddy.. I ll make sure to invite EFCC for you.. All your assets will be seized. Ba a nan zai tsaya ba. You will fall in front of everyone.. I ll make sure they sue you and your company for poor Workmanship.. Zan tabbata they impose sanctions for your company ta yanda zai zama ba kai ba shigo da wasu manyan kayan gine gine na zamani cikin k asar nan. After all this Daddy. Ni, Aliyu Aliyu Maitama, your never wanted son will personally charge you for a series of discriminations while working under your company. Duk wasu cin mutuncin da ka mun a wann Kampanin naka sai nasa ka cinyesu gaba d aya. I ll make you lose everything. Alk awari ne.! "

Muryar mahaifiyarsa Ya sinkayo tana fad in irin farin cikin da take ciki burinta yana gab da cika. Sai kuma ya hango Daddy wanda tuni ya nufi study d insa. Cikin sauri yabi bayan mahaifin nasa.

Daddy ya d ago yana dubansa. Haidar ya shigo cikin study d in sosai. Su duka biyun suna duban juna. Daddy yace

 What now.? Mai kuma kake nema.?

"Zama Haidar yai saman kujeran dake gaban table d in Daddy. Ya d auki pen ya zara plane sheet mai d aukeda alama, adireshi had ida sunan company dake bisa table d in. Ya mik a ma Daddy. Lokaci guda yake furta  You and I are both businessmen Daddy. And we know how things work a duniyar kasuwanci. Since everything here is about business Daddy. Zamuyi shi a rubuce, sann mu saka hannu to avoid business pitfalls.. "

Daddy ya tsaresa da idanu yayinda Haidar yaci gaba  We will both sign this agreement tabbacin babu janye yarjejeniya daga baya.

"Daddy ya amsa takardan kafin ya ketata gida biyu  Na riga na gama yarjejeniya da mahaifiyarka. Bana magana biyu. If things go wrong, believe me your Mom will face the consequences. Yana ida fad in haka Ya nuna masa k ofa."

Haidar yai Shiru yana mai jinjina kansa. Har cikin ransa yake jin babu abinda zaisa Ya janye duk wasu k udirinsa gameda wann wofin ahalin.

**

A b angaren Mommy kuwa ta kira Asshe ta sanar da ita yanda sukai da Daddy harma da Haidar.

Asshe tai Shiru kaman mai nazari  Amma Aunty Kwaise na fara tsoro da lamarin nan. Ta ya zaki saka aurenki on the line..?

 Ta ya bazan saka nawa auren at risk ba Asshe.? Har yaushe zan jira na gyara ahalin bayan ga dama ya sameni. Asshe na shirya sadaukar da komai domin ceto ahalina.

Asshe ta furzar da huci  Aunty Kwaise I find it strange wai Haidar Ya amince tashi guda. Shin har haka yake son wann project d in.. Anya son da yake ma aikin yakai yai making huge decision irin wann..? Kuma shi Engr yasan Auren wata kika shirya yi ma d ansa.?

Ta girgiza kai kaman Asshe tana dubanta  Ta Ya zai sani Asshe..? Haidar ma na fad a masa zai iya rabuwa da matar a wata uku ne dan na samu amincewarsa a sauk ak e. Amma kinsan su duka biyun Babu Wanda yasan mak asudin auren. Dukkansu kafin su ankare aikin gama ya gama.

Asshe ta kuma jinjina kai  Ciniki ta fad a kenan. Yanzu zamu iya zuwa asibiti mu biya kud in jinyar mahaifinta..

Mommy ta kuma jinjina kai  K warai.. Bana so a d auki lokaci Asshe. Kawu Bana da mutanensa zasu zo su sameki ku tsara komai. Su karb i auren a nad o makarin asirin a kawota. Kud i ba matsala bane Asshe. Zan kashe ko nawa ne domin wann buri nawa Ya cika.

"Asshe ta kuma jinjina kai  Shikenan Aunty Kwaise. Bakida matsala, zan tsaya ra ayin daka Har Allah ya shige mana gaba. "

Mommy suna ida wayan ta fito parlor yanda ta tadda Anisa ta kifa kanta sai kuka take.

Mommy ta k araso a birkice tana tambayarta meke faruwa.

Anisa ta d ago tana dubanta dan tinda taga Haidar yazo gidan gashi taji ana batun Aure. Bugu da k ari akan idonta Mommy ta shige d aki tana magana da Amminta a waya Wanda ta tabbata bazai shige zancen auren suke ba. Shin iyayenta basu fahimci irin son da take ma Haidar bane. Idan har ba auren Haidar zatayi ba toh ma zaman me take a gidan. Take ta mik e tana kuma fashewa da kuka ba tareda tace da Mommy komai ba.

Mommy tabi bayanta da kallo kafin ta tab e baki tace  Sangarcin sun motsa kenan. Bata kuma bi takan Anisa ba taci gaba da sabgoginta dan yau Ji take tamkar kaf damuwarta na gidan duniya Ya yaye.

**

"Asshe ta dubi Umma wacce ta cakare cikin tsadaddan leshi d anubansu, Tai far da idanu  Wow Umman Ummul kinga kuwa yanda kika fito kikai kyau.. Kyaunki na asalin k abilar Fulbe Ya kuma bayyana.. Gaskiya kud i zasu amshe ki.. Kin ganki kuwa wa zaice kin haifi Ummul.. "

Umma ta ci gaba da wahse baki tana juyi gaban madubi tana duban kanta  Allah ko Hajja Asshe.. Toh ai gwara kar na Saba tinda ba samun irin wann tufafi zanyi kullum ba.

Asshe ta kuma murmusawa  Inji waye.. Ai saidai ki dinga kyautan su ma. Ke ai yanzu kin girmi irin wad nn ma saidai na order daga k asar waje.. Kekam fah yanzu kin zarce sa anninki  Yarki taci sunanta Uwar alkhairi ta bud e Miki k ofofin alkhairi.. Ke fa yanzu da matan gwamnoni zaki dinga jerawa..

 Na shige tsaran Yaya.. Umma tace tana kuma washe baki.

Asshe tace  Waye kuma Yaya..?

 Tani kishiyata.. Umma ta bata amsa.

Gajeren tsaki Asshe tai tace  Saidai ta soma kiranki da Yaya daga yanzu dan kin Riga kin amshe girman. Ummul d inki ta k wace Miki girman.. Ta aje mata hanshak in handbag shak e da kud i  yan dubu dubu ciki tace  Wann naki ne ki razani Tani dasu. Dan tinda Asshe ta gane Suwaiba ba kwad ayayya bace burinta kawai shine ta burge kishiyarta harma da sauran jama an dake tsangwamar  yarta su shiga taitaynsu sann Ummul d inta Tai irin auren da yaran Tani basuyi ba ta k udiri niyyan cika ma Umma wann buri nata. Dan sosai matar ke sakata nishad i.

Asshe ta fice tana fad in bara ta duba Hilala ko ya shirya dan shine zai kaisu.

Umma ta jinjina Kai tana kuma murmusawa. A fili take furtawa bayan Asshe ta fice  Tani kenan.. Dake da  ya yanki Kun gama mana wulak anci.. Yau idanunki zasu gane Miki abin mamaki.. Yau zakiyi nadaman duk wasu abubuwan da kika jima kina min cikin gidan nan.. Ummulkhairy da kike aibatawa Har kina ambatonta da Ummulsharri toh yau sharrinki zai koma kanki Tani.. Ki jira bayyanata.!

SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!*

*16*

*©þSameena Aleeyou& *

Safiyar Washe gari gidan Hajja Fannah suka fara nufa ko an samu wani bayani gameda Umma. Saidai har kawo wann ranar babu Umma babu labarinta babu wani bayani tak amaime da ita. Ummul sai juya wayar Umman take cikin hannunta nokia k irar 3310 duk taji jiki ta kod e. Hawaye suka kuma gangaro mata. Gashi sun tadda Hajja Fannah ma bataji dad i ba kwance take lik is dan tin bayan tafiyar Hisham jikinta ba dad i k ok ari kawai take. Ummul ta dubeta tace  Hajja ko dai asibiti zamuje.?

"Hajja Fannah ta murmusa cikeda jin dad in yanda Ummul ta damu da damuwarta  A a Ummul, ba sai naje asibiti ba.. Zuwa anjima zazzab in zai sauk a in sha Allah. "

Ummul ta jinina kai suna masu mata fata da addu an samun lafiya itada Khulsum.

Khulsum ce ta soma mik ewa yayinda Ummul ma ta mik e suna mata Sallama da fad in zasu biya Asibiti wajen Abba su dubasa daga can zasu k ara komawa police station ko an samu wani batu gameda mahaifiyarsu.

Ummul ta d an dubeta  Hajja zamu iya barinki ke kad ai naga kaman yau jikin naki da d an nauyi.

Hajja Fannah ta murmusa tana mai mik ewa zaune sosai dan hankalin Ummul d in Ya kwanta  Kinji Ummul nifa zazzab i ne ke damuna nasan kuma bazai shige typhoid d in nan da ya sakani gana kwana biyu ba. Banison zuwa asibiti ne su tara min magani dan bana shiri da had iye k waya Shiyasa ko Hisham ban sanar dashi ba dan nasan yanda kika dage naje asibiti haka shid inma zai dage. Toh kafin ku min taron dangi gashi can na dafa ruwan zogale ma inata sha dan nafi gane wann. Ta k arashe cikin k ok arin nuna jarumta irinta maras lafiya.

Ummul ta murmusa kad an. Sosai take jin Matar har cikin ranta. Sun mik e suna kuma mata Sallama ta k araso hannunta rik eda  yan kud ad e ta mik a masu  Ungo nan kuyi kud in abun hawa.

Dukansu biyu girgiza kai suke suna fad in a a ta barshi.

Ta d an b ata fuska tana fad in  Au baku d aukeni uwa ba kenan idan har zan baku abu kuk i karb a. Ta dubi Khulsum  Ungo nan karb a maku ita Ummul ai tasan karonmu. Idan bata amshi kyauta na matsayin malamar ta ba ai ta amsa matsayin  Yata. Can k asar zuciyarta kuwa Matar D anta ta kirata.

A dole dole suka amsa dukda dama basuda ko sisin da zai kaisu asibiti wajen Abba balle Har su tafi police station maganan case d in Umma.

Suka kuma mata godiya had ida fatan samun lafiya kafin suka fice.

Suna tafe cikin adaidaita Khulsum ta dubi Ummul  Adda mai zai hana mu fara zuwa police station d in tinda kinga asibiti ko munje ba Lallai Mama da yaranta su bari mu shiga wajen Abba ba.

"Ummul ta girgiza kanta  A a Khulsum, koda zasu hanamu mu je d in dai. Muji ya jikin nasa Ya kwana tinda idan muka tafi maganan neman Umma ba Lallai mu dawo da wuri ba har sai munji yanda al amarin Ya kwana. Kinsan ofishin  yansanda cases da yawa. Inaji a jikina da izinin Allah yai za a samu Umma. Ta k arashe cikin tsananin rawar murya irin na Wanda Ya gama karaya amma tawakkali Ya hana furta hakan."

Khulsum ta jinina kai tana amsawa da Allah Ya sa a samu Umma ya kuma bawa mahaifinsu lafiya. Ummul ta amsa da Ameen daidai sansa mai adaidaita Ya diresu k ofan asibiti.

Suna dosowa haraban ward d in suka hango Mama da Badi a. Ga Azeema a gefe harma da mijin Azeemar Habibu. Sai wallahi tallahi suke baka ma gane mai suke fad i dukda wai k asa k asa sukeyi basa d aga murya kar ajisu a fatattake su.

Azeema fad i take  Wai kuna so kuce mun tun yammacin jiya kud ad en suke hannun Tasi u kuma wayansa a kashe.?

Habibu yaci gaba da salati yana tafa hannu. Ya dubi Mama wacce ko iya cewa komai batayi. Huci kurum take. Fuskar Tasi u ne kawai ke mata gizo cikin ido. Allah ya gani da zataga Tasi u yanzu a gabanta zata iya shak esa Har sai an k wacesa.

Cikeda zak ewa Habibu yaci gaba  Wann ai zancen banza kenan.. Ta Ya za a ce kun kira shi Tasi u kun dank a masa ragamar komai irin haka. Mai zai hana baku tuntub i ita Azeema ta kirawo nata mijin matsayin shaida ba..Wann ma ai ba magana bace tinda kud in nan ba kud in Bad ia bane ita kad ai.. Ehe kud i ne na magada.. Kuma shago da ba shagon sata ba ya ma za ace an sayar cikin rahusa haka. Nawa kowacce zata samu cikinku.?

Badi a dake aika masa mugun kallo tace  Toh wai kai Malam naka a wanne.. Ko harda kasonka ne cikin gadon.?

Azeema ta katseta  Ai naga gadon na uban Tasi u ne da kika gayyatosa Ya kwashe kud ad en Ya gudu. Toh wllhi na ranste da Allah bazata tab a sakuwa ba wai bindiga a ruwa. Wllhi yanzu zan kirawo Yaya Salima tinda duk abinda ake itama bata sani ba. Na ranste da Allah sai an mana kashin hakkinmu ehe. Ko kuma wllhi na gayyato maku hukumar hisba nace Kun saida gadon mahaifinmu dake kwance gadon asibiti.! Ta k arashe sai huci take.

Habibu sai bud e hannaye yake yana kuma ingiza Azeema. Fad i yake Ahtoh magana kenan a fito masa da hakkin matarsa.

Azeema ta Ciro waya da zummar kiran Salima kenan suka sinkayo kukan Mama. Ta kamo bakin mayafi tana matse idanunta  Ni Tasi u zai tona ma asiri a garin nan.. Na rufa masa asiri yana d an wiwi na d auki  ya na basa a tunanina zaiyi hankali ashe ni ce  yar wiwi.

" Mama ba fah kuka zakiyi ba, nemo Tasi u Ya kamata kuyi yanda ya shiga Ya fita dan wllhi muddin Tasi u baizo ba daga nan ofishin hukuman hizba na nufa na zayyane masu komai. Kun raba gadon mahaifinmu da ransa.! Azeema tace tana huci."

Habibu yai saurin shiga tsakiya kaman wani alk ali  A a a a baza ayi gaggawan gayyato hukuma ba tinda abin duka na gida ne. Kamata yayi a binciko yanda Tasi u yake duk rintsi. Yanzu zan tafi yanda shi Tasi un ya cika zama na tuntub i abokansa tinda dai baza a samesa a gida ba. Na tabbata baiyi nisa ba. Ya k arashe yana mai wucewa cikin sauri.

Ummul da Khulsum suka dubi juna cikin tsananin shock. Mama da Badi a saida shagon Abba sukai kenan ko mai hakan yake nufi.? Innalillahi wa inna ilaihi raji un.

Suna a haka aka zo neman kud in magungunan Abba wanda kusan kwana biyu kenan yana skipping wasu treatments d in masu matuk ar mahimmanci.

Mama sai ta hayyayako ta soma bala i tana fad in ta gaji da zaman asibiti ma jinyar da yak i ci yak i cinyewa.

Nurse yace  Yanzu babu kud in da za a masa jinyar.?

Azeema tace  Kurma ne kai baka ganin tashin hankalin da muke ciki ne.. Damfararmu fah akayi..

K arasowan su Ummul suna tambayan mai ake nema gameda jinyar mahaifinsu yaja hankulan su Badi a. Ita kam Mama har yanzu fah bata wani gane mai ake ciki ba hankalinta kacaukam naga Tasi u da kud ad

18 / 103