AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   94 / 103

279K to 282K   out of 306.8K words

ni ban isa ba.!

Haidar ya dubi Mommy da mamaki  Mommy sabuwar mata kuma..? Ni Haidar.?

 Auho karya ma aka maka kenan..!

Daddy yace  Shi fah al amari na aure ba abin wasa bane Haidar. Bai kamata ka maida wann word din abin wasa ba. Kai ya kamata kafi kowa sanin hakan.

Cikin d aurewar kai Haidar yace  Daddy meyasa zanyi wasa da al amarin AURE. Idan akwai Wanda zaifi daukan al amari na Aure da mahimmanci that person should be me. Because I once joke with it kuma naga yanda Ya juya mun.

Mommy tace  Shi kuma sak on da ka tura ma Ummulkhair na menene.?

Haidar Ya dan saci duban Ummul dake zaune daga gefe saman carpet d in yace  Mommy ni ban tura ma Khairy wani sako mai kama da haka ba. Eh quite alright na shigo wajenta na tadda tana bacci.. I didn t wanna wake her up sai na d auki Baba Ali na fice dashi to spend time with him.. Ya d anyi k asa da murya yana fadin  I wanted so badly to be with my family.. Shiyasa na fice dashi zuwa toy store..

Ummul ta dubesa da mamaki jin ya b oye ma iyayensa ce masa da tai ya fice bata son ganinsa bata buk atarsa. Mai hakan yake nufi.? Shin hakan yana nufin tsananin son da Haidar ke mata ne yasa ya b oye kalaman da ta furta masa matsayinsa na mijinta ga iyayensa kodai wani dalili ne na daban.?

Muryarsa ta sinkayo yanda yaci gaba  Na tura mata text cewa ina tareda D a na ne so that she shouldn t worry.

Mommy tace  Ai sak on da ka tura d in bazai karya ba.

Daddy yace duk akan sak o ake wann rikicin. Ina sak on yake.?

Mommy Ta dubi Ummul cikeda confidence ita a dole sune akan gaskiya ba Haidar ba tace ta nuna sak on da ya tura mata na cewa yakai ma matarsa yaron.

Nan ne fah gaban Ummul ya fad i dan ita dai bama ta karanta sak on da Haidar d in ya tura mata ba. Kawai dai bayan ficewarsa da Baba Ali da taga ya tura mata sako kawai sai ta saka ma ranta ya tafi dashi ne kaman yanda tace

ya koma yanda ya fito bata bukatarsa tinda taji yace his son needs him and he missed him. Bugu da k ari da taga Ya d auki tsawon lokaci bai dawo da Baba Alin ba kawai sai ta saka ma ranta haka d in ne. Jiki ba kwari ta mik a ma mommy wayar sanda ta kai daidai kan sak on.

Daddy kaw yace da Mommy  Read it loudly.

Jiki a sanyaye Mommy ke duban sak on.

Daddy yace  Ke muke sauraro Kwaise. Nan kotu muke. Ki karanto a warware matsalar yarana.

Murya a sanyaye Mommy tace  Na am Engr.

Sosai Daddy ya tsareta da ido had ida jinjina mata kai alamun ta karanta sak on.

A hankali Mommy ta soma karanta sak on kowa naji _ I will spend time with my son.. Na kosa watannin da Mommy ta d ibar mana su cika. Na kosa mu kasance tare mu ukun.. Kaman dai ahali. I love you so much Khairy. And I can t wait to be with you again.! _

Tinda Mommy ta soma karanta sakon jikin kowa yai sanyi Babu kaman Ummulkhair. Ga kunya da Ya gama lullub e ta kaman k asa ya tsage ta nitse ciki. Abinda Hajja dai ta fad i Ya tabbata hasashen Ummul Ya raya mata wann tunani gameda mijinta.

Hajja ta kula da yanayin da Ummul d in ta tsinci kanta ciki gaban sirakanta sai kawai ta mik e ta amshi Baba Ali hannun Mommy ta k arasa ta kamo Ummul tace suje ta bama yaron abincin sa. Ai kaman jira take sum sum tabi Hajja kanta sanne a k asa suka nufi k ofa. Haidar Ya saci kallonta daidai sanda suka iso kusan k ofa zasu fice. Ya kashe mata ido guda yana matse murmushinsa. Harda furtawa a hankali  Mission accomplished. Labb ansa ne kawai suka motsa. Ta kuma sadda idonta cikin saurin tana ayyanawa cikin ranta wato Haidar da nufi yai abinda yai. Tabbas hak arsa ta cimma ruwa tinda gashi an isa gaban Daddy. Gashi ya sata jin kunya da alama shi ko ajikinsa. Dan a iso gaban Daddyn ma yai abinda yai. Sauri sauri ta fice biyeda Hajja tana jin wani sabon kunya na kuma lullubeta.

Haidar ya mik e shima cikeda risinawa Ya kuma bama iyayen nasa hakuri kan kuskuren da yai tareda alkawrin irin hakan bazai kuma faruwa ba in sha Allah. Ya k arasa ya tattari toys d in da ya shigo dasu Ya fice yabi bayansa su Ummul da kayan wasan.

Daddy ya tsare Mommy da ido. A matsayinsa na D a namiji idan ya fahimci abinda ke faruwa dai Matarsa ne Tai fin k arfi ma D an nasa ta aje masa mata da D a tak i bari su tare gidansa Tun bayan da suka d auro auren Haidar d in da iyalinsa a karo a biyu. Ya jinjina Kai yana duban Mommy wacce ta d an sha jinin jikinta.

Jiki a sanyaye tace  Engr wai lafiya kake ta kallona haka.?

Daddy yace  Dole na kalleki Kwaise kin shigo da k ara kotu ashe kece dai mai laifin.

Mommy ta marairaice fuska tace  Ni ce kuma mai laifi Engr..?

Daddy yace  Eh mana.. Laifinki mana. Ni na rasa zaman me iyalin yaron nan suke a nan..? Meye manufarki na aje masa iyali a nan...?

Mommy tace  Engr naga haihuwa fah tayi..

 Toh dan ta haihu sai ki hana ma yaro iyalinsa.? Harda wani watanni da kika d ibar musu.. A wani aya ko hadisi kikaji hakan.?

Mommy ta girgiza kai kad an  A a Engr ba ko d aya.. Amma ai..

 Babu wani amma a nan Kwaise. Ki kyale yaro ya tafi da iyalinsa haka nan.

 Engr naga wai watanni ukun da na d ibar musu saura sati biyu ne kawai su cika. Cewar Mommy a sanyaye.

Daddy yace  Su cikite sati biyun a gidansu. Kar iyalin yaron nan su kuma kwana gidan nan. Ki barsu haka su tare yau d in nan. Kinga dai abinda ya faru hannunka mai sanda D anki yai Miki. He wants his family next to him. Ya kuma baki matsayin ki as mahaifiyarsa da Ya biyo ta hanya mafi sauk i da zaki fahimcesa.

Mommy ta jinjina kai  Yanzu yau d in su tafi Engr.?

Daddy ya kuma gyara zamansa cikin kujera  Toh mai zasu miki a nan d in Kwaise.?

Mommy tace  Wai dama gani nai idan suka cika watanni ukun sai mu kira namu shagalin taron sunan da bamu samu munyi ba.

 Tafiyarsu bazai hana muku taron sunanku ba Kwaise. Daddy ya bata amsa yana mai daukan remote control na tv cikin hannunsa.

Mommy tace a sanyaye  Shikenan Engr.. Idan haka kace.. Barinje na sanar dasu su shirya. Ta dan kara duban Daddy da Ya maida hankalinsa kacaukam ga TV tace  Na kawo maka shayin ne.?

Daddy ya girgiza Kai yace  No barshi zuwa dare. Sai ya k arada  Kimin kiran yaran nan Haidar da Ummulkhair.

Mommy ta amsada  Toh Engr. Kafin ta fice.

Nasiha mai ratsa zuciya Daddy ya musu gameda zamantakewa kafin ya saka musu albarka Ya sallame su.

A ranar dai Mommy ta hakura ta sakar ma Haidar matarsa harma da D ansa. Kafin dare ta tura wasu daga cikin ma aikatan gidan suka tafi can gidan Haidar d in suka gyare ko ina tsaf.

A d aki Hajja ta zaunar da Ummul Tai mata nasiha da Ya danganci aure da zaman aure. Ta k ara nusar da ita mahimmanci communication tsakanin ma aurata dan da yawan aurarrki Sun lalace ne sakamakon rashin daidaiton fahimta Wanda lack of communication Ya haifar. Ta k ara nusar da ita gameda dabarun kula da miji da jawo hankalinsa sann tace duk abinda Ya shige mata duhu a gidan Aurenta she should call her kai tsaye.

Koda Ummul ta shigo yima Mommy Sallama kanta a k asa. Dan yau d in wani mugun nauyin Mommy din ne ya k aru a idonta. Mommy tashi mata albarka had ida jero masu add uo i na kariya. Ta rungume Baba Ali cikin hannunta tana jin kaman su bar mata yaron kaman kar su tafi dashi. Sosai yaron Ya shiga ransu kaf gidan jimami da begen tafiyan Baba Ali suke. Haka ba don Mommy taso ba ta mik a sa ma Yâ Gumsu tana fad in kullum a kawo mata maigidanta yini.

Ummul harda d an hawayenta sanda suka fito daga b angaren Mommy dan gaba d aya yau d in sosai jikinta yai sanyi jin yanda kowa ke mata nasihohi masu tsayawa a rai.

Suna ficewa Haidar Ya shigo wajen Mommyn dan mata nasa sallaman.

Ta d an d aure fuska ba tareda ta dubesa ba.

Ya k araso ya duka wajen k afafunta. Hannayenta ya kamo cikin nasa yace  Har yanzu fushi kike Dani Mommy.? Haba Mommy na.. I said I m sorry fah.!

Ta dubesa a dak ile  Kaga Haidar ka tashi ka wuce. You can t keep them waiting.

Ya dan marairaice fuska  Amma Mommy haka zan tafi without your blessings.

Kunnensa ta kama kad an taja tace  Dan albarka.! Tashi kaje Allah Ya muku albarka. Allah ya kare ku da dukkan sharri..

Haidar ya amsa da  Ameen Mommy na. I love you.

 Maza tashi kaje haka nan.. Tace tana mai gyara zamanta.

Ya murmusa yana jin k aunar mahaifiyar nasa na dad a ratsa zuciyarsa. Har ya kai k ofa ya sinkayo muryarta tana furtawa a hankali  I love you more.. May you always be protected.

Murmushi ya saki kafin ya fice yana furta Ameen Mommy na a hankali.

**

Koda suka iso gidan sai jikin Ummul Ya kuma macewa. Ta soma tuno abubuwan da suka faru watanni shabiyu baya. Yaa Gumsu tace da ita ta shiga da k afar dama sanda sukai stepping a main door din gidan. Haka nan Ummul ke taka cikin gidan tana jin wani bak on al amari na faruwa da ita. Gidan yana nan a sanin da Tai masa sai wasu yan sauye sauye da baza a rasa ba.

Tinda ta shigo d akin zuciyarta ke tsinkewa. Taci gaba da tuno abubuwan da suka faru a wann d akin bugun zuciyarta na k aruwa. Takai dubanta ga gadon dake d akin sai tai saurin rintse idonta. Sai tana jin kaman lokacin ne komai ke faruwa.

Alamun tab a k ofa da taji Ya sata saurin waigowa. Haidar ta gani tsaye daga k ofa Ya hard e hannaye yana dubanta.

Tai k ok arin janye idonta daga gareshi sanda Ya soma takowa zuwa gareta.

Ganin sai Ya tuna mata abubuwan da Ya faru tsakaninsu a wann d akin. Sabon haushinsa da takaicin abinda Ya mata Ya taso mata. Ta janye jiki cikin sauri tana mai k ok arin ficewa daga d akin amma sai Haidar yai saurin rikota.

Ta d an dubesa ba walwala  Ni ka kyaleni.

Ya d ago gajiyayyun idanunsa yana dubanta  Khairy wai ban baki tausayi ba..

Hararsa ta d anyi  Aw kaine ma abin tausayi ko ni da kasa naji kunya gaban Daddy.?

Ya murmusa kad an yana dan ciza lip d insa na k asa kad an  Aw wai ke dama baki karanta sak on ba kika tada hankali Harda kai k arata gaban Daddy.?

Kaman zatai kuka tace  Ai kai ka shirya hakan dama. Duka laifinka ne.

Ya kuma murmusawa  How am I at fault here.? Ni sak on da na tura daban sak on da kika sanar dasu Mommy daban. I don t remember telling you nayi wani aure ko inada wata mata ba.. Ban san ina kika samo wann idea d in ba.

Hararsa ta kumayi  Da kunne na naji kana fad a ma Aunty Asshe ai. Har cewa kake zata hada maka lefe ko mommy bata sani ba.

Ya dan fito da idanunsa waje  Aw.! wai dama kina lab e kina jin duk hirarmu da Aunty Asshe.? Ya dan tsareta da ido  Wait.! Were you eavesdropping?

Ta kuma dubansa kaman zatai kuka wann karon  Ni wann kawai naji fah.. Kuma ban damu ba dan zaman Lagos Ya aureka. Ban damu da kai ba kaman yanda baka damu dani ba. Kuma ni sabida Mommy da Abba kawai na amince da aurenka.!

"Sosai taso basa dariya sai Ya dan murmursa yana yana shigar da ita jikinsa  Wow someone s jealous..! Tell me, do you love me this much.? Ya k arashe teasingly bai daina matseta cikin jikinsa ba."

Tab e baki Tai kad an tana kauda fuska.

Ya kamo hannunta yana fad in  Taho nan kiji.

Ta d an cije tak i tabi bayansa.

Ya kaikaito yana dubanta cikin marairaice fuska  Please don t give me this attitude Khairy.. Not tonight please.. Wllhi na yarda you are not an easy woman. I ve been trying tirelessly to win you back for the past 12 months.. Dan Allah kiyi hakuri yau kam ki saurareni kinji Khairy na. Wllhi na tuba.!

Yanda ya marairaice yana maganar dole ya baka dariya. Ta kuma tsuke fuska kaman bazata bisan ba sai ta tuno jawaban da Hajja Tai mata kawai sai ta tsinci kanta tana mai take masa baya.

Suka k arasa yai musu masauk i saman chaise-longue.

Tsareta da ido yai yana dubanta. Ta d an dubesa sai ta kauda fuska  Nifa ban son yawan kallo..

 If only you know how much I missed you Khairy.. Ya fad i bai janye idanun nasa daga barin dubanta ba.

Batace dashi komai ba sai kauda fuska da ta kumayi.

Haidar ya kamo hannayenta cikin nasa  I don t know where to start.. Na rasa da wanne zan fara..

Ta dan dubesa a dak ile  Fara da labarin matarka ta Lagos.

Ya dan murmusa  Khairy are we going to talk about this again.? Wai ni dakata.. How many times do I have to explain myself.?

Ta tabe baki kad an  Idan ba mata kake dashi a Lagos ba Meyasa zaman can ya aureka..?

Ya dan furzar da huci kad an sai Ya Ciro wayarsa ya nuna mata fuskar wayar. Hoton road construction ne ya bayyana a fuskar wayar. Ummul ta dubi wayar cikin sanyin jiki. Haidar yaci gaba  Aiki ke kani Lagos. Akwai road project da Kampaninmu keyi a Lagos.. And I m in charge. So idan kinji na tafi Lagos site nake. Happy.? Ya k arashe yana dubanta. Ya dan murmusa  Ai bansan Har haka aka damu dani ake kishi na ba..?

Cikin inina take furta  Ni.. Ni ba kishi nake ba. Tana maganar tana avoiding k wayar idonsa irin Wanda kunya ya lullub e.

"Murmushi Haidar keyi kafin ya kamo hannayenta cikin nasa. Ya d anyi gyaran murya kad an  First, zan fara da baki hakuri Khairy.. Na sani ban kyauta ba in many ways. For the past few months na baki sarari ba wai dan na dena sonki ba. Sai dan Ki samu breathing space.. I thought I was suffocating you Khairy..! Ya dan kamo hannayenta cikin nasa  Na baki space ne ba don na daina sonki ba sai don kiyi healing.. Because time is the only remedy I believe& But believe me it hurts.. It hurts more than you can ever imagine& Ki yarda dani.. A daddafe nayi watannin nan.. But then I had no choice but to punish myself.. For you.. "

Ta d ago ta dubesa da idanunta da suka cika da rauni wann karon.

Haidar ya dan numfasa  Now that we are finally together zan cike miki wann gurbin Khairy... I promise to make it up to you. Yaci gaba da jinjina Kai yana dubanta  Thank you for choosing me .. Thank you for being my wife again.. I promise you won t regret choosing me.. I might not be a perfect husband.. but I ll try my best to be the best.. Best Partner for you.. And best Dad for your kids.. Our kids.! Ya kuma matse yatsunta cikin nasa  And this

94 / 103