AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   30 / 103

87K to 90K   out of 306.8K words

can zamuyi ciniki a tsanake. Sai ta murmusa tana k are ma Asshe kallo harda kashe mata ido  Kar ki damu k awalliya zamu sha hirarmu ta k awaye a mota. Ta k arashe tana d aka ma Asshe bugu a cinya harda kecewa da dariya. Ta dubi driver tace yaja mota su tafi kar rana yai masu a hanya. Driver kaw yai yanda tace dan dai Asshe kam ta kasa katab us cikin motan. Abun matar Ya koma bata tsoro. Ta d auki Suwaiba shashasha amma wann kam ko shakka babu gogaggiya ce . Tanaji tana gani suka d auki hanya tareda Dije babu kuma yanda ta iya. Abinda take tsoro ne yake gab da aukuwa. Mai zai faru idan wann matar da ta zame mata k arfen k afa ta bud e baki ta sanar da uwar Haidar komai. Ta tabbata Kwaise zata iya d aureta Har igiya yayi saura sann asirinta gaban miji da kishiyoyi harma da yaranta Ya tonu. Lallai Ya zama dole ta san yanda zata b ullo ma wann matar. Idan ta kama ta b atar da ita tun akan hanya ne kafin su isa zatai hakan. Dole ta canza salon yanda zata tunk ari wann mahaukaciyar Matar da burin fansan ran D anta Ya rufe mata ido. Haka dai Asshe taita sak awa tana kwancewa cikin mota. Gaba d aya kallo d aya zaka mata ka gane a birkice take."

**

A b angaren Umma kaw sassafe da rabon fad an yaran Mama ta tashi. Badia da Azeema sai tona ma juna asiri suke Azeema na fad in sai Badia ta nemo B arawon mijinta yanda ya shiga ya fita. Yayinda Badia ke fad in gwara nata mijin a sata Ya tsaya ita kaw Azeema ba Wanda baisan Habibu k aton kwarto bane Wanda baya raina mai d ankwali. Nan dai akaita fad a Umma na k ok arin rabiya amma inaa saida dai akai chaa a k ofan b angaren nasu kaman ko yaushe ana bama ido abinci.

Azeema taci gaba da fad in  Oho dai gwara ni mijina baiyi sanadin rufe uwata a police station ba. Hasalima fad i tashi yake ba dare ba rana dan ya fidda mahaifiyarmu da wann macucin mijin naki ya jefata ciki.. Kuma wllhi idan Har baki fito da Tasi ba zan tona miki asiri wajen Jami an tsaro dan ba Mama bace kawai ta saka hannu a takardun bogin da mijinki ya kawo na saida Shagon Abba harda ke macuciya azzaluma.!

Haba nan fah Badia ta janyo Azeema dambe ya kaure tsakaninsu. Umma ta shiga tsakiya tana k ok arin rabiya aikaw akai jifa da ita gefe. K um kakeji jini ya b alle a goshin Umma. Ta dafe kanta dake juya mata tana shafan jinin dake zubowa daga goshinta. Da rarrafe Umma ta bar wajen ta shige d aki dan ba mutan gidan kawai ba har mak ota lek ensu suke suna Allah wadai irin wann ahali. Saikace ba jiya akai auren Ummul ba wacce kowa yake tunanin sabida ita ahalin suka gaza samun kwamciyar hankali. Sai gashi yau an wayi gari babu Ummul da akai mata lak abi da annoba cikin gidan amma da tashin hankali suka wayi gari kaman dai ko yaushe.

Umma ta matse bakinta tana jin kukan gaske mai k arfi na taso mata musamman da taji abubuwan da mutane ke fad i. Ta kuma shafan goshinta taga jini. Ta rintse idanunta tana tunanin  ya yanta a daidai lokacin da jini ke fitowa daga goshinta. Ta aurar da Ummul bisa son zuciyarta sann ta kori Khulsum. Ummul take hangowa tana share mata jinin goshinta cikin tsananin nuna soyayya da kulawa yayinda take hango Khulsum tsakiyan Azeema da Badia tana k ok arin k watar wa mahaifiyarta hakkin rauni da sukai mata a goshi.

Umma ta fashe da wani irin kuka mai ciwo. Lallai mutum baya gane kiman wani ni ima da Ubangiji yai masa baiwa dashi sai ya rasa wann abun.

A haka Umma taci kuka da suntumemmen goshi ita kad ai a d aki.

"Rayuwa kenan ko babu rabuwa akwai mutuwa. Mu zama masu godiya ga d imbin rahamomin ubangijinmu garemu tun kafin daman hakan ya kufce mana. Tomorrow is not promised. Mu so juna muyi hakuri da juna. Mutanen da Allah ya albarkace mu dasu cikin rayuwarmu. Walau iyaye,  ya ya, miji, mata abokan zama da sauransu. Rayuwar duka batada tsawo. Abinda hak uri bai kawo shi ba tashin hankali bazai bayar ba. Allah ya mana muwafak a duniya da lahira. Ameen."

**

A can b angaren Mama Tani kuwa yanda taga rana haka taga dare a police station. Fuskarta ta kumbura suntum sakamon Mari da tasha hannun tsagerun  yanmatan da aka had asu cell d aya. Sallah ne kawai yake ceton Mama daga bugun da take sha hannun tsagerun nan.

Saiga Mama tana sallah cikin cell harda nafilfili. Har bata fatan ta ida sallah gudun kar su ci gaba da cutar da ita. Yara k anana Har tausa suke sa ta masu idan batayi ba taci bugu.

Ta kula ko neman agaji take wajen  yansandan basu kawo mata d auki musamman wann matar da ta gansu da Habibu.

Ta nemi a fitar da ita zataje fitsari. Da k yar da sid in goshi aka fitar da ita tinda bata jima da fita alola ba. Addu a take Allah Ya had ata da Habibu Ya sanar da ita yaushe za a fiddata. Kaman daga sama ta bayan d akin da aka kaita fitsari yanda band akin suke a jere ta soma jin maganganun ta wata  yar window. Muryar Habibu takeji daga window d in yana kwantar ma  yarsandar hankali da fad in shi fah ba taimakon Mama Tani zai ba. Dama yayi zaton zai cimma Tasi u ne kafin abubuwa su lalace. Dan haka bazai jefa kansa a uku ba dan wann bakwaiye Ya rantse har kotu sai an tafi. K arshe gidan Kasu Tani zata tafi babu ranar fita.  Yarta kuma babu amfanin da take masa saima cike masa d aki da tai dan haka a yau d in nan zai rubuta mata takarda tinda Tasi u Ya gudu da kud ad en. Aure zaiyi Ya saka amaryarsa a d akin.

Sai ga Mama tana sakin fitsarin jikinta. Ta kama k arfen window ta d ale tana dubansu  Habibu.. Irin cin amana da yaudara da zakai ma Azeema kenan..! Amma Habibu Allah Ya tsine maka albarka. Ka cuceni ka cuci Azeema. Habibu Allah bazai barka ba. Kan wann kilakir ka wulak anta Azeema.?

Kafin takai aya taji sauk an tagwayen Mari a fuskarta.  Yar sandar Habibu ce tai mata Marin  Ki iya bakinki kisan a ina kike. Cewar budurwar Habibu Yayinda Habibu ke mik a mata farar takarda  Tazo gidan sauk i tinda kina kusa. Ga wann ki bawa  yarki idan gantalinta Ya d ebota ta nan tinda ba mutuncinki suke gani ba balle suzo dubiyanki. Kar na koma gida na tadda tsummokaranta cikin d akina. Sak o na baki ki sanar da ita. Gyara zan fara a gaggauce dan amarya ta zan aje ciki. Ya k arashe yana kashe  yarsandarsa da murmushi.

Mama sai Tai mutuwar tsaye tana juya takardan da Habibu Ya mik a mata cikin hannunta. Bata san meke wakana ba har saida  yarsandar da tai mata rakiya fitsari ta tasa k eyarta.

Fitsarin da ta juyesa jikinta kenan ba tareda taje band aki ba. Innalillahi wa inna ilaihi raji un. Meke faruwa da ita da yaranta? Daga wacce miji Ya bata sak on sakinta ta hannun mahaifiyarta sai wacce miji Ya cuta ya kuma gudu Ya barta. Sann a dalilinsa aka kame uwarta aka gark ame. Shin wann wace irin rayuwa ce. Sai ga Mama tana kuka shar shar da hawaye hannaye biyu aka  Wayyo ni Tani naga takaina.! Habibu kaji tsoron Allah. Ka tuna ko mutuwa na kunyar idon uwa. Yanzu da wani bakin zan goranta ma Suwaiba ni Tani.  Yar Suwaiba ta tafi d akin Miji ni nawa yaran Sun dawo a jere. Wllhi bazata saku ba. da na koma na fuskanci tozarci yo gwara na Mutu a nan.! Ta kuma kurma kururwa.

Tsawa budurwar Habibu ta daka ma abokan aikinta cewa su shige da Tani cikin cell d inta su gark ame.

**

Abuja

"Tsaye suke a can construction site d insu, yanda zasu gudanar da babban project na Kampaninsu."

Dukansu sanye suke da kaya irinta k wararrun Engrs. Reflective safety jacket kalan d orawa mai ratsin bak i sai safety helmet mai d aukeda tambarin kamfaninsu daga gaban *MB*

Su kusan hud u sunyi tsaye gaban wani tapkeken sketch. Design Architect Hisham sai kwararo bayani yake yayinda sauran ke jinjina Kai kowa yana fad in abinda ya k ware akai.

Hisham na hankalce da Haidar Wanda Sam hankalinsa bai tare dasu. Excusing Kansa yai ya k araso yanda Haidar ke tsaye jingine jikin mota. Shima d in cikin shiga irin tasu yake saidai shi babu jacket saman rigarsa sai ko helmet.

Hisham yai masa k uri hannayensa zube cikin aljihun jeans d insa. D an k arasowa yai kusan Haidar d in had ida jingina jikin motar. Ba tareda ya dubi Haidar d in ba ya soma fad in  This is not like you Engr. Ban Saba ganin ana aiki jikinka a mace ba.. I expect to see Haidar mai jajircewa da na sani dan ban tab a tsammanin Dad d inka zai mik a maka ragamar aikin nan cikin sauk I ba.. Snn kaji yanda abokinsa yake yabawa team d inmu baice komai ba baiyi yunk urin dakatar dashi ba kaman yanda ya saba a baya. Kawo yanzu sun hango future ma Kampanin tareda kai. Zan iya ce maka na hango yau d in a k awayar idanunsa. Ko bai furta maka ba he s proud of you..

"Furzar da huci kad an Haidar yai yana mai gyara tsayuwarsa hannayensa zube cikin aljihunsa yake duban masu tonon k asa daga gefe  But unfortunately I m not a perfectionist, a workaholic like my Dad. Ya karkato yana duban Hisham sosai  Ban damu ba yayi alfahari dani ko kar yayi. I don t give a damn.. "

"Hisham ya d an girgiza Kai yana duban Haidar d in  So tari mukan kasa ganin blessings da Allah ya mana baiwa dasu har sai mun rasa. Ka gode ma Allah Haidar ka girma da iyayenka biyu a raye kuma suna tareda kai. In my own case is a different story. Ban samu daman sanin mahaifina ba. Ban samu daman had uwa dashi ba. Ya d anyi fasali kafin ya murmusa  But it s fine I m not complaining. Alhamdulillah, At least I have my Mom with me. And to me"

she s more than enough you know. Ya kuma murmusawa yana jinina Kai  Bazamu iya k irga d inbin ni imomin Ubangijinmu garemu ba.

Dukda sanyi da jikin Haidar yai sai ya kauda Kai gefe dan shi gani yake da mahaifinsa da babu shi duk d aya ne gwara ma ace babun Watak ila bazai masa irin k iyayyan da yake masa a yanzu ba. Duban abokan aikinsu yai kana ya kauda zancen da fad in  Komai ya kammala saura fara aiki. Soil test ya rage. You take care of the report while I m away..

Hisham ya zuba masa ido shaye da mamaki. Ya d an girgiza kai  While you are away.? What does that mean..? What do you mean by that.?

"Murmushi Haidar yai  It s good to take a break, don t you think. "

Har lokacin dubansa Hisham yake da mamaki  Seriously.! Ina zaka Haidar.?

 To Cuba. Jirgina gobe da safe ne in sha Allah..

 Business trip.? Hisham ya tambaya yana dubansa.

 Am I using business terms here.? Bakaji mai nace maka bane. Vocation zan tafi of course.

Hisham ya d an Ware idanunsa. Kafin ya soma magana Haidar ya dakatar dashi  Don t even start.

Hisham ya jinjina Kansa a hankali  Bazaka saurareni ba na sani. But why Cuba.? Jiya fah nake gani a labarai Hurricane killed at least 6 people there& Couldn t she think of a better place. Ya tambaya yana duban Haidar d in tinda yasan wann bai wuce aikin Matarsa Dareen ba wacce yayi imani tarayyarta da Haidar d in Babu wani alheri tinda aure ne da Har yau iyayensa basuda labari.

K ok arin bud e motarsa ya soma  Zamuyi magana kaikam..

Har ya bud e motar zai shige Ya juyo ya dubi Hisham murmushi saman fuskarsa  C mon haka zaka barni na tafi bazaka min fatan alheri ba. What if this is the final goodbye. What if hurricane ya ritsa dani a can.?

Hisham ya k araso ya d an punching muscle d in Haidar guda  You shut up jerk.!

Dariya sukayi su duka biyun kafin suka rungume juna Hisham na fad in zasuyi aikinsu tareda nasara cikin yarda da ikon Ubangiji. A haka sukai sallama kowa naji a cikin zuciyarsa zasuyi kewan juna.

Hisham yai tsaye yana bin bayan motan Haidar da kallo. Murmushi ya saki yana mai ayyanawa cikin zuciyarsa tinda ba wani aiki mai tsanani da zasu fara yanzu zai tafi Kano. Ya kuma sakin murmushi sanda yake hango beautiful innocent face d inta a k awayar idonsa. Ya shirya tafiya neman aurenta wann karon. Ya shirya sanar da ita abinda yakeji gameda ita. Even though he s not expert a wann b angaren but zaiyi iya k ok arin sa ya tabbata bata kufce masa ba. He s been rejected so many times wanda hakan yasa neman aure da  yanmatan suka fita Kansa. But wann karon ya shirya yak in Neman auren Ummulkhairi da duka k arfinsa. Ya kuma sakin murmushi mai kyau zallan k aunarta na d awainiya dashi.

**

"Yanda Mommy keta faman shiga da fice saida abun yai mugun d aure ma Anisa kai. Mommy fah tarba na musamman taketa faman shirya ma masu kawo Amaryar Haidar. Jikin Anisa gaba d aya ya mace, zuciyarta ta karaya ganin yanda Mommy keta d aukin wann aure. Ta tabbata ko wacece matar Haidar ta gama samun gurbi mai girma cikin zuciyar Mommy dan sosai take son wann aure. Ita gani take Ammi b ata lokacinta kawai take dan Mommy bazata bari Haidar Ya rabu da matar nan ba cikin watanni k alilan kaman yanda Ammin nata ta sanar da ita."

Suna jin shigowar Mota Mommy tai saurin mik ewa tana fad ad a murmushinta. Lokaci guda ta dubi Anisa tace maza su sauk a k asa ga matar Haidar ta iso.

Saurin rik o Mommy Anisa tai tana murmushi da yafi Kama da yak e  A a haba Mommy. D an dakata mana kefa uwa ce. Ki bari ni na sauk a. Ma shigo miki da ita.

Bata jira cewar Mommy ba ta nufi k asa tana mai rausayar da ido had ida furzar da huci dan wani mugun takaici ne Ya cika mata zuciya yacce kasan  yar gwal za a kawo gidan.

SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU.!*

*23*

*©þSameena Aleeyou& *

"Mommy ta gaza zaune ta gaza tsaye. Zuciyarta sai harbawa yake, ta rasa sukuni ne zuciyar nata ya samu sakamakon kawo makarin asirin Haidar da akayi kokuwa yarda da amincewan Haidar Wanda batada tabbas akai ne. Koma dai tsoron abin ya k unshi rasa rai ne. Sai ta fara tuhumar kanta anya bata kasance mai son zuciya ba. How could she kill another person s child for her own to survive. Saurin girgiza kai tai dan bata son irin tunanin nan su shige kanta. Dole ne yasa tayi hakan. Ance so so ne amma son kai yafi. She needs to save her only son no matter the cost, koda kuwa Ya k unshi rasa rai ne. Da wann tunanin zuciyarta ya samu natsuwa. Tai zaune cikin kujera tana jiran shigowarsu."

Inna Dije na rik e da hannun Ummul gam take k are ma katafaren gidan kallo Wanda ta masa lak abi da fadan shugaban k asa.

"Suna shigowa wani irin k amshi ne da zatace hancinta bai tab a karo da irin shi ba tsaban dad i shi ya daki hancinta, nan ta hangi wata hamshak iyar mace wacce kallo guda zakai mata ka tabbata tayima babu bugun girma. Tana ganin Asshe jik akk iyar mace wayyaya sai taga ashe gaban Hajiya Kwaise Asshe ba komai bace. Kama daga yanayin suturan dake jikinta muhallinta harma da gogewar fatar ta. Dije ta

30 / 103