AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   64 / 103

189K to 192K   out of 306.8K words

abubuwa da dama dake cikin duhu. Ina fatan a lokacin da duhun nan zai yaye miki Ummul bazaki sameni cikin wad anda suka ci amanarki ba. And you can count on me dan ciwon  ya mace ta  ya mace ce. Ta k arshe tana murmushi had ida bud e mata marfin mota  A cikin gidan nan trust no one but yourself Ummulkhair. Tabbas Wani Auren nasara ne. Amma Wani Auren halak a zai kaika.! Allah Ya tsare hanya. Ta k arashe da murmushi. Tana ida fad in haka ta juya ta shige cikin gida zuciyarta na mata fari k al. Dan ta tabbata ko ba komai ta cika shakku cikin zuciyar Ummul. Wani abu ma sai randa k wai Ya fashe gaba d aya.

Tabbas Anisa tayi nasaran jefa mata waswasi da shakku cikin zuciyarta. Shin da gaske ne ita d in ta zak e da yawa.? Batasan mai Anisa take son sanar da ita ba. Sann koda wann auren tun usul bata tsammaci farin ciki ko wani abunda yai kama da wann cikinsa tun farko ba. ta tsinci kanta cikin tsananin shakku da rud ani Wanda bataji irinsa a baya ba. Sann sosai taji tana buk atan sanin mai Anisa take son sanar da ita musamman gameda mijinta Haidar. Haka har ta isa asibiti tunanin da take kenan jikinta duk a sanyaye.

*

Asshe bata iya kwanaki garin ba ta tarkasa ta dawo Kano dan sosai ta firgita da lamarin  yaruwarta dole ta dawo gida ta samu ta shawo kan matsalar kafin komai Ya ida kwance mata musamman da idonta ya tabbatar mata idan  yarta Anisa bata k arashi rayuwarta gidan yari ba toh kuwa ba shakka zata k are a turu ganin irin abinda take wanda yafi kama da hauka tuburan duk dan akan Haidar. Da fari ta saka ma Ummulkhair guba a turare sann ta d aura alhakin kan Mommy har ta tafi jail tai kwanaki dik akan haka. Yanzu ga had arin mota da ta shirya ma Haidar wanda k iris bai rasa ransa ciki ba. Lallai ya zama dole tasan abinyi.. Dole ta raba wann jarabebben aure na Ummulkhair da Haidar wanda ta zamto silarsa a farko ko dan ta ceto  yarta Anisa.

*

Kano..

"Sun had e su uku a parlorn Hajiya Asshe. Mama Tani wacce bata jima da shak an iskan  yanci ba, Inna Dije sai kaw Uwar gayya Hajiya Asshe."

Tani ta girgiza kai cikin rashin fahimta tana duban Inna Dije  Dije kina nufin kice wann matar ita tayi belina ba sirakan Suwaiba ba.? Sann so kike kice mun duk zaman dad I da naga kinayi da Suwaiba a halin yanzu dama ba na gaskiya bane.? Dije wai meke faruwa ne.?

Inna Dije ta murmusa tana duban Tani  Tani banda abinki.. Wann ma ai sirkar Suwaiba ce. Kuma ke a tunaninki ni Tani zan tab a yafe ma Suwaiba da  yarta Ummulkhair ne. Kar ki mance a dalilin bak in k addarar Ummulkhairi na rasa tilon D ana Fa izu.! Kuma ke kinfi kowa sani Tani. Dije bata yafiya sai d aukar fansa.! Yau d in nan zan sanar dake wace kalan Aure Suwaiba taima  yar D anuwana dake kwance yana jinya wanda zai zamto Miki makami da zaki kori Suwaiba da Auren cin amana da tai miki. Tani na san komai Suwaiba zata Miki a halin yanzu. Duk wani halacci na k arya da zata Miki bazaki tab a mance bak in cin amana da ta miki na aure Miki miji bayan kin aminta da ita da tayi ba. Haka ne?!

Tani tai shiru tana duban Inna Dije wacce ke sakin huci.

Tani sai ta girgiza kai a hankali  A a Dije. Yo ni a halin yanzu wani makami nakeda shi Wanda zan yak i Suwaiba dashi bayan yarana da a kullum nake goranta mata cewa sunyi aure suna d akin mazajensu gasu nan duka sun dawo gida daga wacce miji Ya koroto sai wacce miji Ya gudu Ya barta. K arewa ma Suwaibar ke kula dasu a lokacin da nake gark ame gidan gyaran hali. Na sani abinda Suwaiba ta min bazan tab a yafe mata ba ko mutuwa Malam yayi amma a halin yanzu banida abinda zan yak i Suwaiba dashi kina gani yarana ma sun koma k ark ashin tutar Suwaiba.. Toh mai yai saura.?

 Malam Isubu Yayana shine kad ai ya miki saura Tani. Dan Dikda kasncewarki  yar ta adda mai saida hakkin miji da ransa da sunan gado ta addacin da Suwaiba tayi yafi naki kuma dik randa D anuwana yasan mai Suwaiba ta aikata a lokacin da yake kwance ya rabu da ita kenan rabuwa ta Har abada.. Kuma idan mutuwar auren yaranki ne Ya tsaya Miki ki taya Suwaiba sharan d aki yanda Ummul zata zauna dan nan da wata d aya jal Ummul zata dawo gida ta jone da naki yaran.!

Tani ta girgiza kai  ban fahimceki ba Dije.? Mai kike nufi.? Wane irin Aure Suwaiba taima Ummul.?

Carab Asshe ta cab e  Auren mutuwa.! Auren warware sihiri.! Auren WATA UKU.!

Take Tani ta mik e a zabure tana dafe k irji  Na shiga uku ni Tani. Auren mutuwa..?!

SameenaAleeyou*AUREN WATA UKU..!*

*43*

*©þSameena Aleeyou& *

Inna Dije ta jinjina kai  K warai kuwa kaman yanda kika ji.

Wata  yar bazawarar dariya Mama Tani tai irin Wanda bai kai ko ina ba  Haba haba Dije. Dani dake munsan Suwaiba.. Koda ace shashasha ce lamba d aya bazata tab a abinda kike fad a mun ba. Koda ace mafarkin Suwaiba da cikan burinta shine taga Ummul dinta a d akin aure ko wane iri ne. Dije munsan Suwaiba bazata tab a gigin jefa  yarta a halak a Har haka ba.!

Asshe ta murmusa tana duban Tani  K warai kuwa da saninta bazata jefa  yarta a auren halak a kaman yanda tayi ba. Burin Suwaiba shine  yarta Ummul tayi aure ko ta halin k ak a ko wani iri ne matuk a sunansa Aure. Tabbas da ace Suwaiba tasan wani irin Aure ta jefa  yarta ciki da nadaman da zatayi sai tafi wanda take ciki yanzu. Ta numfasa kafin taci gaba  A Yarjejeniyar da mukai da nida Suwaiba shine  yarta Ummulkhair Auren Kwangila tayi mai k ayyadadden wa adi Wanda wa adinsa watanni uku ne. Sam ban sanar da Suwaiba ga asalin sahihin manufar Auren ba. Hasalima ban sanar da kowa bayan  Yaruwata da muka shirya Auren tare sai ku da Ya zama dole na bude maku cikina dan bazan iya wann yak in ni kad ai ba. A halin yanzu Babu abinda nake so kaman Ummul ta fice daga rayuwar  Yaruwata tinda na kula Ummul ta riga tayi tasiri a zuciyarta. Ba haka na shirya abun ba.. Domin kuwa a halin yanzu  Yaruwata mahaifiyar mijin Ummul Auren gaskiya take son D anta yayi da Ummulkhair ba AUREN WATA UKU kaman yanda muka faro daga farko ba.

Tani ta dubeta da mamaki sai ta girgiza kai  Toh mai kike so muyi a nan.? Ta yaya zamu raba auren da bamu muka k ulla ba.?

Inna Dije ta murmusa  Mu kad ai ne zamu iya datsen Auren sabida mu keda kusanci da Ummul da kuma Mahaifyarta Suwaiba. Hajiya Asshe batada abokin tarayya domin kuwa  yaruwar tata da tai komai domin ita asirin Suwaiba yayi tasiri akanta tinda gashi ta makance da soyayyar Ummul ma d anta. A halin yanzu Suwaiba ta aminta da mu Tani. Da wann aminci mu kuma zamu yi amfani mu tsinke Auren  yarta sann mu d au fansar duk wasu abubuwan da tai mana.!

Tani tai shiru kaman mai tunani sai kuma ta girgiza kai kad an  Amma idan Har Ummulkhair Auren mutuwa tayi mai zai hana mu kyaleta ta Mutu cikin wann aure kinga Babu babban fansa da zamu d auka kan Suwaiba tamkar ta rasa  yarta da ta k wallafa rai akanta tin haihuwarta. Musamman ma ke da kika rasa tilon D anki ta dalilin bak in k addararta.

"Dije tai  yar bazawarar dariya wann karon  Idan dan wann ne da na jima dayi Tani. Idan kashe jinin Suwaiba shine fansar ran Fa izu ai Khulsum tana nan gabana da tuni na b atar da ita. Kar ki mance  ya yan Suwaiba duk yanda naje nazo  ya ya na ne.. Sann ai mutuwar Ummul bazai mata ciwo ba musamman idan a gidan Aurenta ta Mutu. Hakan na nufin burin Suwaiba na aurar da Ummul Ya cika kenan. Ai bari kiji Tani Ummul ta dawo gida sann tasan duk wani badak ala da mahaifiyarta ta tafka da sunan Aurar da ita sai yafi komai yi ma Suwaiba ciwo. Dik randa Ummulkhairi tasan cewa Mahaifiyarta ta siyar da ita ne domin ta zamto makarin asiri da sunan Aure zata tsani Suwaiba, zatayi danasanin kasancewarta mahaifyarta sann zatayi nadaman duk wani biyayya da ta jima tana mata. Ba a nan kawai ba, Mijinki Yayana zai tsani Suwaiba zai guje ta Ya rabu da ita rabuwa ta Har abada kai kowa nata sai Ya guje ta. Dan babu Wanda zaiji abinda Suwaiba ta tapka bai kyamaceta ba. Yanzu kin fahimci manufata.? Ta k arashe tana tsare Tani da ido."

Makirin Murmushi Tani ta saki irin Wanda ta jima batayi ba tin kafin a gark ame ta a gidan gyaran hali  Lallai dole na jinjina Miki Dije. Wann shiri naki Ya shiryu Ya kumayi daidai da fansar da na jima ina so na daukan kan Suwaiba amanata da taji ta aure min miji bayan na aminta da ita.! Har na hango idon Suwaiba a lokacin da Malam zaiji cewa Matar sonsa Suwaiba ta mik a yarsa mafi soyuwa ayi tsafi da ita.! Ta kece da wata iriyar muguwar dariya Dije na tayata.

Asshe ta dubesu tana murmushi  Toh ni babu abinda zance sai hamdala tinda dukkanmu mun samu matsaya guda shine mukai Suwaiba k asa warwas. Abinda zamu maida hankali yanzu akai shine ku kuje kuci gaba da shashantar da Suwiaba kuna nuna mata cewa Lallai kuna tareda ita dan taji dadin sakin jiki daku ta yarda cewa tuba na gaskiya kukayi. Nima kuma zan maida hankali ga  Yaruwata da shirye shiryen da take na tariyar Ummul da Haidar da zaran an sallami Haidar d in daga asibiti. Bazamu bari ayi wann bikin tariyar ba. A daidai wann lokacin zamu k addamar da duk wani shirin mu sann mu lalata komai. Zan raba D an  Yaruwata da zuri ata da annobar da na kawo mana cikin zuri a. Sann ku kuma zaku d auki fansar ku akan Suwaiba. Duk kun amince da haka.?

Gaba d aya suka jinjina kai suna masu jaddada k udirorinsu.

**

Abuja&

A hankali yake takowa cikin parlorn bayan kiran da Ya samu daga Hajiya Kwaise Maitama cewa tana nemansa. Koda Hisham yaji sak on nemansa da Hajiya kwaise keyi baiji ko d ar ba cikin zuciyarsa sann baiyi k asa a gwiwa ba ya amsa gayyatar nata.

Cak Ya tsaya tsakiyar katafaren parlorn na alfarma bayan one of the maids ta masa iso. Wann shine ya kamata ace Ya kasance rayuwarsa amma Hajiya Kwaise ta masa denying. Ta koresa a gidan mahaifinsa tin yana ciki baizo duniya ba. Ya d aga kai yana kallon wani hoton Haidar da ba a jima da kafawa a parlorn ba. Shi kansa Haidar baisan da hoton ba dan yana asibiti Mommy tasa aka saka hoton. A Office aka masa hoton bayan ya gama gudanar da wani presentation. Yayi kyau sosai k warjininsa sosai ya bayyana cikin hoton. Wani irin k atutun bak in ciki ya tokari Hisham. Wann duka rayuwarsa ne amma ta sace komai daga gare shi ta baiwa D anta shi kad ai. Ya tsane su gaba d aya. Kuma babu Wanda zai ragar masa cikinsu.

Yana nan tsaye wata maid din ta k araso ta k araso ta cika centre table da kayan motsa baki. Ta kuma tanbayesa ko yana son tea ko coffe. Ya girgiza mata kai had ida fad in kar ta damu abinda ta kawo ya wadatar. Tai excusing kanta ta fice. Har lokacin Hisham na nan tsaye gaban hoton Haidar ya had e hannayensa ta baya yana kallon hoton.

Sallaman Mommy yasa shi kaikaitowa yana dubanta.

Kaman ko yaushe Hajiya Kwaise Maitama ta sauk o zuwa parlorn cikin shigarta ta alfarma. A da saidai ka hango izza da isa a tattare da ita amma a halin yanzu annuri fari a da walwala kake hangowa a kyakkyawar fuskarta.

A sanda take takowar nan Hisham kaw cikin zuciyarsa cewa yake  Kece sila.. Kece silar komai.. Baki cancanci yafiyana ba Kwaise Maitama.

Ta k araso da murmushinta tana nuna ma Hisham wajen zama  Bismillah zauna mana.

Shid inma murmushi ne saman fuskarsa ga kwantar da kai da yake irinta girmamawa Wanda zaka ranste Har cikin ransa ne. Saida ya duk a Har k asa ya gaida Mommy cikeda risinawa da girmamawa Wanda hakan sosai ya kuma birge Mommy ta kuma jin ta aminta sosai da tarayyarsa da D anta.

Ta amsa da sakin fuska tana fad in Ya tashi ya hau kujera ya zauna.

Hisham yai yanda Mommy tace cikeda girmamawa ba.

Mommy ta dubesa bayan ta tambayarsa mutanen gida da aiki. Hisham yace  Kowa lafiya Mommy. Aiki kuma mun gode Allah. Ya k arashe da murmushi saman fuskarsa.

Mommy ta murmusa tana fad in Masha Allah.

Dak ik a ya dan gifta kafin tace  Arc. Hisham ko.?

Hisham ya murmusa  Hisham d in dai Mommy.

Itama murmushin tayi  A a gwara dai na baka title dinka. I heard that you are one of our best architects a nan M&M Builders. Cikin raha da k ok arin sako barkwanci take maganar wanda a baya ba d abi arta bace.

Hisham Ya dan murmusa  K ok ari kawai muke Hajiya.

Itama ta murmusa  Toh ma sha Allah. Allah ya taimaka.

Hisham Ya amsa da Ameen.

Mommy ta dan gyara zama kafin tace  Hisham wata  yar alfarma nake buk ata daga wajenka.

Ya d ago Ya d an dubeta sai Ya girgiza Kai  Alfarma kuma Mommy.. Wace iri kenan.?

Wani folder ta dauko gefenta ta mik a masa tana fad in ya duba ya gani.

Hisham ya saka hannu biyu ya amsa.

Mommy taci gaba a sanda yake warware folder d in  Plan ne na gida. Ina so ka duba kai nazari akai.

Hisham Ya ida warware folder d in yana dage takardun yana gani.

Mommy taci gaba  I want to surprise your friend.. My son.

Hisham ya dago ya dubeta  You mean Haidar.?

Mommy ta jinjina masa kai  He s my only son.. Our only son nida mahaifinsa. Tai maganar da murmushi saman fuskarta Wanda yake nuni da tsananin k aunar da take ma D an nata.

A cikin zuciyarsa Hisham yace  Sabida kinyi sanadin raba d ayan d ansa da ahalinsa. Amma a fili sai Ya murmusa

 Okay.. And mai za ayi da wann.?

 Nasan kanada masaniyar cewa tsawon lokaci alak an Haidar da halinsa akwai babban tangarda ciki since you are his best friend and possibly his only friend nasan kanada masaniya kan wann.

Hisham ya jinjina kai a hankali  Haka ne Mommy.. And believe me burina shine Haidar ya shirya da ahalinsa.

"Mommy ta kuma jinjina kai  Hakan yasa na gayyato ka domin ka min wann aikin. After all, layinka ne. "

Hisham Ya kuma jinjina kai kafin Mommy taci gaba  Wann plan na gidan da na dank a maka shine gidan da muka fara zama cikinsa nida Mahaifin Haidar wato Engr Aliyu Maitama a lokacin da muka dawo Abuja.. Ina so Haidar da matarsa Ummul su tare a wann gidan da zaran an sallamesa daga asibiti. Na dank a maka ragamar komai duk wasu gyare gyare da sauye sauye Wanda yayi daidai da ra ayin Haidar ayisu kafin bikin tariyarsu da zaran an sallamesa daga asibiti. Kai abokinsa ne nasan kasan ra ayinsa tsare tsarensa. Inaso ayi komai to his taste ta yanda zaiji dadin bazatan. Duk wani abinda ake buk ata don t hesitate to let me know. Kar ka mance na sanar da kai wann din Bazata ne. So ko Boss dinka a Office ina nufin Mahaifin Haidar banso ya sani.. Is our little secret for your dearest friend. Ta k arashe murmushi saman fuskarta.

K ak aro murmushi Hisham yai dukda mutuwar zaune da yai yana sauraron Hajiya Kwaise kafin ya shiga jinjina kai  Bakida matsala Mommy. Haidar tamkar D anuwa na d aukesa ba aboki kawai ba. Zanyi komai to the best of my ability in sha Allah.

Mommy ta murmusa tana dubansa. Yanda yace D

64 / 103