AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   39 / 103

114K to 117K   out of 306.8K words

sashen Mommy ko ban fita ba. Haka ne.? Leena tai Shiru sai muzurai dan batai zaton wann bagidajiyar zatai tunanin cameras ba. Batamayi zaton tasan da zaman cameras din ba. Ta juyo ta dubi Anisa cikeda tsoro. Sai Anisa ta kashe mata ido alamun ta kwantar da hankalinta she had everything under control.

Mommy ta jinjina kai  K warai akwai cameras a wasu hanyoyi da zai sadaka da d akuna cikin gidan nan. Shi zai tabbatar mana idan Ummul ta shiga d akina ko bata shiga ba.

Anisa ta jinjina kai tace k wari a duba footage.

Saidai koda aka duba cameras na cikin k waryar gidan kawai aka duba kuma da alama duk Sun samu fault dan haka ba a ga waye ya shiga d akin ba.

Leenah ta rausayar da ido cikeda k osawa tana fad in Ummul batada sauran hujja.

Ummul ta girgiza kai tace  Na cikin k waryar cikin gida kawai aka duba mai zai hana a duba na waje. Shi zai tabbatar ya kuma tantance waye ya kawo sark ar b angarenta.

Leenah ta dubi Anisa wacce izuwa lokacin ta gama razana dan zallan cameras na cikin gidan Tai tampering banda na haraban gidan tinda bata kawo abun zai kawo haka ba.

Mommy ta jinjina ma tunanin Ummul dan koda aka duba footage na haraban gidan Ya hasko wata maid din gidan sanye da uniform dinta ta nufi bangaren Ummul da sark ar rike hannunta saima juyasa take tana waige waige.

"Leenah ta rausayar da ido  See, this doesn t prove you innocent Ummul. It could be an alibi so that no one would suspect you. I m sure this is pretty mandated. Bakinku d aya kawai bata mana lokaci kike a nan. "

Mommy ta daka mata tsawa da fad in Tai masu shiru. Sai kuma ta juyo sosai tana duban Leenar dan ta kula zak ewarta da k ok arin ganin ta d aura laifin kan Ummul yayi yawa. Mommy ta girgiza kai kad an tana kuma duban Leenah  Waye ya baki daman saka hancinki cikin al amarin gidan nan.?

Leenah ta sha jinin jikinta. Ta dan matsa gefe tana bama Mommy hakuri. Take Mommy tasa akai mata kiran maid din.

Ba a jima ba Maid din ta bayyana gaban Mommy wacce ta tsareta sosai da ido. Sai rawa jikinta keyi dan tsoro.

Cikin murya mai tsoratarwa Mommy ke tambayarta waye ya bata umarni da ta kai sark ar d akin Ummul.

Maid din taci gaba da sunkuyar da kai tana girgiza kai. Ta d ago tana dubansu a tsorace. Anisa ta Zare mata ido. Sai ta girgiza kai ta shiga nuna Ummul d in tana fad in ita ta bata umarni taje ta b oye mata sark ar a b angarenta bayan ta d auko. Cikin harshen turanci mai aikin tai maganar.

"Leenah ta murmusa  My hunch was right, after all. Gashi Ummul Vicky ta bada shaida akanki. Bakinku d aya. Shin har yanzu kinada sauran hujja.? "

Mommy ta kuma tambayar Vicky tabbata Ummul ce ta bata umarni. Vicky tace eh haka ne.

Girgiza kai Ummul take tana dubanta kafin ta k araso gabanta  Kika ce ni na baki umarni.?

Sai ta d ago tana duban Ummul d in dan bataji mai tace ba sabida ba hausa take ji ba. Ummul ta kula mai aikin bata jin hausa. Sai ta murmusa a hankali tana hamdala cikin zuciyarta dan da alama duk yanda mugun zaibi yaga Ya kulleta sai Allah ya bata k ofan fita sabida batada hakki.

Taci gaba da duban Maid din tana mai ci gaba da furta  Amma baki jin yaren da nakeyi. Haka zalika nima bana jin yaren da naji kinyi magana dashi. Shin ta Ya akai har na k ulla cinikayya dake.? Ta ya akai har kika iya d aukan umarni daga bakin wacce baki jin mai take fad i.?

Shiru sai kallon Ummul da take cikin rashin fahimtar mai take cewa.

Mommy ta jinjina kai cikeda gamsuwa da yanda Ummul ke fayyace komai dalla dalla.

Mommy ta dubi Leenah tace  Yanzu kika mana proving a nan cewa Ummul bata jin turanci haka ne.?

Cikin sanyin jiki da daburcewa Leenah ke duban Mommy ganin table na k ok arin turning.

Mommy taci gaba da jinjina kai  Idan haka ne bana tsammanin zata iya dogon magana har su shirya wani plan da Vicky wacce sam ba hausa take ji ba.

Kowa ya shiga jinjina al amarin yayinda zuciyar Ummul Ya cika da hamdala.

Anisa ta sake baki tana kallon ikon Allah yanda Bagidajiyar nan zata kamasu gidadancin da suka raina.

"Leenah ta janyo Anisa gefe tana mata k usk us  Oh Girl, this is not happening.. What s she doing.? My goodness! Is she a detective now.? I never imagine zatai irin wann tunanin maiyasa kika bada aikin ma wann maid d in da batajin hausa. Tai maganar tana satan duban Ummul. Kafin ta kuma kwantar da murya daidai kunnen Anisa  I thought you said you ve everything under control.. looks like it s gonna backfire.. Hajiya Kwaise bazata yafe mana ba Neesa. Oh no.. I m scared. Mai zai faru idan tasa  yansandan su tafi damu.? This is all your fault Neesa. I shouldn t have involved myself in your plans. "

Anisa ta furzar da huci Har lokacin k usk us suke yayinda Mommy ta tistiye Vicky tana tambayar sai ta sanar da ita waye ya bata order.

Leenah ta kuma tambayar Anisa  Girl what do we do now.? Your grand plan turned out to be brainless. Are you that stupid Neesa. Didn t it occur to you hakan zai iya faruwa.?

 Oh shut up Leenah.! Banyi tunanin haka ba. You know why.? Because your stupidity is contagious.. Ke kika shafa mun shashancinki.

Ta k arashe daidai lokacin da idon su Mommy gaba d aya yayo kansu dan Vicky direction d insu take duban sanda Mommy ta titsiyeta.

Mommy taci gaba idonta kan su Anisa  Tell me Vicky. If you don t want to go to jail alone. Who s your accomplice. Who ordered you to frame my daughter in-law.? Tell me now.! Mommy ta k arashe cikin tsawatarwa.

Ganin haka yasa Anisa yin alama ma Vicky da yatsarta tana nuna mata Leenah cewa tace Leena ce.

"Hannu na rawa Vicky ta nuna Leenah  It s her.. She payed me to do a clean job. But believe me madam, I only accepted her offer because I desperately needed the money.. Please don t fire me. Have mercy on me.! Ta k arashe cikin kuka tana duk awa gaban Mommy."

Leenah ta saki baki cikin tsananin shock jin yanda aka aza mata laifin komai tashi daya. Ta soma girgiza kai tana duban Vickey  Me.? Hey excuse me.! What crap are you talking about.? Why would I do such a thing.. What could be my motive. I have nothing against her..! Tai maganar tana duban mutanen dake wajen cikin k ok arin kare kanta. Leenah ta tafi ta shiga jijjiga Vicky tana fad in ta bud e baki ta fad i gaskiya cewa ba ita ta sakata ba.

Vickey ta nuna credit alert da Leenah tai mata dan dama da account d in Leenah akai payment d in sabida account din Anisa yak i transfer kuma ba cash a hannunta. Leena tace akwai kud i cikin account d inta bari ta tura ma Vicky. Nan Anisa tace Tai payment d in 100k zata bata daga baya. Hakan yasa da Vicky ta nuna kud in da ya shiga account d inta sunan Leenah ya fito. Vicky taci gaba da fad in ta tura kud in ne zuwaga mahaifiyarta dake jinya dan sayen magani. Shiyasa ta amsa tayin da Leenah Tai mata cewa taje ta aje sark ar a d akin Ummul.

Leenah ta saki baki ta juyo tana duban Anisa wacce Tai kaman batasan meke faruwa ba.

Zata kuma magana Anisa ta dakatar da ita da fad in  Oh shut up Leenah.! Bansan haka halinki yake ba. Bansan zaki k ulla ma Ummul irin wann sharrin ba I shouldn t have invited you here in the first place.

Leenah ta saki baki tana duban ikon Allah jin yanda k awarta Anisa Tai incriminating dinta ta kuma aza mata laifin komai tashi guda.

Leena baki na rawa take furta  But.. But wait..

" Oh Leenah kowa yaga evidence da sunanki. Ke kika biyata Tai aikin without my knowledge. Amma nasan dalilin da yasa kikai haka k awata. You did it out of your concern for me. A tunanin ki zaki rama min abinda Ummul ta mun a SPA ne Shiyasa kikai haka, right.? "

Leenah ta kasa cewa komai sai duban k awarta Anisa da take da tsananin mamaki.

Anisa ta juyo ta dubi Mommy  Mommy dan Allah kiyi hak uri. I know Leenah.. I know my friend is not a bad person. Misunderstanding aka samu. Tai briefing Mommy kan abinda Ya samu fuskarta duk akan Leenah ta d aura laifin Har abinda ya faru a spa. Sam bata nuna ma Mommy tasan da plan d in Leenah na k ona fuskar Ummul ba Wanda ya juya nata fuskar.

Anisa taci gaba  Mommy Leenah thought she was doing it for me. Ta zaci hakan da Tai tamkar ta rama mun ne. Kinsan kishi irin na k awaye. Kishi take da Ummul zata k wace mata k awancenmu. Musamman da yau da tazo taga yanda nake da Ummul d in. Ta kuma duban Ummul  Ummulkhair please forgive my friend.

Muryar Mommy ta sinkayo tana fad in  Dama nasan za a rina. A yanda taketa k ok arin d aura laifin ma Ummul. She s the real perpetrator. I dont care if she s your Friend. Criminals are not welcome in my house. And this won t go unpunished. She must pay for what she did to my daughter.

Ta dubi d aya daga cikin ma aikatan gidan tace ta kira mata  yansanda. Matar ta jinin kai  Right away Madam.

Vicky sai kuka take tana fad in a mata rai. Yayinda Leenah mamaki ya hanata katab us.

Sai jan k afafun Ummul Vicky take tana fad in ta yafe mata.

Tsawa Mommy ta daka ma Vicky da fad in  Shut your mouth and get up from there! You are leaving this house right this instant. I don t have room for criminals like you in my house. Ta kuma jaddada mata sai ta fara mik asu ma hukuma daga ita Har Leenah.

Duk sai jikin Ummul yai sanyi. Yarinyar ta bata tausayi. Da alama cikin ma aikatan tafi kowa k arancin shekaru. Sann taji cewa da tai kud in da ta amsa wajen Leenah ta aika wa mahaifiyarta dake jinya ne. Sai ta tuna nata mahaifin dake kwance yana jinya. Ta tuna mak asudin zuwanta gidan itama yarda da auren da Tai sabida ta ceci mahaifinta dake jinya ne itama. Sann sadakinta shine kud in jinyar mahaifinta. Tabbas kowa zai komai dan ya ceci iyayensa. Sai taji kaman batada wani maraba da Vicky.

Cikin sauri Ummul ta juyo ta dubi Mommy kaman zata fashe da kuka take fad in Mommy tai hakuri ita ta yafe masu kar a kirawo  yansanda.

Da kyar Mommy ta hak ura da kiran  yansandan sabida rok on da Ummul Tai mata. Amma kam ba don Ummul d in ba da daga Leenah Har Vicky sun kwana ofishin  yansanda.

Mommy ta bada umarni ma babba cikin ma aikatan gidan cewa a raka Vicky waje da kayanta ta koreta. Ita kuma Leenah ko me kamanta securities suka kuma bari ta shigo gidan a bakin aikinsu.

Harda Anisa akaima Leenah rakiya waje. Sai kallon mamakin cin amanar da Anisa Tai mata take ma Anisar.

Anisa ta dubeta bayan Sun rage saura su biyu  Let me call you a cab for you..

D aga mata hannu Leenah tai alamun dakatarwa  Ki barshi bana buk ata. You know what Neesa ban tab a zaton zaki ci amanata irin haka ba. Ta ya zaki d aura min laifin da banyi ba. You planned the whole thing. Sann kin d aura min laifi kaman wata sakarai. You know what? I think you re right. I m stupid and that s why I remain loyal to you. Tana gama fad in haka tasa kai ta shige kaman zata tashi sama ba tareda ta kuma bi takan Anisa ba.

Juya ido Anisa Tai had ida furzar da huci kafin ta koma cikin gida.

"Nan ta tadda Mommy ta had a kaf ma aikatan gidan tana kafa masu warning. Ta dafa kafad an Ummul tace  She s my Son s wife. I expect each and everyone of you to treat her with absolute respect, Including you Anisa. Tai maganar tana duban Anisa da shigowarta kenan kafin taci gaba  The same respect da zaku bama D ana Haidar. Bana so makamancin abinda ya faru yau Ya kuma faruwa. Do I make myself clear.? "

Gaba d aya suka jinjina mata kai hadida amsawa cikeda risinawa

**

Bayan Ummul ta koma sashenta tana zaune saman darduma Ida sallarta kenan Anisa ta shigo da murmushi saman fuskarta.

Ummul bata nuna mata komai ba dan itama wann sassanyar murmushin wanda a baya Anisa ta d aukesa shashanci da gidadanci a halin yanzu shakkar wann murmushin take shine dai saman fuskar Ummul.

Ta zauna tana tambayarta an sha ruwa lafiya.

Ummul ta amsa mata da sakin fuska. Nan Anisa ta soma bata hakurin abinda Leenah Tai tana mai kuma tabbatar mata Lallai Babu hannunta cikin abinda Leenah da Vicky suka k ulla mata.

Murmushi Ummul ta kuma yi  Babu komai Anisa kar ki damu. Suma ban k ullacesu ba. Daga k arshe Allah Ya bayyana gaskiya. Ba wayona bane ba kuma dabarata bace. Allah ne Ya dube ni da rahamarsa Ya wanke ni daga

k agen da aka so min. Na kuma gode masa da Ya wanke sunana daga k agen sata. Ina kuma fata ya shiryi duk masu tunani irin nasu damu baki d aya.

Anisa ta jinina kai  You are a good person Ummul. You have a clean heart that s willing to forgive and forget. Yanda kika wanke kanki cikin hikima ya burgeni. I wish zan zama kaman ke.

Ummul ta murmusa  Duk wanda ya dogara ga Allah Allah ya isar masa. Kuma duk wanda yaji tsoron Allah Allah zai samar masa mafita. Ba yin kaina bane Allah yakan wanke bayinsa da akai masu k age ba tareda sun aikata laifin ba. Kaman yanda Ya wanke Ummuna Aisha (RA) daga k agen da azzalumai suka mata. Kaman yanda Ya wanke Annabi Yusuf (AS) daga k agen da aka masa. Kaman yanda Ya wanke bayinsa muminai da dama daga k agen da aka masu. Kaman haka yanke wanke bayinsa da basuda hakki. Na gode masa da ya wanke ni daga k agen da aka min ba tareda hakki ba. Amma ni Ummulkhair banida wani wayo. Saidai Inaso mutane irinki da Leenah su fahimci English is just a language and not a means to measure one s intelligence or education. Snn duk wani wayewar da yai karo da koyarwar addininmu da d abi u da kyawawan al adunmu ba sunansa wayewa ba. Tai maganar murmushi saman fuskarta.

Baki sake Anisa ke kallonta  So you can speak English.?

Ummul ta murmusa  Ba sosai ba abinki da Wanda taje makaranta na gwabnati.

A hankali Anisa ke jinjina kai  Na yarda da duk abubuwan da kika ce. A yau kin kuma tabbatar min da haka.  Ta kamo hannayen Ummul  Mommy tayi zaton ni zan koya miki abubuwa musamman zamantakewan rayuwar civilized world. But it turned out ni ce wacce ke koyo wajenki. Yau na raina duk wani exposure na Ummul.

Ummul ta girgiza kai  A kullum ko wani shafi na rayuwar mu darasi yakan bude mana dan mu koya. Kullum cikin koyo muke a duniyar nan. Kaman yanda muke had uwa da mutane iri daban daban. Ta d an murmusa  Nima ina koyo daga gareki Anisa.

Shiru Anisa Tai sai kuma ta saki murmushi da yafi kama da yak e.

Tin daga wann rana Ummul ta samu sanyin abubuwan da Anisa ke mata. Sai ta koma kaman tana shakkan Ummul d in koda bata nuna a fili ba. A kwanakin da alama Anisa ta maida makaman yak inta.

**

Kano&

Batai k asa a gwiwa ba dukda fargabn abinda ka iya zuwa yazo ta nufi gidan Hajiya Asshe. Juyin duniya Umma tayi amma masu gadi sun hanata shiga sabida dokan da Asshen ta basu tin kwanakin baya.

Asshe na kitchen tana had a

39 / 103