AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   76 / 103

225K to 228K   out of 306.8K words

a wann rayuwar. A lissafi Ummul ta cika watanni uku tin bayan da k addararren Aurenku ya k are.. Hakan na nufin ta fice daga iddarka.. Ni kuma yanzu zan tafi na gina nawa soyayyar cikin zuciyarta& All my sacrifices are finally going to pay off A fili k arasawa yai ya dafa Haidar kad an fuska fal damuwa. Cikeda kulawa yake furta  Haidar bazan Barka ka koma irin rayuwar k uncin da ka fuskanta a baya ba. Ka tafi ka nemo matarka yanda ta shiga ta fita.. Ni kuma zan tafi na nemo maka Dareen yanda ta shiga ta fita ko dan wann innocent soul d in dake cikinta. Ya k arashe damuwa sosai saman fuskarsa.

Haidar bai iya ce masa komai ba sai shafe fuskarsa da yai da tafukan hannayensa.

A haka Hisham ya tattari files d in da ya shigo dasu ya fice fuskarsa d aukeda mugun murmushin da ba kowa ke iya fahimta ba. Cikin zuciyarsa yaci gaba da ayyana Ummul tasa ce a halin yanzu.

Da wann farin cikin Hisham ya taho garin Bauchi zuciyarsa fari k al da nufin ya tafi Neman Dareen a zahiri kuma wajen Ummul yazo da niyyan k ulla soyayyarsa.

Babu Wanda yasan da zuwan nasa. Hajja batai mamaki ba dan dama ya saba mata irin wann zuwan na bazata. Saidai ta kula wann karon da wani irin farin ciki yazo maras misaltuwa.

Suna cikin gaisawa da Hajja yake tanbayarta  Hajja nace ina Ummul kuwa..?

"Bata kaiga basa amsa ba suka hango Ummul da fitowarta kenan daga babban parlorn da Hajja ke sana arta na d inki, nan suka hangota tana tafiya da kyar tana dafe garu tana kame kanta dake matuk ar juya mata.. Kafin suyi wani aune jiri ya kusan kaita k asa. Hajja ta nufeta hankali tashe ta tallafota tana ambaton sunanta dan tuni idanunta sun soma juyawa."

SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!*

*51*

*©þSameena Aleeyou& *

"Bud e ido tai sai gani tai fanka na wainawa saman kanta, ta yunk ura zata tashi sai taga igiyar drip daure hannunta. Nan ne ta fahimci saman gadon asibiti take. Ta waiga kad an sai taga wani mutumi da ko shakka Babu Likita ne tsaye daga gefe hannunsa rik eda file kansa kife kaman yana rubutu."

Hankalinsa naga abinda yake ta sinkayo muryarsa yana mata sannu.

Ya k arada  Malama Ummulkhair right.? Ta jinjina kai kad an.

 Kina Jin wani pain..? Akwai yanda ke Miki ciwo.? Ya k arashe yana mai janyo kujera had ida zama gefen gadon.

Ta d an girgiza Kai sai ta dafa kanta kad an  Kaina na d an juya min sann yana ciwo. Sai ta dan tab a gefen cikinta kad an tace  Ciki na na ciwo kad an ta gefe.

Ya jinjina kai  It s normal to experience such pains in early stage lokaci zuwa lokaci.

Bata gano abinda yake nufi ba amma tana Jin heartbeat dinta na k aruwa da sauri. Kaman yasan tana jiran Karin bayani ya soma jero mata wasu tambayoyin.

 Amma& Yaushe rabonki da kiga al adarki.? Yai tambayar fuskarsa na nuna alaman tsananin kulawa.

Sai ta kalleshi da mamaki. Ganin irin duban da ta masa yasa shi d an sakin murmushi  Kinga kar ki ba ma tambayar wani manufa na kula kaman.. Baki fahimci meke damunki bane bayan kin d ebe watanni cikin yanayin..

Kanta ya kuma k ullewa.. Ta d an girgiza kai  Dr.. Meke faruwa dani..? Dan Allah Ka mun bayani.. Ta fad i duk a d an tsorace

Jinjina kansa yai yana kuma tabbatar da hunch d insa. Sai Ya dan girgiza Kai kad an yace  Kar ki damu ba wani abin tashin hankali bane.. Amma ki amsa min tambayata first. When last kikaga menstrual period d inki.?

Sai ta soma tunani.. Ita zata iya cewa damuwa da tashin hankalin da ta tsinci kanta ciki yasa ta ma mance wani abu wai shi menstrual period. Ta girgiza kai tace  Ni.. ni & Ni ban sani ba.. Ta basa amsa tana d an kauda fuskarta.

Dr ya rage girman idanunsa had ida girgiza kai kad an cikeda mamaki  Is it possibile.?

Ta d an dubesa fuska d aukeda alamun k osawa wann karan dan Likitan Ya fara hawa kanta da tambayoyinsa marassa kan gado.

Sai Ya dan tab e baki kad an yace  Ina mijinki.?

"Tambayar ya kuma tunzurata, ya fama mata gyambon dake cuziyarta, ta kuma jin wani k atutun bak in ciki ya tokare mata mak oshi. A kufule tace  Bani dashi.! "

Sai ya kuma girgiza kai cikeda mamaki  Baki dashi kuma..? I.. thought mutumin can da ya kawoku keda mamarki mijinki ne..

 Na fad a maka bani da miji.. Ni Ummulkhairi banida wani miji..! Ta fad a kaman zata fashe da kuka.

"Likitan ya dan jada baya kad an yace  Ok.. Ok easy.. Sai ya soma bud e file d in dake hannunsa yana duban file d in yake fad in  Amma sakamakon gwaje gwajen da muka Miki Ya tabbatar kina d auke da juna biyu har na tsawon watanni uku which is why kikaji Ina miki tambayoyin da nake miki.. Amma sai na fahimci wann shine karonki na farko shiyasa Har juna biyun Ya shafe tsawon wann lokacin a jikinki tareda kin fahimta. Although pregnancy is not typically visible at 3 months, especially in a first pregnancy.. Most women begin to show in the second trimester, around 16- 20weeks.. However,&  Aya yai ma kalamansa sanda ya d ago yana dubanta dan idanunsa naga file din dake rik e hannunsa yaketa wad ann bayanan da sam babu mai saurarensa balle fahimtarsa ga dukkan alamu."

Abu d aya zata iya cewa taji cikin kalaman nasa shine juna biyu bayan wann kalman bata sake fahimtar komai ba&

Dr ya dan girgiza kai yana dubanta  Hello.. Are you with me..? Ya fad i cikin k ok arin dawo da ita daga duniyar da ta b ace ciki.

Dubansa take tana girgiza kai tana jin kaman duniyar ke juya mata  Ju..juna.. biyu..!! Ta fad i labb anta Har rawa suke.

Ta kuma girgiza kai cikin rashin fahimta  Mai.. Mai hakan.. yake.. Nufi Dr.. Ni.. Ni Ummulkhair.. Juna biyu..? Ta k arashe tana nuni zuwa gareta hannunta na matuk ar rawa haka ma muryarta.

Dr ya jinjina Kai alamun tabbatarwa  Of course. You are 3months pregnant.

Sai ta soma girgiza kai  A a.. A a baku gwada daidai ba Likita& Dan Allah ka sake gwadawa.. ni banida komai..

Cikin tsananin damuwa mai gauraye da tashin hankali take maganar.

Dr ya shiga nuna mata sakamakon yana fad in  Gwaji na jini mukayi wanda ya tabbatar da hakan.. Ina shawartanki da ki rage stressing kanki sann ki rage shiga damuwa ko dan lafiyarki da lafiyar abinda ke cikinki& I ll prescribe some medications for you.. Sai a kiyayesu.. Ya k arashe yana k ok arin mik ewa.

Kuka ta fashe dashi tana girgiza kai  A a Dr.. A a..Dan Allah ka cire mun cikin.. Wllhi bana so.. Dan Allah ka ceceni..

Shima wann karon a kufule yake dubanta  Bakiyi kama da maras Kamun kai ba da nace ta wani hanyar daban kika samo.. Amma ko ta ina kika samu ki sani bama cire ciki a nan.. Excuse me.. Ya k arashe yana k ok arin ficewa yayinda Kukan Ummulkhairi Ya karu Wanda hakan yasa Hajja dake daga bakin k ofan d akin shigowa ba shiri.

Dr ya dubeta  Yauwa.. Akwai magunguna da zan rubuta mata dan Allah sai a kula ta sha su akan kari..

Hajja ta jinjina kai  Eh akwai yarona da Ya kawomu yana waje.. Zai sayo magungunan. Bai kuma tsayawa sauraronta ba ya fice.

Hajja Tai sauri ta k arasa ga Ummul dake cazgan kukan kamar wacce aka aiko mata sak on mutuwa.

 Ummulkhair.. Jikin ne..? Ta tambaya cikeda damuwa.

Shiru Ummul bata bata amsa ba sai kuka da take tana girgiza kai.

Hajja ta dubeta sai ta dubi takardan dake aje saman drawer dake gefen gadon. Nan taga pregnancy test ne kuma ya nuna positive. Ji Tai tamkar jinin jikinta Ya k afe. Taji kaman an d add aure jijiyoyin jikinta.. Ummulkhair juna biyu ke gareta.. Innalillahi wa inna ilaihi raji un.. Duk abinda ke faruwa da Ummul tono mata nata bayan yake.. Tamkar dai reputation ne na abubuwan da suka faru da ita shekarun baya.. Dama a yan kwanakin taso ta fahimci hakan saidai

tayita kore tunanin abin dan guje ma tono nata bayan. Sabida duk abinda zaisa ta waiwayi baya guje masa take. Saidai ga dukkan alamu duk yanda kaso guje ma wani abin sai Ya tono kansa a wasu lokutan..

"Hajja ta fad a duniyar tunanin abinda Ya faru da ita shekarun baya. Auren ta da Mahaifin Uban cikin Ummulkhair wato Aliyu Maitama kuma mahaifi ga tilon D anta Hisham.. Sai kuka da muryar Ummul ta sinkayo tana fad in  Dan Allah Hajja nikam bani son wann cikin.. Dan Allah kar ki bari na haifosa.. Dan Allah kisa likitocin nan su ciresa.. Ki taimake&  Batakai aya ba Hajja Tai k arfin halin tattaro k arfinta ta rufe bakin Ummul da k arfin gaske  Kul. Ko da wasa kar na sake jin kalamai masu kama da wann daga bakinki Ummulkhair.. Da iliminki da karatunki.. Da addinininki..? Haba Ummul this is not like you.. Ba haka Ummul d in da na sani take tunani ba.. Mai hak uri a duk halinda ta tsinci kanta ciki.. Kinyi hak uri a lokacin da kika fuskanci k alubale na JINKIRIN Aure da fashe fashen Aure. Kin karb i k addararki kuma in sha Allah kin dace da jarabawa. Toh ki sani yin Aure ba yana nufin k alubale da jarabawa Sun k are bane. A a wani sabon babi na karatu da jarabawa ne rayuwa ta kuma bud e miki.. Shi kansa zaman auren karatu ne kaman yanda mutuwar Auren zai iya zama jarabawa a gareki. Ki sani ba akanki aka fara mutuwar Aure ba haka zalika ba akanki za a daina ba& Kowa da yanda rayuwa take zuwa masa.. Kowa da irin k addararsa a rayuwa. Kowa akwai abinda aka sanya masa jarabawarsa da k alubalen sa cikinsa. Ta dan numfasa sai Ta kamo hannayen Ummul cikin nata wacce Har lokacin hawaye ke kwaranya mata  Duk abinda kikaga Allah Ya hukunta ma bawa, Allah yasan dalilin da Ya k addari aukuwar hakan.. Taho nan.. Ta k arashe tana rungumo Ummulkhairin daga zaune.. Sosai Hajja ta rungumeta zuciyarta fal tausayinta. Cikin zuciyar nata take fad in  Ko ni da suka sheganta nawa cikin ban ciresa ba.. Dan haka Bazan tab a bari makamanciyar tunani irin wann yayi tasiri a zuciyarki ba. A fili kuwa murmushi take tana rungume da Ummul d in   Ya ya rahama ne.. Kyauta ne mai girma Wanda Allah kad ai ke bama wanda yaso cikin bayinsa.. Insha Allahu zaki haifo abinda ke cikinki lafiya kuma zai zamto mabudin alkhairi da sauyin rayuwa mai inganci a garemu baki d aya.. "

Cak Hisham dake daga bakin k ofa hannunsa rik eda ledan maganin da Dr yai prescribing ma Ummul yaja Ya tsaya sakamakon kalaman da yaji na fita daga bakin mahaifiyarsa.. K iris Ya rage ledan dake hannunsa bai sunce Ya fad i k asa ba& Mai hakan yake nufi..? Ummulkhair ciki ne da ita..? No.. No way.. Allah yasa ba Daidai yaji ba. Babu wani ciki tattare da ita.. Haidar bazai masa haka ba..! Watanni uku Sun cika ta fita daga iddan Haidar bazai yuwu ace ciki ne da ita ba.. It can t be& It definitely cannot be. Bai sadaukar da komai dan ya rasata daga k arshe ba..! Jikin Hisham yaci gaba da rawa a daidai sanda ya kuma sinkayo muryar mahaifiyarsa tana tabbatar da juna biyun dake jikin Ummulkhair.. Zufa yaci gaba da karyo masa ta ko ina.. Da baya ya soma komawa ba tareda ya iya shiga d akin ba.

A nan cikin d akin kuwa Hajja duk ta zak u sai d auki take. Bata san dalili ba amma sai ta tsinci kanta cikin matsanancin farin ciki gameda samuwar cikin. Ji take tamkar zatayi jika nata na kanta dan  ya ta d auki Ummulkhair koda a zahiri abinda ke cikin nata Ya kasance tsatso kuma jika ga mutanen da suka zamto silan durk ushewar rayuwarta.

A b angaren Hisham kuwa tashin hankali maras misaltuwa Ya shiga. Bayan dawowarsu gida can k uryar d aki Ya k ule ya shiga dunk ule hannunsa yana sakin huci.. Ya bigi garu da hannun nasa yana furtawa a hankali cikin karaji  Damn you..! Damn you Haidar..! How dare you..!How could you do this to me.! Yaci gaba da sakin huci gumi na tsartsafo masa. Ji yake da zaiga Haidar gabansa da Ya shak esa da iyaka k arfinsa. Yana nan a haka wayar Ania Ya shigo masa.. Ya dubi wayar yana ci gaba da sakin huci kaman bazai d aga ba. Sai Ya koma ya zauna ya janyo wayar ya daga ba tareda Ya daina sakin huci ba.

Yana d agawa daga d aya b angaren Anisa tace dashi  Ango ka sha k amshi.. I know by now ka fayyace ma Ummulkhair irin soyayyarta dake lullub e cikin zuciyarka.. Watak ila Har an fara zancen saka muku rana. Toh nima dai Albishir na kira na maka dukda nasan kace ya kamata mu daina kiran juna tinda hak armu na raba tsakanin Ummul da Haidar ya cimma ruwa.. Na kiraka ne na sanar dakai cewa Aunty Kwaise taje Har Kano ta d aukoni ta dawo Dani gidanta.. Kuma kasan mai yanzu treating dina take da kyau har wani respect naga tana bani da kula na musamman.. Yanzu bata min kallon shashasha kaman yanda take min a baya.. Na tabbata bazai jima ba zan saye zuciyarta kamar yanda Ummul ta lashe zuciyarta. In no time zata aura min d anta dan wllhi sosai ta d aukeni da mahimmanci wann karon.. Finally burina zai cika Hisham.! Ta k arashe tana  yar tsallan murna.

 Shut up.! Shut the hell up.!! Hisham ya daka mata tsawa kafin yaci gaba cikin huci  Kina jina idona idon tsinannen Haidar d in nan sai kashesa..!

A d an tsorace Anisa ta waro ido waje kaman Hisham d in na kallonta tace  Excuse me.. Mai kake cewa.. Kan wane dalili zaka kashe Haidar dina..?

 Shut up Neesa..! Kar ki sake ambato min sunansa..! That Imbecile made sure ya bar wani babban dalili da zai hana k arewar alak a tsakaninsa da Ummul..!

Anisa ta girgiza kai cikin rashin fahimta  Ban fahimceka ba.. Alak a kamar ya..?

 He made sure ya bar gudan jininsa tattareda ita..! He ruined all my plans.. All our plans. Duk abinda muka jima muna shiryawa zai zama aikin banza..!

Anisa da taji maganar a bazata cikin rashin fahimta tace  What do you mean..? Mai kake nufi ya bar gudan jininsa&

So kake.. Kace min like.. Ummul is pregnant..?

Hisham ya furzar da huci  So kike na maimaita miki.. He made sure he impregnated her kafin ya rabu da ita.. I hate him..!

Anisa ta soma girgiza kai  A a.. We can t let this happen.. Haidar can t find out about this.. No one should find out bout this.. She can t be pregnant.. She can t give Haidar a child do you understand Hisham.. Dole muyi komai domin kawar da wann cikin.. No matter the cost..!

Hisham baice komai ba sai huci da yake ci gaba da furzarwa.

Anisa cikin tsananin damuwa da tashin hankali taci gaba  Hisham wann cikin shi zai sake k ulla igiyoyin Auren Haidar da Ummul da mukayi komai domin tsinkasu. Idan har muka bari wann ciki ya tabbata har aka haifosa kashinmu ya bushe.. Dan zamu rasa komai.. Dole muyi komai domin kawar dashi kuma kaine zakayi dan kaine kake tareda ita..

 Mai kike nufi..?

 Ina nufin duk yanda za ai mu cire wann cikin.. Bazai yuwu a haifosa ba..

 How..? Ta ya hakan zai kasance.?

Anisa tace  Kawai ka kaita asibiti a cire ko ka saka mata magani cikin wani abin sha ta sha Ya fice.. Is as simple as this.

"Wann karon murmushi Hisham yai kafin yace  Lallai na

76 / 103