AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   63 / 103

186K to 189K   out of 306.8K words

an Wanda hakan Ya dawo da hankalinta gareshi. Yai mata alama da ido da ta k araso ta zauna.

Ba musu ta k araso saidai idonta a k asa dan ita dai tinda ta sanya masa riga ta kuma kasa had a ido dashi.

 Can I take my drugs& now.? Yai maganar yana mai kai dubansa ga agogon bango dake manne d akin. Alamun yana nuna mata lokacin shan maganin zai shige.

Sai ta dubi magungunan ta girgiza kai  Ban.. Ban san ya zanyi ba.

Ya tsareta da ido sai yace  Come close.. I ll show you.

Da dan dubesa sai ta d an matso kusansa kad an. Shi kaw har lokacin ya tsareta sosai da ido  Closer.! Ya furta a hankali. Ta kuma dubansa sai ta d an kuma matsowa.. Saida ya tabbata ta matso kusansa sosai kafin yace ta d auko parantin maganin ya nuna mata. Ita dai jinsa kawai take amma da ganinta zaka fahimci a tsorace take.

Ta d auki glass cup da bottle water da mutumin ya shigo dashi ta soma tsiyayawa hannunta sai rawa yake alamun nervousness. A haka take yunk urin kai ruwan da maganin bakinsa Har lokacin hannunta bai daina rawa ba. Shi kaw Haidar sosai ya tsareta da ido. Charaf yai grabbing hannunta. Wanda hakan Ya sanyata d ago ido tana dubansa a d an tsorace.

Shid inma ita yake kallo  Just.. relax..! Ya fad i yana mai kai hannun nata saitin bakinsa har lokacin idonsa akanta.

A haka dai ta ko k arta ta basa maganin. Akazo maganar abinci zata tashi nan ma yace bazai iya moving arms dinsa ba she should feed him. Haka dole ba yanda ta iya ita ta basa abinci. Ko wani motsi nata kan idon Haidar. Ranar dai ta zamto tamkar personal nurse d insa. Dan duk wani abu da suke na kula da majinyaci baya bari suyi ita takeyi saidai Wanda yafi k arfinta ko layin ma aikatan lafiya ne kawai. Dik yanda taso ta zille ma Haidar Ya kasa barinta.

Can dare tana kishingid e saman sofa shi kaw sai kallonta yake daga nan saman gadonsa ta majinyata. Nan yaga ta tak ure waje guda ta k udindune cikin hijab dinta.

A hankali Ya mik e daga saman gadonsa da kyar. Ya tako zuwa yanda take. Zama yai gefenta yana k are ma fuskarta kallo. Kallo irin Wanda bai tab a tsayawa yai mata ba. Hannu yasa yana zare Hijab d in hakan yai daidai da juyin da zatai. Take yaji wani abu ya tsargar masa kaman electric shock. Nan yake binta da kallo head to toe. Ya jima sosai yana k are mata kallo kafin ya karkatar da ita kad an Ya kwanta nan gefenta kasancewar kujerar mai fad i ne sosai. Ya matso da ita cikin jikinsa Ya janyo abin rufuwar Ya rufa musu.

**

A can gida kuwa yanda Anisa taga rana haka taga dare. Sai kai komo take a d aki ita kad ai tana safa da marwa. Ta lallaba ta tafi d akin da aka sauki Amminta.

Ta tsaya tana kallon mahaifiyar nata dake sharan bacci tana tunanin hirarsu da Mommy da ta sinkaya a asibiti gamed auren Haidar da Ummul.

Kodai ta tashi Ammi ne ta sanar da ita taji komai. Tasan komai a halin yanzu.? Toh Amma Hisham yace ta bar masa komai.. Ya mata alkawarin zai cire Ummul daga rayuwar Haidar ko ta halin k ak a.. Idan ta sanar da Ammi wani abu yanzu shirinsu da Hisham ka iya b aci. Bazata bari hakan ta kasance ba. Sauri sauri ta koma nata d akin. Ta kagu gari ya waye ta bullo da wata hanyar da zata samu taje ta duba Haidar da Ummul tinda Haidar dai ya mata iyaka da asibitin.

**

Asubahin fari ta farka tana mamakin yanda bacci mai nauyi ya dauketa itada take yawan farkawa cikin dare. Nan tajita cikin jikin mutum kuma. Zuciyarta ta tsinke. Ita tsoro ma abin ya bata dan Sam bata kawo a zuciyarta majinyaci irin Haidar ka iya mak alewa gefen kujera har yayi bacci irin haka ba.

Ta yunk ura a tsorace zata tashi sai ta sinkayo muryarsa yana sakin  yar k ara had ida rik e gefen hak ark arinsa. Su duka biyu duban juna suke kasancewar akwai hasken dim-night cikin d akin.

Tai saurin mik ewa tsaye daga kan kujerar tana kuma kallonsa.

Ganin da gaske na cikin pain dan har lokacin bai daina tamke ido yana dafe hakarkarinsa ya sanyata saurin duk awa gabansa tana tambayarsa  Da zafi ne.? Na bige maka ciwo ko.? Dan Allah kai hak uri wllhi ban kula bane.! Ta k arashe maganar kaman mai shirin kuka.

Sai Ya daina tamke idon da yake yana Ware idanunsa a hankali yana kallon yanda take magana kaman itace cikin pain d in.

Ta d an saci kallonsa  Kai hakuri zan tabbata na taho da abin rufuwa yau in sha Allah.

Ya tsareta sosai da ido kafin ya girgiza kai kad an had ida lumshe idonsa  It s fine.. Ya fad i a tak aice.

Ya mik e a hankali yana fadin  I.. Will use the bathroom.. It s subh prayer time already..

Ta jinjina masa Kai a hankali  Kana buk atan taimako na.?

 No I.. Can manage. Ya fad i yana dingisawa har ya nufi hanyar bathroom din.

Yana shigewa ta zauna had ida sauk e deep breath. Hannunta na rawa ta janyo mayafin da ya rufesu dashi. Sai ta runtse idonta da sauri wai yau ita Ummul ke bacci mayafi guda da Haidar.. Kunya ne.? Damuwa ne? tsoro ne? Duk sai ta ma rasa mai ke mata yawo cikin zuciyarta.

A b angaren Haidar Shima haka nan ya lumshe idonsa a bathroom abubuwa fal zuciyarsa. Cikin zuciyarsa yake tuhumar kansa  What s wrong with you Haidar.? Why are you so soft with her..? Take zuciyarsa ta shiga tuno kalaman mahaifiyarsa garesa  Ka ba ma kanka dama da Ummulkhair.. Kamin wann Haidar koda shine abu na k arshe da zan buk ata wajenka.

A fili yake furta  Sabida Mommy. You are doing it for Mommy and because of Mommy.. Kaman yanda ta buk ata.

Da safe kuwa su duka biyun yanayinsu ya dan sauya bayan baccin da sukayi tare musamman ma Ummul wacce ta kasa had a ido dashi. Gaisuwa ma k asa k asa tai masa. Haidar nata karantarta.

Sassafe take shirin tafiya gida dan ta samu ta kintsa kanta kafin ta dawo. Zata fice ta sinkayo muryarsa  Khairy.!

Cak ta tsaya tana sauraron sunan da ya kirata dashi.

Haidar yaci gaba  Don t take long.. And.. kar ki sake ki zo da wani abin rufuwa asibitin nan.

Sai ta dubesa da mamaki  Amma maiyasa.?

Ya tab e baki kad an  Hospital rules.!

Ta jinjina Kai a hankali tace  Shikenan bazan zo dashi ba

Haidar ya jinjina mata Kai sihirtaccen murmushi saman labb ansa. (Kunji wani salon wayo wajen Haidar. Wai asibiti ta hana zuwa da abin rufuwa daga gida.)

Ita dai Ummul Haka ta fice tana mamakin wann wane irin asibiti ne masu tarin dokoki da k a idodi.

Bayan ficewar ta da kad an Anisa tai knocking a k ofa. Duk a tunaninsa Ummul ce ta dawo. Kai tsaye ya bada izinin shigowa.

Ga mamakin sa Anisa ya gani rik eda jakan kaya. Ya tsareta sosai da ido alamun yana jiran ba asi tinda yasan ya mata iyaka da asibitin.

Ta k ak aro murmushi tana masa gaisuwar da bata samu amsa ba.

" What are you doing here? I thought I made it clear to you&  Saurin katsesa tai ta hanyar d ago masa jakar Kayan  Kayan Ummul& Mommy ce ta Aiko ni na kawo.. Sai ta d an saci kallonsa  And.., I& wanted to check how you ve been holding up.. Laifi ne hakan..? After all, we are cousins. "

Katseta yai  I just don t want you here.. Don t you get it

Kuka ta fashe dashi tana mai barin d akin. Ta rasa mai tai ma Haidar yake mata irin wann kiyayya.. Toh kodai ya fahimci da saka hannunta ne a had arin da ya samesa.? Dole ta nemi Hisham su san ta yanda zasu bullo ma al amarin.

**

Hisham ya dubeta sai kuma ya girgiza Kai yana murmushi  Kar ki bani dariya mana Neesa. Quite alright Haidar na zargin had arin mota da ya samu shiryayyen abu ne.. Amma ina mai tabbatar Miki ba kece yake zargi ba.

Anisa ta dubesa ta d an girgiza kai  Ta Ya ka tabbatar da haka.? Sann waye yake zargi.?

Hisham Ya murmusa  Wani hujja yakeda shi da zai zargeki.?

Shiru bata basa amsa ba.

Hisham yaci gaba  A kalaman Haidar cewa yayi yana zargin wani ne dake boyayyen agenda akansa. Waye keda dalilin ganin bayansa.?

Shiru bata amsa ba.

 Dareen.! Ita ce kawai takeda motive na hallak a Haidar tinda ta rasa shi bazata bari wata ta same shi ba. Haka ne.?

A hankali Anisa ke jinjina kai.

Hisham yaci gaba da murmusawa  Which is why dole na cimma Dareen kafin Haidar Ya cimmata.. Ya kaikaito sosai yana duban Anisa  Duk abinda nakeyi.. Everything is calculated. Ki bar mun komai kaman yanda na fad a.. Aikinki kawai shine ki saka ido akan Haidar da kuma Ummul.

Ta rausayar da ido  But it is not as easy as it seems. Haidar is making it difficult.

Ya kurbi drink dake hannunsa had ida d age kafad unsa kad an ya tabe baki  You must do it. You don t have a choice. Find a way to keep an eye on those two

Ta shiga jinjina kai a hankali tana furzar da huci.

Basu ida maganar ba wayar Hisham tai ruri Haidar ke kiransa.

Ya murmusa yana duban wayar  Speak of the devil& he shows.! Ya furta a fili kafin ya d aga kiran.

Bayan Sun gaisa irinta abokai Haidar yace  I sent you an email.. Since you can t come to visit.

Ya murmusa  Haba abokina ba haka bane.. Kasan asibitin naku ne na turawa. Komai d an k aida.. And work s been too demanding lately.. Musamman da yake baka nan. On the other hand ga neman Dareen da nake. Kasan bazan tab a barinta ba sai na nemota ta biya abinda ta aikata ma abokina.

 Speaking of Dareen. Are you free?

Shiru kaman bazai amsa ba Ya soma yan kame kame Haidar Ya katse sa  You know me. I don t take no as an answer. Ina jiranka. Daga haka katse kiran yai.

Duban Anisa yai yana huci. Cikin zuciyarsa yake ayyana Ya tsani yanda Haidar keyi kaman wani boss d insa bayan cewa ko a haife ne shine gaba da Haidar d in..

Anisa ta katse shirun da fad in  See Kai gashi yana nemanka amma ni cewa yake anyi restricting zuwan visitors.

Hisham Ya furzar da huci  Kinsan meye matsalar?

Anisa ta girgiza kai alamun a a.

 Bazai yuwu Ummul ta ganni wajen Haidar ba all our plans zasu lalace ne. No Ummul bazata ganni wajen Haidar ba. It will be a disaster.

Anisa ta murmusa  But this is the perfect time da ya kamata ka visiting Haidar because Ummul bata wajensa ta tafi gida. I believe ma Shiyasa ya samu chance na kiranka.

Hisham yace  You sure.?

 Hundred percent.! Ta basa amsa tana mai jinjina kai.

 Perfect! Yanzu abinda zaayi kiyi maza ki tafi gida ki rik eta ki hanata barin gida Har sai nayi alerting naki. Ma ana sai na bar wajen Haidar.

Anisa tace  An gama Barinyi sauri na tafi kafin ta fito nasan sai ta tsaya tayi wanka tayi wasu abubuwan.

Daga haka sukai sallama da Hisham. Shi Ya nufi asibiti wajen Haidar ita kuma ta nufi gida wajen Ummul.

A can gida kuwa Mommy sai nan nan da Ummul take tana fad in maza maza ta gama shiryawa driver ya maidata. Mijinta majinyaci ne bai kamata ta barosa shi kad ai ba. Asshe kanta sai mamaki take ganin yanda Mommy keyida Ummul. Lallai Anisa tayi gaskiya da tace idon Mommy ya rufe akan Ummul. Gani take kaman an canza mata  yaruwar tata da gaske ne. Gaba d aya Mommy ta tashi daga Aunty Kwaise da ta sani ta koma wata abu daban. Ita kanta Asshe lamarin tsoro Ya fara bata. Ta zuba ma sarautar Allah ido ta kasa katab us.

A haka Anisa ta iso gidan ta taddasu sai karantar Mommy take tana ganin yanda take ingiza Ummul tayi ta tafi wajen mijinta. Makirin Murmushi Anisa tai tana jinjina kai dan har ta hasasho ta yanda zata tarwatsa Auren Haidar da Ummul. Muddin ta fayyace ma Ummul komai zata fahimci Hajiya Kwaise Maitama azzalumar mace ce ba soyayyan gaskiya take nuna mata ba. Kawai tana mata duk abubuwan da take ne don amfanin kanta da D anta. Tabbas Ummul zata tsani Kwaise da tsinann auren da tai ma da d anta Wanda boka Ya had a. Ta k arashe tunanin tana mai kecewa da Makirin murmushi.

A k ofan fita daga sashen Mommy Anisa ta cimma Ummul. Suka sakar ma juna murmushi had ida gaisuwa.

"Anisa ta k arada  Ba dai har zaki wuce ba.? Kafin Ummul ta kaiga bata amsa ta kuma sakin murmushi tana mai dafa kafad an Ummul d in  It s fine, Ya kamata ki tafi kin baro mijinki shi kad ai& I Miss having you around Ummul.. Kinsan bahaushe yace sabo turken wawa "

Suka murmusa a tare kafin Anisa ta mik a mata jakan hannunta  Ga wann kar na rik eki da surutu.

Ummul ta d an girgiza kai kad an cikin rashin fahimta  Ta mecece.?

 Kayanki ne a ciki. Nayi tunanin na kai miki su asibiti sanin cewa zaki buk ata amma sai mijinki Ya koreni dasu.. Kamar dai ko yaushe. Ta k arashe tana mai k ak aro murmushi.

Jikin Ummul Ya d anyi sanyi  Kiyi hak uri Anisa& 

"Saurin dakatar da ita Anisar tai  No no.. You don t have to apologise for his behaviour. Kar ki samu damuwa.. Nasan Haidar since childhood.. He s rude, arrogant, short tempered.. and sometimes unpleasant to be around.. Ki yarda dani, idan da sabo na saba da halin d anuwana.. "

Da mamaki Ummul ke dubanta dan ko ba auren soyya sukai da Haidar ba sosai taji zafin kalaman da take fad i kansa. Amma sai ta danni zuciyarta ta murmusa  Baki tunanin kalaman da kike sunfi kama da cin fuska.?

Shiru Anisa batace da ita komai ba.

Ummul ta murmusa had ida dafa kafad ar Anisa  Kar ki damu banyi fushi ba. Dan dik abinda kika lissafo gameda shi kwalliya na d aukesu. Domin kaw sosai suke k ara masa k warjini da birgewa. Ta k arashe murmushin nan nata dake tunzura Anisa saman fuskarta.

Murmushin da yafi kama da yak e Anisa ta k ak aro  Of course. Haka ne.. Let me walk you to the car.. Ta k arashe tana mai kamo hannun Ummul d in suka nufi mota.

A hanya Anisa ke ci gaba da fad in  Mutanen gidan nan sunyi kama da mutanen kirki koda ahalin ya kasance birkitaccen ahali mai tarin gib i.. Haka ne.?

Ummul ta dubeta cikin rashin fahimta.

Anisa ta murmusa  Ko wani d an adam yanada sirrikansa.. Amma akwai wasu abubuwan da sirri baida muhalli cikinsu. Kamar dai Aure. Haka ne.?

Ummul ta kuma girgiza kai tana karantar yanayin Anisa. Tana danganta maganganun Anisa da tunanin kodai Anisa tana so ta sanar da ita cewa tasan yanda akayi aurenta ne.? Amma batada wani sirri da ta b oye ma Haidar gameda aurensu face iyaka da Umma tai mata da d aukacin ahalinta Har na tsawon watanni uku ciki harda mahaifinta dake kwance yana jinya. Bata Ida tunanin ba ta kuma sinkayo muryar Anisa daidai sanda suka isa jikin mota.

 Kina tunanin kinsan ahalin gidan nan ne Ummul.? Ko kina tunanin kinsan mijin da aka aura Miki ne.? Ina shawartar ki kar ki zak e da yawa.. Don t get too attached. Be warned.! Cikeda gargadi tai maganar kafin ta murmusa  Akwai

63 / 103