AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   37 / 103

108K to 111K   out of 306.8K words

a wayan salula ne. Meyasa Umma zata yanke mata hukunci mai tsauri irin wann. Shin ko haka take a al adarsu idan anyi aure sai bayan watanni uku kai magana da ahalinka.? Bata jin hakan ne. Ta lumshe idonta wasu hawayen suka kuma gangaro mata.

Tana a haka taji ana knocking a b angaren ta. Ta mik e Tai k ok arin kintsa kanta kafin ta nufi k ofa.

Ga mamakinta Anisa ta gani tsaye tana sakin huci.

Ummul ta sakar mata sassanyar murmushi had ida bata hanya  Bismillah shigo.

Anisa ta watsa mata harara kafin tasa kai ta shigo. Sai faman yatsina yank wanannen fuskarta da bai Ida warkewa ba take.

 Ba zama nazo yi ba. Ban kuma zo dan na rama abinda kika min ba dan naga kin sha jinin jikinki. Sak o Mommy ta bayar a kawo miki. Tai maganar tana mai aje turaren saman centre table.

Ummul ta katseta  Ni ban miki komai ba Anisa. Ke shaida ce keda k awarki ku kuka shirya abunku.

Ganin Anisar ta tsareta da ido Ya sanyata samun k warin gwiwar ci gaba  Ni bana nemanki da fad a. Kuma ki yarda dani har cikin zuciyata banji dad in abinda Ya sameki ba.

 Oh please shut up! Spare me your false sympathy. Taci gaba da takowa gaban Ummul. Tana huci take nuna fuskarta. Muryarta ya soma rawa alamun kuka  Just look at my face.. Look at what you did to me. Kalli yanda fuskata ta lalace.. This is what you want right.? Farin ciki kike ko..? Na sani tun farkon zuwanki gidan nan baki sona.. Amma ban tab a tunanin zaki min abinda kika min ba. Leenah ita ce ta zuba miki cream din ba ni ba. Meyasa kika zab i b ata nawa fuskar& It was Leenah s plan and not mine. Bansan ta shirya Miki haka ba amma ki zab i cutar dani. Look duba kiga abinda kika min. Ta k arashe cikin kuka.

Jikin Ummulkhairi yai sanyi. Ta soma girgiza kai  Anisa ki yarda Dani banji dad in abinda ya samu fuskarki ba. Amma ki sani shi rayuwa abinda ka shuka fah shi ke dawo maka. Idan khairan khairan idan sharri sharri. Ya kamata ki d auki darasi cikin abinda Ya faru.

 You are not in a position to dictate to me what I should do with my life. Idan kuma shawari ne ban nema ba. We are not even friends to begin with. Ta k arashe tana juya ido.

Ummul ta kuma girgiza kai  Ni bance mu zama k awaye ba. Amma ki sani bana neman abokin fad a.

Anisa ta kafeta da ido sai kuma ta marairaice fuska ta k arasa saman kujera ta zauna tana Shafa fuskarta. Ta d ago tana duban Ummul da idonta masu zuban ruwa  You are right you know. Duk abinda ka shuka a duniyar nan shi yake dawo maka. At first I hate you Ummul.. Bazan b oye Miki ba. Ina kishinki musamman ganin yanda daga zuwanki gidan nan hankalin Mommy da soyayyarta gaba d aya ya koma kanki. Ta mik e Tai tsaye gaban Ummul da idonta masu zuban ruwa  I m not a bad person Ummulkhair. I m so sorry for everything I did to you.. I don t want us to fight anymore.. Ko bamu zama kawaye ba I believe we can get along and live in peace.. Ta k arashe murmushi saman fuskarta. Ta mik a ma Ummul d in hannu murmushi saman fuskarta  Mu mance komai mu zauna lafiya.

Sosai Ummul tasha mamaki da sabon sauyin Anisar. Amma sai ta murmusa ta mik a mata hannu sukai musabaha. Anisa Tai saurin hugging d inta tana fad in fad a tsakaninsu Ya k are tayi alkawari.

Ta dubi saman dining table yanda abinci suke nan a jere alamun tinda aka kawo ma Ummul d in bata ko tab a ba.

Ta murmusa ta dubi Ummul  Don t tell me you still haven t eaten. Koda yake zaman kad aici Babu dad i. Come zo muje. Barin tayaki cin abincin.

Ta janyo hannun Ummul suka nufi dining table. Anisa tace da Ummul ta zauna ita zatai serving d insu. Ta zuba abinci ta shirya table.

"Nan suka zauna suna facing juna itada Ummul d in. Ganin Ummul ta matsar da table knife gefe yasa Anisa murmusawa tace  Ya kamata ki koyi cin abinci to our level. You must keep your table manners. And that includes the use of utensils. Kar ki mance ke sirkar gidan nan ce a yanzu. Hakan na nufin, your social status has changed. You"

"should learn how to mingle with upper class people. Mijinki Haidar mutum ne da ya girma cikin wayayyu sann yake hulda da wayayyun mutane, so you must adopt our lifestyle. Anisa ta k arashe tana gyara zamanta ta d aura napkin saman laps d inta. Sai faman kwarkwasa take."

Ta dubi Ummul tace tai irin zaman da Tai.

Murmushi Ummul Tai had ida yin yanda Anisa tai.

Anisa tace  Good. Haka wayayyun mata ke zama bisa table especially in public. Yanzu ki d auki fork and knife muga.

Ummul ta kuma murmusawa dan harga Allah dariya Anisa ke bata. Nan tai yanda Anisar tace. Anisa ta girgiza kai

" No, fork should be in your left and knife in your right. Like this. Ta k arashe tana nuna mata."

Murmushi Ummul ta kuma yi. Sai ta girgiza kai wann karon  Amma addininmu harma da al adarmu basu koyar damu cin abinci da hannun hagu ba. Shed an shi yake cin abinci da hannun hagu.

Anisa ta kauda fuskarta gefe tana juya ido. She had no other option than to put up da wann Bagidajiyar.

Sai ta juyo ta murmusa  Of course you are right. Kinyi gaskiya. Na gode da kika tunasar dani. Ta k arashe murmushi saman fuskarta. A haka sukaci abinci Har Ummul Tai mata rakiya sanda zata tafi.

Sai mamakin canzawar Anisar Ummul d in take. Amma cikin ranta taji dad i da suka shirya da Anisar dan harga Allah bata neman abokin fad a.

Anisa tana shigowa ta tadda Mommy zaune a parlor alamun tana jiran shigowarta.

 Mai ya tsaidake can.? Shin kin bata turaren da na baki ki bata ko kin tsaya shashancinki ne. Mommy ta tambaya tana duban Anisar .

Murmushi Anisa tai  Na bata Mommy. Tace ta gode sosai. Taji dadin kyautar dan tin kafin na bar wajen ta shafa. Annurin fuskar Mommy ya k aru jin tayi amfani da turaren. Anisa taci gaba  Na tsaya na tayata cin abinci ne Mommy. Sai kuma na mata hira.. Ta k araso ta zauna kafin taci gaba  Da alama kad aici na damunta. Dan ko abinci bata wani iya ci. Kar kiga yanda taci abinci sosai da muke tare.. Ta kuma muskutawa  Em Mommy nace why not gobe Ummul ta shigo muci abinci gaba d aya tare. Zata d an rage kewa kuma zata k ara samun daman sakewa damu tinda har yau Haidar baizo ba..

Mommy ta murmusa  Da alama ku biyun Kun fara sabo sosai. Sai ki samu ma aikatan kitchen ku shirya komai.

"Anisa ta murmusa  Okay Mommy.. Ta mik e tana murmushi. Har ta soma tafiya ta juyo  Em.. Mommy nace, can I invite my friend over..? Sanin ba ko wani shirgi Hajiya Kwaise ke bari a kawo mata cikin gida ba Shiyasa ma ta tambaya."

Mommy ta jinjina kai  Of course you can.. Tai maganar tana murmushi zuciyarta fari sol tinda Anisa ta sanar da ita Ummul tayi amfani da turaren da ta bata. burinta Ya kusa cika. Haidar d inta zai dawo gareta.

**

Saida Anisa tai shirin kwanciya kafin ta d aga waya ta kira Leenah. Tana tsaye gaban mirror tana cleansing soyayyan fuskarta da auduga taci gaba  I told you Leenah. Yarinyar nan sai tayi nadaman soyan fuska da tai. Zamanta a gidan nan yazo k arshe. Kedai kizo da wuri ki sha kallo. Kar ki damu na karba Miki katin gayyata daga wajen Hajiya Kwaise Maitama dan kinsan da k a ida ake shigar mata gida. Matsalar kawai I need someone who can help me to carry out my plan .

Leenah ta murmusa  Girl I ve got your back. Just say the word kiga aiki da cikawa.

 Oh shut up Leenah! As if your tiny brain is capable of helping me out.. last time I checked stupidity dinki ne yasa fuskata ta soye.

"Leenah ta murmusa  Haba Neesa trust me we re not going to repeat the same mistake.. You need me. After all, I m the only one you can count on. "

"Shiru Anisa tai  Fine. But wait , if you screw up my plan Leenah. I swear I m going to kill you myself. "

Leenah ta murmusa  I m on it girl. Kar ki damu zamu shirya komai ta yanda yarinyar zata bar gidan a gobe. I give you my word.

Jinjina kai Anisa take tana sakin murmushi lokaci guda tana duban fuskarta a mirror. A fili take furta  Tomorrow I am going to get rid of my problem. Goodbye to you. Ummul..! Ta k arashe tana mai fashewa da dariya had ida duban kanta cikin mirror.

**

Bayan ta Ida shirin baccinta alwalwa ta d auro ta soma jero nafilfili tana kai kokenta ga Rabbil Izza. Kama daga kan sabon rayuwar da ta tsinci kanta ciki zuwa ahalinta da ta baro Har dai izuwa kan wann k addararren aure da Ubangijinta Ya jarabceta dashi. Auren da batada tabbaci akan makomarsa auren da har kawo wann rana bata san kalan mijin ba bata kuma da tabbacin mijin Ya san da ita. Dan dik kyautatawa da d imbin alherin mahaifiyarsa gareta bata tab a jin a ranta ta samu sukuni cikin fargaban abinda ka iya zuwa yazo cikin auren. Addu a ta dingayi Allah ya shiga al amarinta. Idan har akwai alheri a cikin auren. Idan har zamanta alheri ne a gidan Allah Ya kawo mata komai cikin sauk i. Haka zalika idan Babu wani alheri Allah Ya sauk ak a mata ya kawo hanyar da zata bar gidan cikin sauk i. Ta jima sosai tana kai kokenta wajen Ubangijin da Babu abinda yafi k arfin buwayarsa. A nan kan sallayarta bacci yai gaba da ita.

**

Cuba..

Bacci yake yana jin Kansa na juya masa cikin baccin. Nan kuma ya soma mafarki da mahaifiyarsa. Mommy ya gani durk ushe gabansa tana kuka hannunta rik eda farin takarda. Tana fad in mahaifinsa yayi canceling project d insa. Saurin amsar takardan yai daga hannunta saidai yana ware takardan yaga sab anin abinda Mommy tace. Domin kuwa takardan sakin mahaifiyarsa ya gani wai Daddy ya saki Mommy. Juyowa yai bayansa yana huci kaman zai shak e Daddy yana fad in maiyasa zai saki mahaifiyarsa. Daddy bai basa amsa ba saima nuni da yai masa da bayan wata mace tana tafe tana jan akwatinta. Jikin Haidar yai sanyi sanda Daddy ke fad in  Mahaifiyarka ita ta saka nata Auren cikin had ari dan wanzuwar AUREN WATA UKU. Ka tuhumi kanka Aliyu.!

Daga haka ya farka daga baccin duk ya had a zufa. Nan yaga yamma ne sosai a agogon Cuba. Around karfe shida na yamma. Ya shafi fuskarsa da tafukan hannayensa yana mamakin baccinsa a daidai wann lokaci. Ba bacci bane yafi basa mamaki kaman mafarkin da ya tsinta kansa da yi cikin barcin. Meyasa hankalinsa ya tashi sanda yaga Mommy na kuka a cikin barcinsa. Baya son ganin hawaye. Baya so yaga ana kuka amma ya sani hawayen Mommy bai tab a damunsa ba. Meyasa ya tsinci kansa yana mai damuwa da hawayenta cikin barcinsa. Meyasa zuciyarsa tai zafi da yaga mahaifinsa ya rabu da mahaifiyarsa.? Wann shine abinda yake fata yake buri tsawon rayuwarsa ahalin ta ruguje ta lalace. Meyasa hankalinsa zai tashi bayan abinda yake buri ne Ya faru cikin barcin nasa. Ya furzar da huci a hankali yana kuma shafan fuskarsa. Can k asan zuciyarsa ji yai yana son kiran Mommy amma wani b angare na zuciyarsa na kuma tunzurasa gameda al amarin iyayen nasa. Why would he even care. Toh su rabu mana for all he cares. Yai gajeren tsaki kafin ya mik e yana neman Dareen yanda ya hangeta cikin pool tana waving d insa tana fad in he should join her.

**

Washe gari ta kama Alhamis hakan yasa Ummul ta tashi da azumi dan dama azumin litinin da alhamis basa wuceta hasalima Sun zame mata jiki.

Anisa ce ta shigo Tai inviting b angaren Mommy kaman yanda Mommyn ta buk ata a Cewar Anisa. Ummul ta shirya tsaf kafin suka jera suka nufo b angaren tareda Anisa.

SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!*

*28*

*©þSameena Aleeyou& *

A parlour suka tadda Mommy. Tana ganinsu ta fad ad a murmushinta. Ummul ta k araso ta zauna daga can bakin carpet ta gaida Mommy. Bayan Sun gaisa Mommy ke ce da ita ta dinga shigowa b angaren tana cin abinci tare dasu duk sanda take son hakan sabida zaman kad aicin babu dad i. Murmushi kurum Ummul tai dan harga Allah sosai take jin nauyin Mommy dukda k ok arin janta jiki da take. Nan take mata godiyan turaren da Anisa ta kai mata injita. Mommy ta murmusa tace Babu komai. Cikin zuciyarta kaw dad i ne ya mamayeta. Daga k arshe burinta yana gab da cika. Haidar ya gama gudunsa duk yanda zaije amma tanada yak inin aikin Malaminsu zai tasiri akansa.

Anisa ce ta janyo hannun Ummul tace ta taso su duba ma aikatan a kitchen. Aiko kaman wacce take kan k aya ta mik e tabi bayan Anisa.

A kitchen d in ma saida ta janyo Anisa suka keb e ta d an mata nasiha kan wulak anta d an adam koda na k ark ashin ka ne. Musamman da taga yanda duk ta birkita ma aikatan da tsiwa.

Anisa ta kauda fuska tana rausayar da ido. Cikin zuciyarta fad i take ki gama duk wani kilibibinki bayan abinda na shirya Miki kin zama tarihi a gidan nan. Zuwan Leenah yasa Anisa barin kitchen d in dan security personnel sun kira daga can gate sun sanar Anisa tanada bak uwa. Hakan yasa bata bi takan Ummul ba ta fice.

Ummul na tsaye gefe ta hangi madara kan wuta yana gab da zuba. Cikin sauri ta isa ta d auki abun motsawa tana juya dan hanasa zuba.

Chef d in da bata jima da barin wajen ba ta k araso da sauri tana bama Ummul hak uri da fad in urgent call ta samu daga gida Shiyasa ta tafi amsa kiran.

Ummul ta murmusa had ida girgiza mata kai  Laa babu komai kar ki damu nima nayi kewan aikin ne. Ban Saba zama haka nan bana aiki ba. Duk sai ina jin ba dad i. Ta k arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarta. Dan ta lura cikin ma aikatan wann wacce ta d an manyanta mai kula da sauran  Yanmatan dake kitchen din ita kad ai taji tana hausa sosai.

Matar ta d an murmusa  I m the chief chef here. I m the one supervising and monitoring the kitchen staff. Kar ki damu munada yawa a nan.. Zamuyi komai kan lokaci in sha Allah.

Ummul ta murmusa kad an  Amma zan d an iya tsayuwa a nan na tayaku da wani abun..?

Matar ta kuma murmusawa  I m afraid you can t. Idan Madam tazo taga mun baki aiki zai iya shafan namu aikin musamman ni.. Kar ki damu zamu kula da komai a nan.. Kije kawai.

Ba don Ummul taso ba ta jinjina kai ta nufi k ofa matar sai sakar mata murmushi take.

Tafiya take a katafaren gidan tana waige waige. Tabbas batada tabbaci idan bata b ace hanya ba. Tana tafe tana tinanin ta ina zata bi nan ta hangi wani k ofa tabi k ofar. Wata ma aikaciyar gidan mai sanye da uniform ta gani.

"Budurwar ta tambayi Ummul  Ma am, are you looking for someone.. Do you need something..? "

Ummul ta dubeta sai tace  Hanya nake nema dan Allah.

Budurwar ta murmusa  Oh that s the way to the main house Ma am. Ta k arashe tana nuna ma Ummul b angaren dama.

Ummul ta jinina

37 / 103