Kurman Allo Sakamakon Kin Karɓar Gaskiya by EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU

Author :  EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category :  KDP NOVELS

Chapter   9 / 80

24K to 27K   out of 237.2K words

akan wanda suke tare manne da juna akan gadon asibiti da kyakkyawan Baby sun saka shi tsakiyar hannayensu tare da rungume shi, Baby yana naɗe cikin farin baby shawl fuskarsa ce kaɗai a buɗe. Alh Aliyu bai ankara ba ya ji wani abu mai ɗan ɗumi-ɗumi yana bin tattausan kumatunsa, bai damu da sai ya goge su ba ya rungume hoton a ƙirjinsa ya ɗauki lokaci mai tsawo a haka sai da ya ji wayarsa tana ringing kana ya tashi ya mayar da hotunan cikin safe ɗin, sannan ya ɗauki wayarsa dake ta faman ruri.
*ALH BASHIR MANSION*
Misali ƙarfe 4:15pm AB ya baro kamfani duk da yana da tarin muhimman ayyuka da ya dace ace ya kammala su kafin tashinsa sai dai ya zama mishi dole ya bar ayyukan duk da irin muhimmanci su agare shi, saboda yana so ya je ya haɗu da yarinyar da Daddynsa ya nema masa bedroom ɗinsa ya wuce ya cire kayan jikinsa ya ɗaura brown towel ya shiga wanka, bai wani ɓata lokaci a wurin wanka ba ya fito saboda har yanzu yana fama da migraine headache sai ma ji yanzu ya daɗa ƙaruwa fiye da ɗazu da safe. Ya shirya cikin farar shadda tasha aiki da zare blue shiyasa ya saka hula blue da blue color sandal irin wanda ake sakaɗa yatsa sosai takalmin suka yiwa fararen ƙafafuwansa kyau, duk da baya ciki yanayi mai daɗi hakan bai hana masa feshe jikinsa da tsadaddun turarunkansa, dama ƙamshi ya zame masa jiki ma'aɓoci so turare ne. Kai tsaye parking lot ya wuce ya shiga motarsa tuni maigadi ya wangale masa gate koda ya isa gidan Alh Habib Bichi ƙarfe 5:44pm bayan ya yi parking motarsa ya aika maigadi ya sanar wa da Mufeeda zuwansa.




#Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo.






littafin nan 500 Naira only




ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130


KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730


Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336






*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.


*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar


*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu


*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce


*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari


*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan


Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500


VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k


NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[12/1/2023, 6:53 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)


NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU




#Love story
#Gwagwarmaya
#Team tagwaye novels


*RUBUTUN ƳAN TAGWAYE ZANGO NA BIYU.*
*TAFIYAR BIYU TAFI ƊAYA*


PAID BOOK




012.


Tsaye yake cikin compound ɗin gidansu Mufeeda, ya jingina bayansa da mota ya harɗe hannayensa akan ƙirjinsa yana ƙarewa harabar wurin kallo. ma'aikata ne maza ke ta kai da kawo, har kuma zuwa lokacin zuwaciyarsa taki amanna da yarinyar da Daddy ya keso ya aura wani irin ƙunci yake ji a can ƙasan zuciyarsa duk yadda zai yiwa Daddyn nasa bayani yasan bazai fahimta ba.
"Salamu Alaikum amincin Allah ya tabbata akan wannan kyakkyawar halittar.
Bai san yayi zurfi duniyar tunanin da ya shiga ba sai da ya ji wata murya mai sanyi tana yimasa sallama, kallonta ya yi na sakan biyu babu laifi tana da kyau ƙamshinta ga baki ɗaya ya gama cika wurin amsa sallamarta ya yi cikin sanyin murya kallonsa kurum take still da murmushi akan fuskarta.
"Da fatan banyi laifi ba dana barka kana jira? Mufeeda ta faɗa da wata irin murya mai jan hankalin duk wani ɗa namiji dama Mufeeda ba dai iya tsara zance ba da tattausan kalamai, murmushi ya kirkira yana shafa beard ɗinsa " mu ƙarasa daga ciki. mufeeda ta faɗa tana juyawa ta fara tafiya cikin takonta mai jan hankali duk da yadda take tafiyar a hankali dan su jera da AB haka bai sa ya cimmata ba. Tana mamakin izzarsa tamkar wanda ya haɗa jini da sarauta
Sai murmushi take saki ita ɗaya koda mahaifinta ya yi mata zance duk da tana jin labarin AB ɗin kuma tana kallon yadda ake ɗora business din kamfanin mahaifinsa a jaridar daily trust ana saka daidai kun hotunan sa
bata taɓa tunanin haɗuwarsa yafi haka ba a fili ba. A parlor baƙi aka yi masa masauki aka cika gabansa da cima kala-kala babu abunda yaci acikin abubuwan da aka aje masa bottle water kawai ya dauka ya sha rabi ya aje Mufeeda ta ɗan saci kallonsa suna haɗa ido tayi saurin sadda kanta ƙasa ta shiga wasa da yatsun hannunta murya can ciki ta kara gaishesa. Ya amsa yana tamabayarta mutanen gidan ta amsa da suna Lafiya, shiru ne ya ƙara ratsawa a tsakanin su har na kusan mintina goma shi ba magana ya iyayi mai tsayi ba bai san me zai ce ba
Ko Rumaisa idan ya je zancen wurinta rabin hirar duka ita take masa, wani wurin ya tanka ta wani wurin yayi murmushi, haka dai ya daure ya yi rabin awa a gidansu Mufeeda duk a takure yake ta kaisa har wurin mama suka gaisa har bakin mota ta rakasa tana ta ƙoƙarin ya sake da ita sunyi musayar lambar waya a tsakaninsu kafin ya shige motar tana tsaye tana kallonsa har ya fita daga cikin get ɗin gidansu. Bai shiga cikin gida ba sai bayan sallar isha Mami da siyama kawai ne a parlor ya zauna kujerar da Mami take mai zaman cin mutum biyu yana gaisheta ta amsa tana kallon yadda ya yi wani irin zuru-zuru
"Kwanan nan baka son cin abinci Abba, ina ganin yadda ka ke zuba abincin watarana ma ba ka tsayawa cinsa musamman da safe haka ka ke tafiya office, wannan miskilancin naka ba ƙaramin haushi yake bani ba matar ka ta shiga uku ,za ka kasheta da ranta idan Allah ya zuba mata surutu tamkar Aku.
Bai san lokaci da ya saki murmushi ba, bai dai ce komai ba Dariya Siyama tayi tana faɗin "wallahi yayanmu da gaskiyar Mami, wacce za ta zauna a matsayin matarka idan ba miskila bace ta shiga 9 Bama uku ba. Duk yadda Hindu ke nacin na bata lambar yaya Abbanmu su rika gaisawa kin bata nayi dan nasan halin kayana har tagaji da naci ta kyaleni. Wani irin kallo AB ya shiga aikawa Siyama dashi ta danne dariya dake cinta ta ɓoye fuskarta cikin kujera.
"Siyama je ki haɗomin cooffe.
Siyama ta mike tsaye ta nufi kitchen dan cika umarnin yayan nata. Mami ta mayar da hankalinta sosai wurin AB tana faɗin "Ya ku kayi da Mufeeda ɗin? Nasan halin ka idan baka son yarinyar nan tun wuri ka faɗawa Daddy, karka bata mata lokaci.
Mami tamkar tasan maganar da ya keso su yi kenan ya tattauna da wani ya rasa dawa ya kamata ya yi maganar.
"Na je Mami. Sai kuma ya sassauta murya ya ci-gaba da faɗin "Mami Amma kina ganin Daddy,ba zai haƙura da maganar auren nan ba har zuwa gaba?" Ko ke ki yi masa magana.
Da sauri Mami ta shiga girgiza kai tana faɗin "Ni zan zauna maka da matar ne?" kawai ka je ka samu Daddyn ka ce baka ra'ayi sai a fasa.
Ɗan fito da ido ya yi yana gami da faɗin."Ni ai bance ban ra'ayinta ba ganin na ke me Daddy ke yiwa saurin lallai sai nayi aure a yanzun.
Mami ta taɓe baki ta ce "Ka daina sakani a matsalarku da ku ka gama maganar da Daddy ai ba ku sakoni aciki ba.
Ɗan shiru Abba ya yi yana kallon Mami kafin yace "Mami ni fa yanzun mun gama daidaita kanmu da Rumaisa har office ta sameni ta bani hakuri.
Wannan karon baki buɗe Mami ke kallonsa cike da takaici take faɗin."Duk irin tozarcin da mahaifinta ya yi mana aranar daurin aurenka shine har ka manta Abba?"
Yadda Mami ta fusata yasa illahirin jikinsa ya yi sanyi ya yi da nasanin faɗawa Mami, zancensa da Rumaisa, ƙarshema Mami bata saurari haƙurin da yake bata ba ta tsallakesa ta bar masa parlor Siyama ta haɗo masa cooffe ga baki ɗaya yanayin sa ya canja har tambayarsa Siyama tayi yace babu komai. Ya kalleta yace ta kira masa Aydah juyawa tayi ta nufi stairs tana riƙe handling ɗin ƙofar za ta tura ta ji sa a rufe Siyama ta shiga buga kofar tana faɗin."Wannan wane irin iskancine za ki riƙa rufe kofa kamar wata marar gaskiya.
Dama Aydah najin ana buga ƙofa da sauri ta mayar da sabon Novel ɗin da take karatu ta mayar dashi cikin bag ɗinta na islamiyya fuska a murtuƙe ta zo ta cire key tana kallon Siyama da ranta ya gama ɓaci. "ubanwa kike rufewa ƙofa sai kace wacce bata da gaskiya.
Ɗan buɗe idanu Aydah tayi akan Siyama tana faɗin."To wai ke yaya Siyama ina ruwanki ƙofar ɗakin ki ko nawa.
Ta faɗa tana wani haɗe rai , ƙwafa Siyama tayi aranta tana faɗin ranar da bata zuwa makaranta sai ta shiga ɗakin Aydah ta bincika me take ita ɗaya a daki dan ga baki ɗaya jikinta ya gama bata bata da gaskiya ko zaman parlor ta rage yi ,dama tunda yaya Abba ya saka mata kayan kallo a ɗakinta ta daina bi a parlor duk magarib sai anji 'yan matan gidan na rigimar canja channel dama ita Aydah drama da take kallo a zee word tun 7 na dare har 10 babu kuma wanda ya isa ya canja channel ita kuma Sadiya star life, Siyama ce mai Kallon African magic idan suka hasala Mami sai duka ta kashe kayan kallo tace kowa ya tashi ya koma ɗakinsa ya yi karatu ko kuma ta mayar tashar (Sunnah Tv) ta ce duk ubanda ba zai iya kalla ba ya bar mata parlor AB yana saka mata nata a ɗakinta aka samu zaman lafiya daman ita ce rigimammiya. "Idan Kin ga dama ki je yayanmu na parlor yana jiranki.
Daga haka Siyama ta juya tabar ƙofar ɗakin na Aydah da yar bingilar rigar baccinta wacce ta sauka dai-dai gwiwoyinta ta nufi cikin parlor sai manyan kalaban dake reto a tsakiyyar bayanta, ta zauna kusa garesa yana shan cooffe yana waya da Rumaisa jin ta kusa dashi yasa ya katse wayar ba tare da yayiwa Rumaisa sallama ba. Yau jin kansa yayi wani iri da Aydah ta zauna da kayan bacci agabansa bai san meyasa ba sai ya ji kansa wani iri watakila hakan yana da nasaba da ya ji ba Mami da Daddy ne suka kawo sa a duniya ba kenan su Aydah ba muharammansa bane."Yayanmu ina wuni duk yau bamu haɗu ba.
Aydah ta faɗa tana kallonsa maimakon ya amsa ta sai ya tamƙe fuska ya shiga faɗin "Yaushe na fara wasa dake a gidan nan?" Gaban Aydah na faɗuwa take kallon fuskarsa?' His sounds so pissed off tuni hawaye suka cika idanunta abun da ya tsana kenan ganin hawayenta, duk da haka bai fasa mata faɗa ba "Yaushe ki ka yi girman daukar min waya ki yiwa babba rashin kunya irin tarbiyyar da akayi miki kenan?"
Tuni Aydah ta gano laifinta cikin rawar murya hawaye na zubo mata take basa haƙuri Amma ina ko kallonta bai yi ba yabar mata parlor rai a bace kife kanta tayi da hannun kujera ta shiga rera kuka, a haka Sadiya ta sameta ta tsaya akanta ta kira sunanta banza Aydah tayi mata ɗan tabe baki Sadiya tayi ta wucewarta kitchen bata ƙara bin takan Aydah ba. Daman rashin kunyarta ba zai bari a shiga sabgarta ba koda tana cikin damuwa.
lokaci dinner da aka haɗu cikin dinning area AB yana zaune gefen Daddy, suna cin abinci dare babu Aydah babu alamarta babu kuma wanda yabi takanta. Sai Daddy ne ya dakatar da cin abincin da yake da mamaki yake tambayar ina Aydah ko tayi bacci ne?" Mami ta taɓe baki tana faɗin "baƙin halin ta keji ban san acikinsu da wa tayi faɗa ba.
Mami,ta kare maganar tana kallon tsakanin Sadiya da Siyama kusan tare suka haɗa baki da ita akan su babu abunda suka yimata, tamkar babu AB daman a wurin ake magana abincinsa yake ci cikin natsuwa Daddy ya kalli Siyama ya bata umurnin taje ta kira Aydah.
Babu jimawa Siyama, ta dawo Aydah tana bayanta da taci kuka har ta ƙoshi idanu sun mata luhu-luhu har lokacin rigar bacci ce ajikinta kallonta kurum Daddy yake har ta ƙaraso cikin rawar murya ta tare da hawayen dake son zubo mata Daddy ya amsa cike da kulawa he still looking at her "bakida lafiya ne?" Sai lokacin hawaye suka shiga zubo mata AB nagama cin abincinsa dama ko takan drama Aydah bai bi ba yayiwa iyayen nasa sai da safe da wani kalan kallo Sadiya take binsa dashi tana jin wani irin sauyi da zuciyarta ta samu game da yayan nata. Ganin yadda Aydah tabi AB da kallo yasa Daddy ya saki murmushinsu na manya watau faɗan tsakaninta ne ita da yayanta, bayan wucewar AB Daddy ya mayar da hankalinsa sosai akan Aydah yana faɗin "Da alamar kunyi faɗa ke da yayanki kuma nasan kece ba ki da gaskiya mamana.
Cikin rawar murya Aydah ta ce "Dan Allah Daddy, ka basa haƙuri nasan nice bani da gaskiya ni wallahi ba zan iya jure fushin yayanmu ba.
Daddy ya daga kai ya mata umurnin tagama cin abinci taje ta basa haƙuri ,abincin turasa kawai take ba tare da tasan ɗan ɗanonsa ba duk lokacin da ta tuna fuskar AB irin yadda ya fusata sai taji hankalinta ya sake tashi idan yayan nata yana fushi da ita har rashin lafiya take ita ma Sadiya AB na barin cikin dinning area ɗin tabar wurin haka kurum take ganin wurin yayi mata fili na ban mamaki ta rasa meke faruwa da ita akan yaya Abba, ko muryarsa taji a parlor suna magana da Aydah wani irin faɗuwar gaba take ji ranar kuma da basu haɗu ba jin take kamar bata da lafiya duk yadda take son dawo da kusancin su kamar yadda suke ada yaƙi bata dama ya rufe kowacce hanya gaisuwarta ma sai yaga dama yake amsawa yau a baƙin ƙofar parlor ta tsaya tana knocking tunda tasan ita mai laifi ce, jin shiru yasa ta shiga Parlor kai tsaye da sallama a bakinta ga mamakinta yana zaune acikin Parlon yana kallon (tvc news)da remote a hannunsa Amma ko kallon ƙofar bai yi ba ballantana tasa ran zai amsa dama tun kafin ta ƙaraso cikin parlor ya kashe Tv ya nufi master bedroom ɗinsa haɗe kanta tayi da ƙofar parlor ta fashe da kuka mai sosa rai...


#Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye Novels
#Kurman Allo






Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only




ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130


KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730


Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336






*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.


*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar


*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu


*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce


*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari


*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan


Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500


VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k


NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[12/2/2023, 4:48 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)


Na
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU


#Love Story
#Gwagwarmaya
#Team Tagwaye


*RUBUTUN ƳAN TAGWAYE ZANGO NA
BIYU.*
*TAFIYAR BIYU TAFI ƊAYA*




013.
https://www.tiktok.com/@maims_kiddies
"Lallai Dr irin wannan kyau haka tamkar kunzo daga ƙasar UK? Gaskiya kayan jikin su Hanan sunyi matukar kyau, amma dai ba'a ƙasar nan kuka siya ba?" Cikin dariya Dr Aisha tace. "A ƙasar nan muka siya, sai dai kamar yadda kika ce ɗin haka ne, duk wannan kayan da kika gani a jikin yaran nan na ƙasar UK ne da *@Maims_kiddie* take sai da su a cikin Nigeria, muma a wajanta muka siya kuma ba tare da munje inda take ba, kayan na gani a Instagram account ɗin ta na *KIDS THRIFTY/OKRIKA STORE.* Kayane masu kyau da kwari daki bari kenan malam Khadija dan tun da na fara siyan kayan yara a wajanta shikenan na dena ganin kyawun na ko'ina. Kema/kuma zaku iya nemanta a Instagram link ɗin dake sama. Za kuma ku iya samunta a WhatsApp ta wannan link ɗin dake ƙasa. Ko lambar wayarta.
https://Wa.me//08101378616












Siyama ta turo kofar room ɗin Sadiya ganinta zaune a bakin gado daga ita sai towel ajikinta da alamar ko wanka batayi ba. Sai wayar hannunta da take famar dannawa da mamaki Siyama ke faɗin."Daman yaya Sadiya ba yanzu za ki tafi school ba?" Dan Allah karki sakani latti yau wanda zai ɗauke mu lecture yana da zafi ko minti ɗaya ka kara bai zai bar ka ka shigar masa aji ba.
"Ni nace ki jirani Siyama ku yi tafiyanku kawai sai zuwa anjima zan tafi. Jin haka yasa Siyama ta juya tabar ɗakin da sauri yar ajiyar zuciya Sadiya ta sauke tasan ita ma tana da lecture ƙarfe takwas na safiyar yau Amma tafiso tayi asarar ta in har zata saka Abba Bashir cikin kwayar idanunta jiya kwana tayi da tunaninsa manne da zuciyarta kowanne juyi da take cikin baccinta shine mutum na farko dake faɗo mata arai ta kudurta aranta yau komai zai faru sai AB ya sauketa a makaranta.
Siyama tana sauka a kasan stairs ta samu Aydah goye da schoolbag ɗinta ga tea da Huwaila mai aiki ta kawo mata da wainar kwai a sama ko taɓawa batayi ba ."wato dan ki ɓatamin lokaci ko breakfast ɗin baki fara yi ba salon ki jamin masifa. Siyama ta faɗa rai a ɓace maimakon Aydah ta tankata kamar yadda ta saba miƙewa tsaye tayi ta nufi ƙofar ficewa daga parlon ba tare da ta ko kalli gun da Siyama take ba wani irin ƙwafa Siyama tayi tabi bayanta
Aranta take faɗin."Ai gara ma da suka samu matsala da yaya Abban,ya rufe masu bakin rashin kunya na kwana biyu Aydah aka fara saukewa sa'annan aka wuce da Siyama. Daga shi sai mami ne zaune cikin dining area suna breakfast har yayi shirin zuwa office cikin ruwan tokan italyn suit wanda sukayi matuƙar karbarsa suka fito da ainahin kyawonsa a sarari ƙamshinsa ga baki ɗaya ya gama gauraye parlorn, da shirinta na zuwa makaranta ta fito cikin Parlor har cikin parlorn ta taka tamkar mai tausayin ƙasa ga sauyin bugun zuciyarta da ya sauya nan take ganin ƴaƴanta zaune cikin dining area ɗin yana breakfast, taja kujerar gafda shi ta zauna ta kalli Mami ,ta gaisheta Mami ta amsa tana faɗin."daman bata fita ba?" ta amsawa Mamin da sai karfe goma take da lecture,ta wutsiyar ido take kallon AB yadda ya yi kamar bai san tana wurin ba."Yayanmu ina kwana, Sadiya ta faɗa a natse ba yadda ya iya dole ya amsa mata kodan saboda

9 / 80