Author : EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category : KDP NOVELS
tare da zaunawa kusa da ita, ƙara tanke fuska ta yi tare da faɗin "nayi tunani Abbu za ka yi wa takwara, kai Bashir Daddy Bashir yanzu kuma ka sake sakawa ɗan mu Bashir, haba abin ya yi yawa.
Ta ƙarashe magana tana turo baki dariya Ab ya yi tare da rungumeta "Baby baki san daɗin nake ji ba a duk sanda Daddy ya yi min kirari da Bashir ɗan Bashir to kin ga yanzu idan ya tashi zai ce min Bashir ɗan Bashir baban Bashir.
Aydah ta fashe da dariya sosai take dariya yana tayata "ina sonka Bee da ba ka dawo rayuwata ba ina jin ba zan sake aure ba har in mutu.
Kyakkyawan murmushi ya sakar mata tare da haɗe bakinsa da nata duniya ta yi musu daɗi rayuwarsu sai san barka.
*ALHAMDULILLAH*
_A nan muka kawo ƙarshen wannan littafi suna KURMAN ALLO, muna roƙon Allah da ya yafe mana kurakuran da muka rubuta a cikinsa, ya kuma yafe muku wanda kuka karanta kuma ya bamu ikon aiki da duka abubuwan alkhairi dake cikinsa_
_Haka zalika muna miƙa saƙon gaisuwa ta musamman da kuma godiya ga dukkanin waɗanda suka sayi littatafan mu na 'yan tagwaye biyar, mun yaba muku kuma mun jinjina muku Allah ya ƙara muku buɗi, lafiya da kuma daukaka, mun gode. Allah ya haɗamu a wata tafiyar cikin aminci_
#Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo.