Kurman Allo Sakamakon Kin Karɓar Gaskiya by EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU

Author :  EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category :  KDP NOVELS

Chapter   50 / 80

147K to 150K   out of 237.2K words

kasance za a fara shagalin bikin Rumaisa da AB kamu za a fara yi a yau ɗinan a wani hadadden hall suka kama amarya Rumaisa tasha makeup tayi masifar kyau kamar ka sace ta ka gudu makeup artists ta musamman tayo haya ɗinta tun daga garin Lagos, komai na bikinta so take ya zama na musamman adade ana zancensa a kafafen sada zumunta(social media) saboda haka manyan kudade Ammi ta karɓa wuri Alhaji Bello madawaki. Gyara kuma tasha shi in and out har na fitar hankali kayan mata ba kalar wanda bata yi amfani dashi ba. Burinta ta gigita AB a daren farkon su.




#Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo.








Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only




ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130


KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730


Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336






*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.


*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar


*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu


*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce


*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari


*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan


Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500


VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k


NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[1/12, 3:46 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)


NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU


Love Story
#Gwagwarmaya
#Team Tagwaye


068.


Shagalin bikin na kece raini ake gudanarwa duk da AB ya nunawa Rumaisa rashin amincewarsa amman sai tayi biris dashi, ta cigaba da aiwatar da shagulgula ta. Sai da abun da ya dara dagulawa amarya lissafi bai wuce yadda aka yi kamu babu dangin ango ko ɗaya da farko abin bai dame ta sai da taji danginta da 'yan uwata sun fara korafi suna faɗar wannan wane irin aure ne ace babu dangin ango koda mutum ɗaya ne. Shi yasa bayan an kammala kamu ta nemi AB bayan ya zo ta fito daga cikin gida zuwa lokaci ta goge makeup ɗin da aka yi mata hatta da bridal outfit ɗin ta cire tasaka doguwar rigar cotton material, sai uban ƙamshi dake zubawa sai kace wacce aka tsamo daga cikin tanker turare. Ƙasancewar gidan nasu cike yake da jama'a 'yan biki shi ya hana AB ƙarasawa ciki sai ya tsaya wajen gate. Rumaisa ta buɗe front seat ta zauna tuni fitinannen ƙamshinta ya cika ƙofufin hanci AB don sai da ya ja ƙarfaffiyar ajiyar zuciya, ya ɗago idanunsa daga screen ɗin wayarsa ya sauke su akan fuskarta, tsanani gyaran jiki da tasha har ya saka skin ɗinta ya yi wani yellow-yellow "Barka da fitowa habibty kin ga yadda kika yi kyau abinki anya kuwa ba sace ki zan ba ina ji kamar ba zan iya haƙuri har zuwa jibi a ɗaura mana aure ga baki ɗaya kin damalmala min tunani.
Dariya Rumaisa tasa yayin da kanta yaƙara girma tana ji cewa tafi sauran mata "Uhm! Ka ji dashi Habibi wai ciwon ajali a ɗan yatsa ɗazu da na tura maka pic ɗin kwalliya ta ai cemin ka yi an canzawa matarka kamanni ba za ka lamunta ba.
"Ai da gaskiya ta Habibty an bi an fante min fuskar mata ta koma wata halitta ta daban ba dole nayi magana ba. Yanzu dai kika fito matar Abba sak!
Dariya suka sa, su duka daga bisani Rumaisa ta dauko ainihin zance da yasa ta nemi ganinsa a wannan daren "Habibi ɗazu a wurin kamu mutane sai korafi suke yi babu dangin ka ko ɗaya musamman dangin Abbana.
"Rass! Gaban AB ya bada wannan sauti nan da nan annuri da yake kan fuskarsa ya gushe, domin wannan wani miki ne da Rumaisa ta tado masa dashi shi wanda yake kokarin ya danne ya kuma manta dashi sai gashi ta tuna masa adaidai lokaci da yake cikin farin ciki domin aurenta shi ne cikar farin cikinsa.
"Ka yi hakuri Habibi naga kamar maganar ta ɓata maka rai ni kaina ban ji dadi yadda aka dinga ce-ce-kuce akan rashin danginka ba, kasan idan ana shagalin biki irin wannan dole za a nemi 'yan uwan ango.
AB ya ja dogon numfashi tare da saukewa cikin raunin murya ya ce "Yanzu Habibty da kika kirani kina min wannan zance me kike so nayi alhali kinsan ba dangin ne dani ba a tunanina za ki faɗa masu ainihin gaskiyar waye ni danginki ne ba wani ɓoye-boye da za ki yi musu.
"Haba! Habibi so kake a dinga yamadidi da ni ace na aure marar asali gaskiya wannan ba shawara mai kyau bace ni kiran da nai maka gobe za a yi dinner ka yi kokari ko wadancan mutane da suke matsayin danginka kasa su, su zo mana amman gaskiya ba zan so ayi dinner ɗinan babu wani da za a gabatar a matsayin danginka.
Sosai AB ya shiga kaduwa wani irin azababben tsoro ya lulluɓe shi har ya kasa furta komai sai faman kallon Rumaisa yake yi, ya kasa yarda Rumaisa ce ta buɗe baki ta kirasa da marar asali a tunaninsa idan kowa zai iya bugun ƙirji ya kirasa da wannan suna ban da ita ashe kallon kitse ne yake yiwa rogo. Tsawon zamansa da ita bata taɓa furta masa kalmar da ta tsaya masa arai ta tokare masa maƙoshi irin wannan.
"Habibi magana nake yi ka yi shiru kar dai ka cemin maganar tawa ta ɓata maka rai naga cikin lokaci guda fuskarka ta sauya ba kamar yanda na zo na tarar da kai ba.
"Ba komai Habibty kuma koda raina ya ɓaci ba abun da zan yi da ya wuce sauyawar fuska, sai dai ina so ki sani ba zan iya cilasta wa kowa ya zo bikinmu idan baya da ra'ayi tun sanda 'yan uwan Daddy suka san gaskiya waye ni da yawansu suka daina hulda dani shi yasa kika ji tun farko na nuna miki bai sai mu yi ire-iren waɗannan bidi'o'i ba. Ke kuma kika kafe.
"Haba Habibi akan me ba zan yi farin ciki Allah ya gwada min aurena da wanda na daɗe ina mafalki musanman yadda aure namu ya zo da complications iri-irin sai yanzu da ya tabbata zan kasa nunawa gaskiya ba zan iya ba. Ka nemi kawai ko su Siyama ne su zo su gayyato ƙawaye su amman gaskiya banaso abun da ya faru a wurin kamu ya sake faruwa a dinner shi yasa na nemi ka tun a dare nan mu yiwa tufka hanci.
"Ki fahimci ni Rumaisa da gaske nake ba zan iya cilasta wa kowa sai ya zo bikina ba. Wannan dinner ba dole bace tun farko ke kika ji za ki iya saboda haka sai kisan yadda za ki yi handling ɗin family and friends ɗinki.
"Habibi abun da za ka ce kenan?"
"To me kike so nace da ya wuce wannan?"
"Shi kenan Allah ya ba mu alkhairi.
Ta faɗa tare da buɗe murfin mota da karfi ta fita, rai ɓace da sauri AB ya fito yana kiran sunanta amma tayi masa banza ta buɗe ƙofar gidansu ta shige ya daɗe tsaye a wurin yana kiran wayarta taki picking daga ƙarshe ma sai ta kashe wayar duka.
Cikin wani yanayi na karayar zuciya ya shiga motarsa ya yo gida tun yanzu kenan zai fara fuskantar kalubale rashin asali wato ba ƙaramin gata Daddy ya yi masa ba na aura masa Aydah da ya yi ashe aurenta shi ne rufin asirinsa, sai yanzu da hakan ta faru tsakaninsa da Rumaisa ƙwaƙwalwarsa ta fahimci manufar Daddy.
Sosai ya shiga damuwa shiyasa yana shigowa gida ya wuce parlornsa dake sama ya zauna akan sofa tare da ture hular kansa zuwa ƙeya sai zazzafar iska da yake ta faman fesarwa daga bakinsa. Anan ya kusa raba dare kafin ya wuce master bedroom ɗinsa yadda yaga rana haka yaga dare, washegari da sassafe Rumaisa ta turo masa da text tana ƙara jaddada masa manufarta. Ban yi mamaki ba saboda tun jiya mamakin da ta shahara dashi bai gama sakinsa ba. Wanka ya yi ya shirya cikin shadda blue in color ya sauko ƙasa da Aydah ya fara ci karo tana kwance akan three seater da waya manne a kunneta sai magana take tana dariya ya yi tsaye yana kallonta sai kuma ya yi gyaran murya hakan ne ya sakata juyawa ta kalle shi da sauri ta katse kiran tana faɗin "Ina kwana yayanmu?"
"Lafiya ƙalau! Ya aka yi yau ba ki je school ba?
"Yayanmu mun kammala exams jiya yau ba a komai shiyasa na bari sai gobe na je na karbo report card ɗina.
"Okay!
Ya faɗa tare da nufar kofar fita "Yayanmu fita za ka yi ne?"
"Eh!
"Break fast fa?"
"Sauri nake yi idan na isa office zan yi.
"Shi kenan Allah ya tsare ya kai ka lafiya.
"Amin!
Ya faɗa a takaice ya juya tare da buɗe ƙofa ya fice ransa duk a jagule damuwa tana so tai masa yawa, yau da matsanancin ciwon kai ya tashi yana fita ya kira Abdulkarim ya tambaye shi inda yake ya ce masa yana office ya zo ya same shi a can, ya juya akalar motarsa ya nufi ma'aikatar su Abdulkarim ɗin. Koda ya shiga office ɗin Abdulkarim har wani hazo-hazo yake gani adaddafe ya nemi kujera ya zauna yana mai dafe ƙoƙon kansa fuskarsa fal damuwa. Abdulkarim ya ture file ɗin dake gabansa ya taso cikin sauri ya nufi wurin AB ya zauna tare da dafa kafaɗarsa "Yadai abokina tun a waya da na ji muryarka jikina ya bani you're not okay faɗamin mene ne?"
"Ak wai ni har sai yaushe zan ji daɗin rayuwata? Ak me na yiwa iyayena da suka zabi su jefar dani batareda su yi tunani hakan zai dinga bibbiyata ne? Me nayi musu da na cancanci haka.
"Calm down abokina ka natsuwa ka sakawa zuciyarka sallama. Kasani kowanne dan Adam yana tafiya ne a bisa bagiren ƙaddararsa kai ka ma godewa Allah da ya musanya maka da mahaifi irin Alhaji Bashir domin samun mahaifi irinsa a wannan zamani sai an tona.
"Haka ne Ak amman jiya maganganu da Rumaisa ta faɗamin sune silar damuwata.
Ɓata fuska Abdulkarim ya yi har yana haɗawa da guntun tsaki shi dama tun fil'azal bason Rumaisa yake yi ba don dai kawai AB ya nace akanta ne cikin rauni murya AB ya kwashe labari abunda ya wakana tsakaninsa da Rumaisa duka ya faɗawa Abdulkarim ai kuwa Abdulkarim ya shiga zazzaga masifa har cewa ya yi "ko yanzu bata ɓaci ba idan ba za ta iya aurenka a haka ba babu dole kowa ya kama gabansa amman ina amfani ace ƙanana maganganu daga wurinta suke fitowa, har idan soyayyar da take maka ta gaskiya ce ina ruwanta da danginka.
Shi dai AB bai ce uffan ba sai bin Abdulkarim kurum yake da idanunsa da suka yi ja, AB bai baro office ɗin Abdulkarim ba sai bayan azhar yau kasa zuwa kamfani ya yi duk da yana da tabbacin tarin ayyukan da ke jiransa da yake so ya kammala su yau ɗinan daga gobe zai ɗauki hutun mako ɗaya domin ci amarci gida ya dawo jikinsa duk ya yi masa wani irin ga wata irin kasala da yake ji a main parlor ya tarar da Aydah da Huwaila suna kallo, Huwaila ce ta fara gaishesa kamin Aydah ya amsa musu da kasalalliyar murya ya haura sama "Auta tashi ki bishi yadda ya dawo ɗinan akwai abun da yake damunsa ga baki ɗaya ya yi wani irin kamar ba Yayanmu ba.
Huwaila tayi magana tana kallon Aydah, da sauri ta yunƙura ta tashi tsaye tana faɗin "Tun safe na gansa ciki wannan yanayi ai na gayamiki ko breakfast bai yi ba ya fita, kuma yanzu ya dawo ba lokaci da ya saba dawowa ba.
"Haka ne yi maza ki je ki ji damuwarsa.
Aydah ta nufi upstairs da saurinta tana tura ƙofar parlor ta hango shi zaune akan sofa yana amsa waya tun kafin ta iso kusa dashi ta tsikayi muryarsa yana faɗin "Haba Rumaisa ya kike so nayi da rayuwata huh? Wannan abun da kike bukata bai mai yiyuwa bane, shiyasa tun farko na nuna ƙi amincewa ta da party nan da kika shirya.
Ya yi shiru can kuma ya sake cewa "Ni fa ba zan iya ba idan har party ya zama dole sai da dangina ki haƙura dashi mana tun da dai kinsan ba dangin ne dani ba.
Aydah ta sauke numfashi tare da zaunawa gefensa "shi kenan ki yi yadda kike so ni dai na faɗa miki farar gaskiya kuna kuma daga kanta bansan me kike so na sake faɗa ba.
Yana ƙarashe magana ya kashe wayar duka yana sauke numfashi ji yake kamar ya dora hannun aka ya yi ta rusa kuka "Yayanmu lafiya kake kuwa?"
Ya tsikayi sanyayya muryar Aydah a dodon kunnensa sai da ya ja deep breath kamin ya furta "Da dama zance Baby abubuwa suna neman su yi min yawa.
"Subhanalillah! To Allah ya ye maka.
"Amin! Ya furta tare da kakkalo murmushin dole.
"Na kawo maka abinci?"
"Uhm!
Ta tashi da sauri ta fice koda ta sauko ƙasa har Huwaila ta shirya masa abincinsa ta jera akan tray Aydah ta dauko ta kawo masa kaɗan ya tsukura sama-sama, Aydah ta tattare raguwa ta maida kitchen ta sake dawowa ta zauna akan kujera dake facing ɗinsa ta saka shi a gaba tana kallo, ita bata yi magana ba shi bai yi ba da ya gaji da kallo da take masa ya tashi ya wuce master bedroom ɗinsa ya ce da ita zai kwanta idan la'asar tayi ta tashe shi.
Ta bangaren Rumaisa ba ƙaramin haushi ta ji ba na yadda AB ya kashe mata waya hatta dashi bai je dinner ɗin ba balle wasu danginsa da take ƙorafi akai, gashi ta kira wayarsa yafi a kirga a kashe daga ƙarshe sai Abdulkarim ta kira shi daman yana jiraye da ita ya yi mata tass sai abin da bakinsa ya manta. Haka aka yi wannan dinner ɗin babu dangin AB daga shi sai friends ɗinsa, har aka tashi daga dinner ɗin Rumaisa bata sakar masa fuska ba yadda take share sa ba ƙaramin ciwo ya yi masa ba sai dai ba shida yarda zai yi. Da aka watse daga dinner su Rumaisa suka dawo gida tun a cikin daren aunty Raliya ta dinga faɗa da zage-zage sai da Ammy ta taka mata birki sa'annan ta dawo cikin hankalinta. Washegari gari da misali ƙarfe 2 daidai aka ɗaura auren AB da Rumaisa a bisa sadaki Naira duba ɗari ɗaurin aure ne da ya tara dubbanin mutane. Bayan an kammala ɗaurin aure maza suka wuce wurin liyafar ci abinci wanda Abdulkarim ya shiryawa abokansu da colleague ɗin AB, kuma har zuwa sanda aka ɗaura aure AB bai sake magana da Rumaisa ba sai bayan kammala ɗaurin aure ya tura mata gejeren text Alhamdullah an ɗaura aurenmu daga yanzu kin zama mallakina Habibty.
Ko kaɗan bai yi tunani za ta bashi amsa ba sai gashi ta tura masa dukkanin godiya da yabo sun tabbata ga Ubangiji da ya nuna mana wannan babbar rana ina tayaka murna Habibina.
Wani kalar sanyayye murmushi ne ya subuce masa duk wata damuwarsa ya nemi ta ya rasa.
Lokaci da labari daurin aure AB da Rumaisa ya riske Mami da Sadiya kowanne su tamkar zai haɗe zuciya Mami ta dinga faɗa da yiwa AB gori tamkar yana gabanta, yayin da Sadiya ta shige ɗakinta ta rufe ta dinga rusar kuka ji take kamar daga wannan aure na Ab ta rasa shi kenan.
Ta bangaren Aydah tun safe da tashi sukuku batada sukuni ko kaɗan ga wani abu da take ji ya tokare mata a maƙogwaro, sai rarrashinta Huwaila da Siyama suke yi tun safe Siyama ta zo gidan nata har dare tana gidan kamin a kawo amarya suka shirya Aydah cikin wani tsadadden lace suka dawo parlor ƙasa suka zauna wanda suka turaren wuta mai azabar Ƙamshin misali ƙarfe 9:30pm suka ji dirar motocin 'yan rakiyar amarya Rumaisa.


#Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo.






Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only




ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130


KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730


Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336






*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.


*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar


*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu


*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce


*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari


*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan


Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500


VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k


NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[1/15, 12:21 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)


NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU


#Love story
#Gwagwarmaya
#Team tagwaye Novels






069.




Wanda suka shigo da amarya cikin parlor daman sallama kawai suka yi basu kara kallan su Siyama dake cikin parlor ba suka rika Rumaisa zuwa sama. Da wani irin kallo Aydah ta bisu tana jin kamar zuciyarta zata faso ƙirjinta ta fito ƙanƙame Siyama tayi wani irin kuka mai cin rai na kwace mata ga jikinta ya dauki wani irin rawa,a tsorace Siyama ta rufe mata baki da wani yanayi a muryarta tace "kiyi shiru Aydah wai so kike suji kukanki sun rainaki.
"Ba zan iya ba yaya Siyam zuciyata, ƙirjina ciwo suke min.
Ta faɗa tana shesshekar kuka tun daga nan ƙasan parlor suke jin hayaniyar ƙawayen amarya a parlon AB basu jima ba sai ga AB ya shigo shi da friends ɗinsa har lokacin Aydah na kwance jikin Siyama tana sauke ajiyar zuciya. Huwaila ce kawai ta amsa masu sallamar cikin raunin zuciya, daman Siyama ko kallo ba su isheta ba. Tana yi tana dauke hawayen dake son su zubo mata jin take tamkar taje ta rufe yayan nasu da duka ta tambayesa me suka yi masa da zai masu Irin wannan sakayyar, sai dai girman da yake dashi a wurinta da kuma matsayinsa ba zata iya yimasa rashin kunya ba. Daman Aydah na jin sallamarsu tayi ƙoƙarin fita daga jikin Siyama,karo na farko a rayuwarta da taji bata son ganin fuskar yayanta da gudu ta shige ɗakin Huwaila gamida rufo kofar, shiru AB yayi yana kallon kofar da ta rufe, Siyama ce tabi bayanta batareda ta gaisheda AB da friends ɗinsa ba. Anan cikin parlor su Abdulkarim suka zauna Huwaila ta nufi kitchen dan kawo masu ruwa.
Da sassarfa AB ya nufi ɗakin na Huwaila zuciyarsa na wani irin bugawa ko kaɗan bai ji daɗi gani Aydah a cikin wannan yanayi ba, cikin shesshekar kuka Aydah ke faɗin."yaya Siyam zan bi ki wurin Mami, ba zan iya zama ba zuciyata fashewa zatayi.!
Dai dai lokacin AB ya turo kofar room ɗin daman Siyama na ganin ya shigo ta raba Aydah da jikinta ta miƙe tsaye, ita ma Aydah tamkar jira take ta tashi ta mike tsaye tana

50 / 80