Author : EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category : KDP NOVELS
yakinin cewa in shaa Allahu za a gansa.
Har washegari babu labarin Abba zuwa lokaci Rumaisah da Aydah sun ci kuka har sun godewa Allah, Kwata-kwata daren jiya babu wacce ta runtse a cikin su. Misali karfe 11:20am Abdulkarim ya sami kira daga police headquarter saboda da ya kai report har hoton ab da na motarsa ya bar hoton motar yana dauke da plate number jami'an tsaro sun sami gani motar AB iya bincike da bin kididdiga da suka yi ya tabbatar musu da motar AB ce da Abdulkarim ya isa inda motar take, yana ƙare mata kallo cikin abun da bai wuce twenty seconds ba ya gane motar AB ce faduwar ƙasa ya yi ya dafe kansa, sai ga Abdulkarim yana kuka da hawaye duk Abdulkarim yana cikin wannan halin hakan bai hana masa kiran Daddy ba ya sanar dashi mummunan labari kamin ka ce kwabo mutuwar Ab ta zagaya ko'ina, suman Aydah biyu Rumaisah kuma jini ya ɓalle mata sai asibiti aka wuce da ita cikin hukuncin ubangiji cikin nata bai zube duka ba aka yi nasarar tsayarda bleeding ɗin tare da bata gado har aka yi addu'ar uku Rumaisah tana kwance asibiti.
Ko Mami da ta zama silar barin Abba gida da labarin mutuwar sa ya riske ta, ta shiga tashin hankali musamman yadda taga yaranta suna kuka Sadiya kamar za ta yi hauka sai sambatu take yi Siyama ce mai ɗan karfin halin rarrashin Aydah tare da yi mata nasiha.
*BAYAN WATA BIYAR*
A cikin watanni biyar ɗinan abubuwa da dama sun faru daga ciki har da dawowar Aydah gidan Daddy bayan ta kammala takabarta yayin da Rumaisah ta koma nasu gida, aka rufe gidan AB. Rayuwar Aydah ta dawo abar tausayawa ta dawo miskila ƙarfi da yaji kullum tana ƙunshe a ɗaki gashi sai shirye-shirye bikin su Sadiya ake yi wanda za a fara shagalin bikin nan da kwana biyu, duk wannan bidiri da ake yi babu Aydah a ciki a duk sanda ta zauna ta dinga shafar cikinta kenan tana ji ina ma ita ma ace tana dauke da cikinsa kamar dai Rumaisah. Idan kewarsa ta addabe ta sai ta dinga kallon pictures dinsa dake cikin wayarta. Mami ta yi faɗa ta yi rarrashinta har tagaji ta zuba mata ido yayin da shi ma Daddy yake cikin matsananciyar damuwa ya ɗauki laifin faruwar al'amarin ya ɗorawa kansa idan kaga Daddy yarda ya zabge ya yi wata irin rama kullum jininsa ƙara hawa yake yi baya jin lafiya ko kaɗan a jikinsa ƙarfin hali kawai yake yi burinsa ya aurar da su Siyama tun da raguwar numfashinsa don ji yake yi jikinsa kamar da wuya a wannan karon ya kai labari. Cikin amincewar ubangiji aka yi bikin Siyama da Sadiya lafiya kowacce aka kaita gidan mijinta sai dai fatar Allah ya basu zaman lafiya. Tun bayan bikin su Siyama abubuwa suka ƙara caɓewa Aydah ga kadaice zaman gida ga kewar yayanta da har ta kasa sabawa da rashinsa. Tun last week aka yi resuming school ta kasa komawa gashi har an fara hada-hadar zana waec da neco, da kyar Daddy ya samu ta amince za ta koma on monday.
Ta ɓangaren Rumaisah cikin jikinta ya zo mata da laulayi mai wahala ga damuwar mutuwar mijinta sai abubuwa suka taro suka yi mata yawa, idan kaga Rumaisah sai ka zubar mata da hawaye duk ramar da Aydah ta yi Rumaisah ta fi ta. Kullum sai Aydah ta kira ta, ta ji yanayin jikinta duk ranar juma'a idan an sauko daga masallaci direba yake kai Aydah gidansu Rumaisa yanzu wata irin shaƙuwa ta ban mamaki ta shiga tsakanin su. Mutuwar Ab ta koya musu ƙaunar junansu a duk sanda suka haɗu basu da hira sai ta irin zaman da suka yi dashi wani abu idan suka tuno dashi sai ya basu dariya, wani kuma sai su fashe da kuka a duk sanda irin haka ta faru Ammi ce ke zama a tsakiyar su ta dinga rarrashinsu bala'in tausayi suke bata. Yau ma kamar kullum bayan Aydah ta dawo daga school kasancewar ranar juma'a ce ƙarfe 12 suke tasowa a main parlor ta tarar da Mami da Hajiya Zeenah suna hira ta gaishe su a takaice ta haura ɗakinta hajiya Zeenah ta dubi Mami tana murmushi tare da faɗin "Wai Mariya haka za ki zubawa Aydah ido kina kallo yarinya za ta kashe kanta akan wanda tuni aka shafe babinsa a doron duniya wallahi Mariya ki yi wa kanki faɗa ki ɗora 'yarki kan hanya ina amfani badi ba rai wanda ya mutu ya mutu kenan har abada ba zai taɓa dawowa ba.
"Bari kawai Zeenah ba kisan irin halin takaici da nake ciki akan lamarin Aydah da mahaifinta sun ɗauki soyayyar duniya sun ɗorawa matatcce ina lure da Alhaji kwata-kwata ya daina bacci sai uwar rama da yake yi da zarar ya buɗe bakinsa baya da wani zance face na Abba, haka zalika Aydah. Magana ta gaskiya Zeenah na kashe maciji ne ban sare kai ba. Na kawar da Abba daga zuri'a ta amma na kasa cire musu shi a zuciya hatta da Siyama da Sadiya basu da zance idan bana sa ba.
"Uhm! Lallai Mariya Daddyn su Sadiya ya ɗauki miki kara da kiyashi daukar marar sani anya kuwa Abba ɗinan bai haɗa tsatso da mayyu ba?" Yaro ya mutu amma be bar mutane suka huta ba.
Da haka suka ci-gaba da hirar su wacce dukkanta akan Abba ne. Bayan Aydah ta yi wanka ta shirya cikin milk colour ɗin Abaya ta yi rolling da mayafin rigar ta fito da ƙaramar purse ɗinta a hannu koda ta fito Mami da Zeenah sun koma ɗakin Mami saboda haka ta fice abin ta direban Mami ne ya sauke ta gidansu Rumaisa ta ce ya dawo da yamma ya dauke ta.
Da sallama ta shiga parlorn gidan Rumaisah na zaune a ƙasan rug tana cin kwado zogale yau da sha'awar cinsa ta tashi shi ne Ammi ta yi mata. Sallamar Aydah da ta ji yasa ta ɗagowa tare da fadada fara'arta ta amsa mata, ita ma Aydah murmushi ta sakar mata ta nemi kujerar da ke kusa da ita ta je ta zauna tana faɗin "Yau kuma me ake ci ne haka maman twins?"
Dai da Rumaisah ta galla mata harara kamin ta ce "wai Baby ba za ki daina zance twins ɗinan ba ko?"
"Akan me zan daina bayan kullum addu'ata akanki ki haifa mana 'yan biyu ki ɗauki ɗaya ki bani ɗaya.
"Uhm! Aydah kenan ai na gayamiki guda ɗaya ne an yi min scanning an tabbatar da hakan kuma in shaa Allah zan ba ki shi.
Dariya Aydah ta yi tare da zamewa daga kan kujera ta zauna dab da Rumaisah akan rug tana faɗin "Kin ga aunty Rumaisah kar ki shafa min zuma a baki sai bayan kin haihu ki ce ba kisan da zance ba. Musamman idan kika haifu mai kama da Yayanmu.
Murmushi kurum Rumaisah ta yi sai ta ƙarashe cinye kwado ta kana ta kai plate kitchen ta wanko hannu da bakinta ta dawo ta zauna kusa da Aydah ta kama hannayenta "Da gaske nake yi baby duk abun da na haifa wallahi zan ba ki shi domin nasan za ki so shi za ki kaunace shi ba za ki taɓa barinsa ya yi kukan maraici ba.
Wani irin farin ciki ne ya lulluɓe Aydah yayin da idanunta suka cicciko da ƙwalla bata baro gidansu Rumaisa ba sai yamma lis.
*LAGOS NIGERIA*
A fusace Aliyu na uku ya shiga ɗakin Anaal wacce ke zaune akan stool ɗin dressing mirror ta ɗora laptop akan lap ɗinta tana wani aiki, yadda Abbu ya turo ƙofar ɗakinta yai masifar haifar mata da faɗuwar gaba tai sauri rufe laptop ɗin ta yada ganinta akan fuskarsa wacce ke murtuƙe "Me kike zuwa yi Kano?"
Abbu ya faɗa babu annuri ko alamar wargi akan fuskarsa. Anaal ta haɗiye wasu busassu miyau tare da kauda fuskarta tana lankwasa yatsunta daman tasan dole sai hakan ta faru saboda jiya ta dawo daga Kano wanda yanzu zuwa garin Kano ya zama matar kamar dole.
"Anaal dake nake magana ki buɗe baki ki faɗamin abun da kike zuwa yi a Kano iya sanina daga ni har mahaifiyarki ba mu da wasu dangi a garin kano bare na ce ko ziyara kike zuwa idan ma akwai dangin acan ba zai yiwuwa ba ace ki dinga zuwa akai-akai ki faɗamin gaskiyar abun da kike ɓoyewa Anaal idan har kika bari na binciko da kaina wallahi sai nayi mummunan saɓa miki.
#Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo.
[2/5, 2:01 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)
NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU
Love Story
#Gwagwarmaya
#Team Tagwaye
096.
Shiru Anaal ta yi ta kasa furta uffan sai faman lankwasa yatsunta take yi tamkar su ne za su kawo mata mafita. Wanda hakan da ta yi yai masifar kular da Abbu ya hasala iya hasala sai huci yake yi, ji yake tamkar ya rufe ta da duka tana 'ya mace za ta dinga yawon banza da na wofi.
"Za ki buɗe baki ki bani amsa ko sai na taɓa lafiyar jikinki?"
"Abbu ka yi haƙuri.
Anaal ta faɗa cikin rawar murya "Ba zan haƙura ba har sai kin gayamin abun da kike zuwa yi a Kano.
Duk yadda Abbu ya kai da nuna fushinsa a fili akan Anaal ta faɗa masa abun da take zuwa yi a Kano amman yarinya nan ta tsuke bakinta ta yi shiru sosai ya harzuƙa har bai san sanda ya yi kanta da nufi ya rufe ta da duka ta arce toilet ta rufe ƙofa da key, da Abbu ya gaji da bambamin faɗansa ya fice daga gidan dukka. Ya nufi the george hotel wurin Maysun duk da ko ita a yanzu ba daɗinta yake ji ba saboda ta sako shi a gaba akan sai ya nemo mata ɗanta. Musamman a kwana nan da take yawan mummunan mafarki akansa, duk ta bi ta addabe Aliyu na Uku damuwa tana neman ta kassara shi.
Ya yi parking motarsa a parking lot din hotel ɗin ya nufi receptionist hankalinsa Kwata-kwata baya jikinsa ko kaɗan bai lura da Alhaji Ƙasim Birema ɗaya daga cikin abokan Ciroma dake zaune a receptionist ɗin yana amsa waya yayin da Alhaji Ƙasim Birema yana ganinsa ya washe haƙora ya yi sauri kashe wayar ya bishi a baya daman yana neman wanda ya sani a garin Lagos ɗin wani muhimmin abu ne ya kawo shi sai dai babbar matsalar sa da ya kasance bai san wasu wurare a cikin garin na Lagos ba. Shi ne yana gani Aliyu na Uku ya ji damuwarsa ta kau yana da yaƙini zai taimake sa ko don albarkacin yayansa Ciroma da yake abokinsa. Ya tashi da sauri yana baza babbar rigarsa ya bi bayan Aliyu na Uku sai dai kafin ya cimma masa ya ɓace masa saboda haka ya dawo receptionist ya kasa ya tsare yana jiran fitowarsa, jim kaɗan sai ga Maysun ta fito a fusace zuwa cikin receptionist ɗin yayin da Aliyu na uku yake bin ta a baya yana rokonta ta tsaya ta saurare shi bata tsaya ba ɗin har sai ta dangana da parking lot zuciyata tana tafarfasa ta shiga zazzaga masa masifa tana kuka. Alhaji Ƙasim yana ganinsu ya taso ya biyo su a baya daga nesa ya tsaya yana kallon su da kyar Aliyu na Uku ya rarrashe Maysun ta haƙura ta koma ɗakin hotel ɗin. Tun daga fitowarsu har komawarsu ciki akan idanuwan Alh Ƙasim yana mamakin miye gamin Aliyu da wannan balarabiyar mata kodai Aliyu ya fara bin matan banza ne. Nan da nan zuciyarsa ta cika da kokwanto Alh Ƙasim Birema yana cikin jinsin mutane masu azababben sa'ido da munafuci haɗe da anamimanci wannan halayyar tasa tun daga yarinta yake dauke da abarsa har zuwa girmansa da abun ya cigaba da habbaka, saboda haka jikinsa yana rawa ya lallaɓo numbern Ciroma don ya fesa masa labarin abun da idanunsa suka gane masa, musamman da yasan cewa babban laifi ne ga jini masauratar kudu ya kulla haramtacciyar alaka da, idan hakan ta faru aka kuma gabatar da gamsasu hujjoji za a kore wannan jinin sarautar daga masaurata idan yana da sarauta za a tube rawaninsa. Saboda haka Ciroma yana picking da kyar ya bari suka gaisa ya kwashe ƙarya da gaskiya ya gayamasa farin ciki ya lulluɓe Ciroma ya ce dashi ya yi kokari ya dauko masa hotunan Aliyu ɗin tare da balarabiyar akwai kyauta ta musamman da zai masa. Saboda haka Alh Ƙasim ya bazama neman yadda zai ɗauki hotunan su sai a washegari ya sami damar aiwatar da burinsa.Ta hanyar biyan daga cikin ma'aikatan hotel ɗin, ba iya hotunan su ba har da video ya ɗauka kala daban-daban, cike da alfahari Ƙasim Birema ya turawa Ciroma ta hanyar whatapp lokacin da Ciroma ya yi arba da hotunan haɗe da video sai da buga ihu idan Allah ya taimake sa, shi kaɗai ne zaune a turakarsa da faɗa ne da mutuncin sa ya gama zubewa.
Batareda da sani Aliyu na uku ba Anaal ta haɗa kayanta, ta bi jirgin safe sai Kano ta dabo tumbin giwa sai wani dan gajeren message da ta tura masa "Abbu kada ka sha wahala nemana, na tafi Kano"
Abbu yana gama karanta text ɗin nata ransa ya yi mummunan ɓaci yasan ko ya gwada kiran wayarta zai tarar da ita a kashe kamar dai yadda ta saba yi a duk sanda ta yi irin wannan tafiyar ta sirri Allah kaɗai yasan abun da Anaal take aikatawa a ɓoye.
*MASARAUTAR KUDU*
Wannan ita ce dama ta ƙarshe da Ciroma ya samu da zai tarwatse rayuwar alhalin mai babban ɗaki ba wai Aliyu kaɗai ba suma zunubin Aliyu ya shafe su domin hukuncin su kora daga masaurata. Ciroma ya kira Galadima ya nuna masa video da hotunan wata irin dariyar mugunta Galadima ya kece da ita ransa wasai don har ya fara hango kansa a matsayin sarkin sabon birnin kudu.
Kilishi ta kalli amintacciyar jakadiyarta ta ce "Jakadiya burukana ga baki ɗayansu sun gama rugujewa a yanzu banida sauran mafita, tun sanda boka mai Gundulelliya ya juya min baya ya ci amana ta na daina gani haske a almurrana a duk sanda na ƙyala ido naga Ciroma ne a matsayin da nake so jinina ya kasance akai na rantse miki da Allah Jakadiya sai na ji tamkar na haɗiye zuciya na mutu.
"Allah ya ƙara miki lafiya da tsawon rai mun riga da mun ɓata kyau tun ran wanka, da mun sani ba mu aikata abun da muka aikata shekaru talatin da takwas a baya da duk haka bata faru damu ba. Yanzu dole mu yi haƙuri mu cigaba da karɓar Ciroma a matsayin ɗan da kika haifa kamar yadda duniya ta daɗe da sani kece mahaifiyarsa.
"Uhm! Ba za ki fahimci halin takaici da baƙin ciki da nake ciki faratt ɗaya ba jakadiya kasancewar Ciroma a raye barazana ce babba a gareni, da kike ganinsa wutar ƙaiƙayi ne zai iya bankado dadadden sirri da muka yi haƙa muka binne, saboda haka kafin ya tona mana asiri ki nemo Dogara lokaci ya yi da za mu yi amfani da wancan ɓoyayyen sirri da muka daɗe muna adanawa yanzu ne ya dace mu yi amfani dashi domin tarwatsa Ciroma, kin ga daga Ciroma har Galadima za su ƙare rayuwarsu a maƙargama yayin da ni kuma zan yi amfani da wannan damar na sanya Ahmadu ya ɗane karagar mulkin kudu wannan ita kadai ce damar da nake da ita domin cimma burina.
"Wannan haka yake uwardakina a wannan karon ƙarshen Ciroma ya zo shi kenan ruwa ya karewa ɗan kada. Ranki shi daɗe ban da ma Ciroma da watau taya za ki raine sa sannan ya fi ki sani kundin sharri.
"Kamar yadda kika faɗa watau da rashin sani wacece ainihin Kilishi shiyasa ya tafka irin wannan kuskure.
Jakadiya ta tashi daga durƙuso da ta yi a gaban Kilishi ta fice da sauri.
Duk wani mai faɗa aji dake cikin masauratar kudu sai da Ciroma ya kira sa tare da 'yan uwansa dukka ga baki ɗaya faɗa ta cika ta yi makil, yasa aka shigo da Ƙasim Birema wanda daren jiya Galadima ya kawo shawarar shi ne ya fadi haramtacciyar alaka da Aliyu na uku yake aikata wa a boye gudun kada ace sharri suka yi masa.Babu kunya balle tsoron Allah Ƙasim Birema ya karkace kai ya shiga fadar ƙarya da gaskiya, nan da nan faɗa ta hartsune da surutu musamman yan uwa Aliyu da suke uwa ɗaya suna fadar ba su yarda ba sharri ne aka yi wa dan uwansu kowa yasan Aliyu kamili ne ta ya zai aikata irin wannan mummunan kaba'ira.
Ciroma kamar wani mutumin kirki ya yi gyaran murya tare da daka musu tsawa wanda hakan yasa fada ta yi tsit!
Ya shiga faɗin "A matsayina na sarkinku, shugaba agareku ina mai matukar ba ku haƙuri a bisa faruwar wannan murɗaɗɗen al'amari sanin kanku ne duk wani jinin sarautar Kudu ba za a taɓa kama shi da aikata mummunan zunubin zina duba da irin kyakkyawar tarbiyyar da iyaye da kakannin mu suka ba mu wacce har kawo wannan ƙarni da muke ciki muna kanta. Idan har Ƙasim Birema yana da kwakkwarar huja da zai iya gabatar wa da fada domin ta gasganta, abun da ya zo mana dashi gaskiya ne ko karya.
Ƙasim Birema gyara zaman sa yana ƙara sadda kansa ƙasa "Allah ya taimake ka sarki mai adalci tun farko da nayi tunani faruwar hakan duba da yadda mutane suke kallon Aliyu na uku a matsayin mutumin kirki, domin gujewa ka-ce-na-ce sai na yi amfani da waya ta a boye na dauke shi hoto tare da videoYa ciro wayarsa aka jona da ƙatuwar plasma sai ga Aliyu na Uku tare da Maysun waɗansu wurare a cikin video har yana rungumarta da sauri Ciroma ya ce aka kashe tv ɗin muni abun ya yi yawa, tsananin baƙin ciki ya rufe magaji ƙarami ya fashe da kuka zuciyarsa ba za ta iya jurewa ba domin yasan shiryayyen al'amari ne aka shirya domin taɓa kima da daraja yayansa, ya miƙe ya baro cikin fada kaitsaye ɓangaren mai babban ɗaki ya nufa yadda ya shigo yana gunji kuka ya yi bala'in ɗagawa mai babban ɗaki