Kurman Allo Sakamakon Kin Karɓar Gaskiya by EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU

Author :  EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category :  KDP NOVELS

Chapter   60 / 80

177K to 180K   out of 237.2K words

da gaske ta gaji idan Abba bai saki Aydah ba komai ma zai iya faruwa da ita kallo ɗaya ta yiwa Siyama dake zaune a parlor tana karin kumallo cikin nishadi da walwala ta nufi stairs,da ido Siyama tabi Mami tana yimata fatan shiriya aranta. Sai da Mami ta tabbatar Daddy,ya fita ta dauki mota ta fice daga gidan zuciyar Siyama duk babu dadi wannan karon kuma bata san me Mami zatyayi ba akan auren AB da Aydah, addu'a kurum Siyama ke yi Allah yasa komai yazo da sauki bata fatan Auren yaya Abba da Aydah ya rabu kamar yadda mami ta so.
"Gaskiya da abun Mamaki Hajiya mariya ace har yanzu asirin nan bai yi tasiri akan Abba ba.
"Kodai ita Aydah tana boye maki ne basa zaman dadi da yayanta?"
"Me zata boye min zeenatu?"Karki manta ni na haifi Aydah na kawota a duniya duk wani takunta a tafin hannuna yake ina jin wancan aikin dai da ya yi ya lalace yanzu tashi za kiyi muje a ɗora sabo,wannan karon har Alhaji Bashir nakeso a saka aciki dan duk yadda nakeso na raba aure Aydah da wannan yaron mahaifinsu shine mutum na farko dake takamin burki.
Wannan karon ko nawa zan iya zubewa Abba yabar rayuwar Aydah har abada ya saketa saki uku,shi kuma Alhaji Bashir ya kori Abba daga gidansa gab aki ɗaya,ya karbi duk wani abu da yasan na shine a wurin Abban wani miskilin murmushi Hajiya Zeenah tayi anzo wurin da take so a taho,daman bata da buri ita da mijinta da ya wuce Abba Bashir yabar rayuwar gidan Alh Bashir na har abada babu wani bata lokaci Hajiya Zeenah ta dauko mayafinta ta raka mami,wurin malam sun ɗan bata lokaci kafin su samu ganin malam.
Anan Mami ta faɗa masa bukatarta
Dan kafin su isa sai da Hajiya Zeenah ta gargadeta akan karta kuskura ta raina aikin da yayi mata a baya kawai ta faɗa masa tana son ai mata aiki wanda yafi wanda yayi mata a baya "buƙatar ki zata biya muna bukatar shanu guda biyu bakar akuya guda biyar za'a yanka jinin ne ga aljanin da zai yi maki aiki.
Cikin rawar jiki Mami tace to zan iya bada kuɗin sai a siya?"
za ki iya bayarwa wannan karon baƙaƙen aljannu ne za suyi maki aiki,daga yaron da za'a yi aiki akansa har mijin naki suna da ibada sosai, kuɗin aikin ki dubu ɗari biyar ne har dabbobin da za'a siya. Dan jim Mami tayi tana tunanin yawan kuɗin dake cikin account ɗinta ba zasu wuce naira dubu ɗari uku ba yanzun ma dubu ɗari biyu ta taho dasu cash,zan iya tura ma ta account idan na haɗa kuɗin.?"
"Babu damuwa za mu sa aljannu su tura maki account number.
Da haka Mami suka yi godiya
suka fita daga ɗakin da baya da baya.
A mota Mami ta kalli Hajiya Zeenah da damuwa a fuskarta tace "Hajiya Zeenah ina zan samu dubu ɗari biyar dukka kuɗin account din na bai kai haka ba.
Da mamaki Hajiya Zeenah ke faɗin "auh dama baki da kuɗin kika saka muka je wurinsa?"ni watarana idan kina faɗin baki da kuɗi sai nayi ta mamaki wallahi,kamar ke matar Alhaji Bashir za'a ce dubu ɗari biyar tafi karfinki.
"Uhm! Hajiya Zeenah kenan kamar dai baki san Alhaji bane,waya faɗa maki haka kawai yake sakin kuɗi batareda wani kwakkwaran dalili ba. "Yanzu dai tunda kina da kaddarori haka ma 'ya'yanki sai ki siyar da wani abu ki biya buƙatarki daman ance ranar biyan buƙatar rai ba a bakin komai yake ba.
"Haka ne zan duba na gani me ya dace na kaɗarr.
Mami ta faɗa a hankali sai tsinewa Abba Bashir take aranta duk yabi ya mayar da ita mushrikar karfi da yaji tana zaman-zamanta yajaza mata masifa.
Da yamma wuraren karfe 5 AB ya fito cikin shirin fita da shi da Rumaisah sun yi kyau har sun gaji kana kallonsu kasan sababbin ma'aurata ne kai tsaye AB ya nufi ɗakin
Aydah da wani irin kallo Rumaisa tabisa dashi tana jin wani katon abu yana tsaya mata a wuya, duk yadda take so ta hana kanta kishin Aydah ta gagara dan bataga wani abun da zata yi kishi dashi ba ajikin Aydah da tafita komai da komai nesa ba ma kusa ba. Banda namiji bai san kunya ba kuma maye ne yana da kamar ita me zai tsinta ajikin Aydah kwailah da ita downstairs ta nufa ta zauna can tana jirasa kar ta tsaya nan ranta ya ɓaci a banza a wofi.
A hankali ya tura kofar ɗakin nata,kwance ya sameta da waya a hannunta tayi nisa cikin karatun da take na littafin (Muhabbatil Qalb)na Asmy b Aliyu har bata so ta tsayar da karatun sai take ganin jaruman cikin littafin kamar ita da yayanta lokaci ɗaya taji an fisge wayar,a mugun tsorace ta dago tayi arba da fuskar yayanta wanda ya haɗe cikin farin voyel mai manyyan zane yayi kyau matuka, zuciyarta ta shiga wani irin dokawa da wani irin ƙarfi kurawa wayar ido yayi na son ganin abunda ya dauke mata hankali har haka Da sauri ya kalleta da zallar mamaki cikin fuskar sa kunya kamar zata kashe Aydah kuma daidai wurin da ake zuba zallar soyayyah tsakanin maina saraki da Asma'a saraki ya duba.
"Baby!!!
yay faɗa da bayannanen mamaki a muryarsa,ko a mafarki ko a gaske bai taɓa tunanin kanwar tasa tana irin wa'yannan karance-karance ba. marairaicewa tayi duk jikinta yayi sanyi, da ido yake tambayarta yaushe ta fara wannan?"jin taki magana ya mika mata wayar da wani yanayi a muryarsa yake faɗin."zamu fita da Rumaisah me zan taho maki dashi?"
Sai da ta kalli fuskarsa ganin ita yake
kallo sai tayi saurin dauke fuskarta cikin nasa,wani irin kishi taji yazo ya rufe mata zuciya wanda bata taɓa jin kalarsa ba,batareda ta kallesa ba tayi masa fatan a sauka lafiya.
Juyawa yayi ya nufi kofa batareda yace komai ba kasa jurewa tayi da gudu taje ta rungumesa ta baya gamida zagaye hannayenta acikinsa wani irin dumi jikinsa ya dauka tsikar jikinsa ta tashi ya saki kayataccen murmushi tare da shafa hannayenta dake zagaye da cikinsa.
"Shagwabar ta motsa kenan.
Ya faɗa yana dawowa da ita gabansa tura masa baki kawai tayi tana so tasan hanyar da zata hanasa wannan fitar tana so ta koyawa Rumaisah hankali da take daukarta ƙaramar yarinya.
Samun kanta tayi da ɗora hannunta akan kafadarsa ta ɗora kafafunta akan nasa saboda tsayin yayan nata ya yi yawa.
Wani irin numfashi AB ke fitarwa mai zafi sai kokarin kaucewa yanayin da baby Aydah ke son sakasa yake buɗe baki yayi da nufin yayi mata magana
tayi saurin hura masa iska wani irin lumshe ido AB yayi yana kiran sunan Allah aransa.
"Baby Aydaaah!"
Ya faɗa yana jan sunan har ya fara fita a hayyacinsa ganin yadda take bin dogon wuyansa tana shafawa aranta ta shiga faɗin."1,2,3 gooooooo saukar bakinta yaji acikin nasa tana yi masa wani irin sha wanda ya kusan zautar da AB yasa jikinsa ya shiga jijjiga yana wani irin rawa zufa na karyo masa ta ko'ina duk da sanyin AC dake cikin dakin, ta ciga ba da kissing dinsa tana tallabe da kansa.
"Allahu Akbar!
AB ya cigaba da zuba kabbara aransa bai taɓa sanin daɗin kiss ba irin wannan lokacin tuni baby Aydah ta cillasa wata duniya,ran Rumaisa idan yayi dubu ya ɓace ta shiga duba agogon hannunta kusan minti goma zaune tana jiran Abba,wannan wane irin iskanci ne da rainin hankali
A fusace ta nufi sama a zuciya tana faɗin."sai ta koyawa Aydah hankali
tura kofar ɗakin tayi batareda neman izini ba dan kallon kofar Aydah tayi
Dan AB har ya fara barin jahar Kano
Wani irin mummunan bugawa ƙirjin Rumaisah yayi tsayawa tayi kamar statue tana kallon yadda AB yake sakin numfashi agaban yar cikinsa,miskilin murmushi Aydah ta saki ganin yadda shock ya kama Rumaisah lokaci ɗaya Aydah takai hannunta kan wandon AB tana jansa da mugun rawa Rumaisah ta buga kofar,da gudu ta nufi ɗakinta tana jin kamar zata shede saboda kishi wani irin mugun kuka ne ya kwacewa Rumaisa da sauri ta rufe bakinta kar Huwaila taji sai kusan ƙarfe shidda da rabi AB ya fito ɗakin Aydah acan ya samu yayi wanka daƙinsa ya nufa ya sauya kaya yana jin kunyar abun da ya aikata,sai lokacin ya tuna da Rumaisah zuciyarsa ta wani irin harbawa da sauri ya nufi ɗakin ta yana duba agogon hannunsa kwance ya sameta akan bed ta cire kayan jikinta daga ita sai yar shimi wacce ta sauka kan gwiwowinta yadda yaga idanunta sun kumbura abun ya basa tsoro da sauri ya nufeta yana kiran sunanta tun kafin yakai ga jikinta taja da baya a wani irin birkice tana daga masa hannu tsayawa yayi da mamaki yana kallonta ita ma ɗin kallonsa take ido cikin ido tana jin wani irin zugi har cikin tsakiyar zuciyarta,ta kasa mantawa da yanayin da ta samu Abba da Aydah ko ita da ya aura dan so bata taɓa ganin ya shiga wannan yanayin ba akanta.
"Habibty ya kuma kika cire kayan kin fasa zuwa asibitin ne?"
A haukace take faɗin."asibiti ashe kana sane? awa ta nawa ina jiranka zaune a parlor kana can kana nanniƙar 'yar cikinka dan Allah Abba bakaji kunya ba?"bakaji wani iri ba ka saka yar cikin ka agaba kana laluba?"wane kalar daɗin baki ne bakayi min ba kafin auren mu. Ka sha faɗamin baka sonta baza ka iya taɓa haɗa shimfiɗa da ita ba sai gashi yau da idanuwa na ganka ka saki tazuge wando ka miƙawa yarinya nan da ka gama rainawa ragamar rayuwarka tana sarrafa ka iya sarrafawa kai kuma sai ihu da sambatu kake zubawa kamar wani wawa kaiconka Abba wallahi-tallahi ka yi asara ka kuma bani kunya ka zama ganga mai baki biyu ka daki nan ka daki can nayi tir da halinka Abba tare da nadamar aure ƙasungumin munafuki kamar ka.
"Rumaisah!!!
Ya faɗa a tsawace ya zuba mata fararen idanunsa da suka fara canja kala yana wani kalan huci.
"Ya isheni haka?"waya bani damar zuwa wurin Aydah ina jin ke kika buɗe min kofar zuwa wurinta ko kin manta ne ba tuna miki, ko kuma so kike naje nayi zina gani da mata acikin gidana wacce Ubangiji ya yarjemin na je gunta a duk sanda buƙata ta taso min?"
Ya faɗa yana tsareta da idanunsa.
"karki fara trying ɗina da yamman nan ki sameni a mota mu je a nema miki lafiya.
Ya ƙarasa magana yana juyawa yana bar mata ɗakin gami da banging door ɗin.
Har cikin kwanyar kanta taji bugun kofar,saboda lafiyarta ne zai sa ta bisa ba wai saboda tana tsoronsa ba daga shi har Aydah sai ta gyara masu zama
saboda rashin ta ido irin na fa namiji wai kamar kato irin Abba Bashir shi zai riƙa haikewa kamar Aydah ita ma da tafita girma da cika watarana jarabar Abban isarta take sai dai ta daure kawai duk da kuwa tana shan maganin mata to ina da bata haɗawa dasu ta tabbata ba za ta iya jure jarabarsa ba,har ta shiga mota suka hau titi babu wanda ya kara magana a tsakaninsu kowane yana ji da miskilanci da ɓacin rai shi a ganin AB akan wane dalili Rumaisa zata tuhumesa akan alaƙarsa da Aydah alhalin tana matarsa,har cikin harabar asibitin Dr Sameer matawalle ya yi parking motarsa Rumaisa ta fitar da waya tana kiran Dr. Sameer matawalle ɗin wanda Auntyn ta Raliya ta haɗata dashi,bugu ɗaya ya dauka cikin sanyin murya take masa bayanin ita ce kanwar Raliya madawaki acikin wayar ya yi mata misalin office ɗinsa ,tana sauke wayar ta nufi reception batareda ta kara kula AB ba bin bayanta kawai yayi dr Sameer matawalle ya miƙawa AB hannu suka yi musabaha ya nuna masu wuri suka zauna kana ya dubi Rumaisa yana faɗin."kin batamin lokaci madam ina da gun da zan je amman haka na share wuri ina ta dakon zuwanki.
Wani irin abu Rumaisah ta haɗe tana jin daci a maƙoshinta idan kuma ta tuna dalilin tsayawar tasu sai taji wani irin abu yana taɓa mata zuciya da ruhi har yanzu tunanin matakin da zata daukarwa Aydah take sai ta nuna mata ita karamar yar iska ce. Maganar Dr Sameer matawalle ya dawo da Rumaisah daga duniyar tunanin da ta faɗa.








#JEEDDAH ALIYU
#ASMY B ALIYU
#KURMAN ALLO.








Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only




ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130


KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730


Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336






*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.


*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar


*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu


*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce


*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari


*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan


Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500


VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k


NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[1/25, 1:45 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)


NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU


#Love story
#Gwagwarmaya
#Team tagwaye Novels




082.




"Madam ya kike ji yanayin jikin naki sannan jini yana zuba sosai ne?"
Sai da Rumaisa ta gyara zamanta kamin ta shiga kwararowa Dr Sameer bayani har ta kammala bai katse ta ba. Ya ɗauki wayar landline ya kira nurse station ya nemi gani nurse Salma bayan ta zo da taimakonta ya yi yiwa Rumaisa duk wani bincike da ya dace ya yi mata, sai dai babban abun da ya ɗaure masa kai har ya kammala bincike nasa babu wani matsala da ya gani wanda zai haifar mata da bleeding.
Ya dawo ya zauna akan kujerarsa ya kalli AB a natse ya ce "Gaskiya Yallaɓai iya bincike da na yiwa madam batada wata matsala da za ta haifar mata da zubar jini, amman duk da haka zan ɗora ta akan wa'yansu magunguna in shaa Allah za a dace.
Ya rubuta musu prescription ɗin ya miƙawa AB godiya Ab ya yi masa tare da sake basa hannu suka yi musabaha akan hanyar su na zuwa gida ya tsaya a wani pharmacy ya siyo mata magani ɗin. Ɗan satar kallonta Ab ya yi yadda yaga ta rafka tagumi sai ya ji tayi bala'in basa tausayi abin ka da zuciyar masoyi, hannunsa ya kai ya sauke mata tagumin kana ya matse hannun nata cikin nasa, ya wani kwatar da murya ya ce "I'm so sorry Habibty nasàn kina jin haushina kisani duk yadda muka kai da ƙi abu ba mu isa mu gujewa ƙaddarar mu ba. Dukka waɗannan abubuwa suna faruwa ne a bisa tsarin Allah, saboda haka ina so ki kwantar da hankalinki ko kaɗan banaso na ganki cikin damuwa kin ji rabin raina?"
Duk da Rumaisa ta ji dadin kalaman sa amma da tuna ko a baya da ire-iren waɗannan kalaman nasa ya yi amfani dasu ya yi mata igiza mai kattun ya ɗora ta akan hanyar da bata bullewa daga ƙarshe sai ta tsinci kanta a tashar kare yabarta da haushin karnuka. A wannan karo idan ta amince da maganganunsa shi kenan fa ta zama sa kayanka mota. Saboda haka ta kalle shi a lalace sai kuma ta kauda fuskarta ta maida ganinta akan ababen hawa dake kan titin.
Yadda AB yaga Rumaisa ta ba banza ajiyarsa sai duk ya ji babu daɗi har yana ɗorawa kansa laifi na biyewa Aydah da ya yi alhali yasan za su fita da Rumaisa kuma fitar tasu ta shafi neman lafiyar ta ne.
"Habibty na ce ki yi haƙuri in shaa Allah hakan ba za ta sake faruwa ba.
"Abba please ka kyaleni na ji da abun da yake damuna daman an ce kana gane masoyinka na gaske ne da zarar ka haɗu da wata lalura don haka yanzu na gama gane matsayin da nake dashi a wurinka tun da ina zubar jini banida sauran amfani a wurinka ka je duk abun da ka yi don kanka.
Rumaisa ta ƙarashe magana tare da rushewa da kuka irin mai cin rai ɗin nan hakan yasa AB ya nemi gefen titi ya yi parking, da sauri ya jawota jikinsa yana bubbuga bayanta.
"Ke ma dai Rumaisa da rigima kike kin fi kowa sani irin matsananciyar soyayyar da nake miki da matuƙar wahala a sami wata mace da za ta haura matsayinki a zuciyata.
"Uhm! A da ba nace a da ne nake da wannan matsayin ban da yanzu da ka dandani jikin ƙaramar yarinya.
"Subhanalillah! Haba Habibty ba girman ki bane faɗar wannan magana ki dinga tauna kalami kafin ki faɗe sa.
A fusace Rumaisa ta fincike jikinta daga nasa idanunta na ambaliyar hawaye ta ce "Na ƙi na tauna ɗin ai gaskiya ce na faɗa akan jikin Aydah duk ka bi ka canza min ka dawo wani susu ko uban me kake ji anata wanda ba ka ji anawa?"
"Oh! Ni Bashir ɗan Bashir yau naga takaina ni dai ba za a ji mutuwar sarki a bakina duk masifar ki Rumaisa ni dai ba zan ce komai ba bakina da alawar madara.
Ya ƙarashe magana yana sake jawota jikinsa ya cigaba da kanainaye ta da daɗin bakinsa har dai ya shawo kanta daga nan ya wuce da ita shopping mall kuɗi ya kashe mata bana wasa ba, babban abun da ya ƙara saka Rumaisa farin ciki yadda taga AB ko sweet bai siyawa Aydah ba. Suna fitowa daga mall ɗin wurin shakatawa suka nufa sai soyayya suke zuba abin su sai gafda da magarib suka baro wurin, akan hanyar su na zuwa gida ya tsaya wani masallaci ya yi sallah yabar Rumaisa a mota da yake ita ba sallar take yi ba. Yana dawowa mota Rumaisa ta kalle shi cikin shagwaɓe murya mai ɗauke da kissa da kisisina ta ce "Habibina ina ta kallon hankalinka ko za ka bani special gift na budurcina da na kawo maka da yawan ƙawayena suna turomin da pictures ɗin kyatuttuka da mazajen su, suka yi musu a daren farkonsu.
Sai da AB ya tashi mota ya hau kan titi kamin ya juya ya kalle ta a ɗage ya ce "Idan haka ne meye amfani sadakinki da na biya kafin a ɗaura mana aure?"
"Ka ji ka da wani zance Habibi sadaki daban wannan tukuici ne za ka bayar ba ka ji wani karin maganar da ake cewa yaba kyauta tukuici ba?"
"Uhm! Haka ne. Amma wannan wata sabuwar bidi'a ce da ku mata ku ka kikkire ta daman can ku bakwso a zauna lafiya.
Dariya Rumaisa tayi tana ƙara kwatawa jikinsa tare da marairaice murya "Allah Habibi haka ake yi kasan kai kifin rijiya ne wasu abubuwan ba damuwa ka yi

60 / 80