Kurman Allo Sakamakon Kin Karɓar Gaskiya by EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU

Author :  EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category :  KDP NOVELS

Chapter   75 / 80

222K to 225K   out of 237.2K words

B ALIYU


#Love story
#Gwagwarmaya
#Team tagwaye Novels




100.




Ganin yadda ya tunkarota gadan-gadan yasa lokaci ɗaya Aydah ta haɗe rai tana ƙoƙarin canja wata hanyar sai dai ta makara jin ta yi an rike hannunta sosai an nufi inda tayi parking motarta,kallonsa ta yi cike da ƙarfin hali waye ya basa ikon ya rike mata hannu har haka?" Ta lura Marwan Garkuwa bashi da hankali a yan kwanakin nan yana takura mata yana mata naci akan abun da yasan ba zai taɓa faruwa ba a tsakaninsu ko a mafarki Barantana a gaske,har ta kai ta kawo tana tsoron ta shigo makaranta taci karo da fuskarsa ,duk inda ta shiga idonsa na kafe akanta. Ta gaji ta gaji da wannan nacin nasa,lokaci ɗaya ta fisge hannunta cikin nasa cikin tsiwa da ɓacin rai take faɗin."meke damunka ne? wai meyasa duk inda na shiga sai ka bini?"kai babu zuciya ne dashe a kirjinka ne wai? Ta ƙarasa maganar cike da wani yanayi a muryarta harɗe hannu ya yi a ƙirjinsa yana kallonta. Sai kace babu wani abu da zai gabatar a rayuwarsa baya ga kallon nata,girarsa ta sama ya tattare ya haɗe wuri ɗaya.
"Buɗe motar da hannunki ki shiga magana za mu yi.
baki buɗe take kallonsa "Saboda ga ka ubana.
Ta faɗa so pissed up a muryarta.
"karki yi trying ɗina da safen nan ko break fast ban tsaya nayi ba na fito dan kawai na zo na ganki shi ne kike so ki ɓatamin rai shiga nace. Ya ƙarasa magana da ɗaga murya yana wani haɗe girar sama da ƙasa.
Dariyar rainin hankali ta fashe dashi wallahi abubuwan Marwan Garkuwa dariya suke bata mutum sai shegen manyyance tasan shekarun Marwan ɗin ba za su wuce 20 years ba tsawon kafa kawai ne ke jansa da girman jiki yana bata umarni sai kace ubanta. "Idan naki ɗin me za kayi?"
hannun rigarsa ya shiga tattarewa lokaci ɗaya ya fisge car key ɗin dake hannunta ya danna motar ta buɗe ganin ya nufota gadan-gadan da gaske daukarta zai yi yasa ta nufi motar cikin tsiwa take faɗin "me kake shirin yi haka?"Marwan wai kai sai kace wani mai shekaru kayi ta abubuwa irin na manya yaro da kai.
Ta faɗa tana buɗe bangaren driver ta zauna fuskarta a murtuƙe,shiga ya yi ya zauna frontseat yana rufe ƙofar hannu yasa ya dannawa kowace ƙofa lock,kallonsa kawai take.
"kara maimaita abun da kika ce a waje?
Wani kalar zaro ido tayi ganin yadda yake kokarin haɗe fuskarsa da tata har tana jin saukar numfashinsa saman fuskarta wani irin bugawa zuciyarta ta shiga yi da sauri ta matsa
ɗan murmushi ya saki ya riko hannunta duk yadda take kokarin kwacewa ya kasa sake mata hannu
Da wata irin murya yake faɗin."fadamun shekaruna basu kai nayi aure ba da kike rainamin shekaru?"wannan karon cikin ido take kallonsa ta fincike hannunta da karfi cikin nasa "ka daina tabani bana so. Da gaske kai ɗin yaro ne dan ba zan iya aurenka ba ka min kankanta.
maganarta ya ji tana bata masa rai rigarsa yake kokarin cirewa a gabanta wani irin ihu ta sakar masa tana wani rufe idanunta babu inda jikinta baya rawa.
"ki buɗe ido ki kalleni ki ga jikina idan akwai yarinta acikinsa.
"Wallahi Marwan zan maka ihu ka buɗe min mota na fita wai meyasa kake min haka ne"?rigarsa ya mayar yana kallonta da wani yanayi acikin idanunsa yake faɗin."ki bani dama naje gidanku na gabatar da kaina a wajen iyayenki,ko yanzu suke so ayi miki aure iyayena basu da matsala ,daga nan idan aka yi auren zan baki ciki na tabbatar maki dani ba yaro bane.
"Wallahi ka daina wannan mafarkin ba zan taɓa auren yaro kamar ka ba. "wai an faɗa maka bani da aure ne balle ka dame ni da zance aure? Wallahi ka fita sabgata ko na haɗaka da mijina Marwan.
Wani murmushi mai ciwo ya yi yana faɗin "nasan mijinki ya rasu ki daina yimin karya magana na karshe komai zai faru baz an iya rabuwa dake ba zyulaiha ki rubuta haka ki aje,kuma ki cigaba da kirana yaro watarana sai kin fusatani nayi maki abun da baki taba tunani ba wanda mu dukanmu ba za mu ji daɗinsa ba ki kiyaye karki kure hankurina.
"To ubana budemin kofa naji.
Ta faɗa cike da tsiwa tana tura masa bakinta
Murmushi ya yi yana shafa sumar kansa,kusan tare suka fito motar ya danna key motar ta rufe ya karbi handbag ɗinta ya saka mata key ɗin
"Mu je ki rakani nayi break fast ko cikin cafteria ne babu komai acikina. Duk kin bin kin hargitsa min lissafi.
Sanin halinsa na naci yasa tayi gaba yana bin ta a baya duk yadda zata yiwa Marwan Garkuwa wulaƙanci ba zai daina nace mata ba.
Haka yake ko cikin class suke suna daukar lecture baya son yaga wani namiji ya zauna kusa da ita,abu ɗaya take so a tare dashi ƙoƙarinsa yana da wani irin ƙoƙari na ban mamaki dan shi ne class rep ɗin ajinsu.Yammatan class ɗinsu kuwa kowace so take Marwan Garkuwa ya kulata wanda ita haka baya gabanta tasan dai ba zata taɓa son Marwan ba,namiji ɗaya ke da wannan matsayi a zuciyarta matsayinsa ba zai taɓa canja ba har tsayawar numfashinta. Yinin ranar duk inda ta sauke kafa anan Marwan ke sauke tasa har ta gaji da yimasa magana ta zuba masa ido.
Bayan ta koma gida da dare kawai tayi tunanin turawa Daddy,lambar Aunty Huwaila. Sai dai acan kasan ranta tana son ganin mahaifinta cikin farin ciki, sai dai bata san ya Mami
za ta ɗauki al'amarin ba. Kusan sati ɗaya da maganar Huwaila da Daddy,kuma tun ranar Daddy yaga Aydah ta tura masa lambar sai dai bai dauka ba barantana ya kira, yau yana office wuraren karfe biyu ya kira Aydah ita ma fitowarta kenan daga lecture,yace idan ta gama lecture ta samesa a office kai tsaye can ta nufa idanunta har rufewa suke saboda yunwar da take ji, kallo ɗaya Daddy ya yi mata yasan yunwa take ji masinjansa ya akai yayo mata take away anan cikin office ɗin Daddy ta shiga cin abinci kamar Allah ya aikota, sai bayan da ta natsu Daddy ya kalleta yana faɗin "wurin Auntynki zamu je tun da har yanzu kin yi shiru kinki gabatar mata dani,baki buɗe Aydah ke kallon Daddy,kafin tace "na fa tura maka lambar tun ranar Daddy kuma naga ka buɗe ba kace komai ba.
"Idan na kirata nace mata me?"mu dai je kiyi mata bayani kafin nawa ya biyo baya. Idan ta yarda zata auri tsoho kamata shikenan idan kuma bata yarda ba ba zan mata dole ba, dariya Aydah ta fashe dashi tana faɗin "Daddy ba ka fa tsufa ba infact kana da kuɗi kuma tsoho da kuɗi yaro ne. murmushi kurum Daddy,ya yi acikin motar Aydah suka nufi gidansu Huwaila Ita dai Huwaila tamkar a mafarki take sauraren Aydah jin wani zance da take kamar almara,da sauri Huwaila ta shiga girgiza kai tana faɗin."wannan cin fuskar ya yi yawa Auta ba zan iya ba bakya tunanin irin abun da zai biyo baya daga wurin Mami. Ni dai tsoro nake ji wallahi.
"tsoron me za ki ji Aunty Huwaila Daddy ne fa Daddyna kin san halinsa fa kuma da kike tunanin Mami,Mami bata da matsala ta canja wallahi.
Haka Aydah ta yi ta fama da huwaila har ta amince,dakyar tace ta je taga Daddy yana zauren gidansu yana jiranta ita zata zauna anan ta jira har su gama
Wani irin nauyin Daddy Huwaila ta rika ji bayan ta fita ta samesa komai ganinsa take tamkar a mafarki haka Daddy,yace kar ta damu ba zai takura mata ba ya bata sati ɗaya ta je tayi shawara idan ta amince zai turo da magabatansa da haka suka rabu. Cikin sati biyu Huwaila ta sake da daddy har ya tura da magabatansa an tsayar da magana baya son bikin ya dauki lokaci aka saka sati biyu za'a daura aure sati biyu daga baya sai ta tare,Daddy Sadiya ya turawa kudi ta account ɗinta akan ta haɗa lefen Huwaila haka ta kira Siyama,a waya suka saka rana suka shiga kasuwa suka rika haɗa kayan lefe suma sai da suka saka gudummuwarsu aciki dan lefe nagani na faɗa suka haɗa,haka Daddy ya shiga gyaran gida ya canja furnitures duka,Mami nata murna yanzu komai ya daidaita tsakaninta da Daddy,suna zaunawa suyi hira kuma yana sake mata fuska sosai.
Ana sauran kwana huɗu a daurawa Daddy,aure da Huwaila da dare Daddy ya yanke shawarar ya sanar da Mami ya kirata a waya kafin ta zo sai da ya tura mata miliyan biyu a account ɗinta ,da fara'a Mami ta shigo falon na Daddy dan tana riƙe da wayarta taga alert kuma daga wurin Daddy ta samu wuri ta zauna, "Daddy naga ka turamin saƙo yanzu Allah ya kara budi da daukaka.
Mami ta faɗa sounding so happy,
"Ameen ameen!
Daddy ya faɗa kafin ya karkace kai ya fara yimata bayani duk cikin bayanan da yake mata daurin aurensa sauran kwana huɗu shi kaɗai ta fahimta.
A gigice ta miqe tsaye hawaye suka wanke mata fuska "tozarcin da ka shirya yimin kenan Alhaji da shekaruna za ka yi min kishiya?"wallahi sai dai ka zaba koni ko ita ba zan zauna da kishiya ba watau shine ka hau gyaran gida kou?"namiji munafuki wallahi ba zan zauna da kishiya ba.
Mami ta ƙarasa magana a fusace tana ficewa fuuuuuu tabar Daddy ,sake da baki
Aydah na kwance a ɗakinta ta saka baby Noor a gaba tana yimata wasa taji an turo kofar ɗakinta da mamaki ta daga kai suka yi ido biyu da Mami, ganin yanayin Mami ya kayar mata da gaba da sauri ta sauko daga kan bed ta nufi Mami,tana tambayarta lafiya?"kuka Mami ta fashe dashi tana samun wurin zama anan gefen bed ɗin Aydah. A tsorace Aydah ke faɗin."Mami ki faɗamin wani ya mutu ne?"
"Ba kara ace mun mutuwa aka yi ba da abun da Daddynku keso ya yi min ba so yake
Ya kunyatani cikin kawayena da yan uwana da tsufan Daddynku zai ce zai kara aure. Shiru Aydah tayi aranta take faɗin "Daddy ya fasa kwan kenan.
Cikin sanyin murya Aydah ke fadin"to Mami meye aciki dan Daddy ya kara aure kinga ba haramun bane?
baki buɗe Mami ta juya tana kallon kalaman dake fitowa daga bakin Aydah."Banyi mamakin jin fitowar wa'yannan kalaman daga bakin ki ba. Daman can ba kaunata kike ba kinfi kaunar mahaifinki akaina munafuka muguwa marar tausayi waya sani koda ke kuka haɗa kai keda mahaifin naki aka munafuce ni. To wallahi babu shegiyar da ta isa ta shigo gidan nan a matsayin kishiyata.
A fusace Mami tabarwa Aydah ɗakin,Mami na shiga ɗakinta ta saka key a kofarta ta dauki wayarta ta kira Sadiya.
Sadiya na dauka Mami ta fashewa Sadiya da kuka. hankalin Sadiya a tashe ta shiga tambayar Mami meya faru."Mahaifinku yake so ya tozartani Sadiya,da yarintata ba ai min kishiya ba sai yanzu.
Shiru Sadiya ta yi ta rasa me zata cewa Mami,sai ta fara rarrashin Mami,
tana faɗin "gobe Mami zamu zo nida Siyama ,dan Allah ki kwantar da hankalinki komai zai zama daidai.
Sadiya ta rika rarrashin Mami, da kalaman kwatar da hankali.
Har ta samu ta haƙura tace ba za ta je ko'ina ba. Washe gari Mami ko kallon Daddy ba tayi ba barantana ta kawo masa break fast Aydah ce ta shiga kitchen ta yiwa Daddyn komai. Banda harararta babu abunda Mami keyi.
Daddy,yana gama break fast ya wuce office ita ma Aydah karfe 10 ta fita school har daki ta sami Mami,tace mata ta tafi school banza Mami tayi mata haka ta gama tsayuwarta ta wuce makaranta bata dade da tafiya ba sai ga Sadiya da Siyama banda faduwa babu abunda gabansu keyi basu san ya mami zata dauki zancen ba,cike da karfin hali Sadiya ta shiga yiwa Mami,bayani tun neman shawarar da Daddy yayi a wurinsu haka Siyama,ta ɗora da nata with shock Mami ke kallon ya'yan nata watau da ya'yanta na cikinta aka haɗa baki akaci amanarta, batareda Mami tace komai ba ta mike tsaye ta nufi toilet da ido suka bi ta,har kusan minti goma ba su ji Mami ta fito ba Siyama ta ƙarasa kofar toilet tayi knocking tana kiran sunan Mami,muryar Mami ta ji tana faɗin "kafin na fito dake da Sadiya ku barmin gidana na kar na fito na yi maku baki.
kalaman Mami ba ƙaramin razanasu ya yi ba ko minti biyu basu kara ba suka bar gidan, Siyama ta kira Daddy a waya tana kuka tana faɗin "ko Daddy za ka fasa auren nan Mami bata dauki al'amarin nan da sauqi ba?
"ki kwantar da hankalin ki Siyama, ni ba ƙaramin mutum bane aure babu fashi idan taga an daura dole za ta hakura.
Da haka Daddy ,ya kashe wayar batareda ya tsaya jin me Sadiya za ta faɗa ba.
Ranar juma'a da misalin ƙarfe biyu na rana bayan an tashi masallaci dubban mutane suka shaida daurin auren Alh Bashir da Huwaila akan sadaki Naira dubu dari.










#JEEDDAH ALIYU
#ASMY B ALIYU
#KURMAN ALLO
[2/9, 7:41 AM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)


NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU


Love Story
#Gwagwarmaya
#Team Tagwaye




101.






*LAGOS NIGERIA*




Duk tsawon kwanaki da Aliyu na Uku ya dauka da dawowa Lagos, Anaal bata dawo ba kuma wayarta a kashe wannan al'amari ya daga masa hankali matuka har ya fara tunani ko masu garkuwa da mutane ne suka yi masa awon gaba da 'ya, to idan sune miyasa har yanzu basu kira sa sun faɗi kuɗin fansa ba?" A halin yanzu ya yanke shawarar zai tafi Kano ya je police headquarter dake Kano ɗin ya kai report jirgin karfe biyu zai bi zuwa Kano ɗin. Sai gashi yau yana zaune a ofishin sa kiran ya shigo wayarsa na mutumin da ya ba wa aiki ya binciko masa Bashir shamaki, da farko ya yi bincike aka ce yana Katsina koda suka je Katsina ba shi bane sunan ne kawai ya zo ɗaya. Cikin sanyi jikin Aliyu ya yi picking, wani kalar miƙewa tsaye Aliyu ya yi "Ka tabbata Kabir Umar kada ka yi min irin na wancan lokaci kasa min hope sai da na je naga ba haka bane?
"To shikenan daman yau zan je Kano sai mun haɗu.
Agaggauce Aliyu ya baro kamfani ya wuce gidansa wanda yanzu, Maysun ce ke zaune a ciki a main parlor ya tarar da ita zaune akan two seater ta rafka tagumi ga baki ɗaya ta rame ta zage, burinta taga ɗanta ba karamin so take yi wa Azhar shi ne rayuwarta. Rashin samun takamaiman inda Bashir shamaki da Maryama suke ya yi bala'in daga mata hankali, kullum da sabuwar karya da Aliyu zai zo mata da ita duk kokari da yake yi bata gani, sai ma ta danganta hakan da karya.
Dauke mata tagumin da ya yi tare da zaunawa gefenta ya ɗan rungumo kafaɗarta "Ki yi haƙuri my love in shaa Allahu komai ya kusan zuwa ƙarshe yanzu nan na sami kira mai muhimmanci Bashir shamaki yana zaune a garin kano hatta da address ɗin gidansa Kabir Umar ya turomin, ki kwantar da hankalinki in shaa Allahu za a ga Azhar ɗinki cikin ƙoshin lafiya.
A maimakon Maysun ta yi farin ciki da jin kalamansa sai ta fusata ta ɗago kodaddin idanuwanta, ta dube shi dasu "Ka ga Ali ka barni na ji damuwar da kai ɗinan kaine silar jefa ni acikinta. Kullum cikin bani fake hope kake idan har ka salwantar min da ɗa dan Allah ka fito fili ka faɗa min gaskiya, na tattara na koma Qatar da ka dinga bani karya cewa za a gansa, ina saka raina akan hakan gwara nasan gaskiya nayi kokari fitar dashi daga raina.
Tun sanda Maysun ta fara magana Aliyu na Uku ya yi mutuwar zaune yana kallonta, babban abin da yafi bashi haushi da takaici bai wuce cewa da ta yi idan ya salwantar mata da ɗa. Me take nufi da wannan kurman allon nata ko tana nufi shi da kansa zai ɓatar da ɗansa na cikinsa. Miyasa a koda yaushe Maysun bata masa uzuri kamar yadda Safiya take masa. Kodai Maysun ta daina sonsa ne shi kaɗai ke wahalar banza akanta?
Ransa ya yi mugun ɓaci ya miƙe tsaye tare da jefa idanunsa cikin nata, cikin fusata ya ce "Duk kokari da nake yi bakya gani Maysun karka fa ki manta kace sanadin shiga ta dimbin matsaloli da har kawo yanzu na kasa warware su, idanuwanki sun rufe kin kasa fahimtar irin halin da naki ciki kanki kawai kika sani idan kina magana dangane da ɓatan ɗanki mai shekara ɗaya, ni kuma yata mai shekaru ashirin da biyar a duniya na nema na rasa yau kwananta takwas bansan inda take ba. Saboda haka ba zan bari akan wani self-interest dinki ki ƙara haifar min da wata damuwa don haka ki tattara ki koma Qatar na yi miki alƙawari zan cigaba da neman ɗanki har izuwa ƙarshen numfashina, idan da rabo na gansa a raye zan kai miki shi har Qatar na damki miki shi a hannunki.
Wani irin zaro idanuwa Maysun ta yi cikin kaɗuwa take kallonsa lallai Ali ya canza mutumin da yake lallaɓata da rirrita ta, tamkar kwai akan spoon wai yau shi ne yake mata magana da kakkausar murya mutumin da a shekarun baya, ko wani ya daga mata murya sai inda ƙarfinsa ya ƙare yau shi ne tsaye a gabanta yana faɗa mata maganganu marasa daɗi har yana iƙrarin ta tafi kasar su.
Wani irin kuka mai cin rai ta fashe dashi kallonta ya yi tare da girgiza kansa ya juya rai ɓace ya haura sama ɗakinsa ya shiga ya canza kaya zuwa farar shadda dimkin babbar riga, jikinsa na fidda ƙamshin turarensa har ya dawo cikin parlorn Maysun na rera kuka gabanta ya tsaya still fuskarsa a haɗe ya ce "Ni zan wuce Kano jirgin karfe biyu zan bi idan za ki cigaba da zama dani ƙofa a buɗe take idan kuma Qatar ɗin za ki koma ina miki fatan sauka lafiya.
Ya karashe magana tare da juyawa zuciyarsa tana masa tuƙuƙi, da sauri Maysun ta taso ta rungumesa ta baya tare da zagaye hannayenta a cikinsa ta ɗora kanta a gadon bayansa "Ka yi haƙuri Ali na kasa riƙe kaina ne gani nake yi kowanne lokaci zan iya tafiya batareda da idanuwana sun yi tozali da Muhammad Azhar

75 / 80