Kurman Allo Sakamakon Kin Karɓar Gaskiya by EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU

Author :  EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category :  KDP NOVELS

Chapter   12 / 80

33K to 36K   out of 237.2K words

sai dai babu ƙarfi ko misƙala-zarrati a jikinsa yini guda har ya yi rama. Ya jiki suka yi masa kafin kowacce su ta nemawa kanta wurin zama ganinsu yasa AB ya fice zuwa masallaci saboda azhar da la'asar dukka a ɗaki ya yi su nan da can bai matsa ba yana tare da Daddy. Ana kammala sallah AB ya dawo shi ya taimaka wa Daddy ya yi alwala kana ya yi sallah anan AB yabar su Mami ya tafi gida ya ɗebo abubuwan buƙatarsa misali ƙarfe 10:15pm Daddy ya umarci Mami da tashi su tafi gida ba don ransu yaso ba suka baro asibitin especially Aydah.
Bayan tafiyarsu Mami Daddy ya kalli AB dake Istigifari da counter ɗin dake maƙale da yatsansa gyaran muryar da Daddy ya yi yasa shi ɗagowa ya yada ganinsa kan fuskar Daddy "Ka yi haƙuri Abba zancen aurenka da Mufeeda babu shi Alh Habeeb ya ce ba zai ba ka 'yarsa ba, duk da nayi iya ƙoƙarina na gani na ɓoye asalin kai waye amma abin yaci tura bansan daga ina ne ake fitar da wannan ɓoyayye sirri ba.
Dogon numfashi AB ya ja kana ya fesar kafin cikin raunatatciya murya ya ce "Daddy ka daina matsanta wa kanka akaina gashi nan silar wannan mutumin har jininka ya yi muguwar hawa, sai ɓoyewa su Mami asalin ciwon naka nayi domin banaso su ma su shiga damuwa kaman yadda ka ke ciki. Daddy wallahi zan iya riƙe kaina in-sha-Allahu ba ka taɓa kama ni da wani mummunan kaba'ira ba. Saboda haka dan Allah ka haƙura da zance aure nan.
Guntun murmushi Daddy ya yi wanda bai wuce iya fatar bakinsa ba shi kaɗai zai iya faɗar halin da yake ciki babban burinsa a duniya yaga Abba ya yi aure sai gashi ya kasa samun cikar burinsa.










#Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo.




Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only




ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130


KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730


Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336






*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.


*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar


*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu


*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce


*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari


*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan


Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500


VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k


NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[12/10/2023, 10:04 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful love story)


NA
ASMY B ALIYU
&
JEEDDAH ALIYU








#Love story
#Gwagwarmaya
#Team tagwaye novels




016.




*RUBUTUN ƳAN *TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU.*
*TAFIYAR BIYU TAFI ƊAYA*


*KIN TABBATA KIN CIKA MACE? BABBAR MACE DAKE JI DA KANTA? KINA CIKIN MATAN DA SUKA SAN KANSU? WANDA SUKA SAN MUTUNCI DA DARAJAR KANSU? KO KUWA KEMA KINA CIKI SAHUN SU O’O?*
*INA KUKE MANYAN MATA? WAƊANDA SUKA SHIRYA DAN GYARA JIKINSU? AURANSU? DA KUMA FARINCIKINSU?”
*KUYI MAZA KU GARZAYA GUN FITACIYGA KUMA INGANTACIYAR MAI MAGANIN MATA DA MAZA DAN AMSAR NAKU KU GYARA DA KANKU WATO MEERAH HERBS WACCE TAI FICE GUN KAWO MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA BA TARE DA ALGUS BA.*
Mun gwada mun gani 💯
Mun gani mun shaida 💯
Anyi mun gani 💯
MAGANIN SANYI
MAGANIN NONO
MAGANIN HIPS
MAGANIN SLIMMING
MAGANIN NANKARWA
GYARAN AMARE
GYARAN MAIJEGO
MALLAKAR MIJI KO MATA
SUBULU DA SCRUB
MAYUKA NA GYARAN JIKI
TURAREN WUTA
MATSI
MAGANIN NI'IMA
MAGANIN TSUMI
INFECTION FLUSHER DA DAI SAURANSU…..Uwar gida, Amarya, Budurwa, Saurayi, Ango, Mai gida? Duk mai kuke jira? Kuyi maza ku garzaya Meerah herbs maganin dake ingantace 💯


08142800199
07068558096










Musamman idan ya tuna da abinda Sadiya ta yiwa Abba sai ya ji zuciyarsa ta ƙara tsinke wa. A natse Daddy yake kallon kyakkyawar fuskar Abba wani irin ƙaunarsa ke bin jini da ɓargon jikinsa "Abba matuƙar ina numfashi a duniya sai naga aurenka domin shine burina kaɗai a duniya.
"Amma Dad....
"Karka ce komai Abba domin na gama yanke wa kaina shawara acikin 'ya'ya da na haifa uku mata don ɗaya ta kasa yi min biyayya ta zauna da kai hakan baya nufi raguwar biyun za su bijere min, saboda haka a karo na biyu zan sake aura maka ɗaya daga cikin ƙannanka.
A firgice Abba ya ɗago manyan idanuwansa yana kallon Daddy babu komai cikin idanuwan nasa face tsoro gami da fargabar a wannan karo bai kuma san da wa Daddy zai haɗa shi ba. Sai dai hasashen sa yafi karkata akan Siyama duk da tana da baiko wani akanta, ko kaɗan bai kawo Aydah a lissafin sa ba. Dukka maganganu da Daddy ya cigaba da yi ba wanda AB ya sake fahimta a dalili zuciyarsa ta bar gangar jikinsa. Satin Daddy ɗaya a hospital aka sallame shi zuwa lokaci jikinsa ya yi kyau sosai, yayin da shi kuma AB ya shiga ruɗani da zance zuci haɗe da neman mafita.
*MOONLIGHT AUTOMOBILE INDUSTRY KANO*
AB yana zaune a office ɗinsa damuwa tayi mishi katutu tun sanda Daddy ya yi masa zance sake haɗa shi aure da ɗaya daga cikin ƙannan shi ya rasa sukuni da walwala, kullum yana ciki tunani, Abdulkarim Safana ya turo ƙofar office ɗin na AB ya shigo har ya iso gaban desk ɗinsa bai ma sani ba a dalili ya yi nisa a tunani, Abdulkarim ya yi tsaye yana ƙarewa kyakkyawar fuskarsa kallo ko bai tambaya ba yasan abokinsa yana cikin tsanani damuwa domin har wata rama ya yi, Abdulkarim ya sauke naunnayar ajiyar zuciya ya ja kujera ya zauna ƙarar ja kujera da ya yi ya dawo da natsuwar AB ya sauke ganinsa akan fuskar Abdulkarim sai da ya furzar da zazzafar iska daga bakinsa, kana ya goge fuskarsa da tafukan hannayensa cikin kasalalliyar murya ya furta "Ak ya ake ciki ne??"
Ya ƙarashe magana tare da miƙawa Abdulkarim hannu suka yi musabaha.
"Me ke damunka ne AB?
"Abubuwa da yawa don bana ce guda ɗaya ba.
"AB duk abunda yake damunka addu'a ya dace ka yi ba wai ka tsananta wa kanka tunani ba kowacce matsala tana da hanyoyin magance wa.
"Ak bana tunani nawa matsaloli suna da hanyar magancewa.
"Kar ka ce haka AB domin bawa baya fita rai da rahamar Ubangiji.
"Haka ne kuma.
AB ya faɗa a gajarce kana ya tashi daga kan kujerar sa ya taka zuwa ga window ɗin office ɗin nasa ya zuge gilashi yana kallon farfajiyar kamfani nasu, shima Abdulkarim ya miƙe ya iso kusa da shi ya tsaya "AB ka faɗamin damuwarka watakila ina da shawarar da zan taimaka ma da ita.
Ba tare da AB ya kalle shi ba yake faɗin "Ak Daddy ya sake bijiro min da zance aure.
"AB aure shine cikar kamala da mutuncinka aure zai ƙara ɗaga darajar ka a idon al'umma haka zalika za ka habbaka sunnar ma'aiki Sallallahu alaihi Wasallam! A ganina wannan ba abin damuwa bane.
Girgiza kai AB ya yi tare da maida gilashi window ɗin ya juya a natse ya nufi ɗaya daga cikin cushion ɗin da ke office ɗin nasa ya zauna ya daga idanuwansa ya kalli Abdulkarim tare da faɗin "Ak zance Mufeeda babu shi saboda labarin rashin asalina ya riske mahaifinta.
"Inna wa'inna illahim raji'um! Ni kam wane munafiki ne yake yaɗa wannan al'amari?"
"Wannan ita ce tambayar da ni kaina banida gamsasshiyar amsarta. Wannan ba shine asalin damuwata ba Ak domin nima na yanke wa kaina shawara koda ina da rabon yi aure ko anan gaba ne duk wacce zan aura zan sanar da ita asali wane ne ni.
AB ya faɗa cikin wata kalar murya mai cike da rauni.
Sai da Abdulkarim ya ja gwaron numfashi ya sauke kafin ya dako cikin mutuwar jiki ya zauna akan hannu kujerar da AB yake zaune akai, kana ya ɗan rungumo kafaɗarsa yana ɗan bubbuga gefen kafaɗar tasa alama dake nuni da rarrashi.
"Ka yi haƙuri AB kowanne ɗan adam da kake gani yana rayuwarsa tana tafiya ne a bisa zanen ƙaddararsa, duk yadda mu kai da nuna maka ƙauna ba mu isa mu sauya ma ƙaddara ba. Don Allah ka saki ranka ka dawo da walwalarka ka karɓi, wannan ƙaddara da hannu bibbiyu.
Kasani AB cikar imani mumini shine yarda da ƙaddara mai kyau ko kuma akasinta, kasancewarka adopted child ba yana nufi kai ɗin ba ka da cikekken asali ba. Kawai dai mutane suna jahiltar adoption ne amma a ƙasashen turawa yadda ɗa da ya tashi a gaban iyayensa yake da 'yanci haka zalika shima adopted child yake da 'yanci kuma ba za ka ga ana goranta masa ba. Sannan idan ka yi duba da yadda naka iyaye suke sonka AB ƙannanka suke matuƙar ƙaunarka ban ga dalili da zai sa ka jefa kanka a damuwa ba.
Tun sanda Abdulkarim ya fara magana AB ya ɗago da idanuwansa yana kallonsa har ya dasa aya bai dauke ganinsa daga kan fuskarsa ba tamkar yana karantar wani abu akan fuskar tasa ne. Dukkansu suka yi shiru na wani ɗan lokaci kafin AB ya kawo karshen shiru nasu ta hanyar faɗin "Dole na shiga damuwa Ak Daddy yana so ya sake haɗa ni aure da ɗaya daga cikin yara nan, ni kuma har ga ba zan iya rayuwar aure da ko ɗayar su, kana gani dai yadda ta kare tsakanina da Sadiya ita da ma ta gama mallakar hankalin kanta. Siyama kuma tana da wanda take so ita Aydah a ma jinginar da zancenta a gefe ba ma za a saka ta a jeri mata ba.
Cike da gundarin mamaki Abdulkarim yake kallon AB kasa cigaba da ɓoye mamaki nasa ya yi har sai da ya kai da furta "Kana matuƙar bani mamaki AB.
"Na me fa??
"A duk sanda ka furta iri-irin waɗannan maganganu akan Aydah.
"Ya kamata kai daina mamaki Ak saboda hakikanin gaskiya nake faɗa Aydah bata cikin jerin mata a wurina.
"Ni kuma sai nake gani Aydah ita kaɗai ce yarinyar da ta dace da kai kada ka yi la'akari da ƙarancin shekarunta ka yi duba izuwa ga tsanani shaƙuwa da juna da ku ka yi duk idan aka ce akwai shaƙuwa tabbas so zai iya shigowa cik....
"Dallah ya isa Ak! Na sha faɗa maka Aydah tamkar 'yar da na haifa nake kallonta kashi, fitsarinta ba kalan wanda ban ci ba ni na raine ta da hannaye nan nawa babu abinda bansan ni ba a jikinta sai kawai na aureta haba Wannan kwamacala ba dani ba wallahi.
"Mtsss! Duk wanda ya ji kana fadar ba abunda ba kasani ba a jikinta zai fassara ka ta wani fanni na daban kasan komai na jikin Aydah sanda tana yarinya ba yanzu da ta balaga ba ko kana nufi har yanzu kai ke mata wanka?"
Sai da AB ya ture hannayen Abdulkarim daga kafaɗarsa ya miƙe a mugun fusace ya nufi ƙofar fita Abdulkarim ya miƙe ya biyo shi a baya sosai AB yake ji ɓacin rai yana lulluɓe shi, ya rasa dalilin da yasa a duk sanda Abdulkarim ya danganta aure tsakaninsa da Aydah yake wani irin baƙin ciki ya danne masa zuciya, da ya aure Aydah gwada ya ƙare rayuwarsa kaf babu aure me zai tsinta a jikinta.
"Ya ka yi shiru ka bani amsa mana har yanzu kai ke mata wanka kaman yadda ka saba faɗa.
"Ba bambanci a wurina domin duk mace da kasan jikinta tun tana jinjira don wasu 'yan ƙananu abubuwa sun fito mata a ƙirji ba zai zama bakon abu a gareni ba, saboda nasan lokaci da bata dasu.
"Maganar banza kake yi AB wannan bai isa ya zama kwakwarar hujja da za ka haramta kanka aurenta ba.
"Dan Allah Ak mu bar wannan zance wallahi yana ƙara linka min sa ɓacin rai.
"Shikenan!
Abdulkarim ya faɗa daga nan motar Abdulkarim suka shiga kowanne su yunwa yake ji don haka suka wuce Gusto restaurants.
*MASARAUTAR KUDU*
"Umma ki yi wani abu akai kaman yadda kike yi a shekarun baya na hana naɗa Aliyu a matsayin sarkin sabon birnin kudu. Umma sarautar nan ko kaɗan bata dace da Aliyu ba da ni ta dace.
Alhaji Hashim ya yi magana yana kallon Hajiya Kilishi dake kishigiɗe akan wata lallausar carpet cike da izza da taƙama take jujjuya yatsun hannunta da suka sha ado da zobunan gold, ta ɗauki dogon lokaci tana jujjuya yatsun nata kafin ta buɗe bakinta cikin wata irin izza ta furta "Ciroma!
"Na'am Allah ya ƙara wadata ki da lafiya gami da nisan kwana.
"Amin! Ina son ka sani Ciroma na fika shiga tashin hankali sa'ilin da labarin naɗin sarautar Aliyu ya riske ni. Bani da wani buri a duniya sama da naga na kawo ƙarshen mai babban ɗaki da 'ya'yanta wannan makirar mata da kake gani Hashim na share tsawon shekaru masu yawan gaske ina shanye baƙin cikinta. Tun lokaci da takawa yake raye nake nuƙurƙusar baƙin ciki har kawo yau ɗinan ba abinda ya sauya.
Hajiya Kilishi ta kasa cigaba da magana wani irin fushi da ɓacin rai ne sosai suka bayyana karara akan fuskarta da babu burbushi imani balle tausayi, sai da ta furzar da iska daga bakinta ta tashi daga kishigiɗa da ta yi ta kalli Hashim kallo idon cikin ido ta yadda zai iya hango tsanani fushi da take ciki "Ban taɓa sanya ko nuna gajiyawa domin cimma daɗen burina Hashim kai sauratar sabon birnin ita ce damuwarka ni kuma ga baki ɗaya sarautar kudu nake so ta dawo karkashin iko da mallaka ta.
Wani irin washe haƙora Hashim ya yi ya ƙara gyara zaman shi tare da ƙara ƙasƙantar da kai, "Allah ya ƙara miki lafiya acikin mu wa kike wa sha'awar wannan babban matsayi?"
"Ahmadu!
Nan take annurin kan fuskar Hashim ya gushe wani irin mashi ya ji ya dakar mishi zuciya, duk da haka sai ya yi ƙoƙarin danne abunda yake ji yana taso masa a ƙahon zuciya "Ranki shi dade Ahmadu fa kika ce?"
"Kwarai kuwa Ahmadu.
Ta faɗa kanta tsaye domin ƙara tabbatar mishi da nufin ta.
"Ranki ya dade Ahmadu fa kwata-kwata baya da sha'awar mulki shiyasa tasu ta zo ɗaya da Aliyu, kuma bana tunani Ahmadu yana da experience akan yadda ake gudanar da mulki ki tsaya ki yi nazari ranki ya dade kada ki yi gaggawar yanke hukunci amma Ahmadu ba zai iya sarauta ba. Ina ma laifin ki zaɓi Yusuf ko Abubakar ko kuma ni ɗinan domin duk acikinsu ni kaɗai nake da experience akan gidan sarauta, kuma ni ne babba.
"Ciroma ina so kasani bana yanke hukunci ba tare da lissafi na ya faɗa daidai ba, duk abunda zan yi a bisa jagoranci natsu da hankali nake yi sa. Ahmadu shi ne lissafi na ya faɗa akansa, ka janye ƙudurinka akan masauratar kudu domin sarautar sabon birnin kudu ita ce ta fi dacewa da kai anan gaba za ka fahimci manufa ta.
"Amma ranki ya daɗe....
"Ya isa Ciroma!
Tai sauri tarar numfashin sa da kakkausar murya.
"Ka fara shiri gobe da safe za mu kai ziyara a akan tudu.
"Tohm! Ranki ya daɗe.
Ya faɗa zuciyarsa na mishi zafi "Na barki lafiya.
Ya miƙe tare da baro katafaren parlorn nata.
*FLAT ƊIN MAI BABBAN ƊAKI*
Mai babban ɗaki tana hakince a parlornta tare da bayi haɗu biyu suna mata massage ɗin yatsun ƙafafunta yayin da biyu ke yanka mata 'ya'yan itatuwa (fruits) amintatciyar jakadiyar ta ce ta shigo ta zube a gabanta ta sadda kanta ƙasa cikin tsanani girmamawa ta furta "Allah ya ƙara miki lafiya yanzu nan magatakarda ya dawo da sakon da kika ce na aika wa da sarkin sabon birnin. magatakarda ya tabbatar min jiya sarkin sabon birnin ya koma Lagos.
Shiru mai babban ɗaki tayi tana nazarin kalaman jakadiya bi da bi wani irin ɓaci rai ne ya bayyana akan fuskar mai babban ɗaki miyasa a duk sanda tai gini Aliyu yake rusa shi? Miyasa duk acikin 'ya'yanta shi ne yafi bata matsala, bata da buri da ya wuce taga ya hau karagar mulkin sabon birnin kudu a duk sanda ta kusa cimma burin ta sai Aliyu ya wargaza mata shi. Tabbas da akwai wani ɓoyayye al'amari a tattare dashi dole ta matsanta bincike domin gano abunda Aliyu ya dau shekaru yana ɓoye mata ta gaji da wannan kurman allon nasa.


#Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo.












Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only




ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130


KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730


Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336






*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.


*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar


*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu


*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce


*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari


*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan


Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500


VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k


NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[12/10/2023, 10:15 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful love story)


NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU




#Love Story
#Gwagwarmaya
#Team tagwaye Novels


017.










*RUBUTUN ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU.*
*TAFIYAR BIYU TAFI ƊAYA*


*KIN TABBATA KIN CIKA MACE? BABBAR MACE DAKE JI DA KANTA? KINA CIKIN MATAN DA SUKA SAN KANSU? WANDA SUKA SAN MUTUNCI DA DARAJAR KANSU? KO KUWA KEMA KINA CIKI SAHUN SU O’O?*
*INA KUKE MANYAN MATA? WAƊANDA SUKA SHIRYA DAN GYARA JIKINSU? AURANSU? DA KUMA FARINCIKINSU?”
*KUYI MAZA KU GARZAYA GUN FITACIYGA KUMA INGANTACIYAR MAI MAGANIN MATA DA MAZA DAN AMSAR NAKU KU GYARA DA KANKU WATO MEERAH HERBS WACCE TAI FICE GUN KAWO MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA BA TARE DA ALGUS BA.*
Mun gwada mun gani 💯
Mun gani mun shaida 💯
Anyi mun gani 💯
MAGANIN SANYI
MAGANIN NONO
MAGANIN HIPS
MAGANIN SLIMMING
MAGANIN NANKARWA
GYARAN AMARE
GYARAN MAIJEGO
MALLAKAR MIJI KO MATA
SUBULU DA SCRUB
MAYUKA NA GYARAN JIKI
TURAREN WUTA
MATSI
MAGANIN NI'IMA
MAGANIN TSUMI
INFECTION FLUSHER DA DAI SAURANSU…..Uwar gida, Amarya, Budurwa, Saurayi, Ango, Mai gida? Duk mai kuke jira? Kuyi maza ku garzaya Meerah herbs maganin dake ingantace 💯


08142800199
07068558096










Tun ranar da Alh Habeeb Bichi ya baro gidan Alh Bashir ya kira Mufeeda ya sanar da ita zance aure tsakaninta da AB babu shi. Tun daga wannan ranar har kawo yau Mufeeda tana cikin ƙunci saboda ta kamu da soyayyar AB atunani ta za ta iya fatattakar soyayyar tasa a farat ɗaya kaman yadda ta shiga zuciyarta a tashin farko, sai dai haƙar ta ya kasa cimma ruwa kullum soyayyarsa ya ƙara habbaka take a zuciyata. Sannu-sannu damuwa ta fara yi mata yawa farin ciki gami da walwalarta suka bar jikinta. Bata da aiki sai na tunanin AB. Yanzu ma tana kwance ne a ɗakinta hoton AB take kallo wanda a shafin sa na Instagram ta same shi zooming ɗin hoton tayi ta yadda fuskarsa ta fito ɓaro-baro gray eyes ball ɗinsa yana ɗaya daga cikin abinda take bala'in so a tare dashi sai kuma pink lips ɗinsa ga kuma kwatatce sajensa mai haɗe da ɗan matashin beard ɗinsa da ya ƙara ƙawata fuskarsa. Wasu hawaye ne suka silalo daga kwarmin idanunta suka gangaro suka saukar mata a gefen wuyanta. Lokaci da Abbanta

12 / 80