Kurman Allo Sakamakon Kin Karɓar Gaskiya by EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU

Author :  EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category :  KDP NOVELS

Chapter   76 / 80

225K to 228K   out of 237.2K words

ba.
Ta ƙarasa magana tana wani irin kuka mai taɓa zuciya da sauri ya juyo ya ƙanƙame ta yana bubbuga bayanta "ko tafiya kika yi Maysun na yi miki alƙawari zan kai miki shi har Qatar.
"Ba za ka gane bane Ali kai dai ka yi kokari na gansa banaso na mutu batare da na ga tilo dana ba.
Wani irin bugawa zuciyar Aliyu na Uku ta yi jikinsa ya ɗauki rawa, da sauri ya ɗago fuskarta yana kallon tsakiyar idanunta "me kike so ki ce Maysun?"
Wani murmushi mai ciwo ta sakar masa "I've terminal blood cancer kowanne lokaci zan iya mutuwa Ali banida lokaci mai tsawo Dan Allah ka taimake ni ka haɗa ni da dana kamin na mutu ina so na gansa wannan shi ne kadai burina a duniya.
"Innalillahi wa'inna illahim raji'un! Hasbunallahu wal-imaal wakil!
Aliyu na uku ya faɗa tare da sakin kafanɗun Maysun da yake riƙe dasu ya dinga ja da baya wani irin jiri ne ya ɗebe shi ya faɗi zaune dabass! Ji ya yi numfashinsa na ƙoƙarin fita daga gangar jikinsa take ƙwaƙwalwarsa ta dinga tunano masa da kalolin magunguna da koda yaushe yake gani Maysun tana sha, idan ya tambaye ta sai ta ce mishi na blood pressure ne bai damu sosai ba saboda yasan hawan jini ya zama gama garin ciwo tun da ko Safiya tana dashi haka zalika mai babban ɗaki, ko kaɗan bai taɓa kawowa ransa cewa tana ɗauki da gaggarumar cuta irin wannan ba. A hankali Maysun ta zo ta zauna kusa dashi cikin muryarta da baya fita sosai ta ce "Ka yafe min boya maka da nayi Ali banaso ka shiga damuwa ne lokacin da muka haɗu a hamburg, na je gani likita ne anan yake tabbatar min da ciwon ya gama zagaye jinin jikina ba zan wuce three to four months a raye ba. Banaso na faɗa maka na dantse maka farin ciki da ka ɗauki shekaru masu yawa ba ka yi ba.
Cikin wani yanayi ya rungumo ta wasu hawaye masu zafin gaske ya ji suna sauka akan kamatunsa, ya ɗauki lokaci mai tsawo rungume da Maysun kamin ya kamata ya nufi kujera da ita ya zaunar da ita ji ya yi ba zai iya tafiya ya barta ba yana gani kamin ya dawo wani abu ya faru da ita dole sai fasa tafiya ya yi saboda ya nema mata ticket ta online bai samu ba sai a washegari suka nufo Kano.
********
Mami hauka ne kaɗai bata yi ba da ta ji ɗaurin auren Daddy ya tabbata, gaba ɗaya yaranta daina amsa musu gaisuwa ta yi dukkansu fushi take dasu yayin da Zeenah ke ta faman zugata tare da yi mata hudubar shaitan tana faɗin Daddy ya zubar mata da mutunci ya rasa wacce zai aura sai 'yar aikinta karta sake ta yarda da wannan wulaƙancin nasa, a takaice babu kalar zuga da bata yi mata ba. Da yake kai nan na Mami sai a hankali sai ta hau ta zauna daram.
*SKYLINE UNIVERSITY*
Aydah suna kammala lecture ta fito daga hall da saurinta da nufi ta ɓacewa Marwan, ta gaji da nacin da yake mata ya bi ya takura ta ya hana mata rawar gaban hantsi. Duk saurin da take yi batasan cewa yana bayanta ba sai murmushi yake abinsa domin yasa, shi take so ta gujewa "Zulaiha wai sauri me kike yi haka?"
Da sauri Aydah ta waiga bayanta fuskarta ta dawo kalar tausayi saboda duk abin da take wa gudu bata tsira ba, karasowa Marwan ya yi yana wani miskilalan murmushi "Mu je yau ƙafana ƙafarki ko bakyso dole sai kin gabatar dani ga yan gidanku shiyasa ma ban zo da motor na ba.
Zaro idanuwa ta yi tare da faɗin "Wallahi Marwan kana da matsala wannan takurawa da kake min ba shi zai sa ka sami gurbi acikin zuciyata ba.
"Kin ga malama ki wuce mu tafi dan ni na yi nisa ko kaɗan bana jin kira.
Harara ta watsa masa haɗe da yi ƙwafa ta juya ya bi ta a baya, bata da yanda za ta yi da rigimarsa dole ta lallaɓa shi su rabu lafiya.
Anaal zaune a Gusto restaurant tana ci abinci da ta yi order, tun zuwanta Kano ta rufe wayarta saboda abun da ta zo gabatarwa asirance. Bayan ta kammala cin abincinta ta yi order wani as usual don duk sanda ta zo cin abinci a Gusto sai ta yi order wani a takeaway ta tafi dashi.
Tana fitowa ta tari adaidaita ta faɗa masa inda zai kaita tafiya sosai suka yi kafin su iso wani plat house ɗan madaidaci dashi a bakin gate aka sauke ta, ta yi knocking mai gadi ya buɗe mata ƙofa ɗaya daga cikin ledar takeaway ɗin ta zo dashi, ta miƙa masa kana ta wuce entrance ɗin gidan a main parlor ta tarar da doctor Maheer yana amsa waya bayan ta yi sallama ta ƙaraso ta zauna kujerar dake facing ɗinsa, ya kammala wayar tare da zuba mata fararen idanunsa cikin sanyi muryarsa ya ce "Alhamdullah! Abubuwa sai tafiya suke yi cikin nasara ina tunani nan da ɗan wani lokaci za a samu abun da ake so.
Sanyayye murmushi Anaal ta yi tare da faɗin "Ina fatan haka doctor ina kuma kara godiya da kokarinka bantaɓa haɗuwa da mutum mai kirki da tausayi irinka ba, ba zan taɓa mantawa da taimakon ka ba,ga abinci na zo ma dashi bansani ba ko kana jin yunwa.
Ta ƙarashe magana tare da aje masa takeaway ɗin hannunta akan centre table.
Jirgin na landing Aliyu ya kira Kabir Umar shi ya zo da mota ya ɗauke su da fari sai da suka fara neman masauki a hotel suka yi wanka suka ci abinci tare da yi sallah, Kabir Umar ya ɗauke su zuwa gidan Bashir shamaki.
Babu kalar rigamar da Mami bata tsiro wa da Daddy dashi ba ita fa a son ranta gara Daddy ya sake ta da ta yi zaman kishi da Huwaila a ganinta zama da Huwaila zai taɓa mata ƙima gara ta bar masa gidansa kawai. Shi kuma Daddy bashi da burin sakinta ya fiso ya haɗa ta da Huwaila don ya kuntata mata, so yake ya gasa mata 'ya'ya gyaɗa a tafin hannunta wannan ita kadai ce hanyar da zai bi domin yasata ta gurbe abun da ta shuka.
Aydah lallaɓa Marwan ta dinga yi da kyar ya barta ta nufo gida shi ma sai ta daukar masa alƙawari ta daina ignoring ɗinsa sannan fa ya barta ta tafi, Aydah tana isowa gida ta wuce ɗakinta ta yi wanka saboda gajiya da ta ɗebo ta saka gown na cotton material mai gajeren hannu, kana ta dawo main parlor, ta kira Bintalo ta kawo mata Baby Noor ta ce ta zubo mata abinci ta kawo mata ɗakinta. Bayan ta kammala cin abinci ta ɗora Baby Noor a cikinta tana mata wasa ita kuma tana dariya a duk sanda ta kalli Baby Noor sai ta ji kewar iyayenta ya lulluɓeta.
Horn ɗin da ake ta faman yi ga Balmo maigadi ya ɗan zagaya banɗaki yau tun safe ya tashi da ciwon cikin sai gudawa yake yi, da sauri ya fito yana ɗaure mazargin wandonsa da gudu ya je ya buɗe gate baƙuwar mota ya gani don tsawon zamansa a gidan bai taɓa ganinta ta zo gidan ba, Kabir Umar ya nufi parking lot ya yi parking jikin Maysun sai wani irin rawa yake yi zuciyarta tana bugawa da ƙarfi. Suna fitowa daga mota Balmo maigadi yana ƙarasowa ya yi musu sannu da zuwa, kana Aliyu ya tambaye shi maigidan yana nan kuwa? Balmo ya amsa da baya nan amman matar gidan tana ciki.
Aliyu na uku ya ce ya yi musu iso a wurinta ya faɗa mata baƙi ne daga nesa.
Balmo jikinsa har rawa yake yi ya je ya isar da sako saboda abubuwan mamaki guda biyu da ya ci karo dasu, wannan balarabiya mata mai kama da Abba ga kuma wani dogon mutumin shi ma yana yanayi da Abba tsayin su kusa ɗaya, ga maganarsa sak irin ta Abba don wannan mutumin da ya gani da ace shekarun sa ɗaya da Abba da ya ce Abba ɗin ne ya dawo. Balmo ya danna door bell Hanne ta zo ta buɗe masa ya ce ta gayawa Mami ta yi bakin larabawa. Hanne ta nufi ɗakin Mami dake upstairs a kwance ta tarar da ita duniya ta yi mata juyin ɗan mangwaro, cikin kwanaki ƙalilan Mami ta zabge ta yi mummunan rama. Cikin girmamawa Hanne ta faɗa mata sakon Balmo cike da mamaki ta furta "baƙin larabawa?
"Eh! Mami haka dai ya cemin.
"Shi kenan ki ce ya shigo dasu gani nan zuwa.
Hanne ta fice ta je ta gayawa Balmo sakon Mami kana ta koma kitchen shi kuma ya je ya gayawa musu, tun sanda suka shigo parlorn Maysun ta haɗe tafukan hannayenta tana mutsutsuka su, wani irin take ji a jikinta. Footsteps ɗin Mami da suka ji tana saukowa daga kan stairs ya saka su kallon upstairs ɗin, ga mamakin su ba Maryama suka gani ba wata baƙuwar fuska ce ta daban da sauri Maysun ta kalli Aliyu don har idanuwanta sun ciko da hawaye "Abu Azhar wannan ba Maryama bace matar Bashir shamaki kodai ba nan ne gidansa ba?"
Maysun ta yi magana da rauni a muryarta.
Hannunta Aliyu na Uku ya riƙo yana ɗan girgiza mata kai alamar ta kwantar da hankalinta, Mami tana sakkowa idanunta suka yi tozali da mutane da ke mata kama da Abba, wani Irin shock ta ji ya kamata ko bata tambaya ba waɗannan mutane suna da alaƙa mai ƙarfi da margayi Abba, don duk tsawon zamanta da Abba ko a hoto bata taɓa gani masu kama dashi irin wadannan mata da miji dake zaune a parlornta, cikin mutuwar jiki Mami ta ƙaraso tare da yi musu sallama, Aliyu na Uku ne ya yi ƙarfin hali amsa mata ta nemi wuri ta zauna tare da kikkiro murmushin dole ta yafa wa fuskarta Hanne ta shigo ɗauke da tray mai ɗauke da drinks da ruwa ta ajiye musu kana ta sake komawa kitchen. Mami ta dube su gabanta na faɗuwa ta ce "Sannunku da zuwa ku yi haƙuri ban waye ku ba idan babu damuwa zan iya sani daga ina kuke wa kuma kuke nema?"
"Sunana Aliyu na Uku wannan matata ce sunanta Maysun mun zo neman Bashir shamaki da matarsa Maryama, sai dai kamar an ba mu wrong address.
Murmushi Mami ta yi tare da faɗin "Ba a ba ku wrong address ba nan ne gidan Bashir shamaki sai dai Matarsa Maryama Allah ya yi mata rasuwa tsawon shekaru talatin kenan da rasuwarta.




Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo.
[2/9, 7:42 AM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)


NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU


Love Story
#Gwagwarmaya
#Team Tagwaye.




102.




Sai da Aliyu na uku ya ja dogon numfashi tare da saukewa ya ce "Allah ya jiƙanta da rahama.
"Amin!
Mami ta faɗa cikin sanyi murya.
"Maigida fa?"
Cewar Aliyu yana jin gabansa na faduwa, don baisan kalar amsar da za ta fito daga bakin Mami ba.
"Yana office bara na kirasa a waya na sanar dashi zuwanku.
Gyada kai kurum Aliyu ya yi yana mai ƙara damƙe hannun Maysun acikin nasa. Mami ta miƙe tare da komawa ɗaki ta kira wayar Daddy, kira uku tai masa amma bai yi picking ba kuma yana gani kiran nata, kawai dai baya da ra'ayin ɗauka fitinarta ya ishe shi cigaba da kira Mami ta yi a fusace Daddy ya ɗaga yana faɗin "Wai ke miye matsalarki ne kin fara kaini bango fa?
"Ka yi baƙi da dukkan alama suna da alaƙa ta jini da margayi Abba idan kaga dama za ka iya zuwa ka gansu.
Abun da Mami ta faɗa kenan tana mai kashe wayarta,ta dawo parlor wurinsu ta zauna.
Anaal ta miƙe tsaye tare da kallon Dr Maheer tana faɗin "Dr bara na shiga ciki na duba sa.
Dr Maheer ya gyada kansa Anaal ta juya cikin salon tafiyar ta natsuwa wacce tana ɗaya daga cikin abubuwan dake jan hankali maza akanta, Dr Maheer ya bi ta da kallo yana ji soyayyarta tana ƙara huda sassan jikinsa sai dai har kawo yanzu ta ƙi karɓar tayin soyayyar tasa. Yanzu ma da ta nemi taimakon sa domin kula da mutumin da ta ce dashi ɗan uwanta ne da fari asibitin sa ya fara jinya daga baya ya dawo dashi ɗaya daga cikin gidanjensa domin ta ce masa bata so, asan mutumin yana raye saboda tsananin son da yake mata ne yasa shi biye mata ya yi mata abun da take so yake kuma cigaba da kula dashi.
Dukka bai fi 30 minutes ba sai ga Daddy ya zo yana arba da Aliyu na Uku gabansa ya yi mummunan faɗuwa ƙafafuwansa suka ƙasa daukarsa anan ya zube guiwayoyinsa, yana sauke numfashi yayin da idanunsa suka fara canza colour, gani Aliyu na uku da ya yi yasa abubuwa da dama suna dawowa masa a ƙwaƙwalwa musamman mutuwar Abba, a yanzu baisan da wane ido zai kalle su ya gayamusu ɗansu ya mutu. Cikin sauri Aliyu na uku ya taso yana zuwa shima ya zube guiwayoyinsa gaban Daddy tare da kama kafanɗun Daddy "Ba...Ba Ba..shir...ina ɗana Muhammad Azhar nasan yana wurinka ko Bashir dan Allah karkace min baya tare da kai?"
Aliyu na Uku ya faɗa cikin raunatacciya murya, wani marayan kuka ne ya subuce wa Daddy, ya ɗora hannunsa kan na Aliyu dake kan kafaɗarsa tun kafin Daddy ya yi magana Aliyu na Uku ya kidime yayin da Maysun ta miƙe tsaye, cikin kaɗuwa take kallonsu "Ka yi haƙuri Aliyu Allah ya yiwa Abba rasuwa watannin biyar da suka wuce, har yanzu ban daina kukan rashinsa ba.
"Innalillahi wa'inna illahim raji'un!
Abun da Aliyu ke ta faman nanatawa gani haka yasa, Maysun ta zo ta dafa kafaɗarsa cikin harshen turanci take tambayar Aliyu me ya faru, kukan da yake kokarin dannewa ne ya subuce masa a lokaci guda, cikin muryar kuka yake fadawa Maysun Azhar ya rasu jiri da take ji tun ɗazu ne ya zo ya kwashe ta, daman can ƙarfin hali take yi tare da sawa ranta son ganin ɗanta yanzu kuma da ta ji ya rasuwa sai ta kasa jurewa, wani irin duhu ya mamaye ganinta ta fadi ƙasa a some kusan a tare Aliyu, Daddy har ma da Mami suka yi kanta jini suka gani yana fita ta ƙofofin hancinta da sauri Aliyu ya ciccibe ta ya nufi ƙofar fita, Daddy da Mami suka bi su a baya kaitsaye, asibitin Softcare da su Daddy ke zuwa aka wuce da Maysun.
Sannu a hankali Anaal take ƙare masa kallo gaba ɗaya an naɗe kansa da bandage, haka ma ƙafarsa ta hagu wacce ke nuni da kariya ce ya yi sai wasu sassan jikinsa dake ɗauke da tanbuna na warkewar ciwuka, hannunsa na dama manne da cannula ana ƙara masa drip. Ba don na'urar da ke nuni da bugun numfashin sa za ka zaci gawa ne.
Tsawon watanni biyar kenan yana cikin coma, har yau ko ɗan ya tsansa bai taɓa motsawa ba. Gashi nan dai ya zama gawa kin ƙi shiga rami. Anaal ta ja kujerar dake facing fuskarsa ta zauna, a hankali ta ɗora tafin hannunta akan nasa, tana shafawa a hankali yayin da hawayen tausayinsa suka cicciko mata a idanuwa "Tun farkon ganina da kai jikina ya bani kai ɗin jinina ne saboda wasu abubuwa da nake ji a duk sanda idanuwana suka kalle ka, ban tabbatar da hakan ba sai da na fara bibbiyarka har na yi nasarar samun gashinka ta hanyar wurin wanda kake zuwa aski a wurinsa, bayan Dr Maheer ya yi gwaji akansa ya tabbatar min da kai ɗin ɗan Abbu ne. Na ji haushi matuƙa da faruwar hakan, domin ina gani kalar soyayya da Abbu yake maka, tun kafin ya ganka kishinka nake yi yayana ina jin tsoron idan ka shigo rayuwarmu za ka kwace min fada a wurin Abbuna, mahaifiyarka za ta kara mamaye zuciyar Abbu ummina za ta zama kara zama bora a dalilin wannan gurgun tunani nawa, sai na yanke shawarar na haddasa gaba a tsakaninka da mahaifinka da ba kasan da zamansa ba. A ranar da zan gabatar da plan b ɗina na kira ka da zimmar aiwatar da manufata, a maimakon na ji muryarka sai na ji wata baƙuwar murya tana cewa dani yau kwana uku kenan da yi mummunan hatsari, shi ma tsintar kai ya yi amman ya kai ka asibiti idan ina da alaƙa da kai na zo asibitin da ya kai, ka. Da farin nace banida alaka da kai sai kuma na yi wani tunani wanda hakan ne yasa na zo Kano, da na zo naga hali da kake ciki yayana sai na ji zuciyata ta karye duk wani haushinka da kishinka da nake ji na nemi shi na rasa dan haka dan Allah ka tashi yayana,idan har ba ka tashi ba, ba zan iya gabatarwa da Abbu kai a wannan halin ba. Mahaifiyarka ta zo bata da buri face ta yi tozali da kai, banaso dukkansu biyu su ganka cikin wannan hali, na tabbata zuciyoyin su ba zai iya dauka ba. Domin kai na dawo Kano na tare batareda da sanin iyayena ba na cigaba da kula da kai, na kuma kashe waya ta saboda bani da hujja da zan gabatar musu da ita da za su bar ni na zo kano na zauna. Shiyasa nake rokon da ka tashi Abba Bashir ka tashi yayana ka buɗe idanunka ka kira ni da sunan da ka saba kirana dashi me ma kake kira ni dashi? Uhm! Mss Anaal! Ka kira ni da suna nan yayanmu.
Har wani sheɗewa Anaal take yi saboda kuka, da yaci ƙarfinta sai kawai ta kifa kanta a ƙirjinsa ta cigaba da kukanta.
Kusan awannin biyu likitoci suka dauka kan Maysun kamin su samu ta farfaɗo, sai dai tun sanda ta farfaɗo ɗin take kira sunan Azhar allurar bacci aka sake yi mata, bacci mai nauyi ya ɗauke ta sai lokacin Daddy ya sami damar ba wa Aliyu labarin Ab, ya yi matuƙar farin ciki da ya ji Abban ɗin yabar tsatsonsa da za su gani su ji sanyi.
*MASARAUTAR KUDU*
Tuni masauratar ta dauki sabon zance sarautar sabon birnin kudu da Ciroma ya ba wa Galadima, wanda hakan ba ƙaramin ce-ce-kuce ya kawo

76 / 80