Author : EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category : KDP NOVELS
faɗa da dimbin mamaki akan fuskarsa don shi bai taɓa ji irin wannan tatsuniya ba, idan har kamfaninsu yana so ya yi cancelling ɗin partnership kamata ya yi su zo tare da wasu daga cikin board members ɗinsu a haɗu da nasu kana sai su kawo hujjojin su da suka sa suke so cancel ɗin partnership ɗin, saboda tun asali gamayyar kamfani ne ya haɗa su dake Germany.
Anaal ta kara gyaran zamanta tare da tattaro natsuwata wurin ɗaya "mr Abba babu zance wasa aciki da wasa nake yi me zai sa na wanko ƙafa na zo garin kano?
"Idan ba wasa kike yi ba to ki sani kin zo min da raini hankali,kamin kula kowanne yarjejeniya akwai sharuddan da ake gindayawa domin gujewa zamba cikin aminci da dai sauransu, wanda hakan yasa dole acikin daya daga cikin gamayyar kamfanoni za a zaɓi ɗaya daga cikinsu a zantar da wannan harkala me yasa ba ki nemi mu hadu a Kamfanin mu kamar yadda na je na sami ku a Kamfanin ku, sai kika nuna mu haɗu a hotel?"
"Wannan ba wata gamsasshiyar hujja bace mr Abba idan ka yi duba daga ni har kai muna da ƙarfin ikon zantar da hukunci ba dole sai a gaban board members ba. Tun da har kaga mahaifina yace a soke yarjejeniyar to tabbas akwai dalili mai ƙarfi don haka dan Allah kada kaga laifina ka sa hannu so nake gobe da sassafe na koma birnin kudu.
"Birnin Kudu!
AB ya tsinci kansa da maimata sunan yana ji wani irin matsanancin faduwar gaba, ga tsigar jikinsa da ta mimmiƙe a hankali yake ambaton Allah a zuciyarsa ji ya yi kamar zazzaɓi zai rufe sa, saboda haka batare da da ya sake magana ba ya dauki document ɗin ya dinga bin yana signing, yana kammala wa ya yi dropping pen ɗin da ƙarfi akan envelope ɗin ya miƙa jiki ba lakka. Ya juya Anaal ta bisa da kallo tana murmushi yana isa wurin motarsa kiran Rumaisa yana shigowa wayarsa sai da ya daidaita natsuwarsa kafin ya yi picking, kukan Rumaisa ya fara tsikayi har wani sheɗewa take yi "subhanalillah! Habibty mene ne me faru ya na ji kina mai kuka?"
Kusan a tare ya aika mata da waɗannan jerin tambayoyi. Kafin Rumaisa ta yi magana Ammie ta karɓe wayar "Abba ka zo gida ka sami ni za mu yi magana.
Daga haka Ammie ta kashe wayar, jikin Ab ya ƙara mutuwa yana tunani me kuma ya faru da mahaifiyar Rumaisa ke so ganinsa shi a tunaninsa Rumaisa ma ta koma gida. Iya hasashen sa ya kasa hasaso masa me ke faruwa?"
Yana isa gidan kansa tsaye ya wuce babban parlor ɗin gida kasancewar yanzu bashida shamaki da gidan.
Ya taki babbar sa'a Ammie da Rumaisa suna cikin parlor zaune kowacce da kalar damuwar dake kan fuskarta Rumaisa kam idanunta sun yi luhu-luhu ga wani uban ta gumi da ta doka. Cikin yanayi na girmamawa Ab ya gaida Ammie ta amsa masa da daurarriyar fuska.
"Abba na kira ka ne domin na faɗa maka takamaiman ciwo da yake damun matarka wata kila idan ita ce ta gayamaka ba lallai bane ka yarda.
Gaban Abba ya doka da karfi, kamin Ammie ta kai da gayamasa ciwo har zuciyarsa ta fara ayyana mai abubuwa barkatai.
"Subhanalillah! Ammie wane irin ciwo ne Allah yasa yana da magani?"
"Yana da don in shaa Allahu daga kan wannan babu ɗan la'ananna da zan ƙara bari ya jefa min 'ya an dai na farko da yarda ubangiji shi ne na ƙarshe.
"Ban fahimci ki ba Ammie.
AB ya faɗa cikin rawar murya.
"Abba asiri ne aka yiwa Rumaisa aka sako mata zubar jini domin a rabata da kai kuma malamin da ya warware asiri ya tabbatar mana da matarka ce tai mata asiri don haka na kira ne domin na gargade ka da babbar murya idan ka koma gida ka jawa matarka kunnen ta kiyaye faɗa da batada makami, idan kuma tana ci ƙasa ta kiyaye ta shuri wallahi-azim karta sake ta kara taɓa min 'ya wannan ma na ɗaga mata ƙafa ne taci albarkacin ka, da duba da nayi da ƙarancin shekarunta wata kila ba ita ce ta yi mahaifiyarta ce. Ni uwa ce wacce bata haɗa ya'yanta da kowa ba akan yarana ba abun da ba zan iya aikatawa ba domin na kare martaba da ƙimarsu.
AB was totally shock and speechless ya yi gun don bai masan me zai ce ba koda yana da abun cewa bai san daga ina zai fara ba. Tun sanda Ammie ta fara kora masa zance zuciyarsa ta yi nisan kiwo don har ta warware masa Kurman allo, don haka ya kwantar da murya ya shiga ba Ammie haƙuri tare da nuna mata komai fa muƙadarri ne daga Allah sannan kuma kada ta yarda da zancen asiri domin zato zunubi ne koda ya zama gaskiya ta guje ɗaukar maganganu malaman tsinbo domin da yawansu makaryata ne kuma haddasana masu haddasa fitina a tsakanin al'umma. Yana dasa aya Ammie ta rufe shi da faɗa har sai da Rumaisa ta taka mata birki sannan fa ta iya yi shiru AB ya sake bata haƙuri cikin kwatacciyar murya ya yi mata alkawarin daga nan zai wuce da Rumaisa Islamic chemist ya karbu mata magungunan musulunci idan ma asiri ne zai sake ta.
"Babu buƙata duk wani magani da za ka karɓo mata na riga da na karbo mata ke tashi ku tafi matuƙar ina raye babu wani ɗan banza da ya isa ya wargaza miki gidan aurenki.
Rumaisa ta tashi jikinta a sabule Ammie ta je ta dauko mata ledar maganinta tare da wani ruwan magani acikin madaidacin golan, ta miƙa mata tana ƙara jaddada mata ta dinga shan magani kamar yarda malamin ya ce.
"Habibi da mota na, na zo.
Rumaisa ta faɗa da suka iso parking lot.
"Ki barta anan gobe direban Ammie ya kai miki kinsan dai ba zan bar ki ki yi driving da dare nan ba.
Rumaisa ta buɗe motarsa ta shiga da suka zo bakin gate ta miƙawa maigadi key ɗin motarta ta faɗa masa ya kai wa Ammie za ta kirata a waya.
Akan hanya Ab sai faman rarrashin Rumaisa yake yi tare da kwantar mata da hankali ta hanyar daddaɗan maganganu koda suka iso gida kaso damuwarta ya ragu da kaso saba'in cikin ɗari, main parlor babu kowa sai tulin shopping bags ɗin Aydah wanda da gangan ta zube su anan so take idan Rumaisa ta dawo ta gani, ai kuwa ta gani ɗin nan da nan ta haɗe fuska ta kalli AB wanda shi kwata-kwata bai lura da bags ɗin ba ya haura sama rai ɓace ta bi shi da fari ta so tai masa magana sai kuma ta yi wani gajeren tunani sai kawai ta wuce ɗakinta Aydah da Huwaila dake laɓe a jikin kofar ɗakin Huwaila suka kalle juna suka kece da dariya har suna kashewa daman suna jin shigowar motar AB Huwaila ta tashi da sauri ta leƙa window taga sun dawo tare, ta kwaso da gudu ta faɗawa Aydah shi ne suka baza bags ɗin. Kuma haƙarsu ta cimma ruwa don sun ga reaction ɗin Rumaisa da sauri suka fito daga maɓoyarsu suka tattare kayayyakin suka kai ɗakin Aydah.
Bayan Ab ya yi wanka ya sauko ƙasa yaci abinci ya koma ɗakinsa babu wacce cikinsu ya nema kasancewar yana cikin damuwa ga cancelling partnership ɗinan da Anaal ta zo masa dashi ga kuma damuwar halin da Sadiya ta jefa Rumaisa yana jin tsoro ta sake aikata mummunan abu akan ɗaya daga cikin matansa, da farko yaso ya bar magana a matsayin sirri yanzu kuma yana gani dacewar ya gargadi Sadiya ya kuma nuna mata yasan abun da suka aikata masa idan hakan ta sake faruwa matakin da zai dauka ba zai mata kyau ba.
Da wannan tunanin ya yi bacci washegari da wuri ya fice zuwa office saboda akwai sababbin motocin su da suka iso jiya da dare hatta da breakfast a office ya yi, daga Rumaisa har Aydah ba wacce tasan sanda ya fita sai a waya Rumaisa ta kira sa ya faɗa mata uzurinsa ta ce za ta yi masa lunch ya aiko direban kamfani ya karɓa masa.
Aydah tana zaune a main parlor Rumaisah ta sauko cikin shigar English wears wani mugun kallo ta wurga wa Aydah ta yi ƙwafa ta shige kitchen, koda karfi ɗaya ta buga Rumaisa ta kammala girkin ta, ta zuzzuba a luxury warmers koda ta fito daga kitchen Aydah ta bar cikin parlor ɗakinta ta wuce ta sake yin wanka.
Aydah tana kammala sallar azhar ta ɗauki wayarta ta kira Ab bai ɗaga ba bayan 'yan mintuna ya kirata back.
"Good afternoon mi amor yau fitar safe aka yi ba ko sallama.
"Afuwan ƙanwata fitar uzila ce ta kamani sababbin motocin mu ne suka iso dole na kasance a kamfani yau ba zan dawo da wuri ba, amman zan ba wa Rabi'u sakonki ya kawo miki Allah yasa zaɓina ya burge ki.
"Saƙona kuma wane irin saƙo Yayanmu?"
"Za ki gani idan Rabi'u ya kawo miki amman ki tanadi tukuici da za ki bani.
Dariya tayi tana ƙara dafe wayar "idan wannan ne bakada matsala Yayanmu.
"Haka nake so ji Babyn yaya Abba ni nasan ƙanwata jaruma ce.
Fira suka yi sosai daga bisani ya kashe wayar.
Yana gama waya da Aydah kiran Rumaisa yana shigowa "Habibi da wa kake waya tun ɗazu ina kiranka sai layinka busy?"
"Kin kammala abinci ne na aiko Rabi'u?"
Ya shashantar da tambayarta.
"Eh! Na kammala shi ne ma dalilin kira da nake maka.
"Nagode my love hope kin sha maganinki?"
"Na sha Habibi kaima kasan ba zan yi wasa ba.
"Haka ne ga Rabi'u nan zuwa da sako zai kawo sai ki basa abinci.
"Okay! Take care I love you.
"I love you too my sugary.
Yayin magana tare da kashe wayar sosai sunan sugary ɗin da ya kira ta dashi ya yi mata daɗi ta tashi ta je kitchen ta dauko katon food basket ɗinta ta aje a parlor after like twenty minutes sai ga Rabi'u ya shigo gidan cikin wata tsalelliyar mota 'yar ƙarama irin ta mata maroon colour sabuwar dal cikin ledarta sai painting ta yana sheƙe da ɗaukar ido acikin rana, gashi an yi mata decorative da ballons different colours hatta da key ɗinta sai da aka yi decorative ɗinsa. Sai dab da entrance Rabi'u ya yi parking ɗinta ya fito ya nufi ƙofa ya danna door bell babu jimawa Rumaisa ta buɗe ƙofa hannunta ɗauke da food basket karaf idanunta suka sauka akan mota ɗin, wani kalar zaro idanuwa ta yi ga baki ɗaya kyawon motar ya tafi da imaninta, cikin kidimewa da gigicewa ta miƙawa Rabi'u basket ɗin ta nufi wurin mota ɗin ta buɗe ta shiga ta maida ƙofa ta rufe yayin da Rabi'u ya bi ta da kallo saboda shi yasan ba ita aka ce ya kawowa mota ba.
AB ya kira Aydah ya ce ta je compound Rabi'u zai bata sako idan ta gani ta kira sa cike da zumudi ta sako hijab ɗinta ta fice tana buɗe ƙofa ta yi tozali da mota favorite colour ɗinta. Wani irin shock ta ji ya kamata sai da numfashinta ya ɗauke na wani dan lokaci sai kuma ta buga ihu very excited Rabi'u yana dariya ya miƙa mata key da gudu ta nufi motar yayin da Rumaisa ta yi nisa a begen motar da bana taba batasan kalar waina da ake toyawa ba da gudu Aydah ta nufi sabuwar motarta cikin zumudi ta buɗe ƙofa sai ta yi turuss! Sakamakon gani Rumaisa zaune a driving seat ta ƙanƙame steering wheel.
#Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo.
[1/30, 1:26 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)
NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU
#Love story
#Gwagwarmaya
#Team tagwaye Novels
087.
Rabi'u tsaye yayi yana kallon matan na mai gidansa,wani irin mummunan bugawa ƙirjin Rumaisah yayi ganin car key a hannun Aydah tana jujjuyasa tana Murmushi, wasu irin yawu Rumaisah ta haɗe masu ɗacin gaske kenan da sunan Aydah aka siya motar?"lallai namiji munafuki ne. Shi ne zai ba wa Aydah mota ita ɗaya banda ita me yake nufi da haka?" Fitowa tayi daga motar tana yiwa Aydah wani mugun kallo kafin ta juya da sauri Aydah ta karaso gabanta tana sakin wani irin murmushi tana juya ido tana faɗin.
"Aunty Rumaisah kinga motar da yayanmu ya bani a matsayin gift na budurcina dan Allah ki tayani godiya tayi kyau ko Aunty?"
Da wani irin nauyi zuciya Rumaisah ta koma cikin parlor ranta yana mata ƙona shi dai Rabi'u lallabawa yayi yabar gidan batareda yayi masu sallama ba. Yana ta mamaki a kasan ransa meyasa mai gidansa yayi haka?"zai ba Aydah mota bai ba wa Rumaisa ba wannan ai babu adalci ko kaɗan gaskiya idan akayi duba ma da Rumaisa tafi zama cikakkiyyar macce bisa ga Aydah to ko don yana gani Aydah 'yar uwarsa ce ko kaɗan Rabi'u bai ji daɗin abun da maigidansa Abba Bashir yayi ba.
Da ihu Aydah ta shigo cikin parlor tana kwalawa Huwaila kira, ita ma Huwaila a rikice ta fito da wani irin murna Aydah ta shiga jan hannun Huwaila bata saki hannun ba sai agaban motar da aka kawo mata.
Huwaila ta zaro ido cikin rawar baki take faɗin."ki kara yimin bayani Auta.
"Yayanmu ya aiko min dashi.
Wani kalar zaro ido Huwaila tayi ta riƙe hanci ta saki wata irin guda "shiga Aunty Huwaila mu duba.
Aydah ta faɗa tana buɗe mata frontseat da sauri Huwaila ta shige tana sakin dariyar farin ciki
Ita ma Aydah gaban motar ta shige,
ya kamata na dauko wayata kiyi min hotuna harda ma motar na turawa yaya Siyam da yaya Sadiya har ma da Mami.
"Bari na dauko maki auta
ai wannan abun farin cikin gara kowa yaji sa.
Dafe kai Rumaisa tayi
tamkar wata mahaukaciyya idonta sun kada sunyi ja jikinta har wani kaɗawa yake saboda bacin rai, tana ta tunanin me ta yiwa Abba Bashir da zai yi mata wannan tozarcin yana nufin yafi jin daɗin mu'amular aure da Aydah akanta?" idan ba haka ba meyasa zai siyawa Aydah motar da ta kudinta ya kai miliyan goma daukar wayarta tayi ta shiga kiran layin Aunty Raliya,tana ɗagawa ta fashe mata da matsanancin kuka mai girgiza zuciya da ruhi.
"wallahi-tallahi ba zan iya kishi da wannan kwailar ba Aunty Raliya mutuwa zanyi.
"Yau kuma me ya haɗa ku?"
Raliya ta faɗa tana sauraren kukan kanwartata.
Nan take Rumaisah ta faɗa mata abun da ya faru ita ma Raliya taji babu daɗi haka ta taya ƙanwarta kishi.
"To ke yanzu wane mataki za ki dauka? Don wannan ma rainin hankali ne.
Cikin kuka Rumaisa ke faɗin.
"wallahi-tallahi jin nake kamar naje na sakawa motar fetur da mamallakiyyar motar dukka
na ƙonasu uban kowa ma ya huta.
Wata dariya Raliya tayi tana faɗin "idan kika ƙonasu kina jin haka za'a barki?" Ɗan shiru Rumaisah tayi tana jin bayanin da Aunty Raliya take mata ta cikin wayar "kema ki nuna masa bacin ranki kawai yau kema a kawo miki sabuwar mota idan har ana son zaman lafiya da kwanciyar hankali
da haka suka yi sallama da Aunty Raliya.
Hakan kuma yasa ta ji ɗan sanyi aranta jin kalar shawarar da auntyn ta ta bata ta kuma gamsu da ita ɗari bisa dari.
"kina ji Auta!
"Ina jin ki Aunty Huwaila yau ina cikin farin ciki na rasa ma me zan yiwa yayanmu wanda zan biyasa dashi saboda farin cikin da ya bani ayau. Ban taɓa tsintar kaina cikin farin ciki da annashuwa kamar yadda nake jin kaina yanzu ba Aunty Huwaila ki bani shawara me ya kamata na yiwa yayanmu a matsayin tukuici wannan babbar kyauta da ya yi min? nasan ba zan iya biyasa farin cikin da ya sakani ba dukka annan ina so shi ma na sanya shi cikin farin ciki.
shiru Huwaila tayi alamar nazari
tayi saurin kallon Aydah tana faɗin "shin kwanan Rumaisah nawa gidan nan?"ɗan shiru Aydah tayi tana faɗin,gobe zata cika sati ɗaya ɗan jim Huwaila tayi tana faɗin."ya kamata mu barsa zuwa gobe Auta tunda ya raba muku girki gobe za ki karbi girki
ya zama dole gobe ki fara shiga kitchen duk wannan sakarcin ki ajesa a gefe ki riƙa yiwa mijinki girki da hannunki a da kaɗan-kaɗan za ki iya.
Nan da nan Aydah ta bata fuska ita fa ta tsani girki gaskiya,ko kaɗan bata son shiga kitchen.
"ke kina yi kuma Aunty Rumaisa tana yi ba shikenan ba?" Ni fa Aunty Huwaila kin san bana son zafin kitchen, duk abun da sai an wahala akansa ba sonsa nake yi ba.
"Auh Allah?"ashe kuwa Rumaisah z ata kwace miki miji wai ke yaushe za ki yi hankali?"haka za ki zauna ba zaki riƙa yiwa mijinki girki ba. Ke bakya jin wani iri ne?"idan ma mafarki kike ki farka zamanki haka ba zai yiyu ba. son jikin ki yayi mugun yawa Auta.
Ita dai Aydah jin Huwaila kawai take yi ranta duk babu daɗi musamman da Huwaila tayi zance shiga kitchen abun da ta tsana kenan.
A gigice Siyama ta faɗa ɗakin Mami tana kwala mata kira jikinta sai bari yake "Mami kinga motar da yayanmu ya siyawa Aydah. Mami kalla kiga ta turamin Mami
new model ce.
Ɗan Jim Mami tayi batareda ta karɓi wayar da Siyama ke bata ba "Allah ya sanya Alkhairi.
Ta faɗa adakile dan shiru Siyama tayi tana kallon yanayin Mami,sai kawai ta juya tabar ɗakin har cikin aranta yayan nata ya gama biyata musamman da Aydah ta faɗa mata
matsayin gift ne na first night ɗinsu ne.
Haka siyama ta rika posting kafafen sada zumunta tana taya little sis ɗin ta murna.
AB bai shigo gida ba sai bayan ishaai a gajiye ya yake, parlor kasa ya tarar da Aydah da Huwaila da gudu Aydah taje ta shige jikinsa tana masa sannu da zuwa tayi wanka tana cikin riga da skirt na kanti wanda suka yi mata matukar kyau,kunya duk ta cika AB ganin yadda Aydah ta wani makalesa a gaban Huwaila.
Huwaila nayi masa sannu da zuwa ta sulale tabar cikin parlor.
"baby na gaji wanka nake bukata.
ya faɗa yana manna mata kiss akan lips ɗinta. Ɗan lumshe ido tayi kafin ta budesa akansa da gaske yana tare da gajiya dan kana karanto hakan
ta cikin fararen idanunsa da suka ɗan faɗa ta karbi suit jacket ɗinsa
da kuma briefcase ɗinsa.
"mu je na rakaka yayanmu.
Tare suka jera har zuwa ɓangarensa ɗan turus Aydah tayi