Author : EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category : KDP NOVELS
bene ya shigo ɗakin a gigice.
#Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo.
[1/31, 2:11 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)
NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU
Love Story
#Gwagwarmaya
#Team Tagwaye.
090.
Aydah tana gani AB ya shigo ta daka tsalle ta yi faɗuwar 'yan bori idan wannan makircin ne ta daɗe da iya shi don haka take yiwa su Sadiya idan sun dake ta muddin tasan AB yana ga wuri har suman karya take yi, shi kuma ya bi ya gigice ya hau su Sadiya da duka sai Mami ta kwace su. Saboda haka Rumaisah batasan wacece Aydah ba shiyasa ta gwada marinta.
"Wayyo! Wayyo Allahna na shiga uku idona aunty Rumaisa kin makanta ni Yayanmu kana ina Dan Allah ka zo ka cece ni aunty Rumaisah ta cire min idona.
Abun da Aydah ke ta faɗa tana maimata wa tare da gunji kuka a rikice Ab ya zube guiwayoyinsa gabanta tare da kama fuskarta ya ɗago ta, ta wani runtse idanuwanta gan-gan wani irin mugun tsoro ne ya rufe shi, cikin masifa ya kalli gefen da Rumaisa take tsaye da sakakken baki tana kallon dramar queen don bata taɓa tsammani Aydah ta iya kalar wannan makircin ba.
"Me kike mata ne Rumaisa?
"Babu abin da na yi mata sharri ne kawai take so tai min.
"Yayanmu bottle ɗin turare ta buga min a idona Dan Allah ka kira Daddy ya yi maka izini ka maidani gidan Mami, ba zan iya cigaba da zama anan gidan aunty Rumaisa ta ce sai ta kwakule min idanuwana.
"La'illaha illallahu muhammadu Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallam! Yaushe na fadi haka ashe yarinya nan munafuka ce ke ni za ki haɗa wa makirci?"
Rumaisah ta yi magana tana zaro idanuwa tare da tafa hannuwa tsoron Allah ne ya lulluɓeta ashe kallo biri da take yiwa Aydah ita kuma tana mata na ayaba sai yau ta kara yarda da karin maganar nan da ake cewa bari raina kankantar allura ita ma ƙarfe ce ɗan hakki da kai raina wata rana shi ke tsone maka ido.
"Ƙarya kike yi Rumaisa da gaske kin buga mata bottle ɗin iya sanina da baby Aydah bata ƙarya don haka idan wani abu ya sami idonta idan duk Afrika danginki ne sai na yi shari'a dake.
Ya ƙarashe magana yana huci sosai hanta cikin Rumaisa ta kada tai mutuwar tsaye, AB ya ɗauki Aydah in a bridal style ya bi ta gefen Rumaisa ya fice daga ɗakin koda ya fito Huwaila tana jikin dauko car key, da sauri Huwaila ta zo dafa Aydah "Sannu Auta Allah ya saka miki.
A hankali Aydah ta ware idanunta da ta rufe su gam ta kalli Huwaila tare da sakar mata murmushi tuni Huwaila ta harbon jirgin ta, zaro idanuwa Huwaila ta yi tana kallon Aydah footsteps ɗin AB a asibiti zai kaita ta kula da gida kamin su dawo ta amsa masa da to.
Kaitsaye asibiti eyes care center ya wuce da ita aka duba idon nata tare da rubuta mata magani abun da ya ƙara harzuƙa Ab bai wuce yadda yaga idonta Aydah guda jini ya kwanta a cikinsa, saboda a ido mari same ta ransa ɓace suka dawo gida ga Aydah sai kuka take masa ita a dole gidan Mami za ta koma. Suna shigowa ya wuce ɗakin Rumaisa ya tarar da ita kwance akan sofa tana waya da aunty Raliya dan tun fitarsu ta daga waya ta kira aunty Raliya domin neman mafita akan tarkon da Aydah ta danna mata. Yadda ya turo ƙofa a fusace yasa Rumaisa ta katse wayar babu shiri ta miƙe zaune tana zarar idon.
"Ashe Rumaisa ke muguwa ce bansani ba? Ashe ke ɗinan za ki iya kisan kai?"
Rumaisa ta haɗiye wasu yawu kafin tattaro jarunta ta yafawa kanta cikin dakewar zuciya ta ce "Ka ga Habibi daina jifana da muguye kalamai yarinya nan muguwar makira ce daga na je na ce ta zo mu ci abinci ta hau ni da zagi ni kuma na ji ba zan iya jurewa ba na mare ta, amma da yake ita ɗin munafuka ce sai ta ce na buga mata kwalbar turare to wallahi-azim sharri tai min marinta kawai na yi.
"To akan me za ki mare ta haifar ta kika yi ne ko me? Da za ki ware wannan ƙaton hannun naki ki mare ta dashi to wallahi karki kuskure hannunki ya sake sauka a jikinta.
"Ko gobe tai min rashin kunya sai na hukunta ta don ba zan zuba ido yarinya ƙarama tana min rashin kunya ba in kuma ka gaji dani ne Habibi babu dole ka fito fili ka gayamin don haƙurina yana dab da ƙarewa, dan ina sonka ba shi ne zai ba ka damar ka dinga wulakanta ni ba.
"Ai kin ji matsalarki ba damar a nuna miki kuskurenki za ki hau faɗar maganganu marasa kai balle kan gado, ni fa zalunci ne banaso. Yarinya nan tamkar amana ce agare mu dukka ita ce mai karancin shekaru acikin mu dole sai mun lallaɓa ta.
"Kashh!
Rumaisa ta faɗa cike da takaici tana dafe goshinta "wai kai Habibi da zarar an yi magana akan Aydah sai ka dinga faɗar yarinya ce yoo yarinya ce tasan ta kwana da namiji ko namiji shirgegen ƙato kamar ka. To na dawo daga rakiyar wannan kalma.
"Yarinya ce mana akanki ke da an maki auren wuri ai da tuni kin haifi kamar ta.
"Iyeee!
Rumaisah ta faɗa tana zazzare idanuwa tare da dafe ƙirjinta "Habibi ka ji tsoron Allah ka dinga fadar abun da hankali zai ɗauka dukka guda nawa nake da zai haifi kamar Aydah.
"Ai tsoron Allah ne yasa na fadi haka don ki kama girmanki kada 'yar cikinki ta raina ki.
"To na ji idan ni 'yar cikina ce kai kuma jikarka don wallahi abin kunya Habibi akanka ya ƙare kai da ke shige wa ɗaki da ita.
"To ai ni namiji ne daman can ba kunya ce dani ba.
"Ai kuwa naga alama.
"Na dai faɗa miki ki kama girmanki idan kika sake dukanta wallahi riƙe ki zan yi ta rama.
Cikin kaɗuwa Rumaisah ta dafe ƙirji al'amari Ab ya fara bata tsoro zuciyarta ta shiga kissima mata shi ma ba banza aka barsa ba domin son da AB yake mata bana wasa bane a yau a waye gari yana gasa mata zafafan maganganu irin wannan da akwai alamar tambaya.
Ya juya yana cigaba karkashin pillow ta runtse idanuwanta Ab ya ƙaraso ɗauke da sallama ya nemi kusa da ita ya zauna tare da riƙo hannunta "sannu Baby ya kike ji idon naki har yanzu yana miki zafi?"
Ya yi magana cikin sanyi murya Aydah ta buɗe idanuwan nata tana faɗin "Da sauki Yayanmu yaushe za ka kaini gida?"
"Baby ina tunani ai mun gama wannan maganar ko?"
"Amman Yayanmu ka...
"Baby please karki ɗaga min hankali mana na ɗaukar miki alƙawari ko ɗan yatsa Rumaisah ba za ta sake nuna ki dashi ba.
Aydah ta turo baki ya saki hannunta ya kwanta kusa da ita ya wani rungumo ta cikin jikinsa kiran sallar magarib yasa shi fitowa daga ɗakin.
******
Sadiya tana kwance a ɗakinta damuwa yana neman ya yi mata yawa duk ta bi ta lalace kullum soyayyar Ab daɗa karuwa take yi a zuciyata, ba yadda bata yi da zuciyarta akan ta ji ta tsane shi amman hakan ya ƙi samuwa, tana so ta yakice shi daga cikin rayuwarta ko za ta huta da azabar da soyayyarsa ke jefa ta ciki. Mami da ta ji shiru yau duk Sadiya bata fito ƙasa ba ta bi ta a ɗakinta, yayin da Mami ta tarar da ita ranta ya yi mugun ɓaci tasan duk saboda wancan Abba ɗin ne take azabtar da kanta, ita kanta Mami a yanzu bata da buri da ya wuce Sadiya ta cire Abba daga rayuwarta tun da ya riga ya yi mata nisa.
"Sadiya wai har yaushe za ki cire sakaran yaro nan daga zuciyarki?" Ni fa ko Aydah dake gidansa da kika ga na yi shiru na zuba musu ido ina jiran zuwa lokaci da zan raba shi da ita banaso Abba ba kuma zan so shi ba ko anan gaba saboda haka ki zuba ido kika yarda zan raba shi da ahalina rabuwa ta har abada.
Sai da Sadiya ta ya mutsa fuska kafin ta ce "Mami na rasa wane irin so ne nake wa yaya Abba da har yanzu zuciyata ta kasa haƙura dashi.
"Koma wane irin so ne ki fitar dashi daga zuciyarki shi ne kwanciyar hankalinki da nawa dukka domin ko kaɗan banaso naganki cikin damuwa.
Wasu zafafan hawaye ne suka shiga bin kumatun Sadiya cike da tausayinta Mami ta rungume ta, tana rarrashinta yayin da can kasan zuciyar Mami take kara jin tsanar Abba tana ƙara kudurta ko ta hali yaya sai ta raba Abba da ƴaƴanta da mijinta.
Huwaila ce ta yi musu dinner saboda Rumaisa ta ce ba za ta taɓa yiwa Aydah girki wannan yasa AB ya umarci Huwaila da ta yi musu kafin Aydah ta sami sauki idanunta ta zai saka ta a catering school ta koyi girke-girke. Lokaci da AB ya kira Rumaisa ta zo su yi dinner ta ce ta koshi saboda haka bai ya
takura ta ba. Yana kammala kallon news ya kira Aydah a wayarsa ta zo ta sami shi a master bedroom ɗinsa ko kaɗan bata kawo komai aranta ba. Ta zura bedroom slippers ta yo ɗakin nasa koda ta shigo yana kwance daga shi sai boxer, duk yasan batada lafiyar idanu amma hakan bai sa ya kyaleta ba har sai da ya sami abun da yake so duk da Aydah ta ji zafi sai da ba kamar ranar farko ba, ta kuma dinga yi masa kukan dinkin ta shiyasa washegari ya ɗauke ta suka je asibiti aka duba wurin har ya haɗe Dr ta ce zai iya cigaba da shagalinsa amma ya dinga yi a hankali ko don duba da ƙarancin shekarun ta. Ai kuwa Aydah ta ji jiki don kuwa Ab bai yi mata da wasa ba yayin da Rumaisa ke nanniƙar baƙin ciki ta kagara ta karbi girki saboda tun ranar da ta yi tsarki ta koma shan magangunanta. Ranar da ta karɓi girki Aydah da Huwaila sun ga kwarkwasa da iyayi shiyasa Aydah tun da magarib ta shige ɗakinta ta rufe duk kiran da AB yake mata taƙi buɗe ƙofa.
Rumaisah yadda taga AB bai nuna dokinsa a fili ba da sanarda shi ta sami lafiya, sai tasha jinin jikinta bata raina kanta ba sai da suka haɗu a shimfiɗa round ɗaya ya yi ya mirgina gefenta yana sauke numfashi kafin kuma ya shiga yi mata korafi "Gaskiya Rumaisa ki rage cushe-cushe da kike yi idan na zo shiga wurin ina ji wa kaina rauni kada garin gyara gira arasa ido don haka ina shawartaki da ki daina don ni ake yi na ce banaso.
Yana karashe magana ya tashi ya shigewarsa bedroom ya bar Rumaisa da sakakken baki, kuka za ta yi ko kuma masifa za tai masa ta ma rasa abun yi me wannan kankanuwa yarinya tai masa ne da ya canza lokaci ɗaya.
*BAYAN SATI ƊAYA*
Gidan AB ga baki ɗaya ya dawo tamkar sansanin yaƙi tsakani Rumaisa da Aydah babu zaman lafiya musamman yanzu da Rumaisa taga AB ya saka Aydah catering school tana zuwa ta fara koyi girke sai ta bi ta tashi hankalinta da zarar taga Aydah kitchen za ta ƙiƙƙire fitina a tsakaninsu, yayin da ita ma Aydah yanzu ta iya tana ce mata kul za ta ce mata ass! AB kullum cikin sulhu yake.
Yau gidan shiru kowacce tana ɗakinta Huwaila kuma ta tafi kasuwa Sadiya ta yi horn maigadi ya buɗe mata gate ta nemi wuri ta yi parking, haka kawai tana school ta ji kewar Ab tana neman tai mata illa ta je office ɗinsa secretary ɗinsa ta ce mata yana gida don ita a tunaninta yana gidan ɗin batasan cewa sun ya fita shi da Abdulkarim wurin sabgogin su.
Hankali kwace Sadiya ta tura ƙofar main parlor ta shigo ta tsaya tana ƙarewa parlor kallon kafin ta ja guntun tsaki, kanta ta haura upstairs parlorn Ab dake sama ta nufa batare da neman izinin ba ta tura ƙofa ta shiga gani baya cikin parlor ta wuce master bedroom ɗinsa anan ma bata gansa ba ita ce har da dubawa bathroom rashin ganinsa yasa hankalinta ya yi mummunan tashi zuciyarta kamar za ta faso ƙirjinta ta fito. Tana fitowa daga ɗakin suka kusan ci karo da Aydah wacce tana ɗakinta ta tuna da kafin Yayanmu ya fita ya ce ta canza mishi bedsheet shi ne ta zo ɗauke da bedsheet ɗin a hannunta kallo-kallo suka shiga yiwa junansu kafin a fusace Sadiya ta ce "Ke ina Yayanmu?
Kallon kin ma raina min da hankali Aydah ta yi mata ta ja guntun tsaki gami da faɗin "Gashi nan goye a bayana.
"Jar ubanan! Aydah ni kike yi wa baƙar magana?"
"Wacece ke Sadiya da ba za a gayamiki baƙar magana ba?" Da fari ma me ya shigo dake ɗakin mijina me kike nema?"
"Sadiya! Aydah sunana kika kira gatsal ba ko yaya.
Sadiya ta yi magana fuskarta cike da mamaki tana kallon fuskar Aydah wacce sai kallon banza take aika mata dashi.
"Kin ga baiwar Allah ka ma hanya ki fice mana daga gida tun kamin na tata miki rashin mutunci ke yanzu ko kunya bakya ji ki ɗebo jiki ki zo har turakar mijin ƙanwarki.
"Aydaaah!
Sadiya ta kira sunanta cikin shouting daman kafin ta zo gidan tasha tortulin ɗinta kan nan nata sama-sama take jin sa.
"Na'am!
Aydah ta amsa tana kallonta a ɗage
"Wallahi ba ki isa ba ki wulakanta ni karki manta kamin Yayanmu ya aure ki ni ce ya fara aure kamin ki shigo gidanan ki zauna cikinsa, har ki amsa sunan matar gidan ni ce na fara amsa wannan sunan, saboda haka ki dawo cikin hankalinki ki san da wacce kike magana kada rudin kuruciya ya ɗibe ki faɗa min maganar da za ta harzuƙa ni na yi miki shegen duka a gidanan babu uban da ya isa ya kwace ki hannuna.
#Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo.
[2/1, 12:50 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)
NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU
Love Story
#Gwagwarmaya
#Team Tagwaye
091.
Kallon amma bakida hankali Aydah take yi wa Sadiya kasa ɓoye mamakinta ta yi har sai da ta furta "Duka fa kika ce Yaya Sadiya? Ki zo har cikin gidan mijina cikin ɗakinsa kuma ki dake ni en gaskiya bakida hankali yaya Sadiya kina bukatar gani psychiatrist.
Aydah tana dasa aya Sadiya ta ɗauke ta da mari ita ma Aydah bata yi kasa da gwiwa ba ta rama marinta, hakan ne ya fusata Sadiya ta rufe Aydah da duka abun ka da karfi ba ɗaya ba sosai take dukan Aydah kamar ba ƙanwa ta da suka fito ciki ɗaya ba.
Ihun Aydah da Rumaisah ta ji yasa ta fitowa da gudu sai ta ji ihun yana fitowa daga ɓangaren Ab sai ta taka birki tana zaro idanu a tunaninta Ab ne yake dukan Aydah nan da nan daɗi ya lulluɓeta ta baza kunnuwa tana ji yadda Aydah ke ihu ga kuma ƙarar fashewar abubuwa da take ji, sai kuma ta ji zuciyarta ta karaya lallai duk laifin da Aydah ta yi wa AB yake mata Irin wannan dukan fitar rai ba ƙaramin laifi bane, idan har bata je ta kwance ta hannunsa zai iya kashe 'yar mutane iyayenta ba za su kyale shi ba tunawa da ta yi hakan zai iya zama silar rushewar rayuwarsa, yasa ta ruga da gudu ta shiga ɗakin turus Rumaisah ta yi tana kallon ikon Allah wanda ya fi gaban mamaki Sadiya ta sheƙewa Aydah wuya da dukkan hannayenta ga Aydah kwance ƙasa wanwar numfashinta yana ƙoƙarin fita daga jikinta, Rumaisah kamar wacce aka mintsina ta ruga ta yi kan Sadiya ta cafke wuyanta ita ma ta shaƙe ta da ƙarfi "Cika ta ko nima na kashe shi shegiya baƙar azzaluma ƙanwarki uwa ɗaya uba ɗaya ce kike neman rayuwarta ke kan wacce irin zuciya ce dashe a cikin ƙirjin ki?"
Rumaisah ta faɗa cikin tashin hankali, zafin shaƙar da Rumaisah ta yi wa Sadiya yasa ta saki wuyan Aydah wacce tuni ta galabaita sai faɗa ya dawo tsakanin Sadiya da Rumaisah, dukan junansu suke yi kamar za su kashe juna Aydah dai tana kwance tana kallonsu tare da sauke wahalallen numfashi. Tun daga upstairs suke suna dambe har suka sauko ƙasa duk sun ji wa junansu rauni, da Sadiya ta fusata sai ta shiga kitchen da gudu ta dauko wuƙa Rumaisah tana gani ta nufo ta da wuƙa gadan-gadan ta kwasa da gudu ta shiga ɗaya daga cikin dakuna dake downstairs idan Allah ya taimake ta akwai key a jikin ƙofar ta rufe. Sadiya ta dinga ihu haɗe da dukan kofar tana faɗin sai ta kashe su dukka biyu dole Ab ya aureta Ab nata ne ita kadai, bata bambanci da mahaukaciya sabon kamu, Aydah da ta ji ɗan kuzari ya zo mata ta miƙe da kyar da nufi ta sauko ƙasa taga abun da ke faruwa saboda yanzu ihun Sadiya kaɗai take ji, tun kafin ta karasa sakkowa ta hango Sadiya da wuƙa tana faɗin Rumaisah ta buɗe ƙofa yau sai ta kashe ta. Wani wawan birki Aydah ta taka, ta juya ta koma ɗakin Ab ita ma ta datse ƙofa wani irin tsoron Sadiya ne ya baibaye tunawa da ta yi Sadiya ta taɓa attempting kashe yayansu ta kuma taɓa yi wa Rumaisah mummunan rauni don haka kisa ba bako abu bane a wurinta.
Sadiya da ta gaji da dukan kofar ta jefar da wuƙa fice a compound ta ci karo da Huwaila hannunta ɗauke da ledoji da ta yo cefane, Sadiya ta gallawa muguwar hararar yayin da Huwaila ta bi ta kallon tsoro a rikice Huwaila ta nufi entrance tana sauri kamar za ta kife ƙasa. Ɗakin Aydah ta fara zuwa ta duba taga bata ganta ba, ta sake fitowa tana kwallawa Aydah kira Rumaisah ta buɗe ƙofa ta leƙo cikin parlor taga Sadiya bata nan Huwaila ce kaɗai a tsaye tana kiran sunan Aydah, da sauri Rumaisah ta fito tana faɗin "Ina Sadiya?"
"Yanzu nan ta fita na haɗu da ita a compound.
Huwaila ta faɗa cikin sanyi murya gaba ɗaya hankalinta yana ga Aydah tana tunani ina ta shiga ne.
Rumaisah ta haura upstairs ta nufi ɗakin da