Author : EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category : KDP NOVELS
bayi da fadawa dake farfajiyar sabgar gabansu suke yi, sai kawai ta yi wuff ta bi ta ƙofar baya da ba kasafai ake amfani da ita a gidan na sarauta ba sai in za a gudanar da wani al'amari dake buƙatar sirri. Da fitar ta ta hango motar Ciroma a gefen hanya da saurin gaske ta isa ga motar wacce tun kafin ta ƙaraso aka bude mata seat ɗin baya, jikinta na rawa ta faɗa cikin motar ta maida murfi ta rufe sai da Ciroma ya ja motar kafin Fulani Umaima ta juya ta kalli Jakadiya tana faɗin "Allah yasa ba wanda ya gamki Jakadiya sanda kike tahowa kinsan al'amari nan yana bukatar zallan sirri?"
"Allah ya taimake ki ina taka tsantsan da dukkan abinda ya shafe ku da izinin mai sammai bakwai ba wanda ya ganni.
"To madallah.
"Jakadiya yanzu ina muka nufa?"
Tambayar da Ciroma ya jefo mata kenan.
"Ranka ya dade birnin gwari.
"Birnin gwari kuma Jakadiya?"
"Kwarai kuwa Allah ya ƙara ma lafiya muddin muna so aiki sha yanzu magani take dole sai mun je birnin gwari wurin boka mai Gunduleliya, domin shine ainihin bokan da ke yiwa uwargijiyata Kilishi aiki kuma tun da muke dashi bai taɓa aiki bai ci ba shiyasa uwargijiyata ta riƙe shi tamau ya zama abin dogaro da tinƙaho ta(wa'iyazubillah Allah ya tsare mana imanin mu)
"To amma Jakadiya kina gani ba Zai fallasa asirin mu a wurin Umma ba kasancewar sa bokanta?"
"Ranka ya dade mai Gunduleliya hatsabibin boka ne mai abin mamaki shi a tsarinsa ba abinda ya fi so yake kuma maraba dashi irin butulci da cin amana, ai na gayawa Fulani Umaima sai da na fara zuwa na nemo izzin zuwanku a wurinsa kuma nan take ya amince har ya yi farin ciki marar iyaka.
"Idan kuwa haka ne Jakadiya mai Gunduleliya shine bangon da zan jingina bayana akansa shine mutumin da zai tsallakar dani ramin da Umma ta haƙa min na kasa tsallake wa shi ne zai kaini da mattakalar nasara.
"Wannan haka yake ranka ya dade.
Jakadiya ta tabbatar mishi da hasashen sa.
Tafiya ce wacce ta ɗauke su tsawon kilomita 252.1km bima'ana 3 hours 33 minutes duk irin mugun gudu da Ciroma ke shararrawa dajin Allah ne falau suka dinga ɗiba har suka iso wata duhu mai sarƙaƙƙiya anan Jakadiya ta umarce su da su yi parking domin iya nan mota take iya zuwa suka ci-gaba da tafiya a ƙafa ga Fulani Umaima da kiba ba ta wasa ba sai nishi da haki take yi daga ƙarshe sai Ciroma ne ya kama ta rabin nauyinta yana ga kafaɗarsa suna tafe yana ƙorafi wata tafiya shi kadai zai zo ba za ta sake biyo shi ba. Ashe tsugunne bata ƙare musu ba saboda ɗan uban Kogi da suka cimma wanda sai sun shiga kwalele an tsallakar dasu, zuwa lokaci ita kanta Fulani Umaima ta gama kisimawa ranta babu uban da zai sake dawowa da ita wannan baƙin daji. Ana tsallakar dasu ba su wuce yi tafiyar mintuna 20 ba suka fara hango wani tafkeken fili mai ɗauke da farin yashi sol har wani ɗaukar ido yake lokaci da suka fara tattaki akansa sai ƙafafuwansu sun lotse a cikinsa kamar masu tafiya cikin ruwa.
#Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo
[12/17/2023, 9:57 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)
NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU
*AREWABOOK*:Jeddah3256
Love Story
#Gwagwarmaya
#Team Tagwaye
027.
Suna fita daga cikin yashi ɗin suka cimma wani gidan kara mai ɗauke da bukkoki uku ga baki ɗaya jikin karan a bi shi da kawuna dabbobin daji a mabanbanta wurare daban-daban ga wani arne wari bunsurai dake tashi Fulani Umaima ta toshe hancinta, Allah ya sanar mata ko kaɗan bata so wari awakai yana mugun ɗaga mata hankali. Can idanuwanta suka yi mata tozali da wasu tirka-tirka bunsurai sun kai su goma kowanne gemin shi na ja da ƙasa ga su da wanɗansu dakwa-dakwan idanuwa. Yadda taga idanuwan bunsurai kafe akanta ya haifar mata da matsanancin faɗuwar gaba da sauri ta kauda fuskarta wani basamuden ƙato ne baƙi wulik dashi ya nufo su yana sanye da ɗan wani ja da baƙin walki ɗaure da ƙugunsa jikinsa duk maiƙo yana tafe uban tumbin sa na rawa sai kace 'ya'ya arba'in ne a cikin nasa mummuna baƙar fuskarsa a haɗe cikin muryarsa mai kama da kukan kwaɗi yake faɗin "Shugabana mai Gundulelliya yana muku barka da isowa daularsa, daular dake cike da biyan buƙata kafin kun isa zuwa gare shi ka'idar wannan daula sai kun fara ciyar da hidimansa abinci, ga kwado can kuna gani kowanne ku ya ɗebo ciyawa ku ciyar dasu cikin ƙauna.
Wani kalan zare idanuwa Fulani Umaima ta yi cikin kaɗuwa take kallonsa kana ta haɗiye wasu busassu miyau cike da tausayin kanta ta yada ganinta akan bunsurai nan masu abin mamaki, bata ankara ba ta ji Ciroma ya cukume hannunta daman can yasanta da tsoron awakai ballantana waɗannan da suka sha bambanta da ire-iren wanda ta saba gani, cike da tsoro ta ɗebe ciyawa ta miƙa musu atare suka farmaki ciyawar tamkar za su haɗa da hannunta, bayan sun gama cinyar dasu kana suka wuce zuwa ainihin bukkar da mai Gundulelliya yake. Suna arba dashi hatta da Ciroma sai da gabansa ya faɗi saboda wasu sassan jikinsa dukka babu su ƙafarsa ɗaya a gundule take haka ma kunnensa guda, dukka yatsun hannunsa goma babu ko ɗaya rabin leɓɓenshi ya cire, haka zalika hancinsa astagfirllah ga baki ɗaya bashi da kyau gani siffarsa ta tashi daga ta ɗan adam zuwa wani mashahurin dodo. Tsabar hatsabibbancin sa zigidir yake sai wani ɗan ganye da ya ɗaura a ƙugunsa wanda bai kare komai na daga tsiraici sa ba, yana zaune gaban kaskon wuta dake ci bal-bal baƙin hayaƙi na fita daga cikin wutar.
"Ciroma barka da zuwa.
"Barka dai.
Ciroma ya faɗa cikin harɗewa harshe.
"Ga wuri ku zauna.
Duk wannan maganar da yake yi idanunsa suna rufe ruff har sai da su Ciroma suka zauna kana ya buɗe idanunsa wanda gara ma ya bar su a rufe su saboda irin abin razanarwa dake cikinsu. "Ciroma ba za ka taɓa mulkin koda sabon birnin kudu ne ballantana karagar mulkin kudu har ka mutu ka komawa mahaliccinka ba za ka taɓa hawanta ba.
Wani irin gumi ne ya karyo wa Ciroma a fuskarsa yasa gefen babbar rigar jikinsa ya goge fuskar tasa cikin kaɗuwa ya kalli mai Gundulelliya muryarsa tana rawa yake faɗin "Yanzu babu wani taimakon da za a iya yi min?"
Mai Gundulelliya ya sheƙe da dariya marar daɗi tsawon lokaci ya ɗauka yana sheƙa dariya kafin ya tsaya kaman anyi ruwan sama an dauke ya wani kalan turɓune mummunar fuskarsa ya ce "Ai tun da ka zo nan Ciroma buƙatar ka ta gama biya lallai za ka yi mulkin kudu za ka shimfiɗa mulki na zalunci amma kasani taurarinka basu da haske ko kaɗan wanda hakan yana nufi akwai wani kurman allo a tattare da kai.
Wani kalan washe haƙora Ciroma ya yi shi ko kaɗan bai damu da zancen ƙarshe da mai Gundulelliya ya yi masa, a ganinsa da zarar ya sami biyan buƙata ya zama sarkin Kudu bashi da wata damuwa a doron duniya.
Yayin da mai Gundulelliya ya ɗebo wasu fararen ruwa kal a wata kwarya suna tafarfasa ya zuba ciki wata batta da aka yi ta da fatar damisa. "Wannan ruwa shi za ka dinga ciyar da sarki Mahmood har na tsawon kwana bakwai idan bai tsallake rana ko ɗaya ba yana shan su tabbas zai mutu idan ya tsallake koda kwana ɗaya ne ba su shiga cikinsa ba zai kwanta matsananciyar jinya, kai kuma za ka hau karagar mulkin kudu.
Godiya Ciroma ya shiga yi kana ya fito da damin kuɗi ya ajiye a gaban bokan sannan suka yi masa sallama. Cike da farin ciki suka koma masarautar kudu.
*MOONLIGHT AUTOMOBILE INDUSTRY KANO*
AB yana zaune acikin katafaren office ɗinsa ga tulin files a gabansa ya kasa duba ko ɗaya ba sosai damuwa ta yi masa yawa. Yanata ƙoƙarin ya gane me Mami take nufi da akan alaƙarsa da Aydah duk iya tunaninsa ya kasa fahimtar kurman Allon na Mami.
Gefe ɗaya ga Sadiya da yanzu ke rawar ƙafa akansa ko kaɗan bayason yadda take wani shisshige masa. Idan kuma ya tuna aurensa da Aydah nan da kwanakin biyar masu zuwa sai ya ji damuwarsa ta ƙara yawa. ƙarfe biyu na rana kiran Mami ya shigo a wayarsa har lokacin yana zaune cikin office ɗin nan da can bai gusa ba hatta da sallar azhar a office ɗin ya yi ta. Bai kawo komai aransa ba daga kiran nata da sallama ya amsa wayar tare da gaisheta da respect ta amsa tana faɗin."idan baka da aiki sosai a office ka je ka dauko Sadiya a makaranta ta kira ni akan na yiwa driver magana ya je ya daukota ni kuma na aiki driver gidan ƙawata Hajiya Zeena. amsawa Mami kurum ya yi da to ya fi minti goma sha biyar kafin ya fice daga office ɗin yana rike da car key a hannunsa sai da ya karaso faculty ɗin su Sadiya sannan ya kirata a waya.
Ba jimawa ta ƙaraso a hankali take takowa cikin wata irin izza da yanga tana ta sakawa Mami da albarka na wannan dabarar da ta yi duk dan tasa ya fasa auren Aydah. Buɗe gaban motar ta yi ta shige ta rufo kofar wata irin natsuwa ta ji yana saukar mata musamman da ta ji ƙamshinsa da ya gama cika motar ya haɗe da sanyi AC. Ta kallesa ido cikin ido ta wani rausayar da kai gefe ɗaya ta ce "Barka da rana yayanmu.
Babu yabo babu fallasa ya yiwa motar key da wani irin gudu ya ja ta zuciyarsa banda tafarfasa babu abunda take duk wannan bai damu Sadiya ba tun da tana tare dashi a gefe tasan wuyarta ta koma gidansa ya shiga hannunta sai yadda ta juyasa duk wannan zafin kan nashi da ɗaɗɗaure fuska da yake mata zai kau.
Yana cikin wannan yanayin kiran Rumaisa ya shigo a wayarsa ɗaga kiran yayi tare da sakawa a speaker
cikin sanyin murya da shagwaba Rumaisa ke faɗin."habeebi yau za ka zo ɗin? pls karkace nooo wallahi ba zan iya jurewa ba kwana nawa ban ganka ba kuma ka ƙi bani damar da zan zo na ganka.
Ta ƙarasa maganar da salon shagwaɓar dake kara narke da zuciyar AB bai san lokacin da ya saki wani irin murmushi rabin damuwar da ya ji ya shiga sai ya ji ta yaye ina driving other half idan na sauka zan kiraki.
"Kasan ina sonka kou?"cikin wata irin natsuwa ya ce."na sani.
"Ka kula da kanka. Ta faɗa cike da kulawa a muryarta."Insha Allah! Ya faɗa yana katse kiran, a lokacin kar kuso ku hango Sadiya yadda fuskarta ta kumbura idanunta suka Kada suka canja kala lokaci ɗaya.
Watau ita haukan banza take ita da Mami akwai ƙura a kasa har yanzu yaya Abba ,yana tareda Rumaisa kenan?"kuma tasan tsananin soyayyar dake tsakanin yayan nata da Rumaisa, ko kaɗan Abba bai lura da yanayin da Sadiyar ta shiga ba ƙofar gida taga ya yi parking batare da ya kalleta ba yana jiran kawai ta fitar masa a mota ya kama gabansa.
Ita ma tana ganin haka tasan ba shiga zai yi buɗe marfin motar ta yi ta fice daga motar.
Mami kawai take son gani a wannan lokaci idan kuma ta tuna yadda yaya Abba ,yake yiwa Rumaisa magana cikin natsuwa sai ta tambaye kanta dama ashe haka ya iya soyayya da tattalin macce har haka duk wannan uban izza nasa da shan ƙamshin nasa.
Wani irin fitinannen kishin Rumaisa yazo ya danne mata zuciya fiye da wanda take ji akan Aydah.
Babu ko sallama haka ta faɗa ɗakin Mami tana kiranta da dukkan ƙarfinta tana jan numfashi tana fitarwa Mami dake tsaye gefen wardrobe tana gyara kayanta ta bi Sadiya da kallo yadda ta shigo mata agigice."ke Lafiya?" Wani zazzafan numfashi Sadiya ta shiga ja tana fitarwa ta yi hakan kusan sau ukku
kafin ta samu wasu irin warm tear's suka dinga fitowa acikin idanunta."ke Lafiya me Abban ya yi maki kuma?" Mami ta faɗa da rawar murya tana kallon Sadiya da take sharar hawaye ta dawo abin tausayi lokaci ɗaya. "Mami ashe yaya Abba har yanzu yana tare da Rumaisan nan da yabi ya nacewa wacce aka wulaƙanta shi akanta?"
"Mami muna hanya ta kirasa baki ga yadda take lankwasa masa murya ba shi kuma sai wani tarairayarta yake.
Mami idan Yaya Abba,ya cigaba da kula Rumaisa zuciyata bugawa zata yi
nayi kuskure Mami laifina ne laifina ne wallahi.
Ta faɗa wani irin kuka mai haɗe da kishi na kwace mata "Da yanzu ina gidan yaya Abba, hankalina kwance mai yasa wannan kalar ƙaddarar zata sameni?" Ta faɗa muryarta na karyewa a hankali.
Tsaki Mami tayi tana faɗin."an faɗa miki ko mahaifinki ya yarda Abba ya nemi auren yarinyar nan a karo na biyu ni zan yadda ne?"ai ta riga da ta rasa shi har abada.!"idan haka bata kasance ba kice ba Mariya bane suna na. So kima daina wannan banzan tunanin ina nan ina jiransa zan basa umurni nima kamar yadda mahaifinku ya basa, zan basa umurnin ya janye auren Aydah a dawo da auren akanki ,cikin rawar murya Sadiya ke faɗin."to Mami idan kuma yaki amincewa fa?"kin san irin biyayyar da yake yiwa daddy fa.
Wani kallo Mami ta yiwa Sadiya ganin haka Sadiya ta ɗauki jakarta da mayafinta ta nufi nata ɗakin. Sai bayan magarib ya hauro upstairs ɗakin Aydah ya fara leƙawa tana kwance akan rug da tulin text books a gabanta ɗagowa ta yi tana kallonsa, cikin sanyin murya ta gaishesa kallonta kawai yake yana mamakin yadda tayi sanyi har haka da adane da ta gansa zata bar duk abunda take ta zo ta kama hannunsa ko ta shige jikinsa."har yanzu ciwon kan ne?"ta girgiza kai tana faɗin ."yayi sauki kallonta ya yi na kusan sakan biyu kafin ya juya yabar kofar ɗakin da ido ta bisa.
Knocking ya yi a ƙofar ɗakin Mami sai da ta basa izinin shiga sa'annan ya shiga ya samu Mami zaune agefen bed tana danna wayarta
Ta amsa sallamarsa ta dauke kanta shigowa ya yi cikin ɗakin ya zauna akan soofa ya saukar da kansa ƙasa
yana son jin Mami me za tace gyaran murya ta yi kafin ta aje wayar hannunta."kana jina Abba?"
Ɗan ɗagowa ya yi ya kalli Mami kafin yace "I' ina jinki Mami .
"Yaushe ka fara take maganar iyayenka?"
Mamakin furucin Mami yake har ya kasa cewa komai kurum ya kalleta ya sadda kai bai daice komai ba dan bai san me tambayarta ke nufi ba
"Dama har yanzu kana tare da yarinyar nan Rumaisa mu ka mayar yan iska kenan."
Wannan karon Mami ta faɗa da ɓacin rai cikin muryarta.
"ku yi haƙuri Mami tun lokaci ta rika bina tana bani haƙuri kuma wallahi ba laifinta bane laifin mahaifinta ne.
Da baki buɗe Mami ke kallon Abba tana mamakin yaushe har ya yi baki haka yana kare budurwarsa agabanta.
"A haka kake so a kai maka Aydah kana cigaba da kula tsohuwar budurwarka?
Ya Rasa me zai ce da Mami wani ƙwafa Mami ta yi tana faɗin."dama kiran da na yi maka ka je ka samu Daddynku ka faɗa masa ka amince a mayar da aurenka da Sadiya auren naka ma da sadiya zaifi akan Aydah. Tun da ni na basa shawara yaki dauka kai sai ka je ka gwada taka sa'ar.
kallo Mami kawai yake rasa ma abunda zai ce mata ya yi jin yayi shiru Mami ta ce "Ko hakan bai yi maka ba Abba na ga ba kace komai ba?" da sauri AB ya girgiza kansa yana faɗin."shikenan Mami I will talk to him."Mami ta tabe baki tana faɗin."better!"za ka iya tafiya.
jiki a sabule ya baro ɗakin Mami ko gabansa baya gani a wannan lokacin maganganun Mami ,yake ta faman juyawa aransa ya ma kasa fahimtar me wannan kurman Allon nata ke nufi shi dai yasan har abada ba zai yadda ya kara auren Sadiya ba. koda Daddy ya yarda shi ba zai yi shiru ba a wannan lokacin gara ya auri Aydah da dai ya auri Sadiya yarinyar da ta yi yunƙuri raba sa da rayuwarsa me zai yi da ita daman kuma yasan shine guarding angel ɗin Aydah ga baki ɗaya Mami ta bata masa mood ɗin fita ya je yaga Rumaisa ko kaɗan baya son Rumaisa ta fahimci damuwar da yake ciki har aka kira ishaai yana jin ana sallah a masallaci ya kasa zuwa.
#Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#team tagwaye novels
#Kurmam Allo.
[12/18/2023, 10:15 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)
NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU
*AREWABOOK*: Jeddah 3256
Love Story
#Gwagwarmaya
#Team Tagwaye
028.
AB da yaga wanki hula zai kaishi dare ga rashin mafita sannan kuma ga na sallah ya tashi adaddafe ya shiga bathroom ɗinsa ya dauro alwala ya fita masallaci duk da yana da tabbacin zuwa yanzu an dade da gama sallah. Kawai dai ba zai iya sallah a cikin gida ba, bayan ya gama sallah ya nufo gida har zuwa lokacin ya kasa tsayar da zuciyarsa a wuri ɗaya sai ya ji kamar ya amince da auren Sadiya sai kuma wata zuciya ta kwaɓe shi, ta kisimamai gara auren Aydah sau million da Sadiya idan ya aure Aydah da matuƙar wahala ya sami matsala daga gare ta. Hakan ma zai bashi damar sake neman the love of his life Rumaisa zai fake da ƙanƙatar Aydah ya aure zaɓin zuciyarsa. Da wannan tunani ya tsaya bakin gate wurin Balmo maigadi ya karbi waɗansu takardu da ɗazu aka aiko masa dasu ya ce aba wa Balmo ɗin ya ajiye masa. karɓa takardun kawai ya yi ya nufi bangaren Daddy, domin akwai tattaunawar data shafi kamfani za su yi tun sanda AB ya shigo har ya zauna idanuwan Daddy suna zube akansa. Bayan ya gaida Daddy ya nemi kasa rug carpet ya zauna tare da miƙa masa takardun hannunsa "Daddy idan ka sami lokaci ka duba wannan yarjejeniyar kasuwanci ne da kamfanin kim's ke son ƙullawa damu har sun nemi zama na musamman dani a kamfaninsu dake Lagos ina tunani gobe ko jibi zan tafi Lagos ɗin.
Har AB ya kai ƙarshen maganarsa Daddy yana kallonsa sai da Daddy ya sauke naunnayar ajiyar zuciya kafin ya furta "Bashir me ke damunka?" ga baki ɗaya ka