Kurman Allo Sakamakon Kin Karɓar Gaskiya by EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU

Author :  EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category :  KDP NOVELS

Chapter   22 / 80

63K to 66K   out of 237.2K words

dukka. Lokaci ɗaya yanayin fuskar Sadiya ya canja tana girgizawa Sarah kai take faɗin."banda wannan. Wata dariya Sarah ta saki tana faɗin."ki sha na yau kawai Sady-B ni na faɗa miki damuwar nan zata rage dan Allah ki sha.
Da haka Sarah ta kwance marfin batare da dogon tunani ba ta kai sa daidai bakin Sadiya dakyar Sadiya ta buɗe bakint tana fara sha ta wani irin ya mutse fuska da sauri ta janye kwalbar daga bakinta tana girgizawa Sarah kai haka tana jin kanta na wani irin juyawa lokaci ɗaya. Sarah ta dinga yi mata dabara har ta shanye dukka ta dauki bottle water ta miƙa mata ta sha rabi anan ta baje tsakiyar ɗakin ta koma ta kishingiɗa tana jin yadda kanta yayi wani mugun nauyi babu shiri ta lumshe idanunta. Gefe Sarah ta koma tana ta lura da yanayin ƙawarta ta har na kusan minti goma sha biyu kafin bacci mai nauyin gaske ya Sadiya. murmushi Sarah ta yi tana faɗin."idan kika farka ke da kanki za ki nemi ƙari wani.
ƙarfe biyu AB ya fita restaurant yaci abinci saboda yadda hanjin cikinsa ke haɗewa wuri ɗaya babu abunda ke cikin cikinsa, tun safe yana gamawa ya koma office bai bar office ba sai karfe biyar tilas gida ya koma dan yin wanka yana ta tunanin zuwa wurin Rumaisa da yamma, ya kamata ya faɗa mata hukuncin da Daddy ya yanke ganin kwanakin nata matsowa. Bai shiga da motarsa cikin gida ba a waje yabarta dan ko kaɗan baya son haɗuwa da mami. Har ya shige ɓangarensa bai haɗu da kowa ba kayan jikinsa ya cire yayi wanka.
Yana cikin shiryawa ne ya ji ana buga masa door bell dan buɗe idonsa yayi da mamaki jallabiyya ya nema ya saka ajikinsa dan ko creams ɗinsa bai gama shafawa ba ya saka (casual slippers)a ƙafarsa ya nufi kofa yana buɗe kofar idonsa cikin na Siyama
da murmushi a fuskarta ta gaishesa ya kalli tray ɗin dake hannunta
"Sannu da dawowa yayanmu ya office?" Mami ta ce a kawo maka lunch, da haka ta isa kan dinning ɗin dake cikin parlorn ta aje masa. Sosai yayi mamakin yadda Mami tasan ya shigo gidan, bai san da cewa Mami magana ta yi da Balmo maigadi akan idan Abba ,ya dawo kai tsaye ya kirata a waya haka ko aka yi yana ganin dawowarsa ya kira Mamin a wayar har yana ce mata bai shigo da motar na kila zai ƙara fita ne. murmushi kawai Mami ta yi watau Abba ya mayar da ita yar iska a lokacin suna zaune da Siyama a parlor Mami ta mata umurnin ta zuba abincin ta kai masa acan bangarensa. Yana tsaye a bakin ƙofa har Siyama ta aje ta dawo.
"Ki jira ni"
Ya ce da Siyama yana barin bakin ƙofar ɗakinsa ya wuce ya buɗe bedside drawer ya ciro keys ɗin motarta ita da Sadiya, tun da ya miƙa mata take kallonsa da murna take faɗin."mungode sosai yayanmu amman ka jawa babynka kunne ta daina yimana rashin kunya.
"Ai bama sai na ja mata kunne ba ita ma motarta na zuwa kwanan nan. Ɗan buɗe ido ta yi tana kallon yayan nasu sai dai ba tace komai ba ta juya tare da ficewa daga part ɗin tana murmushi tasan wasa yake wane mahaukacine zai siyawa Aydah mota, daman ko kallon abincin da Siyama ta aje bai yi ba ya koma master bedroom ɗinsa ya ci-gaba da shiryawa yana gama shiryawa ya fice daga gidan sai da ya fito gidan ya sauke wata irin ajiyar zuciya sosai Mami ,tasha mamakin Abba yadda ya mayar da ita wata shashasha ya ƙara ficewa batare da ya shigo ba. Yana driving ya yi dialling lambar Rumaisa tamkar jiran kiran nasa take ta dauka agagauce cikin muryar kuka take faɗin."wallahi ka daina sona habeebi.
"Ina hanya.
Ya faɗa tare da saurin katse mata hanzari duk sai haka sai da take furta
"Da gaske kake yi Habibi?
"ko na koma ne?"
Da sauri tace "A'ah sai ka ƙaraso.
Da haka ya sauke wayar wannan karon kuma bai san ta yaya Rumaisa zata karbi wannan al'amarin ba. ƙofar gidansu Rumaisa ya yi parking motarsa ya kirata a waya bai fi minti goma ba da kiran nata sai ga ta, ta buɗe ƙaramar ƙofar dake haɗe da gate ɗin gidansu tun kafin ta karaso ya sauke glass ɗin motar riga da skirt ne ajikinta na Atamfa sun yi mata kyau sosai sai dan karamin veil ɗin da ta ɗora kan kafaɗarta light make up ne akan fuskarta wanda ya kara fito da asalin kyawunta ta yi masa kyau ba kaɗan ba.
Kallonsa kawai take cin karo da fuskarsa kawai da ta yi yanzu duk wani haushinsa da take ji tun jiya ya ɓace daga zuciyarta.
Tana mamakin yadda bata iya fushi dashi, fitowa ya yi daga motar yana ci-gaba da kallonta ƙasa-ƙasa kamar yadda ita ma take kallonsa girar ta dukka biyu ta dage."kayi kyau sosai Habibina!
Ta faɗa a hankali ,kafin ta kuma ta cigaba da ƙarewa kayan jikinsa kallo na tsanake baƙin yadin filtex ne ajikinsa sai links da aka yiwa hannuwan wani sanyayyen murmushi ya sakar mata irin mai shiga jiki yana shafa sumar kansa mai kama da ta labarawan asali murya can ciki ya ce "Ban kai ki ba habibty.
"Zagina kake yi.
Buɗe mata manyan fararen idanunsa yayi ,camera wayarta ta saita ta shiga daukarsa pics tana faɗin "kai ba zaka gane kyan da kayi bane.
Bai ce da ita komai ba iyankacin sa ya yi murmushi dawowa tayi daf dashi ta shiga daukarsu video duk da bai yi dariya ba Amman a hakan ya yi mata kyau sosai. Ya girgiza kai ya rasa soyayyar Rumaisa da son hotuna.
Idan kaga hotonsa to Rumaisa ce ta tilasta masa yinsa. "Mu shiga daga ciki wai meyasa kake parking motar ka a waje?." Ta faɗa da yanayin marar daɗi a muryarta, kin manta Daddy..
Da sauri ta katsesa tana faɗin."baya gari fa ta karɓe car key ɗin motarsa ta shiga ɓangaren driver ta tada motar ta doshi get ɗin gidansu tana yiwa maigadi horn sai da ya leƙo ganin Rumaisa ce ya buɗe gate ɗin da wani irin kallo ta bisa ganin yadda yasata take ta danna masa horn sai kace wani kurma gyara parking motar tayi.
Har lokacin tana mamakin AB da yaki shigowa ,tana kawowa wurin maigadi ta yi masa wani shegen kallo ta fice daga gate ɗin a tsaye ta samu AB yana jiranta ƙarasawa tayi wurinsa tana faɗin."kaga na shiga mota kaki shiga kuma ka zo ka yi tsaye anan mu karasa aciki mana.
Kallonta yake da wani yanayi dake kwance cikin idanunsa mai cike da zallar ƙaunarta bin bayanta ya yi har zuwa parlorn da suka saba zama duk lokacin da yazo gidan. Kayan motsa baki ta aje masa agabansa ta dauki glass cup ta zuba masa lemu..


#Love story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo.








Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only




ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130


KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730


Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336






*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.


*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar


*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu


*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce


*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari


*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan


Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500


VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k


NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[12/19/2023, 11:07 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)


NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU




*AREWABOOK*:3256


Love Story
#Gwagwarmaya
#Team Tagwaye


030.


"Habeebi!" Rumaisa ta kirasa cikin sanyi murya ganin yanayinsa ba haka ta saba ganinsa ba, sai da ta ƙarewa masa kallo ta sauke numfashi kafin ta ce "meke damunka ne kwanan nan?"duk ka zama wani iri.
murmushin iya fatar baki ya yi mata yana shafa beard ɗinsa yana kallon yadda take wani bin jikinsa da kallonsa tamkar mai neman wani abu a jikin sa tana kallon yadda idanunsa suka fada duk girmansu sai da suka shige "ka rame bakada natsuwa tare da kai ka daina boyemin damuwarka.
Rumaisa ta faɗa da wani yanayi a muryarta da tasa zuciyarsa wani irin dokawa.
"Zan kara yimaki laifi Rumaisa amman karki manta a kowanne yanayi sonki ne manne a zuciyata karki dauka da son raina zan yi miki wannan laifin ina sonki!"inason ki Rumaisa wallahi ke ce macce ta farko da zuciyata ta fara so da ƙauna.
Yadda yake ta maimaita yana sonta yana kara narkar mata zuciya har ya fara daga mata hankali kamar wani abu mai girma zai gifta a tsakaninsu.
"Zan dauki kowanne irin laifin da za kayi min banda....
Tun kafin ta karasa ya katseta dan yasan me zata faɗa."Daddy ya yanke shawarar auramin Aydah a karo na biyu nan da jibi.!"
Shi kansa yadda ya faɗi kalamar cikin da sauri yasha mamaki yana kallon yanayin Rumaisa da ya canja lokaci ɗaya, tamkar bata fahimce me yake nufi ba. Ganin yadda ta zama lokaci ɗaya yasa ya dawo kusa da ita hannunta ya kama ya damƙe cikin nasa yana ganin yadda idanunta suka cicciko da kwallah lokaci ɗaya, "Ki sani Rumaisa aurena da Aydah ba zai canja alakarmu ba Rumaisa idan mahaifinki ya amince dani bayan aurena da Aydah zan aureki saboda ke ce zaɓin zuciyata.
Kalamansa banda ƙona mata rai babu abunda suke cikin tsanani ɓacin rai ta ce "ka aureni a ina? Na haƙura Bashir da gaske na haƙura da kai.
Ta faɗa cikin fita hayacinta.wasu irin hawaye ne ke fita akan fuskarta tana jin yadda jikinta ya dauki wani kalar dumi kamar zazzaɓi zai rufeta lokaci ɗaya.babu abunda zai canja Rumaisa."meyasa kike shakkar soyayyar da nake yimaki,aure zakayi meyayi saura a tsakanin mu kuma auren da Aydah
Wani irin murmushi take saki wanda bai da alaƙa da farin ciki "Daga ranar da ka haɗa gado da wata macce daga ranar zan daina sonka.! Ba zan boye maka ba ina da kishin da Ni kaina ban san kalarsa ba musamman akan ka Bashir. Tun kafin ma hakan ya faru na faɗa maka kar ya faru kaga na canja ka ce dan me?"
Kallonta yake yana juya Kalamanta aransa, kina nufin da ƙanwar tawa zan haɗa gado Aydah ce fa?
Ya faɗa a hassale hakikanin gaskiya Rumaisa ta fara harzuƙa shi akan me za ta ce ya haɗa gado da Aydah, sai kace bashi da ƙwaƙwalwa a kokon kansa, maganganun ta su yi matuƙar yi masa muni.
Rumaisa ta kalle shi a lalace ta ce "Wannan ɓangaren bai da yare"!
Ni dai na hakur....
Tun kafin ta ƙarasa ya fisgota cikin jikinsa abunda bai taɓa faruwa ba a tsakaninsu tana jikinsa tana jin yadda ƙirjinsa ke wani irin bugawa sosai ta rungumesa hawayenta na sauka kan ƙirjinsa "Zan iya mutuwa habibty idan kika sake cewa na haɗa gado da Aydah she's like a daughter to me babu wannan zance a tsakanin mu
na amincewa Daddy da aurenta ne saboda ba zan iya masa musu ba Rumaisa dukka Aydah nawa take da za ki yi wannan kalar tunanin me ma ta sani acikin rayuwar aure? ki kwantar da hankalin ki Rumaisa babu abunda zai canja ni naki ne na har abada Aydah kawai zata cigaba da zama a karkashin kulawata da ta girma ta mallaki hankali kanta ni kaina zan samu mata mijin da ya dace da ita zan rabu da ita cikin sauki batare da Daddy ya ji zafina ba.
Ita ma Aydah a matsayin yaya take kallona na kuma tabbata har abada ba za ta canza min wannan matsayin ba. Na maki alƙawarin babu abunda zai canja matsayin Aydah a zuciyata.
Ɗagowa ta yi daga cikin jikinsa tana dan ja da baya kusancinsu yasa take jin wani iri kalamansa kuma ba karamin sanyayya mata zuciya suka yi ba tasan halin AB baya magana biyu kuma tasan babu abunda zai cira ajikin Aydah yarinyar da ma nonuwa basu gama tsayawa a kirjinta ba me za ya yi da ita amma sanin da ta yiwa butulci irin na ɗa namiji sai kawai ta ce "Habibi na yarda da kai ɗari bisa ɗari amma inaso kauda duk wani kokwanto da zai zo min anan gaba Habibi me zai hana ka rantse da Alqur'ani ta hakan ne kaɗai zan ƙara yarda da kai ɗin nawa ne ni kaɗai.
Wani malalaci murmushi ya yi yana faɗin "Habibty ba ki yarda dani ba.
"No Habibi wallahi na yarda da kai the only problem ku maza ba ku da tabbas yanayin ku tamkar na hawainiya ne koda yaushe kuna iya canza kala.
"Habibty da kin yarda dani da ba za ki nemi na rantse da Alqur'ani ba ki tuna Rumaisa Alqur'ani ba abin wasa bane.
"Ai shiyasa na ce ka rantse dashi idan har ka amince ka yi rantsuwa dashi ni kuma zan nemi hanyar da zan sa Abbana ya amince da aurenmu, yanzu zaɓi ya rage naka kuma ta wannan hanyar ce zan ƙara tabbatar da ni kaɗai ce a zuciyarka.
Duk yadda AB yaso Rumaisa ta janye zance rantsuwa da Alqur'ani amma ta kafe lallai idan da gaske yana sonta dole sai ya yi abinda take so daga karshe baram-baram suka rabu a fusace ya yi mata sallama ya koma gida.
Sai dab da magarib Sadiya ta tashi daga naunnaye baccin da ya ɗauke ta a ɗakin Sarah da kyar ta iya tashi zaune wani irin azababben ciwon kai take ji a hankali ta dafe goshinta tare da runtse jajjayen idanuwanta da suka mata dankaran nauyi ta dauki ten minutes a haka kafin ta yada ganinta a cikin ɗakin Sarah bata nan room mate ɗinta kaɗai ta gani kwance a nata gado tana chatting da wayarta Sadiya ta ja deep breath tare da sauke wa ta kalli Esha cikin nauyin harshe ta kira sunanta "Esha!
Da hanzari Esha ta waiga gafen da Sadiya take cikin fara'a ta ce "Ah! Sadi-B kin falka?
"Uhm! Ina Sarah?
"Ai kuwa Sarah ta daɗe da fita ita ce ma ta bani gadinki da tuntuni na fita kin ga babu daɗi kina bacci mufi ce mu barki ke kaɗai a kwance.
"Nagode Esha! Ni zan wuce gida idan Sarah ta dawo ki ce ta kira ni dan Allah tun da ta fita gantalinta nasan ko na kira ta ba zan same taba, ta kashe wayarta.
"Shi kenan zan faɗa mata ki gaida min da Siyama.
"Za ta ji!
Sadiya ta faɗa a takaice tare da ɗaukar handbag ɗinta, ta fice Esha ta bi ta da kallo tana murmushi sai kuma ta taɓe baki ta maida ganinta kan wayarta, Sadiya tana tafe dizzy yana ɗibar ta adaddafe ta isa wurin da ta yi parking mota da wata irin kasala ta ja motar sai da iso gida abinda ya faru da ita ya fara dawo mata da sauri ta dauki robar ruwan faro dake cikin motar ta wanke fuskarta tare da gogewa da mayafin jikinta dole ta mayar da baƙin gilashinta ta rufe mota ta nufi cikin gida kafin ta tura ƙofar main parlor sai da ta ƙara daidaita natsuwarta musanman da take jin damuwarta ta ragu daga kashi sittin a cikin ɗari. Idan Allah ya taimake ta mai aikinsu kaɗai ta tarar a parlor ita ma tana ƙoƙarin arranging throw pillows ɗin kujerun da yaran Aunty Safeena da ta zo dasu suka wargaza su wanda basu daɗe da tafiya shine Mami tasaka kimtsa parlor ɗin. Kallo ɗaya Sadiya ta yiwa Huwaila mai aiki ta haura upstairs da gudunta tana zuwa ta cire kayan jikinta da suka yi wani kalan uban squeezing ta faɗa bathroom ta yi wanka.
*MASARAUTAR KUDU*
Yau kusan kwana uku da Ciroma ya dawo daga wurin boka mai Gundulelliya, damuwa tana neman tayi masa yawa saboda ya rasa ta wacce hanya zai bi ya ciyar da sarki Mahmoud ruwan da bokan ya bashi gashi zuciyarsa ta kasa haƙuri da muradinsa. Gashi kuma lokaci da sarki Mahmoud ya ɗiba na naɗin sarauta da za a gudanar a masarautar ta kudu sai daɗa karatowa yake yi. Hankalin sa ya ƙara tashi saboda baya so wa'adin da Sarki Mahmood ya ɗiba ya cika ba tare da ya aiwatar da shirin sa ba. Sai kwatsam! Wata shawara ta faɗo masa da ya nemi Galadima duk basa shiri da junansu, domin idan ya ce zai yi wannan tafiyar shi kadai to kuwa ba zai taɓa cimma gaci ba.
Ƙasanwar burinsu ɗaya da Galadima naso sarautar sarkin sabon birnin to kuma da ya sami damar mulkar kudu ga baki ɗayanta sai yaga dacewar ya shigo da Galadima cikin tafiyarsa idan Allah yasa, burinsa ya cika shi kuma zai naɗa shi a matsayin sarkin sabon Birni. Da wannan shawara ya nemi ganawar sirri da Galadima a wani gidan gonarsa duk da ya kwana da sani irin 'yar tsamar dake tsakaninsu. Galadima ƙani ne ga margayi sarki Usman Mustapha na uku shi ne ƙarami a cikin 'ya'yansa bayan rasuwar sarki Usman Galadima yaso a bashi sarautar kudu duba da manyan fada suka yi da ƙananu shekarun sa ba zai iya riƙe babbar karagar mulki irin wannan a bisa duba da cancantar Mahmood da kuma yawan shekaru da Mahmood yafi dasu tare da goyon gogewa akan sha'anin sarauta sai suka bashi wannan sarautar daga baya da Galadima yaga sarautar Kudu ta subuce masa sai ya dawo kan sauratar sabon birnin kudu anan bai yi nasarar samun ta saboda Aliyu, mai martaba sarki Usman ya ba wa ita tun kafin ya bar duniya, a tunaninsa tun da sarki Usman ya rasu manyan fada za su jagoranci a basa sarautar duba da ya girme wa Aliyu nan ma bai yi nasarar ba saboda yadda Ciroma ya hana mishi rawar gaban hantsi. Da farko Galadima bai so amsa kirar nasa ba saboda yana tsoro idan ba wani makirci ne ya haɗa mishi saboda ya kwana da sani makirci irin na Ciroma. Daga baya kuma sai yaga dacewar ya je ɗin dama tsakanin su shege ne yasan makwanci shege, kowanne su mugun kai ne. Bayan Galadima ya iso gidan gonar ta Ciroma sai ya hango shi zaune a cikin wata rumfar hutawa, fuskarsa a murtuƙe ya isa wajensa ko sallama bai masa ba ya shiga faɗin "kai makiri uban makirar mai fuska biyu me kake nema gare ni da za ka aiki amintaccen bawanka da suna kana so ganina?"
Sai da Ciroma ya yi murmushi mai cike da zallan mulki yaƙara lafewa a jikin kujarar da yake zaune akai "Kai fa cikakken musulmi ne Galadima duk ka kasance mai sabawa Allah bai kamata a matsayina na

22 / 80