Kurman Allo Sakamakon Kin Karɓar Gaskiya by EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU

Author :  EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category :  KDP NOVELS

Chapter   37 / 80

108K to 111K   out of 237.2K words

biyo bayanta."Yayanmu dan Allah kayimin rai ka saki AYDAH kamarya Dani gidanka ko kaɗan baka dace da ita ba wallahi."ta faɗa cikin Muryar tausayi kallonta yake yana mamakin halinta da son zuciyarta.tau naji kibani wata daya sadiya zanyi tunani akai,cikin farin ciki Sadiya ke faɗin."dan Allah da gaske kake Yayanmu?"daga mata kai kurum yayi miƙewa tsaye tayi cike da wani irin farin ciki take faɗin."sai da safe yayanmu,kar mami ta nemeni dan Allah karika daukar wayata dan allah.nan ma dai daga mata kai kurum Abba,yayi ta juya tana faɗin."bari ta tafi batareda tayi tunanin neman Aydah ba daman ba ita ta kawota ba.bai samu natsuwar zuciya ba sai da sadiya tabar gidan.acan kasan ransa yana ta tunanin yadda zai shigo da maganar auren Rumaisa a wajen daddy ta yadda bazaiji haushinsa ba maybe idan yayi aure sadiya ta hakura.shiryen-shiryen tafia Legos AB ya shigayi bai sanar da Aidah ba sai ana gobe zai wuce.
Da dare AB da Aydah suna zaune a downstairs parlor shi yana kallon wrestling ita kuma ta dukufa akan rabin ranta (phone) sai da aka gama haska wrestling ɗin ya tattara hankalinsa akan Aydah ya kira sunanta cikin natsuwa "Baby Aydah!
"Na'am!
Ta amsa batareda ta ɗago ta kalle shi ba.
"in-sha-Allahu gobe zan yi tafiya zuwa Lagos zan bi morning flight ba zan wuce one-two days ba. Za ki koma gidan Mami da zama kamin na dawo. Gobe daga school direba zai kai ki can, kafin ki kwanta ki tabbata kin haɗa abubuwan buƙatarki.
Ɓata fuska Aydah ta yi a yanzu sam bata so zuwa dalili kuwa furuncin da Mami ta yi akanta, rau-rau ta yi da idanunta har sun cicciko da ƙwalla ya lura da yanda yanayinta ya sauya nan take ya matsa ya kama hannunta ya haɗe cikin nasa cikin kwatar da murya ya ce "Baby menene ya naga idanunki sun ciko da ƙwalla?"
"Yayanmu ka tafi dani banaso zuwa gidan Mami za ta dinga tsangwama ta.
Iskar ya fesar daga bakinsa kamin ya kara langwasa murya cikin rarrashi da dabara da ake yiwa yara ƙanana marar wayau "Baby ba zai yu na tafi dake ba kinga kina zuwa school ga islamiyya, banaso na katse miki karatu da ba don haka ba ai kema kinsan ƙafana ƙafarki. Yanzu ki yi hakuri ki je tsananin daɗewa ta kwana biyu ina dira Kano zan je na taho dake. Ki list duk abunda kike so zan siya miki kin ji Babyn yaya Abba?"
Duk da wannan daɗin baki da ya yi mata ta amince ne kawai amman ba don tana ji farin ciki tafiya can gidan ba. Tun da ya ambaci tafiyarsa gobe Aydah ta sha jini jikinta ita fil'azal bataso abunda zai nisanta ta da yayanta koda na wuni ɗaya ne. Duk lokacin da tafiya ta kama shi zuwa wani garin da kuka suke rabuwa shi kanshi yasan irin shaƙuwa dake tsakaninsu bata wasa bace. A fakaice yake satar kallonta ta ajiye wayata tana sharar hawaye. A hankali ya shigar da ita jikinsa tasa hannayenta ta zagaye waist ɗinsa ta sunne kanta akan cikinsa duk da yana zaune amman kanta ba zai kai a ƙirjinsa ba saboda tsawon da Allah ya yi masa AB is very long and huge ga Aydah 'yar firitt da ita. Sannu-sannu yake taping bayanta irin yadda ake rarrashin rigimammun yara masu kukan banza "Oh! My Baby stop crying kinsan banaso kukanki ko?"
Ta yi nodding head.
"To goge hawaye insha-Allah har na je na dawo ba abunda Mami za ta yi miki.
Ya ƙarashe magana tare da ɗago haɓarta ya goge mata hawayen kan fuskarta daga ƙarshe ma shi ya haɗa mata ɗan ƙaramin akwatin ta kafin ya kwanta sai da ya tattara inners wears da sleeping dress ɗinta dake cikin laundry basket ya wanke mata saboda yasan halinta ko sanda tana gida da kuka Mami take tsareta kamin ta wanke su, har sai da ya kai da haɗa baki da Huwaila mai aiki duk sanda ta je gyara mata ɗaki ta dinga wanke mata saboda wannan wanki da take yiwa Aydah har salary yake mata a boye. Yanzu kuma da babu Huwaila dole ya wanke mata shi fa har gobe kallon 'yar kankanuwa yarinya yake wa Aydah shiyasa a koda yaushe cikin lallaɓata yake. Bai kwanta ba sai around 12 sai da ya yi waya da Rumaisa kamin bacci ya dauke shi. Duk da bai kwanta da wuri ba hakan bai sa ya yi missing jam'i ba, bayan ya sauke Aydah school ya wuce gidan Mami da akwatin sannan kuma ya yi mata sallama da yake Daddy ya yi tafiya zuwa abuja akwai friend ɗin Daddy dake neman kujerar senate shiyasa yanzu bai cika zama ba.
Siyama kaɗai ya tarar a main parlor da sauri ta taso ta karbi luggage ɗin Aydah a hannunsa ta gaida shi ya amsa da sakakkiyar fuska ya tambayi Mami ta ce tana sama a gurguje ya yiwa Siyama bayani zai yi tafiya ta kula masa da ƙanwarsa "Siyam please take good care of her and don't let her cry or worry kada ki barta ta dinga zama gun da Sadiya take.
Murmushi Siyama ta yi duk da wannan bada amana ba yau ya fara ba don ko Mami da haifi Aydah idan zai yi tafiya sai ya bata amana ta kula mishi da ita kada ta saka ta kuka, kalamansa shi na ƙarshe sune suka haifar mata da sakin murmushi. Ta wuce da akwatin Aydah ɗakinta shi kuma ya wuce ɗakin Mami sai da ya yi knocking Mami ta bashi izinin shiga, sannan ya tura kofa ya shiga tana tsaye a jikin closet ɗinta ya durƙusa ya gaisheta, ta amsa mishi ba yabo ba fallasa cikin sanyi murya ya ce "Mami tafiya ta kamani zuwa Lagos Aydah za ta zauna anan kamin na dawo Dan Allah Mami ki yi hakuri da ita kinsan yarinya ce sai ana hakuri da ita.
Murmushin takaici Mami ta yi kamin ta ce "To ubana daman ka saba ɗora min dokokin akanta ba yau ne ka fara ba kafin ka dawo har baby bottle zan siya na dinga feeding ɗinta madara ko ba ka ce Baby bace?
AB ya sadda kansa ƙasa Mami kuma ta ja guntun tsaki "Dallah tashi ka bace min da gani shashasha kawai ba dai taurin kai ne da kai ba to kuwa a haka za ka kare acikin raino.
AB ya miƙe jiki a sabule ya fice direban gidan ya kira ya faɗa masa idan lokacin tashi Aydah ya yi ya je ya dauko ta har da kyautar 20k ya yi mishi duk dan ya dinga zuwa daukarta on time.
Jirgin da ya dauko passengers daga Kano ya ya yi landing a Murtala Muhammad International airport, koda AB ya fito daga jirgi direban kamfanin Kim's Automobile industry yana jiransa ya dauke shi kaitsaye kamfanin suka nufa kafin AB ya fito daga mota sai da ya kara gyara zaman facemask ɗin da ke kan fuskarsa, shi mutum ne wanda duk sanda zai shiga taron jama'a yana kokarin kare lafiyarsa. A matsayin Anaal na marketing manager ta tattaro dukka bayanai cinikayya na kamfanin tuni conference hall ɗin ya cika kusan duk wanda ke cikin hall ɗin fuskarsa yana dauke da facemask bayan gudanar da tattaunawa tsakanin kamfanonin biyu daga nan yarjejeniyar ta fada kowanne bangare ya yi signing aka yi pictures daga nan taro ya watse sai dai wannan meeting ɗin da aka yi babu Aliyu na Uku saboda jiya ya wuce cotonou wasu daga cikin motocin su suka iso dole kuma ya kasance a wurin. Shiyasa bai samu damar hallatar wannan meeting ɗin ba.
AB yana buɗe murfin mota zai shiga ya tsikayi muryar Anaal na uku tana kiran sunansa, sai ya maida murfin ya rufe ya waiga bayansa cikin tafiyarta mai kama da yanga take tunƙaro sa.






#love story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo




Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only




ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130


KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730


Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336






*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.


*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar


*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu


*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce


*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari


*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan


Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500


VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k


NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[1/2, 9:41 AM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)


NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU


Love Story
#Gwagwarmaya
#Team Tagwaye


049.


Sosai yake mamakin dalilin da zai sa ta tsayar dashi bayan sun riga da sun kammala abunda ya haɗa su sai da ta iso gaf dashi ta ce "Mr Abba ya za ka tafi ne ba ko sallama?"
Batare da ya cire facemask ɗin fuskarsa ba ya amsa mata da cewa "Ina sauri ne zan wuce masaukina.
"A'ah gaskiya bai kamata ka tafi ba because we are responsible for your accommodation and everything you need before you go back to kano wanna alhakin yana kanmu ne.
"No thanks mss Anaal I can take of myself because garin Lagos ba bako bane a wurina already ma na yi booking ɗakin a villa toscana hotel ni zan tafi sai wani lokaci idan Allah ya sake haɗa mu.
Kamin Anaal ta sake magana har ya ɓalle murfin mota ya shiga daman direba yana cikin motar yana jiransa yana shiga sai kawai ya ja motar Anaal ta bi motar da kallo gabanta yana cigaba da faɗuwa tun haɗuwarta dashi a conference hall take ji kwatakwacin irin wannan faɗuwar gaba har kuma yanzu da suka rabu gaban nata bai fasa faduwa ba ta rasa dalili.
Direban yana sauke Ab a villa toscana hotel ya wuce reception ya karɓi key ya wuce ɗakin da ya kama wanka ya fara yi sannan ya hau gado ya kwanta bacci ya sha sosai don sai around 4:30pm ya falka idan Allah ya taimake shi ya yi sallar azhar kamin ya kwata agurguje ya yi wanka ya shirya cikin milk colour ɗin jallabiya mai gajeren hannu ya yi sallah la'asar yana gamawa ya kira reception akawo mishi abinci ya tsakura sama-sama da yake Abba mutum ne da bai cika cin abinci irin sosai ɗinan ba kuma bayaso zama da yunwa. Rumaisa ya kira suka sha firar su ta soyayya har yana faɗa mata gobe zai dawo saboda tun a yau ya kammala abunda ya zo yi bayan sun yi sallama ya fice zuwa harabar hotel ɗin ya ɗan miƙa ƙafafunsa.
A Kano kuma bayan an tashi daga school direba ya je ya dauko Aydah ɗari-ɗari ta shigo main parlor kaman wata baƙuwa Mami da Huwaila kaɗai ta isko a parlor duk sai tasha jinin jikinta cikin murya mai cike da tsoro ta gaishe da Mami a dage Mami ta kalleta ta watsar cikin tsawa ta ce "Riƙe gaisuwarki banaso gida kuma ba zan hana miki zama acikinsa ba saboda gidan ubanki ne amman ina da right da zan hana ki gaida ni. Daga yau daga rana mai kama da yau ba zan sake amsa gaisuwarki ba har sai kin yi abunda nake so. Ba dai kin zaɓi shege marar asali akaina ba to daɗi abun ba ke kadai na haifa ba. Ki je ga ki ga Abba wallahi ba baki nayi maki ba da yardar Allah daga ke har uban naki sai ya sakaku kukan da sai hawayen idanuwanku ya ƙafe.
Aydah ta yi zugun tana kallon Mami can kuma ta kwantar da muryarta ta ce "Mami wai dan Allah me Yayanmu ya yi miki ne kika tsane shi har haka shin meye laifin mu meyasa ita yaya Sadiya ba za ki lurar da ita ta yarda da ƙaddara ta yarda da komai tsari ubangiji ne duk kafiya da nacinta ba zai sa Ubangiji ya sauya abunda ya tsara mata a rayuwarta ba?"
A mugun fusace Mami ta miƙe tsaye ta ɗauke Aydah da mari, ta kuma daka mata tsawa "watau Abba ya fara tattaɓa miki jiki ko Aydah?" Kin fara sani daɗin namiji shine kike min rashin kunya.
Cikin muryar kuka Aydah take faɗin "Mami kema kinsan Yayanmu ba ɗan iska bane balle ya taɓa min jiki kuma ko ya taɓa ai ni matarsa ce addini ya halatta masa ni halak-malak ya yi yadda yake so dani.
"La'illaha illallahu muhammadu Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallam! Hasbunallahu wal-imaal wakil! Zulaiha ke ce ko kuwa wata Zulaiha ce aka musanya min?
Mami ta yi magana cikin ɗimaucewa gaba ɗaya yau Aydah ta shayar da ita zallan mamaki har ga Allah Mami ɓata taɓa tunani yarinta da wautar Aydah zai sa tasan menene aure da manufofin sa ashe kallon kitse da take yiwa rogo ashe tana yi mata kallon biri ne tana mata na ayaba. Cikin kaɗuwa Mami take cigaba da kallon Aydah da baki buɗe.
Aydah a shirye take a yau ɗinan ta kare martabar aurenta da yayanta duk kallon da suke mata na ƙaramar yarinya kar take kallonsu tana bin su ne a haka ba wai dan batasan me aure yake nufi ba. Banda ma su da abin su ta ya za a ce batasan aure ba to da ina amfanin zuwan ta islamiyya da littatafai da ake karantar dasu da suka shafi aure da hakkokinsa.
Cikin kuka ta cigaba da cewa "Wallahi Allah ba zan taɓa yi abunda kike so ba Mami saboda ina son mijina ina so zama dashi ada ina kallon aurenmu ta wata siga ta daban amman a yanzu da na fahimci ba abunda yaya Sadiya take so sama da mijina nima a yanzu ina son abina na kuma shirya fuskantar duk wani kalubale akansa.
Da baya-baya Mami ta koma ta faɗa kan kujera tana dafe saitin da zuciyarta take wani irin bugawa take mata ga kuma tsanani shock da ya lulluɓeta. Aydah ta duƙa ta dauke backpack ɗinta da garin marinta da Mami ta yi ta faɗi daga kafaɗarta daman akan kafaɗarta take, ta haura upstairs da gudu ta shiga ɗakinta ta rufe da key ta faɗa kan gado tasa kuka da taga ji da kukanta ta jefa yantsata a baki ta yi baccin dole.
AB ya nemi gefen swimming pool nesa inda babu mutane ya zauna ya zura ƙafafuwansa acikin ruwan sanyi su ya ratsa jikinsa ya lumsashe manyan idanunsa ya dauki lokaci a haka kamin ya buɗe idanunsa, sai kawai ya tsinci kansa da son kira Aydah yasan zuwa yanzu ta dawo daga school islamiyya ce bai da tabbacin ko ta je tun da daman can sai ya yi artabo da ita kafin ta tafi.
Can cikin bacci Aydah ta ji ringing ɗin wayarta ta zubura ta tashi ta miƙa hannunta kan bedside drawer ta dauko backpack ɗinta ta yi unzipping gefen aljihun jakkar ta ciro wayarta tana ganin sunan yaya Abba ta ja ajiyar zuciya, cikin dushewar murya ta ce "Hello Yayanmu da fatan ka isa lafiya ya hanya?"
Ras! Gabansa ya faɗi sakamakon yadda ya ji muryata ke fita.
"Kuka kika yi ko Baby?"
"A'ah! Kawai dai koda kiranka ya shigo ina bacci.
"Oh! I'm so sorry for interrupted your sleep my baby Allah yasa kada na jawo miki headache.
Ya faɗa with so much caring acikin muryarsa.
"To ai ni taimakona ka yi Yayanmu saboda ban yi sallar la'asar ba ko uniform ban cire ba na yi bacci.
"Aydah sarkin ƙazanta oya tashi ki je ki yi wanka da sallah idan kika gama ki kunna Data za mu yi vid call I really want to see my Baby face.
Dariya ta yi mai ban sha'awa "me too ina so naga fuskar yayana yini guda kurum har nayi kewarsa.
Murmushi ya yi mata mai ɗan sauti wanda sautin ya sauka a kunneta kana ya kashe wayarsa.
Da gudu ta shiga bathroom anan ta cire uniform ɗin jikinta ta jifar ta kunna shower tana wanka take tunano fuskar Mami sai kawai ta kwashe da dariya da sauri ta rufe bakinta da tafin hannunta da tuna tana banɗaki ne. Watau yau Mami za ta yini ta kwana da mamaki ita wai kallon yarinya take min za ta ga yarinta kuwa.
Aydah ta faɗa cikin zuciyarta tana gama wanka ta fito ta tsane jikinta da hand towel ta saka half cotton gown wacce ba ta wuce cinyoyinta daman ire-iren kayanta kenan matuƙar ba fita za ta yi ba, ba za ka taba ganinta da suturar kirki a cewar suna mata nauyi da ta kammala sallah ko addu'a bata yi ba ta cire hijab ta yi flinging dashi ta hau gado tare da kunna Data wayarta, tana gani yaya Abba online ta saki murmushi shi kuma yana can yana chat da rabin ransa Rumaisa kusan sau uku Aydah tana mishi magana bai yi respond ba sai kawai ta kira shi vid call ɗin yana gani kiranta ya katse sai da ya gama hirar sa da Rumaisa suka yi sallama yana tsoron ya yi laifi a wurinta sannan ya kira Aydah zuwa lokacin Aydah har ta yi fushi sai dai fushin nata ba wani tasiri yake yi ba ta yi picking kyakkyawar fuskarsa ta bayyana akan screen ɗin wayarta "Hey my little Baby yau kin ci abinci kuwa?"
Sai da ta cuno baki kamin ta amsa mishi da eh.
"Meyasa ba ki je islamiyya ba?"
"Yayanmu ba na gayamaka bacci nayi ba.
"Owk! Na ji ya naga idanuwanki sun yi luhu-luhu kaman kin yi kuka.
"Ni ban yi kuka ba to me ma zai saka ni kuka?
"Yoo ai ke ƙanƙani abu ma sai ya saka ki kuka duk duniya babu abu mai sauki a wurinki Aydah irin kuka.
"Kai Ya.... innalillahi! Yayanmu menene nake gani a bayanka?"
Yadda ta yi magana a tsorace tana ɗaga murya ya yasa shi kaɗuwa har ya juya babu shiri macce sanye cikin bikini yadda ya kalleta ita ma haka ta yi mishi kur da nata idanunta taga kyakkyawa har wani kara langwashe jiki take yi.
"Yayanmu! Dan Allah ka daina kallonta ita da wacce take tsirara bambancin su kaɗan ne fa.
Ya tsikayi muryar Aydah sai ya dawo da ganinsa akan wayarsa yana murmushi, yayin da Aydah ta bata fuska "amman dai yayanmu wannan matar 'yar iska ce ko?"
Murmushi kawai ya ci-gaba da yi Aydah sai ƙara lekawa cikin waya take yi ta yadda za ta hango ta.
tsanani mamaki ne ya rufeta tasake cewa "yayanmu daga ita fa sai pant da bra wallahi tana kama da 'yan iska ko yayanmu?"
AB ya yi murmushi haɗe da cewa ba kama bace Baby dama can 'yar iska ce.
"To Allah ya isa ban yafe mata ba tun da ta kalla min yayana.
Aydah

37 / 80