Author : EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category : KDP NOVELS
bai dace Aydah taji maganganun da muka tattauna ba. Ya faɗa yana murza goshinsa da tafin hannunsa kukan Aydah yake ji yana hargitsa sa. Cikin sanyin murya ya kira sunanta banza tayi masa maganganun da su kayi da Abdulkarim akanta ba karamin tsaya mata arai sukayi ba. Kenan shima yana cikin jerin mutane da ke mata kushen halitta?'meyasa kowa ke kallonta yar kankanuwar yarinya don kawai bata da manyan boobs da duwawu.
Yasan Aydah ba jin rarrashi take ba.
"Tashi muyi magana baby.!"Ya faɗa cikin sanyin murya mai dauke da rarrashi acikinta.
"ka tafi dan Allah Yayanmu ni bana son magana dakai."
Ta faɗa sounding so very pissed up
kara kiran sunanta yayi haka yasa ta miƙe daga kan gado ta nufi hanyar toilet cikin wata irin rigima yana jin yadda ta wani bugo kofar har cikin kwanyar kansa ya ji hakan. Yafi minti biyar zaune yana kallon ƙofar fitowa daga toilet ɗin, ganin Aydah batada alamar fitowa yasa shi barin dakin.
Har kusan karfe 3 na rana yana a ɗaki tamkar wanda aka yiwa duka har waya yayi da Daddy kuma ya tambayi Aydah ya faɗa masa tana bacci har fargabar haduwa da Aydar yake yi. Car key ya dauka yaje ya siyo masu abinci yana dawowa direct ɗakinta ya nufa da abinci yana tura kofar ɗakin nata suka yi ido biyu daita tana zaune kan abun sallah da alamar sai lokacin tayi sallar azahar ,tura masa baki tayi tana wani kauda kanta gefe bai san lokacin da ya saki murmushi ba tsaye yayi a bakin kofar cikin kwantar da murya ya ce."Salamu Alaikum yar budurwa kinyi min izini na shigo ashe kin girma ban sani ba."wani irin kuka ta fashe dashi ta tsani wannan kalmar ta budurwa da yaya Abba ke kiranta dashi, taga abun nasa yayi yawa, ware ido yayi yana kallon yadda ta saka kanta cikin kafafunta tana yimasa kukan tabara ƙarasawa yayi wajenta ya aje ledar takeway ɗin kan bed side drawer. Zama yayi agabanta ya tankwashe kafafunsa.Aydaah!!"ya kira sunanta da wani irin tone da yasa ta daga ido ta kallesa hawayen idanunta suka kasa tsayawa.
"Ɗazun me kika gama faɗa an raina maki halitta kuma bakyason kalmar budurwa yaya kikeso nayi baby.?"ta turo baki tana faɗin."Ni banda manyan kaya right sai itace keda manyan abubuwa nima shekaruna zasu kai yayanmu ba sai kunyi min gori ba.
Ta karasa maganar a fusace da kuma muryar kuka kokarin miƙewa take tsaye hannu ɗaya yasa ya fisgota
Ta zube akan jikinsa kifa kanta tayi acikin jikinsa ta cigaba da rera kukanta a hankali shiru yayi yana sauraren kukan nata yadda yake hargitsa masa zuciya ko kaɗan baya kaunar kukan Aydah kuma yasan ba wai jin rarrashi take ba sai an taki sa'a. Tunani yake me zai mata ta manta da maganganun da suka tattauna da Abdulkarim,yayi da yasanin tattaunawar nan da Abdulkarim bai taɓa kawowa ransa zata ji ba da basu fara taba."my better half.!"Ya faɗa daidai kunnenta make masa kafada tayi tana kara tura kanta cikin jikinsa
"Me zanyi maki wanda zaisa ki huce dan Allah?" Mu fa bada wata manufa muka faɗa ba ana maganar aurena da Rumaisa ne kurum keda za kiyi karatu meye hadinki da wannan auren huun."Ya faɗa yana saka hannunsa yana tallabo fuskarta duka yana kallon cikin kyawawan idanunta da suka rine saboda kuka. Ta turo baki tana jan majina take faɗin."ai ko za ka faɗa bai kamata ka faɗa gaban abokinka ba yayanmu."kuma ai na san kai yayana ne babu aure a tsakaninmu idan kana faɗar ban cika macce ba batamin rai kake."to na daina daga yau kin haƙura?"make kafada tayi yayi rolling ɗin eyes ɗinsa yana faɗin."to faɗamin me zan maki ki hakura?"abu biyu.!"ya daga kai kafin yace "ohhhh really??"dage girarta tayi duka biyu ɗin. "Tau ina jinki."gabanta na faɗuwa take kallonsa bata san taya zai karbi zancenta ba ,duka tana bukatar abu biyu ɗin da zata faɗa yanzu, tasan kuma da wuya yaya Abban ya amince zai ma iya daukar ɗayan yayi mata to ɗayan fa?"tana bukatar waya da gaske friends ɗinta suna da waya wanda suke group ɗaya banda ita.
Kuma tasan matsalar rashin wayarta
duk daga wurin yaya Abba ne, daga Mami har dayddy basu da matsala.
Jin tayi shiru yace "baki shirya magana ba yunwa nake ji dauko mana plate muci anan, "Yayanmu dan Allah ka kaini gida anjima da dare sai mu dawo dan Allah.
Yadda tayi narai-narai da ido yasa yaja numfashi yana kallonta yake faɗin."naji ɗaya bayan la'asar zamu je faɗi daya,wannan karon hannunsa ta kamo ta rike cikin nata hannun tana kallon cikin idonsa, cikin rawar murya ta ce."Dan Allah Yayanmu za kayi min ɗayan?" Ka fara yimin Alkawari yayanmu."ki faɗa baby.!"
"Yayanmu dan Allah ka siyamun waya duka Friends ɗina suna waya.
Ta karasa maganar tamkar zata fashe masa da kuka girarsa ya tattare wuri ɗaya yana kallonta kamin ya ce "Tashi ki dauko plate da spoon muci abinci."ganin babu wata walwala acikin fuskarsa yasa ta miƙe tsaye ta fice daga ɗakin cikin sanyin jiki. Har suka gama cin abinci bata ga walwalar yaya Abba ba.Ya kalli ɗakin da alamar yau bai ga shara ba, "ki gyara ɗakin nan tas kiyi wanka idan munyi sallar la'asar zamu fita. Da haka ya fice daga ɗakin,cikin ƙunci ta share ɗakin tamkar zata yi kuka ganin yadda bayanta ya riƙe sai huɗu da rabi ya shigo ɗakin nata zaune take gefen bed da riga da skirt na Atamfa ajikinta kalar purple da baki kayan sun zauna daidai jikinta ga mayafinta nan aje agefe da ƙaramar handbag ɗinta ɗakin ya shiga karewa kallo sai da yayi masa yadda yakeso ya kalleta yace ta taso su tafi. Haka tabi bayansa tana yafa ɗan ƙaramin veil ɗinta da duka bayanta a waje bai damu da yanayin shigarta ba dan yasan yarinya ce...ko a mota zaman shiru suka yi sai dai ganin inda ya nufa da motar yasa ta kallesa da sauri ko kallonta baiyyi ba ya cigaba da tukinsa a natse. Manyan wayoyi ne aka zube agabanta ya harɗe hannunsa a ƙirjinsa yana kallon fuskarta yadda farin cikinta ya bayyana nan take.
"Ki dauki wacce kikeso baby mubar wajen nan.!"hannu tasa tana daukar manyan wayoyin tana jujjuyasu a hannunta idonta ya kai kan latest iPhone ta dauka ganin yadda ta riketa yace ita kikeso?'"daga masa kai tayi da sauri tana tsaye ya bada card ɗinsa aka cire kudin,wani irin farin ciki ta tsinci kanta acikin tun cikin parking lot ta kasa daurewa ta rungumesa tare da peck ɗin kumatunsa "Allah ya biyaka da aljanna yayanmu.
Ganin yadda ta rikesa ta zagaye hannunta a bayansa ya ɗan sunkuya tana faɗin."baby.!"da sauri ta sakesa ta karasa bangaren driver ta buɗe masa tana kallonsa still wearing a loverly smile shimfide akan fuskarta, shiga motar yayi ta mayar da kofar ta rufe zagayawa tayi frontseat ta buɗe ta shiga ta mayar da kofar ta rufe,kai tsaye office ɗin MTN suka nufa aka siya mata layi akayi mata register,tana ganin sun dauki hanyar zuwa gidansu bata san lokacin da ta riƙe masa hannu ba tana sakin yar dariya take faɗin."thank you yayanmu.
Ai yana gama parking cikin parking lot ta balle marfin motar ta ruga da gudu zuwa cikin gidan tun kafin ta shiga cikin parlor take kwalawa su Siyama kira hardasu Mami, Sadiya da Mami ne zaune a parlor Sadiya tana zaune gefen Mami, yayin da plate a hannun Mami tana feeding ɗin Sadiya basu dade da dawowa hospital ba jiya cikin dare suka kwasheta sai yanxu aka sallamota, da sauri Aydah ta zagaya ta bayan kujera ta sakala hannunta cikin wuyan Mami."I miss you Mami i really miss you.!"wata uwar tsawa Mami tayi mata tana faɗin.''kasheni za kiyi da ne kin wani riƙe min wuya dallah cikani.
Sauri Aydah ta saketa tana ɗan turo baki zata yi magana AB ya shigo da sallama cikin takunsa na izza da kasaita tuni parlorn ya game da kamshin turarensa, tunda ya bayyana cikin parlor Sadiya ta kafesa da idanunta wani irin bugawa zuciyarta take da sauri da sauri tamkar zata fito daga ƙirjinta samun kanta tayi da miƙewa tsaye cikin bin Umarnin zuciya da gangar jikinta ta nufesa daga Mami har Aydah kallonta suke shima tsayawa yayi cak!"yana kallonta yadda tayi wani irin rama na ban mamaki tana karasowa gafda shi ta haɗe filin da yayi saura a tsakaninsu rungumesa tayi sosai tana zagaye hannayenta a bayansa,wani irin kuka mai rauni gamida wani irin ciwo Sadiya ta fashe dashi. Jin yayi zuciyarsa ta karye lokaci ɗaya sai kokarin rabata yake da jikinsa cikin wani irin raunin murya ya kira sunanta "Sadiya!" Yana kokarin cireta daga jikinsa"Yayanmu Please karka rabani da gangar jikinka dan Allah wallahi zan iya mutuwa.
Ta faɗa tana rikesa sosai tamkar wacce za'a yiwa kwacensa, cikin wani irin murya taji Mami ta kira sunanta."ta rasa sadiya wace irin manya ce !"wannan masifa har ina tamkar babu zuciya a kirjinta. Dakyar AB ya raba Sadiya da jikinsa yana jin kukanta na tabasa tamkar zata shede riƙe hannunta ya yi ya karasa daita cikin parlor ya zaunar daita ɗaya daga cikin kujerun dake zagaye da parlor."meyasa bazaki yarda da ƙaddara ba Sadiya?. Babu abunda ya canja matsayinku a zuciyata ina jinku tamkar wa'yanda muka fito ciki ɗaya daku. Ita Aydah bata tsaya sauraren dramar tasu ba ta nufi up stairs wurin Siyama dan gwada mata wayarta.
AB ya kalli saitin da Mami take tana riƙe da plate ɗin shinkafar da take baiwa Sadiya cikin wani irin sanyin murya ya gaisheta ta dauke kanta akansa ta kalli Sadiya kamar zata shege jikinsa."za ki taso ki karasa cin abincin ko sai kin gama nacewa mutumin da bai san darajar ki ba mutumin da bai san halacci ba, runtse ido yayi yana jin kalaman Mami na ratsasa suna samun wurin zama a zuciyarsa tare da illata ruhinsa, miƙewa tsaye yayi ya fice daga Parlor da wani irin kallon tsana Mami ta bisa da tana da iko da ta kashe Abba Bashir da hannayenta ta tsani duk wani abu da ya shafesa tana ganin yadda Sadiya ke famar goge hawayen da suka kasa tsaya mata har lokacin ba zata iya haƙura da soyayyar yayan nata ba ba zata iya rasasa ba ya kamata tayi wani abu akai dan zuciyarta na gafda bugawa.
Siyama na rike da wayar Aydah a hannunta take faɗin."lallai yayanmu yana ji dake baby sis?"kin san nawa wannan wayar take kuwa? Tafi tawa fa tsada fa. Aydah jin tayi kanta ya ƙara girma bata san lokacin da ta juyawa siyama ido ba. Siyama ta haɗa wayar ta saka mata caji anan ɗakinta zamanta ta gyara akan gadon Siyama ta kalli Siyama dake rike da wani text book tana dubawa ta daga kai ta kalli Aydah ganin ta bata rai lokaci ɗaya,
"Ban san me nayiwa Mami ba kwanan nan tabi ta tsaneni nida yayanmu.
Ta faɗa da wani irin sauti mai karya zuciya anan ta baiwa Siyama labarin yadda Mami tayi mata, murmushin gefen baki kurum Siyama tayi mata
ita kanta mamin fushi take daita tun ranar da aka daura auren Abban da Aydah bata kara samun farin ciki ba
Komai tayi Mami tayi ta hantararta tana mata tsawa tana ce mata munafuka sai kace ita ta daura auren Abba da Aydah."Yanzu kije ki bata haƙuri maybe kinyi mata laifi.
"To kuma idan naje tayi min tsawa fa ko ta korani?"
"Ai bazata yi ba tunda haƙuri za ki bata.
Da haka Aydah tabi shawarar Siyama da ido Siyama ɗin tabita har ta fice daga dakin na Siyama. Acan ƙasan ran Siyama tausayin little sis ɗinta ne manne a zuciyarta babu kowa a parlor juyawa tayi ta koma sama ɗakin Sadiya ta buɗe a hankali ta ɗan tura kanta suka yi ido biyu da Sadiyar da take bin ta da wani mugun kallo a bakin kofa ta tsaya tana ƙarewa Sadiyar kallo sai yanzu ta lura da yar ramar da tayi wacce kana gani har cikin idanunta.
"Yaya Sadiya bakida lafiya ne?"
"Ubanwa ya faɗa maki bani da lafiya ki wuce ki barmin ƙofar ɗaki ko na taso nayi kuli-kulin kubra dake.
Ɗan turo baki tayi ta juya tabar kofar ɗakin na Sadiya dake masifa tana jin da kusa ga Aydah take da ta kwada mata mari tana kin yadda Sadiyar ke kwala mata kira akan tazo ta rufe mata kofa da gudu Aydah ta ƙarasa ƙofar ɗakin Mami."
#love story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo.
Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[12/31/2023, 10:25 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)
NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU
*AREWABOOK*: Jiddah 3256
Love Story
#Gwagwarmaya
#Team Tagwaye
047.
Ta tura ƙofar ɗakin Mami cikin sanɗa ta ƙarasa kaman munafuka cikin yanayi na tsoro ta yi sallama Mami wacce fitowar ta daga bathroom kenan ta gallawa Aydah uwar harara tana faɗin "Me kika zo yi min a ɗaki?"
"Mami zuwa nayi na ganki Allah Mami na yi kewarki.
"Mtss! Ai ni Aydah kin gwada min da wuya ake yanka, tun da har kika zaɓi bijere min ki duba hali da 'yar uwarki take ciki duk akan wannan gantalalle yaro amman kika iya amincewa da aurensa Sadiya ta mutu ko tayi rai ke kan ba abunda ya shafe ki, sai walwala da farin ciki kike yi. Ke ko kunya bakya ji kin aure mijin'yar uwarki.
Hawaye ne suka fara bin kumatun Aydah Mami tana gani ta fara dulmiyar da tunani Aydah sai ta matsa kusa da ita ta kama haɓarta ta ɗago da fuskarta ta jefa idanunta cikin na Aydah, cike da wayau ta cigaba da faɗin.
"Aydah ki tuna Abba shine wanda ya raine ki haifar ki ne kawai bai yi ba, amman duk wani abu na halittar jikinki ba wanda bai sani ba to taya ma kike tunani wanda ya gama sani cikin da waje na halittarki zai iya zama dake a matsayin matarsa. No matter how Abba ba zai taɓa iya kallonki a matsayin matarsa ba gara ki yiwa Daddynku bori ya raba aure nan Abba ya sami damar mayar da Sadiya.
Girgiza kai Aydah ta shiga yi hawaye suna taruwa akan kuncinta "Mami ki yi haƙuri ba zan iya bijirewa Daddy ba saboda ya yarda dani kuma yana da tabbacin zan masa biyayya bayan duk wannan yadda da ya yi min sai na watsa masa ƙasa a ido wallahi Mami ba zan iya ba. Kawai dai zan miki alƙawa....
"Ya isa na ce ya isa Aydah tunda har ban isa dake ba ban isa na saki ko na hana ki ba, kama hanya ki tafi karki sake zuwa inda nake daga yau babu ni babu ke wuce ki barmin ɗakina shashasha kawai.
"Mami Please!!
"Fita ko na rufe ki da ɗan banza duka useless girl.
Mami da ta fahimci Aydah za ta cigaba da yi mata magiya sai kawai ta kama damtse hannunta ta tura ta waje ta rufe ƙofarta, Aydah ta faɗi zaune a take ta fashe da matsanancin kuka cikin sauti mai ƙarfi, sautin kukanta ne yasa Siyama fitowa da sauri yayin da Sadiya tana jin kukan Aydah ta saki murmushi zuciyarta, ta cika da farin ciki tasan kukan nata yana da alaka da Mami ta cije lower lips ɗinta tana kisima irin abubuwa da za ta yiwa Aydah har sai ta bar gidan Abba bada shiri ba.
"Subhanalillah! Aydah menene me kike yiwa kuka?"
"Yaya Siyam!
Sai kuma ta kasa cigaba da magana ta rushe da kuka.
"Talk to me lil sis ko faɗuwa kika yi ne?"
Aydah ta girgiza kanta cikin harɗewa harshe ta ce "Mami ce Yaya Siyam.
"Ikon Allah! Aydah dan Mami ta kore ki daga ɗakinta ai bai kamata ki dinga wannan taratsin kukan ba. Sai a zaci wani mummunan abu tai miki.
"Yaya Siyam ba korana kaɗai ta yi ba cewa ta yi babu ni babu ita kar na sake zuwa inda take. Yaya Siyam miye laifina anan ba ni nace Daddy ya aura min Yayanmu ba radinsa kansa ya aura mana junanmu kuma dukkan mu ba za mu iya bijirewa masa ba. Duk da dukkan mu ba son junanmu muke yi ba.
Numfashi Siyama ta sauke ta ɗaga Aydah ta miƙe tsaye ta kama hannunta suka nufi ɗakinta ta zaunar da ita gefen gado kana ta zauna kusa da ita cikin taushin murya take faɗin "Duk yadda nake so na fahimtar dake Aydah ba za ki taɓa ganewa ba kawai dai zan ce dake duk abunda Mami za ta ce ko ta sakaki ki amsa mata kurum amman kada ki yi ko ɗaya kawai so nake ki daina musu ko gardama da ita.
"Yaya Siyam....
"Please Aydah don't say anything ki yi abunda nace kin ji lil sis bana ji daɗi yadda Mami ke treating ɗinki.
Aydah ta share hawayenta da suka kasa tsayawa ta tashi ta fice da sauri Siyama ta ciro mata wayarta daga charging ta maida charger ɗin acikin box ɗin wayar, ta bi bayanta AB yana zaune a mota yana waya da Rumaisa Aydah ta buɗe front seat ta zauna tana sharar hawaye da bayan hannunta, batareda da ya kashe wayar ba ya maida hankalinsa kanta yana firfito da idanunsa "Ke da wa me aka yi miki kike kuka?"
Aydah bata yi magana ba sai kawai ta kifa kanta a dashboard tana shasshekar kukanta wanda har da shagwaɓa acikinsa, ga baki ɗaya AB ya ruɗe ya manta da waya yake yi ya ajiye wayar batare da ya sami damar disconnected ɗin kiran, ya ɗago fuskar Aydah tuni fuskarta, ta ta caɓe da hawaye da majina "Ya subhanalillah! Please Baby, stop crying, I don't want to see tears coming out of your eyes kukanki yana saurin ɗaga min hankali wallahi.
Zuwan Siyama ne yasa ya maida tambayarsa zuwa kanta cikin sanyi murya ta faɗa masa ita da Mami ne bai ce komai ba ya karɓi wayarta da Siyama take miƙa mata.
"Ki shiga gida Siyama mu za mu wuce daman ta matsa ne na kawo ta sai dare na dawo na dauke ta amman tun abun ya zama haka gara